Showing 321001 words to 324000 words out of 391264 words

Chapter 108 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2622

Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan"

Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....."

kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..."

Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor.

fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka kaWa jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravinS'

Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane, kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..."

_________________________________
'?


*Chief Owais=?%?

Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su.

Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana Waya daga cikin Elders na gidan kurkukun ?addara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba.

Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya naWe kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha ..

Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin.

"Owais ne"

"Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi.

baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha.

yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit...

"Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu.

A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa.

"Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji dadin maganarshi.


Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa.

Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya le?o mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan"

"Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni"

Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata"

dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi.

"Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport, wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani"

dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi.

Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu
Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ?ara dankon zumunci atsakaninmu da shi"

kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen
Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma ya?iya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.."


"Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki"

"Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa"


"Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace.

Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba" Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne"

gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa..

"Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi..
Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye"

Shiru ya Wanyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina"

da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba.

"Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa"

Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi.


Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa"

"Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi

Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince"

fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai

"Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you"


"Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba,"

"Ina fata kaji alfarmar da Wan naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan.

Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi..

Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi.

"Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice.

kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..."

waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"?



Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka"

harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya sha?e wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa.


Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"!

Hankalin Sharafudeen ba karamin tashi yayi ba, He couldn't believe that wai owais ne ke yi masa magana kamar zai doke sa? Babu tausasa harshe? Anya bai fara shaye shaye ba? Ko dai har yanzu ?wayar maganin bancin daya bashi ce ke aiki ajikin shiW'S'



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?=?%?=?%?
'?*



*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: =?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???

~<><><><><><><><><><><><><><><><>
'?~

~______________________________________~



Cikin sanyin murya ya furta"Owais, bayan dana hana ka zuwa kai farmakin sai da kaje ko? Ka daina jin magana ta Owais! " ya faWa idanunsa akan ciwon goshinsa daya Wan le?o batare da saninsa ba.

"Lafiyata bata shafeka ba! Kuma Daga Rana Irin ta yau babu ni babu kai! Ni ba dan ka bane, kakane shine mahaifina mutumin kirki ba irinka ba, Kuma na rantse ka jira ka gani..."

yana ?arasa maganar Ya jefar da hannun sa daya ru?e, Ya juya azafafe Yabar Part din Ko sallama bai je yayi ma baba Obie ba.

Ya tafi Yabar Sharafudeen cikin rudani, bai taba zaton owais zaiyi masa haka ba, Kai ko a mafarki, Ji yayi bazai Iya jurewa ba, Cikin sauri Yabi bayanshi Yana fitowa Ya hango Motar Owais dake fita, da sauri ya nufi Security Details dinsa tunkafin ya karaso suka bude mashi cardoor din motarsa Ya shiga ciki, ya basu Umarnin su kai shi Gidan owais.

Chief yana zaune seat din baya na motar, ya rufe gefen fuskarsa da hanky, Idanunsa sun kaWa jawur, bai ta6a karaya da rayuwar duniya ba irin wannan karan yayi fatan ace ba'a halitto shi acikin ta ba, wai mahaifinsa matsafi ne! fasiki mai shan jini da cin naman mutun, Ya Ilahi!

"Sir, motocin mahaifinka suna abiye da bayan mu" SA din dake driving dinsa ne yayi maganar, aransa ya furta wato mutumin nan saida ya biyo ni!

Motarsu na shiga main gate na villa dinsa Ya ba Security officers Umarnin karsu kuskura su bar kowa ya shigo gidan.

Bayan ya fito daga Motar, Cikin sauri Ya Part dinsa Yana kokarin Haura wa kan stairs Unexpectedly muryar Shi ta katse hanzarinsa"Owais? Lalacewar taka har takaiga ni kake bada Umarnin a hana shugowa gidan ka"?

Dafe kanshi yayi da hannu Waya wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin shi Ya tsani jin koda muryarsa.

a cikin kunnansa yake jiyo takun tafiyar shi bai motsa ba har ya karaso ya zagayo ta gaban shi suka fuskanci juna.

Gabansa ya dan fadi ganin hawaye na sintiri kan kuncin mahaifinsa.

Cikin raunanniyar murya yace"owais, Dan Allah ka fadamin Laifin me namaka? Wlh Hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har baka fadamin ba..." Zuciyarshi taso ta karaya, amma In ya tuna wanene Mahaifinsa nasa sai yaji kamar ana kara rura wutar ?iyayyarsa a zuciyarshi.

Bai ko kula shi ba, Ya nemi ra6awa ta gefen shi zai wuce, cikin sauri Sharafudeen Ya dam?i Arm dinsa.

Cikin karyayyar murya yace"Owais, in har ba so kake zuciyata ta buga in mutu ba, ka fadamin laifin me nayi maka da yaja har kake zargina! wai ni owais, mahaifinka"!

Kallo mai cike da tsana Chief Ya watsa mashi kafin yace"kafi kowa sanin laifin da ka aikata min, zaifi ka fita sabgata, don bazan taba fahimtarka ba, kawai ka jira lokacin da zan fallasa asirinka a bainar jama'a.."

ya faWa tare da bangaje hannun sharafudeen Ya kara gaba Ya shige part dinsa Yayi locking room door dinsa rai a6ace.


A bangaren Mai girma sharafudeen Kasa motsawa yayi, al'ajabi da bakin Cikin maganganun da Owais ya gaggaya masa sun ru?e zuciyarshi tamau sun hana kafafunsa motsawa, Ya rasa ya zaiyi bai ta6a sanin Owais yana da kafiya da taurin kai ba Sai yau da Allah ya nuna masa, tunani ya soma yi waya kamata Ya kira ya fada masa halin da yake a ciki!.

Tsadaddar Wayarsa Ya zaro Ya daga aljihu ya shiga call logs Ya danna ma Number din da yayi saving da jini Waya kira, Tana fara ringin yayi picking..

A mutunce suka gaisa da junansu kafin Yace"pls ko zaka kira Owais, kuyi magana, akwai wani abu da ke damunsa ya?i fadamin may be kai ya sanar dakai" tun daga yanayin muryarsa prime minister Hateem Ya fahimci dan uwan nasa yana acikin damuwa.

Othe other hand prime minister yace"Okay, Don't worry, I'll call him Just calm down and take care of yourself for me"

"Okay, Nagode kaima ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama ya juya ya tafi zuciyarsa a hautsine..


*ANEELERH*


Ta fi karfin rabin awa tana safa da marwa a tsakar dakin ta, tana ta tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin, tun da ta saurari maganganun Ana gabanta keta faduwa, Hankalinta ya?i kwanciya, damuwarta Ina Ana? Tana raye ko ya kashe ta? batajin zata Iya hakura taja baki tayi shiru batare da tayi gaggawar daukar mataki ba ko dan ta kwatarwa Ana hakkinta, ta kuma ku6utar da family dinta, zuciyarta ce ta dinga azalzalarta da tunzurata akan taje ta tunkare shi kaitsaye ta fada masa ta san komai sannan tayi masa barazana in har bai fada mata ina take ba zata tona masa a asiri uban kowa yasan me ya ke aikatawa sannan ta kaishi kara gurin hukuma.

Kwakkwaran Numfashi taja, fuskarta babu annuri ta fito daga dakin bata iske kowa a falo ba, Mami da ummi suna a kitchen suna aikin lunch.


Bata nufi ko'ina ba sai Wakin Uncle dan Iya, da kwarin gwiwa take tafiya yayin da bugun zuciyarta ke ?aruwa Ga tsoro tanaji amma ahaka ta dage ta durfafi dakin nasa har takusa kutsa kai Cikin Wakin taji kamar an ruke kafafunta dakatawa tayi da yin tafiyar, nan take brain dinta ta fara tariyo mata maganar Ana.

_watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda yace bazai kyaleni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kunga ni kadaice agidan, yanzun nan naga shigowar shi shiyasa na gudo daki don in samu damar yi maku video, dan Allah don sonku da manzon Allah saw Aduk lokacin da kuka kalli videon nan kuyi gaggawar kaishi ?ara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login