Showing 21001 words to 24000 words out of 391264 words

Chapter 8 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2551

da addu'a Allah ya bashi lafiya...



Lumshe ido chief owais yai, bakomai yake tariyowa ba face ranar da suka fara tozali da juna shi da danish suna a saman bene, suka jefa ma junansu kallon kallon, aranshi ya ayyana ba lallaima idan yaron ya dawo hayyacinsa ya kula prime minister ba saboda Yana da ilmin sanin halayyar Wan adam, da ido kawai ya kalli danish ya fuskanci yana da wuyar sha'ani, yin mu'amala da shi ba abu ne mai sau?i ba.



"In sha Allah zan tayaka da addu'a, ni dai fatana ka daina sanya damuwa aranka, ka kwanta ka yi bacci, muna da liyafa a gobe"



Yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar prime minister ta cikin wayarshi.



"Nagode da kulawarka agareni my son, Allah yayi maka albarka" amsa mashi yayi da ameen

Har zaiyi rejecting kiran muryarsa ta sake katse shi

"Pls kada ka koma bacci, ka tashi ka shiga toilet ka dauro alwala, kayi mashi nafila ko da raka'a biyu ce, Allah ya bashi lafiya"



Babu musu yace"In sha Allah zanyi" bayan sunyi sallama, chief owais yayi shiru yana tariyo kalaman Daddy hateem, shi kanshi yafara hasashen tabbas akwai wani 6oyayyan sirri dake a tattare da kaunar da uncle dinsa ke yima yaron Allah kadai yasan ko menene.



Jefar da wayar yayi saman gadon, kafin ya mi?e ya zura ?afafuwansa ?asa inda ya ajiye gucci slippers din sa, yun?urawa yayi ya mi?e ya nufi switch din dakin ya kunna a hankali haske ya gauraye ko'ina, wato wani hamsha?in bedroom ne, komai na cikinsa launin royal blue and white colour ne.



A gaban dressing mirror ya tsaya tare da Waura hannun shi Waya ya dafa mirror chair.



Wasu hadaddun Cashmere pajama ne a jikinsa riga da wando masu tafshi launin sky blue, sumar kanshi tasha gyara sai daukar ido take yi ga wani kamshi dake fita daga cikin ta, chief karshe ne a fagen haWuwa.



Moving slowly ya nufi ?ofar toilet dinsa ya shiga daga ciki, alwala ya Wauro ya fito fuskarsa da lemar ruwa ya nufi walk-in closet dinsa jim kadan ya fito sanye da jallabiya, ya hau kan darduma ya dai daita nutsuwarsa da kyakkyawar niya ya kabbara sallah.



A kalla yayi kusan raka'a goma sha takwas batare da gajiyawa ba, har sai da yaji kafafuwanshi sun soma rurru?ewa tukunna ya dakata, ya zauna yana jero addu'o'i duk dai akan danish yayi su kamar yarda Uncle hateem ya nemi alfarmar yayi mashi.



Bayan ya kammala komawa yayi saman bed nasa ya kwanta, tare da kai hannu ya Wauki wayar shi, jim yayi yana mai mamakin ganin sakonta, a kalla sunfi wata biyar ko sallama basa yi ma juna, shiga cikin message din yayi, tare da karanta sakon da ya gani, ko kusa bai ji su a zuciyar shi ba, saboda kokwanton da yake yi, video din Ya kunna ya fara kallo, yana faman lumshe idanun shi, tayi mashi kyau yaji dadin kallon video din, almost 3 times yana maimaita kallon shi, kafin daga bisani ya fita daga chat din ya daura idanunshi kan hoton wallpaper din sa.



A tsanake yake kallon baby face dinta, ta zare idanunta a hoton daga ganin hoton screenshot din shi aka dauka, kuma anyi hoton ne batare da sanin ta ba.



Sam baya gajiya da kallon hoton, A hankali ya Waura soft pink lips dinsa saitin fuskar ya sumbace ta, kafin ya Waura hoton saman kirjinsa a haka bacci yai awon gaba da shi.



________________________
'?



Ta?i runtsawa ta addabi kowa ta hana su bacci saboda Jazz baizo ba, tace in har baizo ba to bazatayi bacci ba suma kuma bazasu yi ba, dakyar Salsabeel Ya shawo kanta Ya samu ya lalla6ata har ta ?yale sauran ?an uwanta suka kwanta a dakunansu, itama takwanta harfa ya kwanta da niyar ya runtsa can tsakar dare yajiyo bugun ?ofa, a firgice ya farka Yaje ya buWe, Khadeeja ya gani tsaye ta ru?e qugu tana faman kumbura mashi fuska tace Ina jazz din yazo? Agogo ya kalla sam yama kasa buWe baki ya bata amsa, tace dama nasan baizo ba, ya manta dani, wlh Allah nima nayi fushi da shi.



Cikin kwantar da murya salsabeel yace"dan Allah kiyi hakuri kije ki kwanta bacci, dare ne yanzu, gobe in Allah yakaimu da safe zan kira maki jazz"

Ma?e mashi kafaWa tayi alamar bazata kwanta ba, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi Waure mata fuska ya daka mata tsawa tare da fadin"Zaki wuce kije ki kwanta ko saina yi ?wallo dake" fashe wa tayi da kuka da gudu ta nufi falo ta zauna saman sofa tana kuka, ko tsoro bata ji ita kadai kamar aljanna" ko ta kanta baibi Yaja kofa Ya rufe Ya koma ya kwanta.



Sai da tayi kukan mai isarta, kafin Ta mi?e tana shafa ciki Alamar yunwa take ji, kaitsaye ta nufi Kitchen ta shiga ta soma kiciniyar kunna gas, tsabar rigima.



Mutsu mutsu tajiyo a kunnanta, hakan yasa ta dakata ta juya tana ?an waige waige don ganin menene, Karaf idanunta suka sauka akan ?atoton 6eran dake tafiya saWaf saWaf Yana tunkarota ba?i wulik da shi, sam bata ji tsoron shi ba, Abun ka game ta6in hankali, Praying Fan ta Wauko cikin sanWa tabi bayan shi ta daddage ta kwaWe shi da fan Win, ko shurawa baiyi ba ya she?a, Bindin shi ta ru?o tana faman sakin nishi tace"Zaka ci ubanka, Kai ne 6arawon dake cinye mana sauran da muka rage a kitchen ko"? Ta faWa tana le?en idanun 6eran Yayi zuzuru dashi.



"Ba zaka yi magana ba? Baka da gaskiya bakin munafuki, kai ne kake gwigwiyar mana bready, Bari na kai ka Gaban Al?ali Ya salsabeel Ya kashe min kai har lahira"



Ta faWa tare da fitowa da gudu ta nufi bedroom din salsabeel, Har Ya koma bacci, Yajiyo muryar khadeeja tana fadin"Ya salsabeel Ka buWe min kofa na kama 6arawon dake cinye mana sauran abincin mu, gashi nan a hannuna, Ya salsabeel ka buWe zai gudu'



Afirgice Ya farka har yana tuntube garin sauri, koda Ya buWe ?ofar Mi?a mashi 6eran tayi

"Gashi ka kashe shi ko ka cire mashi hannayensa"

Fuskarshi a yamutse ya kalli 6eran da idanunsa masu dauke da bacci, sun kaWa jawur da su, yayi mamakin da har ta iya kamo 6era, tun da suka fara zama gidan bai ta6a ganin gifcin 6era ba sai yau.



Muryarshi adisashe yace"khadeeja ba zaki barni inyi bacci ba? Ke baki runtsa ba nima kuma kin hana in runtsa, Meke damun ki ne"?

Ta6e mashi lips dinta tayi alamar zata fashe mashi da kuka

Da sauri yace"ya isa ni bance kimin kuka ba, Yanzu fada min ya kikeso ayi da 6eran nan da kika kama"

"Ka cire mashi hannuwa" gyada kai yayi tare da sanya hannu ya kar6i 6eran"ki jira ni yanzu zan dawo amsa mashi tayi da toh, fita yai daga dakin tana atsaye tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannunsa babu 6eran

"Yana ina"?

"Na cire mashi hannuwa na yar" murmushi tasaki"mun hutu da masifa ko"? ?aga mata gira yai alamar eh

"Muje na rakaki daki kiyi bacci" ma?e mashi kafada tayi"Ni yunwa nake ji, kaje kitchen ka dafa min abinci"

Wahalallan kallo yabita dashi gaba Waya ta takurasa

"Shikenan muje" Ya fada tare da yin gaba tabi bayan shi suka shiga falo, ta zauna saman sofa.

Kitchen Ya shiga bawan Allah ga gajiyar bacci A haka Ya dafa mata indomie, Ya haWo mata da water bottle, Ya shigo Da plate din Ya mi?a mata, gefen ta ya zauna don yasan koya koma daki indai batayi bacci ba to shima bazai runtsa ba.

Yana kallonta Har ta cinye taliyar ta kora da ruwa, kwanciya tayi saman sofa din ta daura kafafuwanta saman laps dinshi bai tanka mata ba, yasan rigima take nema, Cikin sa'a bacci yai awon gaba da ita, A hankali Ya zame ?afafuwanta ya mi?e tare da Waukarta ya nufi upstairs da ita, a kan gado ya kwantar da ita, yabi da bargo ya lullu6e mata jikinta, kafin ya fito ya datse kofar dakin nata, cikin sauri ya nufi dakinsa don ya kwanta ya karasa baccin dabai isheshi ba, bayan shigarshi daki har ya kwanta ya soma tunanin ko me ya hana jazz zuwa? Tun safe yake jaraba kiran layin shi baya picking, har ta 6angaren danish ba a kira shi ba wunin yau, fatan shi Allah yasa lafiya da wannan tunanin bacci 6arawo ya Wauke shi.



*=؋?BENAZIRd'*



Kwance take a saman darduma, tun bayan data kammala sallar Isha bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, yayin da zeenatu take a can saman gado tana bacci.



Tana a nannaWe cikin dogon hijab dinta, tayi nisa acikin baccin ta, Ba zato ba tsammani hasken fitilar bedroom Winta ya Wauke Wuff, wani iko na Allah ba wutar gidan bace ta samu matsala, Wakinta ne kadai hasken ya Wauke, abun ka game bacci sam bata ji alamun hasken dakin ta ya Wauke ba.



Kwatsam! taji an dam?i wuyanta, tsabar zafin sha?ar da akayi mata ne yasa ta ware idanunta waje, bata iya ganin komai sai duhu ba?i wulik a idanunta

Wani irin mahaukacin bugun fargaba zuciyarta keyi mata, Hankalinta a matu?ar tashe ta soma kokarin kwace wuyanta daga hannun mutumin daya sha?eta, wuyanta tuni ya soma yi mata zogin azaba, zufa ta ko'ina ta wanke fuskarta, duk yadda benazir taso ta kwace kanta sai dai kash takasa, ga zeenatu kwance saman gado sai dai babu halin da zata iya buWe baki ta nemi agajin ta, koma wanene yayi mata muguwar sha?ar da ko yatsanta takasa Wagawa, bakinta tamkar an Waure mata shi takasa buWe shi, hakan yasa tafara kukan zuci tana ambaton sunan Daddy, mommy, yaya shurem, Zeenatu, A karshe ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un tacigaba da anbatonta acikin zuciyarta.



Tana acikin wannan mawuyacin Halin har tafara fidda rai da rayuwa kwatsam wayar zeenatu da ta ajiye kan gado ta soma ringing, taken karatun al'?ur'ani mai girma ne, Kamar Walkiya taji alamun an sakar mata wuyanta, kuma nan take hasken Wakinta ya kawo, a gigice ta zabura ta mi?e zaune tana faman zazzare idanunta, bin ko'ina na dakin tayi da kallo bata ga kowa ba, Lamarin ya daure mata kai, tagaza gane meke shirin faruwa da ita? Don wannan yafi karfin a kirashi da mafarki, tabbas akwai me son rabata da rayuwarta, lokaci Waya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ?aramar yarinya ita kadai tasan radaWin da wuyan ta ke yi mata, zeenatu dake ta sharar baccin ta tuni ta soma mutsu mutsun farkawa saboda sautin kukan benazir daya fara addabar kunnuwanta, da sauri benazir ta tsagaita da yin kukan gudun kada zeenatu ta farka taga halin da take a ciki, cikin juriya ta mi?e ta zame hijab din jikinta, ta jefar da shi gefen gado, gaban madubi taje ta tsaya tana kallon wuyanta yayi jawur da shi hada sawun yatsun hannuwan mutun rudu rudu..



Hakika Ta gigita ta kuma tsorata a yanzu ta ?ara tabbatarwa kanta cewa akwai me son ganin bayan ta? Wanene? Laifin me ta aikata da har ake son kashe ta? Zuciyarta ce ta raya mata cewa zai iya yiwuwa jinnu ne, tafi yarda da abun da zuciyan nata ta raya mata saboda babu wanda take zargin zai iya yi mata haka acikin mutanan da take rayuwa da su,ta dai yanke shawarar zata sanarwa yaya shureim ko dan su nemi mafita a tare.



Miryarta na rawa ta furta"Ya Allah ban cutar da kowa ba, Kada ka bada damar da wani zai cutar dani" ta jima atsaye gaban mirror, zuciyarta cike da rudani, ta nufi toilet, tsawon mintuna kafin ta fito jikinta da alamun lemar ruwan da ta watsa ma kanta.



Tunawa da kiran wayar da akai mata ne yasa ta nufi bakin gado ta Wauko phone din ta soma daddanawa call logs ta shiga nan take taga missed call na bakuwar number din nan



Sai da ta fara kallon agogo, karfe wani abu na dare kafin ta danna call tana faman zazzare idanunta, jikinta nata kerma kamar wadda aka kada ma mazari



Adai dai wannan lokacin Unaisah tana a zaune kan darduma ta zumbula hijabi a jikinta ta Waga hannayenta sama fuskarta sharkaf da hawaye bakomai take yi ba face yima danish addu'ar samun lafiya, Batul tana a kwance gefen ta, tun bayan da boss ya tashe su domin yin nafilfilin da za su yi kowannansu bai koma bacci ba, duk suna a dakunansu suna yin sallah, ita dama batul bata da jumurin yin sallah duka raka'a biyu ta samu tayi adaddafe kafin bacci yai awon gaba da ita, shigowar kiran wayar ta ne yasa takai hannu ta dauke ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, a inda ta ajiye ta gefen prayer mat din da suka akai



Ko da tayi tozali da layin da take ta dannawa kira taga da shi aka kirata Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin yin picking din kiran, hadi da kara wayar a kunnanta.

Tamkar kurame sunyi shiru suna sauraran sautin fitar numfashin juna.



Jira take taji wanene mamallakin layin nan daya kira, Haka zalika itama benazir jira take tafara jin wanda ya Waga kiran yayi mata magana.



Jin shirun yayi yawane yasa unaisah tace"Assalamu Alaikum" sautin daddaWan muryarta ne ya daki kunnan Benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faWuwar gaba ba.



Muryarta babu nutsuwa ta amsa mata sallamar"Wa'alaikum Salam, barka da dare, dan Allah zan iya sanin dawa nake magana" ta fada cikin ?agara.



Shiru Unaisah tayi tana tunanin wacece wannan matar mai muryar ?an gayu? Daga ji dai wayayyiya ce.



Jin shiru ba'a ?ara magana ba yasa banezir furta"nayi magana anyi shiru b'a bani amsa ba, in ansan baza'a tanka min ba meyasa za'a takurani da kira da tsakar dare"? Har zata katse kiran Unaisah tayi saurin cewa"Aunty kiyi ha?uri, bakisan wacece ni ba, nima bansan ki ba"



Ajiyar zuciya Benezir ta sauke kafin tace"okey, amma meyasa kika kira layina bayan baki sanni ba"!



"Nayi kuskurene wurin rubuta number din da zan kira"



"Okey" shiru su ka yi, babu mai magana na tsawon mintuna kafin benazir tayi karfin hali cewa"meye sunan ki? Shekarun ki nawa"? ta tambaya ne jin muryar kamar ta ?aramar yarinya



"sunana Unaisah, shekarata goma sha shida, ke fa"?



Murmushine ya bayyana akan fuskar benazir, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin farin ciki ba.



"Sunana Aunty pretty, Amma fa ni ba yarinya bace, na girme ki, Shekarata talatin da wani abu"



Murmushi unaisah tayi ita kanta dadi take ji, duk da halin damuwar da take aciki silar kiran nan ya haifar mata da kwanciyar hankali.



"Kiyi hakuri na kiraki bisa kuskure, sannan na katse maki baccin ki"



"Kada ki damu, Naji dadin haduwa dake"



Shiru sukayi Kamar karsu Kashe kiran haka suke ji.



"Baki so na sake kiranki"? Unaisah ce ta jefa mata tambayar .



Murmushi benazir tayi don ta fahinci yarinyar batason su daina magana.



"Ina so mana, tun da naji muryarki naji kin kwanta min araina, da ace babba ce ke da mun kulla kawance sai dai kin min ?an?anta"



Cike da zumuWi Unaisah tace"zan dinga kiranki muna gaisawa a matsayin aunty na, Idan kuma kina da Wiya kamar ni, ko ?anwa to ki hadani da ita sai mu dinga zumunci"



"In sha Allah, yanzu ki kwanta ki yi bacci kada mommyn ki ta kama ki kina waya da dare, gobe zan kiraki mu ?arasa gaisawa, Yanzu kinga dare yayi,"



Kamar karsu rabu, Haka sukayi sallama da junansu, fuskar kowannansu dauke da murmushi.



Karatun kur'ani benazir ta kunna a wayar, saboda ta fahimci Kiran wayar da akayi mata sautin karatun kur'ani ya fita shine silar da Aljanin daya sha?eta ya gudu, Gefenta ta ajiye wayar, ta kwanta tare da jan bargon da zeenatu ta lullu6a da shi, itama ta lullu6e kanta, zuciyarta acike fal da annurin farin ciki, Harta kosa gobe tayi, kodan ta kira Yarinyar su ?ara gaisawa, ita kadai take ta tufka da warwara har ta yanke shawarar zata haWa yarinyar da zeenatu su dinga zumunci, in yaso ita sai ta kar6i layin maman yarinyar suna gaisawa da wannan tunanin wani baccin ya kuma daukarta.



Bayan Unaisah ta kashe Kiran, wani irin daWi take ji, aranta ta ayyana meyasa nake farin ciki akan matar da bansan wacece ita ba, wata'kil ma maman Sajeed ce, dole gobe in fada mashi munyi waya da matar dake a ru?e da layin wayarsa, bata koma bacci ba sai da ta kara zuwa dakin danish cikin daren ta le?a don ganin koya farka, kamar yarda suka barshi haka ta same shi, addu'o'i ta ?ara tofe shi da su

ta ru?o dogayen yatsun hannayensa ta sumbace su, tasha kuka a yayin da take agefen gadon shi ta ro?i Allah akan ya ba man dinta lafiya tamkar zatayi hauka ita kadai a dakin sa ko tsoro bata ji, raba dare tayi tana gadinsa har bacci yafara kokarin daukarta sai da aka fara kiran sallar Asubahi tukunna ta baro dakin tana sharar kwalla..............=?%?=؋?
'?





*FRIDAY MORNING*



*Hajjaty the head maids*



Sautin ringing Win wayar pravin ne ya katse mata baccin ta, A hankali ta buWe idanunta masu dauke da bacci ta kalli ceilling na tsawon mintuna kamar mai nazarin wani abu, sam ta manta da abun da ya farkar da ita daga bacci har saida aka ?ara kira tukunna ta mi?a hannu saman mattress ta janyo wayar ta karata a kunnanta ba tare da ta duba sunan mai kira ba.



BankaWo kofar toilet da akayine ya firgitar da ita kafin tayi wani yunkuri taji ya fisge wayar daga hannunta, har sai da gabanta ya faWi ganin kumfar sabulu a jikin shi, Ko sutura babu haka ya fito daga bathroom zindir haihuwar uwarsa, duk dan kada taWaga mashi waya' juyawa yayi da sauri ya koma toilet, hajjaty dake kallon shi da tsantsar mamaki ta mi?e zaune tare da jingina bayanta jikin headboard tana jiran fitowarshi

Badajimawa ba pravin ya fito daga toilet waist dinsa daure da towal, fuskarshi babu walwala tunkafin tayi mashi magana yai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login