Showing 126001 words to 129000 words out of 391264 words

Chapter 43 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2577

hotunanta da nake Yi shiyasa Ya gane ta, Ni dai Yanzu Ki taimaka min zahra! Inason na tabbatar da abun da nake hasashe! Taya zamu Iya ganin ta"S'S'S'



"Auntyna Ganinta ba abune mai sau?i ba, dama ace bangaren su hajiya saratu suke da zama zaifi min sauki in nemi alfarmar ganinta, amma gaskiya tunkarar chief owais ba abune mai sau?i ba! Kinsan Yanayin aikin su na jami'an sirri wallahi in ma suka ji maganar zasu Iya tuhumarmu"



"Wallahi zahra In har ban samu ganin Yarinyar nan ba Hankalina bazai ta6a kwanciya ba, ke koda Zasu tuhume ni ne, gobe sai naje estate din nasu..." da kwarin gwiwa tayi maganar




"?wara mu bi komai a sannu, kada mu ce zamuyi gaggawa tun da bamu da tabbacin in itace dagaske...." kafin zahra ta ?are maganar Aneelerh ta katse ta da cewa"zahra itace! Nifa ba makauniya bace, wallahi unaisah ce Yarinyar nan, tun fa tana jinjirarta muke kula da ita, shayar da ita ne kawai banyi na, tayaya bazan gane fuskarta ba"? Idanunta cike tab da kwalla ta furta maganar

"Ki taimaka min zahra, dan Allah, ko dan saboda Halin da mahaifiyarta take a ciki, wallahi bakiga tashin hankalin data Shiga ba a lokacin dana sanar da ita zancen 6acewar su, ba dan zuciyar imani ba da tuni zuciyarta ta buga...."



Ru?o hannunta zahra tayi a cikin nata"ki kwantar da hankalinki aunty aneelerh, kada ki bari hawayen dake taruwa a cikin idanunki su zuba, muyi hakuri zuwa gobe inyaso sai muje can estate din nasu watakil adace su barmu mu ganta..." cikin kwantar da murya tayi maganar donta fahimci nema take ta zauce har lokaci bata daina kallon hoton ba



"Mezai hana mu tuntu6i Ziyad? tun da shi yasan da zancen 6acewarsu kuma yana da hotunan Unaisah da na tura masa ko shi zai iya yi mana hanyar haWuwa da ita"



"Good Idea Auntyna, Yanzu Ki kwanta Ki huta, Gobe saimu ?arasa maganar"



Jinjina kai tayi"shikenan zahra, Allah yasa zan Iya runtsawa, Bakisan Yadda na ?agu da son ganin Yarinyar nan ba, fatana Allah Yasa itace Win."



"Amma kunyi waya da su aunty Benazir din? Sun isa gida Lafiya?



"Na kira layinta bata Waga ba, sai zuwa gobe zan sake jaraba kiran ta.."



Suna Cikin Yin magana Baby Junaid Ya fara mutsu mutsu zai farka daga bacci



"Junaid zai farka, Ki koma gurinsa, ni zan wuce aunty aneelerh,



Mi?a mata wayar tayi"mu kwana lafiya zahra"



Fucewa tayi daga dakin, Aneelerh ta koma kan gado ta janyo junaid on her chest ta rungumesa




Babu alamun zata Iya runtsawa saboda zumudin jiran gobe tayi, abu biyu ne suka tsaya mata aranta, na farko damuwar Benazir, na biyu yarinyar nan mai suna Unaisah...



*HAJJATY*



Can cikin bacci ta soma jin motsi a dakin ta wanda yayi silar farkar da ita, tayi zaton pravin ne Ya shigo shiyasa batai yunkurin tashi ba sai ma ta ?ara gyara kwanciyarta, kwatsam kamar daga sama tajiyo ?arar faWuwar wani abun firgigit ta zabura zaune tana faman zare idanunta jikinta Ya hau 6ari ta fara laluban fitila zata kunna hasken Wakin, akan kunnanta taji takun tafiyar mutun adai dai lokacin ta samu damar kunna light din kamar walkiya taga gifcin mutun Ya lullu6e jikinshi da bargo, wata irin zufa ce ta keto mata numfashinta na hauhawa take kallon ?ofa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? r cike da mamakin wanene Ya shigo? don kwata kwata baiyi kama da pravin ba...



Wurga ido tai akan tsakar dakin bakhhoor burner din da take ajiyewa kan mirror shi ta gani kan floor daga gani kado shi akai



Lamarin Ya Waure mata kai, saukowa tay daga kan gadon ta, gaba Waya tsoro Ya kamata, dama ?warin gwiwarta pravin ne gashi baya nan Yana can dakin Hajiya saratu.



Tayi mamakin ganin bedside drawer dinta a buWe, zukunna tayi gaban drawer din yatsun hannunta na kerma ta curo album din dake a ciki mai Wauke da hotunan auransu, cike da tashin hankali take bubbuWe su ganin ba'a Wauki hoton Ba Yasa Hankalinta Ya Wan kwanta, da sauri ta mike taje taja ?ofar ta datse, ta sanya key



Komawa tayi gefe gado ta zauna har time din jikinta bai daina 6ari ba gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, tun da gashi har an fara kawo mata hari adakin ta, Allah Allah take gari ya waye pravin yazo don ta faWa masa abun da ya faru



______________________BATOOL
'?



Tsakar dare ta farka sakamakon fitsari da ya matse ta, saukowa tayi daga kan gado



Mi?a tayi kafin ta nufi toilet din tana dab da zata shiga, tajiyo sautin murya ?asa ?asa Ana magana har sai da taji gabanta Ya Wan faWi da sauri ta kalli gadon su duk a tsammanin ta ummi tana akwance ashe bata nan fululluka ta lullu6e da bargonta sai yai kamar mutun na akan gadon



Kanga kunne tayi don ta ?ara tabbatarwa da kanta muryar waye take ji ?asa ?asa kamar ana raWa



"Kaima kasan bazan ta6a yin kuskuren da wani zaisan ina a tare da kai ba, yanzu haka da nake Yi maka magana ina a cikin toilet saboda bani kaWai bace a Wakin, akwai Waya daga cikin yaran da muke kula da su, Yarinyar tana sona, a tare muke kwana da ita........"



?agowa batool tayi da kanta, Idanunta aWan zare babban abun da take jima tsoro da wa aunty ummi take magana a tsakar daren nan kuma acikin toilet? Wanene? Da har take faWin bata son asan tana waya da shi?



Gaba Waya tashiga ruWani, ?ara kanga kunnan tay jikin ?ofar



"Bazai yiwu ba, Ni Bazan Iya yakice ta daga gare ni ba, na faWa maka Yarinyar bata da matsala, she is innocent bayan haka bata da wayon da har za ta sanya min ido..."



"Meyasa baka son kowa Yasan Ina atare dakai? kamar wani mara gaskiya kodai bakasan sunan ka Ya 6aci ne a idon jama'a"?



Ta sake ji ummi ta faWa, can kuma sai tajiyo tayi wani sauti mai kama da nishi nishi da jan numfashi



Kwatsam tari Ya kubcewa batool waro idanu tayi kafin jiki na 6ari ta watsa aguje ta kashe light din dakin ta haye kan gado ta ja bargo ta lullu6e tana faman sauke ajiyar zuciya



A fujajen Ummi ta fito daga toilet din, yar rigar bacci ce a jikinta shara shara, kai tsaye ta sauke idon ta kan gadon, ganin batool a kwance tana bacci Yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, juyawa tayi ta koma cikin toilet din taja kofa ta datse



Batool dake a kudundu ne cikin bargo jin alamun ta rufe kofarne Yasa ta ?ara jin hankalinta Ya kwanta, ta kudiri aniyar saita faWa ma Unaisah maganar da aunty umminsu keyi a toilet, saboda ta tsorata gani take kamar akwai wani abu a ?asa duk da bata zarginta.



Ga fitsari cike da mararta amma saboda abun da Ya faru Ta hakura da yin shi, ta matse shi kuma cikin ikon Allah wani baccin Ya sake daukarta



____________________UNAISAH ANGEL



Kiraye kirayen sallar asubahin da aka farayi ne Ya farkar da ita, addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta mi?e zaune ta Wan jingina bayanta jikin headboad



Kayan baccine a jikin ta, Milk colour riga da wando masu kyan gaske da alama baccin bai sake ta, sai faman lumshe idanu take Yi



bakomai take tunani ba face Aunty pretty Winta, bata ta6a damuwa da ita irin na Yau ba, Wani irin marmarin son jin muryarta take Yi aranta ta ayyana ko awani hali take a yanzu?



Canza akalar tunanin nata tayi akan danish, murmushi tayi tunawa da haukansa na jiya har yanzu inta tuna abun da yai mata sai taji wani irin yanayi atare da ita



Ta Wau lokaci tana ?an tunane tunane, kafin ta ware gray eyes din ta, hannu takai ta Wan bubbuga kafadar deeja dake bacci tana jan minshari



"Sis ki tashi time din salla yayi" cikin magagin bacci deeja tace"Ni ki kyale ni, waike kullum sai munyi sallah ba a hutawa...."



Murmushi unaisah tayi"Pls kada ki wahalar dani..."



Da?yar ta samu khadeeja ta farka daga bacci, bayan sunyi alwala suka sanya hijabi a jikinsu,

Ko da suka kabbara sallar khaddeeja ba ibadar ce agabanta ba, da zarar unaisah tayi sujjada ko ruku'u sai ta daddage ta Wuma mata dundu abaya



Baiwar Allah, ahaka ta daure suka kammala sallar, bayanta har wani zogi Yake mata,



Batasan Ya zatai da ita ba, Haris ne Yaja mata shi da ya fara kawota dakin su don ta kwana,



Akan darduma bacci Yai awon gaba da khadeeja



Mi?ewa tay da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan mirror cike da zumuWi ta danna ma aunty pretty call tasan i warhaka ta farka Yin sallar asuba



Almost 3 times wayar tana ringing ba'ay picking ba, duk da haka bata hakuraba ta sake jaraba kira



Cikin sa'a Akai picking batare da anyi mata magana ba



Calmly unaisah tay mata sallama tare da cewa aunty pretty barka da asuba, kin tashi lafiya....." shiru ba alamar za'ay magana

"Naji kinyi shiru bakice komai ba, dan Allah kiyi min magana jiya har mafarkin ki nayi ..." kafin unaisah ta ?are maganar wata murya ta ratsa ta da cewa"Wacece Ke? Kuma wa kike nema"?



Wani irin shock taji, Har saida gabanta Ya faWi jin muryar Yarinyar sai taji kamar ta ta6a jinta awani wuri



"I'll hang up if you don't talk!'"



Da sauri tace"sunana unaisah, aunty pretty nake nema"



"Oh ko ke ce kika kira wrong number rannan"?



"Ni ce"



"Okey, me wayar ba ta farka daga bacci ba..".



"Wacece ke"?



"Cousin dinta ce, sunana zeenatu" lokaci Waya taji yarinyar ta shiga ranta, ta rasa a ina ta ta6a jin muryarta tabbas akwai wadda ta sani mai irin voice din ta



"Dan Allah, Idan ta farka daga bacci ki faWa mata na kira,"



"Toh sai anjima" tana fadan hakan tay rejecting call din



?urawa screen din ido Unaisah tayi, yayin da kwakwalwarta ke cigaba da tariyo mata voice din zeenatu.



A bangaren zeenatu bayan sun gama waya da unaisah, mikewa tay daga kan darduma jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta Waya ru?e da wayar cikin sauri ta fito ta nufi dakin Benazir



Kamar yadda suka bar shi jiya haka ta same shi a garkame, dr shurem daya kwana awurin kiran sallar asuba ne Ya farkar da shi lokacin da zeenatun tazo baya awurin sun tafi masallaci



Knocking kofar tayi"aunty benazir dan Allah ki buWe min ?ofa, inason ganinki, jiya na damu da halin da kika shiga, ko baccin kirki bansamu nayi ba..." shiru babu alamun zata buWe mata.



"Zeenatu ki daina wahalar Yi mata magana ba buWewa zatay ba, halin ta ne tun tana ?arama in Ranta Ya 6aci sai munci wahala kafin mu shawo kanta..." hajiya layla ce tay maganar, baiwar Allah daga ganin idanunta ko bacci batay ba sunyi ja idon Ya ?an?ance



Muryar zeenat kamar zata fashe da kuka tace"tun jiyafa take a daki kulle! Bata magana, Idan wani abu Ya same ta fa..."



Shigowar Su dr shureim ne Yaja hankulansu ga dubansu, Su ukune tare da Alhaji musa da Alhaji ubaid duk sun sanya jallabiya a jikin su.



Zeenatu na ganin daddynta, da gudu ta nufe shi, ta faWa kan kirjinshi tana kuka take fadin daddy aunty benazir ta?i buWe ?ofa tun jiya, dan Allah kasa a balle ?ofar, bana so wani abu Ya same ta...'



Fuskarsa babu annuri Yace"meyasa zaki damu kanki akanta? Ba ita ta kulle kan ta ba ne? Ko wani Ya rufe ta ne..." bai kare maganar ba hajiya layla ta katse shi cikin 6acin rai tace"wai kai wani irin bauWaWWan mutun ne? Baka da tausayi ne kwata kwata arayuwarka? Jiya kana ganin halin da ta shiga har faWa maka akai amma saboda rashin imani sai cewa kai a kyaleta in ta gaji zata buWe kofar saboda ba yarka bace ko..."?

bata ?are maganar ba Alhaji ubaid Yai hanzarin katse ta da cewa"dan Allah kiyi hakuri ki daina Waga masa murya, jiya agajiye muka dawo gidan shiyasa Yace haka" harara ta wurga masa"kai ay saboda yarkace jiya ka hana idon ka bacci duk da agajiyen ka dawo gida, na tabbata da ace yarsace ke ahalin da benazir take aciki wallahi ba zaka iya runtsawa ba...." tun da tafara magana Alhaji musa Yake bin ta da kallo, arayuwarsa Ya tsani mutumin dake masa faWa Yana Waga masa murya, babu wanda ya ta6a gigin yi masa hakan sai hajiya layla....



Dr shureim Bai tsaya kula su ba, ya juya ya nufi dakinsa zuciyarsa sam bata masa dadi, lamarin Family dinsa Ya fara gundurarsa kwata kwata ba zaman lafiya daga wannan sai wannan



Jinjina kai Alhaji musa Yayi, ba tare daya tanka mata ba, har Ya Waga ?afa zai wuce Hajiya layla ta dakatar da shi ta hanyar shan gaban shi



Da mamaki Ya dago Yana kallon ta



"Wallahi babu inda zakaje! In har bakasa an buWe kofar dakin benazir ba ni kuma bazan ta6a bari kabar wurin nan ba..." tana huci ta faWa haWi da ru?e qugun ta, wlh a lokaci niyar kwashe ta da mari yayi amma sai Ya fasa Yatsun hannunsa har kerma su ke tsabar 6acin rai, wai shi yau mace zata tari gabansa? Batare da jin shakkarsa ba? Wacece ita? Dame take ta?ama ne"?



"Layla ba haka mukai dake ba! Kin manta alkawarin da kikai mun na cewa ba zaki ?ara shiga huruminsa ba"? Azafafe ta kalli Alhaji ubaid"ban manta ba, amma wallahi Yau bazan raga masa ba, ay shi yasan ta yadda zaisa abude kofar, don haka bazan tsaya inaji ina gani in rasa ?ata ba dole yasa aballe kofar can" ta yi maganar tana watsa masa harara...



Fashewa da kuka zeenatu tayi jikin ta har jijjiga yakeyi, cikin shesshekar kuka tace"daddy dan Allah kasa a bude kofar, ni bana son inga kuna samun sa6ani atsakaninku, dan Allah daddy ka taimaka mana..." kukan zeenatu ba karamin tafasa zuciyarsa yakeyi ba

Gauran numfashi Yaja, tare da Wan jinjina kansa Yana huci kamar mayunwacin zaki ya dubi hajiya layla da tai masa ?erere kamar zata rufesa da bugu

A fakaice taga Ya sakar mata wani shu'umin murmushi har saida taji gabanta Ya faWi

Sassauta fushin fuskarsa Yayi"naji zan buWe ?ofar, ki bani hanya na wuce" matsawa tayi idanunta akan fuskarshi Ya nufi kofar dakin benazir



Yana ?arasawa bakin ?ofar, Ya Waura faffaWan tafin hannunsa, turata yayi wani iko na Allah sai ga ?ofar ta buWe

Kallon Juna Alhaji ubaid da Hajiya layla sukai, abun da daure kai tun jiya suke gabzar kofar donta buWe babu wanda bai jaraba karfinsa ba amma duk abanza ko motsi batayi amma shi daga turawa ta buWe wani irin ?arfi ne da shi? Basu tsaya dogon tunani ba, jiki na 6ari suka nufi Wakin zeenatu da gudu ta rigasu faWawa a ciki.



Shugarsu keda wuya kowan nan su Yaci burki, Abun da suka gani Yayi matu?ar Waga hankulansu, kamar matatta haka suka hangota kwance kan floor rabin jikin ta a cikin toilet dake a buWe, kamar irin tayi gudu ta kife awurin har kanta Ya daku goshin ta Ya fashe



"Innalillahi wa'inna ilaihirraji!"un"! hajiya layla ce ta zagba salati tana tafa hannayenta, zeenatu da ta gama ruWewa agaban benazir ta zube bisa gwiwowinta, takai hannu tana tatta6ata Aunty benazir! Meke damunki dan Allah ki tashi inna lillahi..mami daddy ku ce ta tashi dan Allah....



da sauri Alhaji Ubaid Yaje Ya Wago da ita, jikinta duk Ya saki ya Wauko ta da hannu biyu ya kwantar da ita akan gadon ta, sumar kanta duk Ta yamutse



Fita hajiya layla tayi jim kaWan ta dawo da robar ruwa ta buWe murfin ta kur6i ruwan tare da furzar da shi kan fuskar benazir



Ruwan na dura tayi wata irin zabura tana ambaton sunan taj ... adai dai lokacin shureim Ya shigo dakin ganin su tsaitsaye bakin gadon ta yasa shi saurin karasawa

Tunkafin yayi magana Hajiya layla tace"shureim ka gani ko? Abun da nake gudu kenan! bansan ya akai ta faWi kasa daga cikin toilet, kanta Ya bugu..."



Hankalinsa atashe Yake kallon Benazir yatsun hannunta sai kerma suke, ta runtse ido tana sambatu kwata kwata bata acikin hayyacin ta

Zeenatu duk ta damu, Hannunta ruke dana benazir sai faman shesshekar kuka take

"Ya akai kofar ta buWe"?

"Uncle din ku ne Ya buWe kofar," ta bashi amsa ataikaice, Alhaji ubaid Tuni Ya fuce Yabi Alhaji musa don Ya fada masa halin da benazir take ciki



A lokacin Har Ya koma Part dinsa, sallamar Alhaji ubaid ce ta katse sa kamar bazai fito ba, don saida Ya Wau lokaci har sai da hajiya sara tace da shi baiji ana sallama bane? Tukunna Ya mike cikin takun izza Ya fito daga dakin

"Me kuma zanyi bayan na buWe ?ofar"? A faWace Ya faWa Yana ?an?ance idanunsa

"Dan Allah ka yi hakuri da abun da layla tayi maka, bata jin maganata naja mata kunne taki bansan ya zanyi da ita ba..." ya mutsa fuska Alhaji musa yai"naji, Yanzu awani hali benazir din take a ciki?



Kamar mai jin shakkarsa Alhaji ubaid Ya furta"mun sameta akwance kan floor, rabin jikin ta a toilet, kamar faWuwa tayi don har kanta Ya daku sosai, ta farka sai dai kamar bata a hayyacin ta shiyasa nazo don na sanar dakai...." ta6e la66ansa yai kafin yace"zanyi magana da likita na, zaizo Ya duba ta" godiya ya yi masa kamar zai masa sujjada, komawa cikin dakin yai hajiya sarah dake a zaune kan darduma ta mi?e tana tambayarshi meya faru ne? Ko benazir ta buWe kofar ne' amsa mata yai da eh jiki na rawa ta fuce daga dakin don taje dubota...



Gaba Waya sun hallara a dakin Benazir kowan nan su Ya shiga hali na damuwa, bada jimawa ba Dr Mark Ya shigo gidan, wani basamuden Likita ne irin african american din nan, yadda kasan Jinin Alhaji musa, Fuskarsa babu fara'a, sumar kansa hada kitson zane, tun da Hajiya layla tayi arba da fuskar dr mark kuma taji cewa Alhaji musa ne Ya kira shi don Ya duba lafiyar benazir, tace wallahi bazai ta6a benazir ba, ai kwata kwata ita baiyi mata kama da likita ba, ta dinga surfa bala'e duk yadda alhaji ubaid Yaso Ya shawo kanta shi da su hajiya sarah akan ta bari aduba ta, amma abun Ya faskara a karshe sai dai Alhaji musa Ya sallami likitan Ya tafi ba tare da ya duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ?ara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login