Showing 252001 words to 255000 words out of 391264 words

Chapter 85 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2572

maimakon taga tashin hankali akan fuskarshi sai taga ya saki tausasan murmushi arude tace"lafiyarka kuwa? Ko bakaji abun da nake magana akai bane" ruko hannayenta yayi acikin nashi, fuskarshi da fara'a tace"mommy zan fada maki gaskiya amma kada ki fadamawa kowa..." cike da mamaki tace"toh, Ina sauraronka" ta fada tana kallon cikin idanun shi
"Benazir taji saukin abinda ke damunta, haukan da kika ga tanayi pretending ne, har tambayarta nayi meyasa take yin hakan? Sai ta nuna min bata son asan ta samu lafiya... Baki asake hajiya layla take sauraron shi tayi mamakin jin hakan aranta ta ayyaba lallai benazir ashe haryanzu tana nan da dabi'arta nayin karyar ciwo.

"Amma shureim baka tunanin akwai wani dalili dayasa benazir take pretending? In ba haka ba taya mutun da lafiyarshi zai za6i zama mai ta6in hankali" ta jefa mashi tambayar

Shiru yayi jimm shi kanshi yayi wannan tunanin amma koda ya tambayeta sai tace mashi bakomai.

"Gaskiya bana tunanin akwai dalilin dayasa yakeyin hakan cos na tambayeta tace min bada wata manufa ba saina rashin son a rabata da azeezaty"

Girgiza kai hajiya hajiya layla tayi"ni nasan kayana shureim, Benazir bata ta6a yin abu batare da dalili ba, dole akwai dalili, ni fa najima ina zargin da akwai wani abu da Benazir ta sani ko ta aikata wanda har yaja akayi mata asiri..."

maganar hajiya layla ta Wan Waga hankalin shi tunawa da bibiyar rayuwar Benazir da akeyi acikin gidan dama kuma yana zargin wanda yayi mata asiri ne yake son karasa kasheta bayan haka itama Benazir din zai iya yiwuwa maganar hajiya layla ta zama gaskiya.

amma saboda bayason Waga mata hankali shiyasa yaki sanar da ita zancen bibiyar rayuwar Benazir da akeyi sai dai ya yanke shawarar zai je dakin Benazir don ya tambayeta meya faru da ita aranar data kulle dakin ta.


Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar Hajiya layla ta katse shi"kaima kana tunanin abunda nake tunani ne ko kuwa" murmushin ya?e ya sakar mata"mami bana so ki sanya damuwa aranki, hasashen da kike ba lallai ya zama gaskiya ba, zai iya yiwuwa wani tayi ma rashin kunya kinsan wasu mutanan da bakar zuciya ga mugunta arai watakil ita ta manta da ta bata masu rai shine su kuma da babu Allah aransu suka yi mata asiri don su kuntata rayuwarta, ko kuma wanda ya aikata mata hakan yayi ne da niyar ya Wauki fansar wani abu da ku ka ta6a yi masa..." dafe kirji hajiya layla tayi da tafin hannunta alamar ta shiga uku itama fa tayi rashin mutunci lokacin da Alhaji ubaid Yake akan mulki tunma kafin ya hau kujerar gomna ba mutunci ne da ita ba, yanzu ne tayi hankali ta gane Allah Waya ne.

"Ni fa ban fada maki donki tashi hankalinki ba, inaso ne na kwatanta maki ba lallai hasashen ki ya zama gaskiya ba, banaso ki matsa ma benazir kan ta ta fada maki meyasa take pretending, mu kyaleta kawai iyakacinmu da ita addu'ane kawai ubangiji Allah Ya kare mana ita daga sharrin duk wani abin cutarwa..." amsa mashi tayi da Ameen ita dai hankalinta bai kwanta da lamarin benazir ba.

sun jima suna fira adakin harya bata labarin zuwansu gidan su Azeezaty duk don ya kara kwantar mata da hankali taji dadi kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsabar farin ciki.


__________________________=ؓ?
'?

akwance take kan gadonta, jikinta sanye da night dress, ta ru?e wayar ta a hannunta, ta nutsu tana kallon hoton fuskar Unaisah dake akan wallpaper din ta... bata gajiya da kallon fuskar ?arta, takan wuni tana kallon hotunan su Unaisah ba tare da gajiya ba.

kwantar da wayar tayi kan kirjinta ta Wage kai sama tana kallon ceilling.

bakomai take tunawa ba face shawarwarin da Aneelerh ta bata akan yadda zata shawo kan Taj ta hanyar kyautata mashi tun shekaran jiya take tura mashi love messages har yau yaki mata reply kamar tay hauka, ta rasa ya za ta yi ta shawo kanshi har jaraba kiran shi tayi tun da ya Waga sau Waya yaji muryarta bai kara picking call din ta ba.

Wago wayar tayi ta shiga cikin whatsapp dinta, a chat dinsu da Anila tayi copying contact din Unaisah data turo mata..

Cike da marmarin son Jin muryarta ta sanya number din tana kokarin yin saving kwatsam ba zato ba tsammani taga number din already akwai ta a contact list dinta da sunan God gift, Yarinyar da ta kira wrong number a matukar rude ta kurawa contact din ido batare da kyaftawa.

lamarin ya daure mata kai tunani tayi ko dai Aneeleerh wrong number ta tura mata?

zuciyarta ce ta raya mata bakya tunanin duk itace? Dama kuma sunansu iri Waya Unaisah hakan na nufin yartace yarinyar da suke waya? Ta jefa ma kanta tambayar, kokwanto ta farayi anya kuwa itace? Yarinyar fa ta fadamata ba abuja suke ba.

"Bari dai na jaraba kira inji" call ta danna almost 20 times ba'ay picking ba, damuwace karara akan fuskarta, jin knocking Win room door dinta yasa ta yin saurin aje wayar kan side drawer ta fara haWe rai zatay pretending...

A hankali ta shigo dakin, Jikinta sanye da dogon hijabi, a tsakar dakin ta tsaya tana kallon Benazir kamar tana jin shakkar tunkararta, tayi mamakin Ganin zeenatu adakinta yau wata rana tun lokacin da aka sallameta ba ta kara kusanta kanta da ita ba.

aranta ta ayyana watakil iskokan dake akanta ne suka saketa shiyasa ta fara neman su shirya da juna

Kurama juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, har na tsawon mituna kafin zeenatu tay karfin halin firta"Aunty Benazir, zan iya shigowa ciki"?

?aga mata gira Benazir tay ba tare data furta mata kalma ba, wucewa tayi kan gadon ta haye tare da juya mata baya

sunyi shiru kamar basu ta6a sabawa da junan su ba

"Aunty benazir ina Azeezaty? Nasan kuna waya da ita, ba ta6a tambayarki ni ba"? Kallon bayanta Benazir tayi kafin tace"kina nufin babyna"? Tace Eh

"Tana tambayarki, duk in mu ka yi waya sai tace in gaida mata ke.." dadine ya lullu6e zeenatu har batasan sa'adda ta aje kunyar gefe guda ta juya suka fuskanci juna ita da benazir

"Itama ta damu dani, kamar yadda na damu da ita kuma tana so na" ta tambaya tana kallon benazir dake kallon ta..

?aga mata gira tay alamar eh

Murmushi tasaki"yaushe zaki kiramin ita mu gaisa"?

"Gobe in sha Allah" washe baki tayi tana faman kyafkyafta blue eyes din ta...

Ita yanzu tausayi zeenatu ke bata, shiyasa kwata kwata bata ru?e ta aranta ba.

Ganin kallon da Benazir ke yi mata yasa tay saurin rufe idanunta, cike da jin nauyinta tace"Aunty benazir dan Allah ki yi hakuri da abun da na maki" murmushi Benazir tayi"zeenat laifin me kika min"?


"Banje asibiti na duba lafiyarki ba, bayan kin dawo ban kula ki ba" yar dariya Benazir tayi"haba karki wani damu wlh, nayi maki uziri ya shureim ya fada min bakyajin dadi .." ajiyar zuciya ta sauke har taji sanyi aranta, ta Wan buWe idanunta akan fuskar Benazir mi?a mata hannu tayi"nayi missing dinki ba kaWan ba sisterna rabin raina, da naganki adakina naji dadi, dariyar farin ciki zeenatu tasaki tare da kama hannun Benazir ta ru?e shi gam a cikin nata.

_________________________________
'?

Bayan sallar Mabrib, gaba dayan su sunyi wanka sun shirya cikin shiga ta mutunci yan matan sun sanya abaya sunyi rolling kamar larabawa, mazan kuma sun sanya jallabiya kusan kalar shigar da su kayi aranar dinner din Hateem sun yi kyau sosai.

a falo suka hallara mutun Waya ke babu acikin su Danish da har yanzu bai karasa shiryawa ba, Ummi ma tana atare da su ta dage sai daukar su pics take yi saboda sunyi mata kyau

"Wai su wanene bakin da zasu zo ne"? Sajeed ne yai tambayar idonshi akan Unaisah, yasan dakyar in batasan su wanene ba,

"Nima bansani ba, na kosa naga su wanene mu kara hakuri su karaso Allah yasa muga alkhairi"

su ka amsa mata da ameen, su jemimah sai yan guje guje suke atsakar falon ita da azeeza da parvin kamar wasu tsararrakin juna har saida ummi ta tsawatar masu kafin suka daina wasan..
"Ku nutsu pls, manyan bakine su zasu zo.."

"Aunty ummi su wanene wai"? Akagare Hanna ta tambaya tana kallonta

Ummi tace"nima bansan su wanene ba, amma boss ya fadamin bakin chief ne, tun da naji hakan nasan ba kananun mutane bane, shiyasa nace ku nutsu kada ay abun da za'aji kunya..."

kallon juna su ka yi, duk sun kagara da su ga su wanene...

Shigowa falon Taj yayi hannayen shi zube cikin aljihun jallabiyar shi, kwata kwata babu annuri akan fuskarshi kamar wanda aka fada ma sakon mutuwar shi.

Kwata kwata basu lura da shi ba har saida Javed Ya ambaci sunan shi kafin hankalinsu yakai gare shi, Unaisah na ganin shi ta nufe shi da sauri donta fada mashi abun farin cikin daya faru na bayyanar Danish azatonta bai sani ba.

tana karasowa Taj yayi saurin kauce mata kamar bai ganta ba, fuskarshi a haWe ya nufi su Naufal Ya mika masu hannu daya bayan daya ya yi musabaha da mazan kafin Ya maida hankali kan su sarah da fara'a yake amsa masu gaisuwar da su ke yi mashi.

gaba Waya ta gaza Waga kafafunta saboda faduwar gaban da taji, hankalin ta ya tashi da ganin abun da daddynta yayi mata, kokwanto tayi anya ya ganta? Ko dai bai lura da ita bane? In ba haka meyasa zai shareta ya nufi yan uwanta?

ta sanyawa ranta cewa bai ganta bane saboda bai ta6a mata hakan ba, cike da kwarin gwiwa ta nufe shi a lokacin yana tsaye, ta fada bayan shi ta rungume shi tana fadin"daddy ni baka ganni ba ne..." rai aWan bace ya furta"unaisah ki sake ni, tun kafin na bata maki rai" ya fada tare da janye hannunta Ya jefar da shi gefe Waya.

aruWe ta kalli fuskar shi, ya haWe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.

Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su
Duk da haka bata kawo komai aranta ba, ta kuma cewa"daddy, chief ya fada maka an ga danish a cikin toilet dinsa..." banza yayi da ita tamkar baiji maganar ba, hakan ba karamin Waga mata hankali yai ba.

komawa tayi cikin yan uwanta ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________
'?=?%?=؋?=ؔ?>???






..." bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi Wan uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun Wauke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"!

A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu haWin kai....


A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi..

Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba"

Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya"

jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba Waya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala.

"Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am..

"What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"!

murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba"


murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba.


"In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara"


da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin faWin"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa"


kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi


"Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce.

Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ?ara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman ya?i, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!.


Chief ya Waura da cewa"nayi alkawarin bazan ?ara takura ma Danish game da zancen kurkukun ?addara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun haWin kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...."

yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi



"Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun ?agara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu faWa masu"


ya faWa yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ?ari"

Dukar da kanshi ?asa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun Wayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya.

yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din"


big guy yace"muna jiranka" mi?ewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan.

Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska.

Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish.


"Inason yin magana dakai" ya faWa tare da juyawa ya nufi upstairs


sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun"


amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana.


"Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai waWanda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba.



Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su"


bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so"


"Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..."



duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.."


bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane.


Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login