Showing 249001 words to 252000 words out of 391264 words

Chapter 84 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2660

Danish.

"nasan za ka yi tunanin kodan saboda ina son ka bamu hadin kai shiyasa nake lallashin ka, ba haka bane, Kamar Yadda Allah ya jarabci Uncle dina da kaunarka nima haka nake jinka a zuciyata"

Unaisah dake atsaye bakin toilet door din gaba daya tana sauraran maganar chief, zuciyarta ta karaya da tausayin su, aranta ta ayyana wannan wata irin zazzafar kaunace suke yi ma shi? Anya Danish bai da ala?a ta jini da su?

Lumshe idanun shi yayi tare da numfasawa slowly ya ware eyes dinsa akan fuskar Chief

Baiyi tsammanin zai tanka ma shi ba, in weak Voice Danish Yace"ban ru?e ka a zuciyana ba, amma ku daina bata min rai in na nuna bana son abu kada ku tursasa min, ni bana so na cutar da kowa, shiyasa na ke6e kaina saboda in sanyaya zuciyata, kamar yadda kake jina a zuciyarka nima haka nake jinka, haWin kaine kawai bazan baku ba, sannan ka yi hakuri da bata maka rai da nayi, I didn't realize I was rude to you and disrespected you until he told me."

runtse idanu chief yayi gam na dan wani lokaci bai furta komai ba, har cikin ranshi yaji dadin maganar da Danish Ya furta mashi na cewa shima yana jin shi kamar yadda yake jin shi, yasan sannu a hankali wata rana zai samu amincewar shi.

Phone ringing dinsa ne Ya sa shi hanzarin buWe idanun shi tunawa da bakin su, wrist watch din hannun shi ya duba.

"Danish, Ka fito daga cikin ruwan nan haka, Inaso Ka shirya, nasan kana jin yunwa, zan sa ashirya mana dinner"

Amsa mashi yayi da Okay

Fitowa Chief yayi daga toilet din, Ya zaro wayar daga trouser pocket dinsa, misscalled ya gani da layin big guy.

Kira ya danna masa bayan yayi picking, big guy ya sanar da shi cewa yanzu haka suna akan hanya sun dauko su commender daga airpot.

fuskar shi da fara'a ya furta Alhamdulillah Allah Ya kawo ku lafiya, bai sanar dashi game da ganin Danish ba, ya bari sai in ya zo gidan ya ganshi.

Bayan sun yi sallama, Ya kira layin Ci ya sanar da shi game da ganin Danish yace ya sanarma sauran abokan aikin su, Ci yayi farin ciki sosai harya shawarce shi akan su lalla6a shi kada su yi duk wani abu da zai 6ata ma shi rai.

Sai da ya kammala yin wayar ya lura babu Unaisah a dakin, ranshi ya bashi may be ta fita ne don ta sanar da uwanta.

bayan fitar Chief da yan mintuna, A hankali Danish Ya futo daga ciki, har ya cire kayan jikin shi, short kadai Ya bari, sumar kanshi dake a jike ta manne ma fatar bayan shi da gefen fuskar shi, tamkar babu kuzari a jikinshi da wata irin kasala yake taka kafafun shi, a duk lokaci daya rikiWa ya dawo suffar shi ta mutane ba karamin jiki yake ji ba.


Gaban dressing mirror ya dakata da tafiya ya dafe gaban mirror Win da tafin hannun shi Waya.

Kunnuwan shi ne suka soma jiyo ma shi motsin mutun a dakin shi, yayi zaton chief ne hakan yasa bai damu daya Wago da ido ya kalle wanene ba.

"Meyasa ka tafi batare da ka fada min inda zaka je ba? Kasan irin tashin hankalin dana shiga na rashin ganin ka"? Da sauri ya kalle ta ta cikin madubin

Tana tsaye abayan shi ta goya hannayenta kan kirjin ta, abayan labulen dakin shi ta la6e saida taga chief ya fita tukunna ta fito don ta samu damar zazzaga mashi masifa.

Har sai da gabanshi ya Wan fadi ganin yadda idanunta suka kumbura sun kaWa jawur ko ba afada masa ba yasan tasha kuka tamkar ranta zai fata.

tuni yasha jinin jikin shi yasan ba zai tsira daga fushinta ba dole ta hukunta shi.

Bai aune ba, yaji ta faWa kan faffaWan bayanshi ta zagayo da hannayenta kan broad chest din shi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rufe idanunta da ke tsiyayar da ruwan hawaye ta dunkule yatsunta kamar yar dambe ta dinga bugun kirjin shi da karfi, duk da hakan bata huce ba sai da ta gartsa mashi ciwo har sau uku akan fatar bayan sh

Ko kaWan baiji zafin abun da tayi mashi ba, ya fahimci irin radadin da taji na rashin shi yasan tayi tunanin Ya koma kurkuku ne. Cikin shesshekar kuka take fada mashi abunda ya faru bayan tafiyar shi.

Zuciyar shi ta karaya ya kara jin tsantsar kaunarta da sonta acikin zuciyar shi, yadda takusa salwantar da rayuwarta saboda shi! Duk da fushin da take da shi na abunda ya faru tsakaninsu hakan baisa ta daina damuwa da shi ba, kamar ma ana kara mata zazzafar kaunar shi.

yayin da yake wannan tunanin idanunshi sun cicciko tab da kwalla a hankali yake kallon hannuwanta dake akan kirjin shi ta gama naushin nashi yanzu tsunkulin kirjin shi ta ke yi duk fa don ta huce radadin daya kunsa mata, zuciyar shi tayi matu?ar karaya saboda tausayin rayuwarsu daya kama shi, yana jin tsoron ranar da mutuwa zatayi masu yankan kauna, yasan dole wata rana Waya ya riga Waya mutuwa acikin su, fatanshi Allah yasa in ma mutuwarce ta fara daukar shi saboda baisan yaga mutuwar Unaisah, ko ma ta Wauke su atare saboda yasan ba lallai ta iya surviving batare da shi ba, yana Waya daga cikin dalilin dayasa yaki yarda ya bada hadin kai saboda shi ya san me zai biyo baya.

Lumshe idanun shi yayi yayin da siraran hawaye suka fara yar tseral kan kuncinsa, shesshekar kukan ta da yake ji a kunnansa ba karamin karya masa zuciya ta ke yi ba.

Sai da tayi mai isarta, tayi shiru tana kara makalkale jikin shi yana jin duk wani motsinta a jikinshi harta bugun zuciyarta da dumin jikinta duk yanaji anasa jikin..

In a weak voice ta fara magana taja jan numfashi

"Ban hana ka tafi duk inda zaka je ba, amma ka fara tunanin wani hali zan shiga kafin ka yanke shawarar tafiyar, sannan in ma zaka tafi toh ka tafi dani, idan ba haka ba zan hadiyi zuciya na mutu ne"

bata kare maganar ba, yai saurin ruko hannunta acikin nashi ya janyota ta dawo ta gabanshi yayi saurin rungumeta tightly a kirjin shi kamar zasu koma mutun daya.

hijab din jikinta ta ji?e sharkaf da gumi kamar babu a.c adakin tsabar hucin da jikinta keyi mata ba, da alama Unaisah ta manta da hudubar aunty umminsu ta kuma manta da sharuddan data gindaya mashi na kusantar inda take sai gashi yau saboda halin data shiga na gudun kada ta rasa shi yasa ta kunsata kanta da shi ta kuma rungume shi saboda tana bukatar jin dumin shi a jikinta, tausayinshi da kaunarshine suka rufe mata ido har tagaza gane abunda take badai dai bane ta manta.


Sunyi shiru babu mai magana acikinsu, ko motsi basa sonyi saboda yanayin da suka tsinsu kan su mai wuyar fassaruwa ji suka inama zasu dawwama ahaka sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi ko ba mutuwa akwai kaddara da zata iya raba su >?z?


Da wata irin kasala Yasa hannu yaja hijab din jikinta ta zame ta dawo kan kafadarta.

ya cusa hannunshi cikin lallausar sumar kanta ya nannaWeta gefe guda ya fiddo da kunnnata na dama.

Saitin kunnan ya daura tausasa red lips dinsa cikin sanyin murya mai dadin sauraro ya furta"kamar baki yarda da kaunar da nake maki ba? Meyasa zaki Waga hankalinki bayan kinsan cewa bazan iya rayuwa batare da ke ba, idan ma kina tunanin hakan toh ki daina...." ya faWa cike da bata tabbaci har cikin kunnnata take jin iskar numfashinsa..

"mutun yana rayuwane tare da ?addararsa sannan bai isa ya guje mata ba, nima haka take agurina, bazan taba tafiya nabarki ba in har bake kika bani iznin in tafi ba, ke kadaice zaki bani umarni in bi, gaba Waya burin rayuwana akanki ne da yan uwana, bazan ta6a rabuwa babu ku ba, duk runtsi duk wuya zan kasance atare daku"

bai ?are maganar ba ta tari mumfashin shi da cewa"ka yi hakuri da abun da ya Omar yayi maka, nasan shine ya bata maka rai, nima raina ya 6aci zanyi mashi magana yadaina bata maka rai" ta fada ba tare da ta dago kanta ba.


Murmushi ya danyi har cikin zuciyarshi yaji dadin maganarta shiyasa yake kara kaunarta saboda kaunar da take masa, zata iya bata mashi rai amma wani bai isa ya daga masa ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yatsa ta kyale shi ba.


"Ki kyale shi, ba laifinsa bane, ni ne na 6ata masa rai, komai ya faru ni naja ma kaina.."


Hankalin shi Yayi mugun tashi da abunda idanunsa suka gane mashi, tsabar kidima da tashin hankali har wani jiri jiri yake gani acikin idanunshi, da sauri ya dafe kofar dakin gudun kada jiri ya kwashe shi ya kife ?asa, Yayi danasanin zuwa dakin Danish dayasan zaiga abunda zai jijjiga
kwakwalwarsa da tashi hankali da baiyi gigin zuwa ganin Danish ba!.

Ya gaza yarda da abunda idanun shi ke nuna mashi da kuma abunda kunnuwanshi suke jiyo mashi.

Angel dinsa ce kwance ajikin namiji sun kankame juna kamar anta da jini? Wlh bai ta6a zaton zatay mashi haka ba, ta karya zuciyarshi ba kadan ba.

bazai juri kallon su ba, adaddafe Ya juya yabar kofar dakin dama yazo ne donya ga Danish Chief ne Ya bashi labarin sun ganshi, bawan Allah da farin cikinshi ya zo don ya bashi hakurin abunda big guy yayi mashi ashe da rabon yaga abun da zai hana shi runtsawa adaren yau.

shi mamakin shi tayaya Unaisah har tasan dadin ta rungumi namiji? A tunanin shi batai wayon da za ta yi hakan ba, bayan haka yana yi mata kallon mai hankali bai ta6a zaton zatay abunda tasan haramun ne ba.

yana tafiya kamar zai kife kasa saboda jirin dake shirin kwasar shi, babban tashin hankalinshi ya zaiyi ya raba ala?ar su? Saboda ya fahimci azababbiyar kaunace atsakaninsu ko romeo da juliet albarka, kai wannan har layla da majnoon sun shallake sai yanzu ya gane dalilin dayasa Wazu ta haukace tabi bayan Danish har mota takusa hankadeta ashe sone Ya makantar da ita.


shi azaton shi shakuwace atsakaninsu ashe shine bai fahimta ba, bakomai yake tunawa ba face alkawarin daya daukarwa kanshi na mallaka ma chief Unaisah, tun kafin ma ta bayyana ya bashi ita, sadakine kadai bai biya, ba yadda za'ay ma ya amince ma soyayyar Unaisah da Danish! Ko ta halin ?a?a sai ya raba su, bama zai ta6a yiwuwa ba, ay bata isa tasa shi zubda girman shi ba, bare aje ga batun bashi kunya.

Acikin zuciyarshi yake ta sambatu kamar wani zautattace.


Peck ya manna mata akan forehead dinta ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu yana ratsa tsigar jikin ta.

numfashi ta Wanja tare da sauke shi kan kirjin shi iskar ta daki fatar shi.

tana kokarin Wago da kanta kamar daga sama tajiyo muryoyinsu Batool daga waje suna ambaton sunan Danish a ruWe ta raba jikin ta daga nashi tayi saurin komawa bayan curtain ta 6oye tana faman sauke ajiyar zuciya.

Bin labulan yayi da kallo baiso suka katse masu hanzarin su ba, murmushi yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba, daga gani yaji dadin faranta masa rai da tayi.

Kamar an korosu suka fado dakin ko sallama babu, da karfin suka hada baki gurin furta"Danish"! Juyowa yayi tare da kallonsu, gaba Wayan su ne babu wanda babu acikin su.

Wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskokinsu, bayin Allah tun da suka dawo daga headquarter tashin hankalin bacewar shi Ya hana su canza uniform din jikinsu ko wanka ba su yi ba.

harya motsa lips dinsa zai yi magana bai yi aune ba gaba daya suka nife shi suka fada kan jikinshi kamar zasu kayar da shi kasa, saboda yadda suka baibaye shi kamar ?udajen zuma, gaba daya sautin kukan su ya cika dakin nashi.

dayasan halin da zai jefa su da bai tafi yabarsu ba, a zaton shi sun daina damuwa da shi ashe har yanzu ba abun da ya sauya na daga kaunar da su ke yi ma shi.


Dakyar ya samu suka kyale shi cikin shesshekar kuka suka fara korefe korafe akan tafiyar da yayi yabar su.

Haris daya fara zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu kowa yana fada masa irin tashin hankalin daya shiga, murmushi yadinga sakar masu kamar zaiyi dariya saboda sun bashi nishadi sun kuma faranta ranshi, ita Batool da tafi su jin jiki pillow ta dauko ta fara buga mashi kan kirjin shi aikuwa kamar jira suke gaba daya suka fara wasa da pillows suka dinga kwala mashi ta ko'ina.

tun yana murmushi yana kokarin kare kanshi harya fara ti?ar dariya kamar sakarkaru haka suka saki baki suna kallon shi cike da mamakin ganin Dariyar shi.

Duk abun da ke faruwa akan idon Unaisah gaba daya ta shagala da kallon fararen hakoranshi masu kyau da tsari sai dariya yakeyi kamar zai sha?e.

ba su kyale shi ba har saida ya faWa kan gadon shi yana fadin ya isa haka na kar6i laifi na bazan kara tafiya nabarku ba.." jefar da pillows din su ka yi kan mattress din sai haki suke suna kallon shi sun kewaye gadon shi.

"Waya faWa maku na dawo" ya tambaya yana kallon su,

Atare suka hada baki gurin furta"daddy Taj"

"Banyi zaton kun damu dani har haka ba..." bai kare maganar ba suka fara naWe hannayen shirts dinsu alamar zasuyi bugu dabi'arsu ce tun a prison..

"Ku kyale shi ya gane kuskuranshi" muryar Unaisah ce ta dakatar da su, atare suka jiyo tare da kallon ta, tana tsaye atsakiyar dakin duk a tunaninsu daga waje ta shigo ba su san cewa tana la6e jikin labule ba.

Haduwa sukayi gaba suka zauna gefen gadon shi, ba zasu iya tuna when last suka nishadantu da Danish irin na yau ba, ya sakar masu fuska sun yi fira cikin raha sunyi nishadi kamar lokacin da suke a prison.


Jin shiru Unaisah bata dawo ba, tun da tace ta jira har yanzu bata ji duriyar ta ba, gajiya tayi da zaman dakin shiyasa ta fito don ta neme ta, sai kuma ta taras babu su a falon har zata juya idanunta suka sauka akan taj dake zaune kan sofa ya zabga uban tagumi kamar wanda ya rasa mafaWi a duniya, tun daga kan yanayin fuskarshi ta fahimci babu lafiya atare da shi, kamar akwai wani abu na damun shi.

Karasawa tayi gaban sofa din da yake ta ambaci sunan shi shiru bai tanka mata ba, har saida ta maimaita kusan sau uku na karshen ne ta Waga murya a Wan firgice ya dago da ido ya kalle ta, murmushi tasakar mashi, da sauri ya fara kokarin danne damuwar shi ya Wan saki murmushin yake yace"Ummi ya kike, kin wuni lafiya" bata amsa mashi tambayarba sai cewa tay"yalla6ai meke damunka ne? Kusan sau uku ina kiran sunanka baka amsa min ba, anya lafiya" still da murmushi akan fuskarshi ya furta"ummi ba komai lafiyana lou, ba abun da ke damuna"

Tunani tayi kodai rashin Danish ne yasa shi shiga halin damuwa hakan yasa tace"Ya mukaji da abun da ya faru na 6atan Danish? Wlh nima Wazu Batool ke fadamin, Hankalina ya tashi ba kaWan ba.." bata kare maganar ba taj yace"oh bakisan An gan shi ba..." waro idanu waje tayi"dagaske"?

"Eh, ay yanzu haka su Unaisah suna acan dakin shi" wani irin ihun farin ciki ta saki tare da firta Alhamdulillah kusan sau uku tace"wlh naji dadin ganin shi da akayi, saboda hankalina ya tashi musamman ganin yadda yan uwanshi suka gaza cin abinci saboda rashin shi.

"bari naje naganshi" har zata jiya taj ya kira sunan ta tajiyo ta dube shi.

"Idan kin shiga dakin, pls ki kirasu, su zo su shirya akwai baki da zasu zo bayan sallar magbrib"

amsa mashi tay da toh, zumudin son ganin Danish Ya hana ta tambayi su wanene bakin da sauri ta juya ta nufi upstairs.

Bin ta da kallo taj yayi har ta 6ace ma ganin shi, sunkuyar da kan shi ?asa yai kamar bawan dake neman gafara, abun duniya ya ishe shi tun dazu bakin cikin abunda yagani yake ta nanukarsa, idanunshi sunki daina tariyo mashi abun takaicin daya gani....


Lokacin da takarasa bakin kofar dakin tunkan ta shiga ta fara jin hayaniyarsu yadda kasan gidan biki ko suna sun cika ko'ina da surutun su.

knocking kofar tayi almost 3 times ba wanda ya buWe mata, zafin dumi Ya hana su ji bugun kofar, murmushi tasaki tare da tura ?ofaf ta shiga ciki

Tsayawa tayi tare da goya hannayenta kan kirjinta tana kallon ikon Allah sun cike dakin shi, wasu akan couch wasu gefe gadon shi har saman gadon.

ta fahimci yau ba karamin nishadi suke ji ba.

Kokari take ta hango Danish din duk sun rufe shi dakyar idanun ta suka hango mata bayan shi ya kifa kanshi jikin pillow, Unaisah tana kishingiWe gefen shi sun shagala da kallon juna, sun bar su Batool sai Wumin surutu suke .

Yanayin fuskartane Ya canza zuwa tsantsar mamaki da rudani, tun da take rayuwa agidan bata ta6a lura da zanan tottoo din shi ba, tasan yana da shi amma bata ta6a ganin dukanshi ba, sai yau datayi arba dashi babu riga a jikin shi, abunka ga farar fata zanan ya fito 6aro 6aro bakomai ne ya rudar da ita face ganin zanan tattoo dinsa sak irin na big boss kamar anyi copying tattoo din big boss an manna mashi abayan shi.

wannan abu ya bata mamaki har ta gaza yi masu magana saboda kallon Abun al'ajabin daya ruke ta..

__________________________=ؓ?
'?

Safa da marwa take yi atsakar dakin ta, fuskarta babu walwala ga dukkan alamu akwai wani abu dake damunta wanda yayi silar shigarta halin da take a jiki...

Sallamar dr shureim ce ta katse zancen zucinta, kamar dama jiran shi takeyi da sauri ta nufe fuskarta ayamutse tace"shureim fita zaka yi ne"?
Girgiza mata kai yai"a'a, wurinki nazo inaso muyi magana ne" ya fada tare da wuce ta ya zauna gefen gadonta, itama ta zauna tana kallon shi cike da son jin wata magana ne zasuyi....

"Meke damunki ne? Yanayin fuskarki ya nuna kamar bakya jin dadi"?
"Shureim lamarin Benazir yana Waga min hankali, kai baka lura ba har yanzu da yanayin ta ba? Wani lokaci tana abu kamar mai ta6in hankali ni tsorona kada ta haukace..." ta faWa sukuku babu walwala,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login