Showing 45001 words to 48000 words out of 391264 words

Chapter 16 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3525

kirjinsa sai kallon su ya ke yi, hankalin ya kwanta babu sauran damuwa.



"Toh, ni ma dai bari na dauki nawa ?an matan" hajiya madina ce tayi maganar da fara'a akan fuskarta ta ruko hannun Parveen da na hannah, ta nufi wurin zaman su da su, gaba daya sun koma ciki, hatta su Hajiya saratu kowa Ya koma mazaunin su wasu suna daga tsaye har yanzu hankalin wasun su bai kwanta da yaran ba, Abunne ya daure masu kai sun gaza samun sukuni a fakaice su ke satar kallon su.



Tuni Daddy sharafudden yayiwa sheikh Imam mazauni a wurin su, umarni aka bawa servers din dake awurin akan su kawo masu abin da zasu ci, nan fa suka fara aikin jera masu abinci kala kala da abin sha sha?e da table...



Wata irin nauyayyar zuciya jemimah take ta faman saukewa, mom turai da sir mubarak sun tasa su agaba sai faman tarairayarsu su ke yi, kamar ?a'?an cikin su.



"Me ku ke son ci"? Cikin kulawa tayi masu maganar.



Jemimah ce tai kokarin bude baki tace"komai ma muna ci" murmushi mom turai tayi, ba karamin burgeta su ke yi ba,



"Ko kin lura yaran nan suna kama da ke? Kamar ?annan Jazz saboda sunyi kama da shi kan shi" murmushi tayi tana kallon Sir mubarak da yayi maganar.



"Nima nayi mamakin kamannin mu" ta fada idanunta akan fuskar Jemimah da azeeza, wadan da tuni suka fara cin abincin da aka kawo masu.



6angaren Su Hajiya saratu kuwa, sun kasa sun tsare sai jifar Parvin take yi da wani kallo mai wuyar fassaruwa, dama su biyune hajiya madina takai su tebur din su, ita da hannah wadda jikin ta keta kerma

"Baki da lafiya ne"? Hajiya laurane ta jefa mata tambayar fuskarta a yamutse, girgiza kai Hanna tayi, ta6e baki tayi"to meye kike ta kermar jiki! Tun da kun riga da kun samu wurin zama, ay sai ku saki jiki kuma ku kwashi arziki" ta fada tana hura hanci.



"Please ni ban kawo su nan da agaya masu magana ba!" Hajiya madina ce ta fada tana mai nuna 6acin aranta, kafin ta mayar da dubanta ga su parveen



"Ku ci abinci mana" da sakin fuska tayi masu magana, parvenn kamar jira takeyi aikuwa ta dauki glass of juice ta fara sha, tana shanyewa ta soma cin fruit salat, bayan ta gama ta koma tana cin spring rolls, Wan zaro idanu hajiya saratu tayi tana kallon ikon Allah, yadda kasan irin kwancen yunwar nan,

Hajiya laurat tace"ba banza ba naga tayi kama dake ashe itama din acici ce" ta fada da zolaya tana yar dariya, parveen dai ko kallo basu ishe ta ba, ta dage damtse komai ci take, har kwara hannah a hankali take dan cakura tana ci

"Wai ni ka Wai ce nake mamakin kamannin yaran nan da family din nan"? Hajiya madina ce tayi maganar,

Hajiya saratu tace"hmmm, ay ni abun ya gama Waure min kai, har yanzu zuciyata ta gaza samun nutsuwa, na ruWe musamman dana ga yaron nan mai kama da hateem" lumshe ido Hajiya laurat tayi tunawa da surar shi don ba karamin tafiya yayi da imaninta ba.



Hajiya muhibbat tace"na girgiza da ganin shi, lokacin da mujeeda ta cire masa mask din fuskarshi araina sai da nace wannan kyau haka kamar Wan sarkin aljanu? Dariya su kayi gaba dayan su



"Ay tun da nayi mashi kallo Waya na kau da ido, saboda wannan kyan nashi kadai ya isa yasa mace fadawa ga halaka" acewar Hajiya laurat



"Ina kananun Yaran nan ?an mata masu kama da tagwaye, wlh yadda kukasan Hajja turai tayi kakin su, ?aramar fuskarta da komai kalar nasu ne, sai kuma wani mai kama da hajjaty kamar anyi photo copy din fuskarta acewar Hajiya mudeena.



"Nima na lura da su, amma fa ni duk ba wannan ba, Yarinyar nan ta burge ni, kwarin gwiwarta ya tafi da imani na....".hajiya muhibbat ce ta yi maganar tana kallon can cikin hall din inda su unaisah su ke



Duk wannan suratan da su ke yi, akan kunnan su Parveen sai dai sam basa ganewa hankalin ta na kan abinci ci, hajiya saratu sai faman satar kallon ta ta ke yi afakaice, tun parven bata lura ba har dai ta gano ta, da zarar ta Wago suke haWa ido da juna.



_________________________=؞?



Gyaran murya Zaki yayi masu, a tare su ka dago suna kallon shi,



"Kunyi shiru baku faWa mana sunayen ku ba"



Murmushi sajeed ya Wanyi



"Ni sunana sajeed, shi kuma Wan uwana Sunansa Naufal"



"Masha Allah, It's a pleasure to meet you both, I hope you will feel at ease with us, sannan ku dauka tamkar ?an uwan ku ne mu" jinjina mashi kai su ka yi alamar eh.



"Okey, Yanzu ina so ku bani mamaki, ku cinye wannan abincin da nasa aka kawo maku" dariya su ka yi gaba Wayan su, har cikin ransu sunji dadin tarbar da zaki yayi masu.



Nan fa suka saki jiki suka soma cin abinci.



?agowa zaki yayi tare da kallon Su captain, yayi mamakin ganin yadda suke dogon wuya suna le?en table din su unaisah.



Da zolaya yace"kun dai ji kunya wlh, ina ajin naku yake"?



dariya ziyad yayi yana fadin"wlh yarinyar ce ta tafi da imanina, ni ka gane bawai sonta nake ba, wannan ay tafi karfin Wan jarida, kawai dai kamar nasan fuskarta, sai dai narasa gane a ina nasanta, abun ya shige min akaina...."



Da?yar captain Yaseer Ya janye idonsa daga kan fuskar Unaisah.



"Nifa ina ji zan canza she?a ne, wlh ko da dukiyata zata ?are ne akan neman waccan yarinyar saina jaraba sa'ata..." justice na murmushi yace"karka soma wlh, domin kuwa iskace zata wahalar da mai karan kara, ay ni tun daga kan kallon dana ga chief yanayi mata raina ya bani cewar da akwai wata a?asa"



Kwa6e fuska captain yayi"kana nufin yana sonta"? Dage mashi gira Justice yai.



Yatsina fuska yayi"again, bayan ya kwace nazli, ga kuma wata, mata biyu kenan zai aura!"



"Ni duk ba wannan ba ma, ganin yaron nan mai suffar lu'u lu'u yaWan girgiza ni, wai ku bakuyi mamaki ba? Ziyad ne ya fada.



"Ay mamakinne yasa ka ji munyi shiru da zancen shi, domin kuwa kwakwalwa zata iya daina aiki" dariya su ka yi jin abun da Justice yake fadi.



"Gaskiya nayi mamaki ace wai yaron nan a daji aka tsince shi, ay hankalima bazai dauka ba, kai daga ganin zubin halittarsa Wan wani ne, shiyasa nifa gaba Waya na ruWe da lamarinsu, kaina a duhu yake, kamanninsa sun 6aci da Uncle Hateem kamar yayi kakinsa kuma gaskiya ina kishi da shi Allah" captain ne ya fada.



Sajeed dake sauraran su murmushi ne dauke akan fuskarshi, Naufal Kuwa gaba Waya ya rasa nutsuwarsa saboda kallon da hajjaty take mashi, Da zarar Ya Wago da idanun shi karaf suke sauka acikin nata, saboda shi ta baro wurin da take ta dawo kusa da table din dake fuskantar nasu ta zauna tana ta kallon shi, ko kyaftawa babu.



Cikin muryar raWa yace da sajeed "waccan matar sai kallo na take yi kamar zata haWiye ni, ta?i bari naci abinci cikin kwanciyar hankali, bansan me na tsare mata ba, ni fa duk na tsorata" da sauri sajeed ya saci kallon inda naufal ke nuna masa ganin hajjaty yasa shi yi ma naufal rada"ka kwantar da hankalin ka, saboda kana kama da ita ne shiyasa take kallon ka" ya fada yana ?ar dariya, shi dai naufal hankalin shi ya?i kwanciya, kamar anyi mashi dole ya kalle ta.



Hakanan take jin shi a zuciyarta, komai nashi sak kalar na yaron ta, bazata ta6a mantawa da suffar shi ba, abinne ya daga hankalinta, ya kuma tada mata tsohon Ciwon dake kwance a cikin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face yaronta da ta rasa tun farkon zuwan su nigeria wannan wani labari ne wanda sai nan gaba kaWan zamu ji shi...>?z?



Dr jazz sai Rawar kai yake yi da su Haris, kamar kannansa, Ya tasa su agaba shi da ibad sai fira suke jan su da shi.



"A cikin ku wanene Haris"? yai tambayar yana duban su, da yake yana fuskantar su, da sauri Javed Ya nuna haris," Wan zaro idanu Dr jazz yayi"masha Allah, kaine haris kenan"? Jinjina mashi kai haris yayi alamar eh, da biyu ya tambaye shi saboda yasha jin labarin shi awurin deeja, tana yawon yin sambatun sunan shi idan haukan ta ya motsa.



Ru?o hannun shi yayi a cikin nashi yana fadin"kun burgeni, ina kaunarku, ganin ku kawai da nayi kun kwanta min arai na" murmushi kowan nan su ya saki.



"Wlh nima Na kamu da kaunarsu, dan Allah ku dawo gidan mu da zama, dama ni bani da abokai a nigeria" ibad ne yayi maganar da yar shagwa6ar shi.



"Kun ?i sakin jiki damu, ko dan baku san mu bane" kallon juna haris da javed su ka yi, sufa basu saba mu'amala cikin mutane ba.





"Okey, yanzu bismillah mu fara cin abinci"



Atare suka soma cin abincinsu, jefi jefi Dr jazz yake satar kallon Haris Aranshi ya ayyana duk ranar da khadeeja ta yi tozali da shi ba karamin hauka zatayi ba.



"Yaya jazz, wadancan twins din sunyi kama da mommy da kai," ya faWa yana nuna su azeeza.



Murmushi jazz yasaki shi kanshi ya kamu da kaunsarsu, tun dazu yake ta faman satar kallon su, ji yake tamkar kannansa na jini.



"Please Ya jazz mu yi wa daddy magana, akai mana su gidan mu, ni wlh bana so suna kuka, kaga mom saratu da waccen tsigai din ko ina ruwansu da rayuwarsu, ni fa shiyasa bana son zuwa nigeria saboda su, ko gajiya da masifa basayi, ina ruwan su da ?addarar rayuwarsu? Su ne suka tsara ma kan su ne? Ni fa kaganni ya jazz ba ruwana da shiga sabgar wani ko in wulakanta sa, wai don basu da asali, sai kace an gaya masu daga sama suka fado, mutun dai ay sai an haife sa yake xuwa duniya ba daga sama aka wurgo saba, balle ace da rashin asali aka haife su," Rai a6ace ibad yakeyin maganar da zallar shagwaba.



Su haris sun saki baki suna kallon shi, komai nashi burge su ya ke yi, ganin suna kallon shi ne yasa shi dakatawa da maganar yana yar dariya yace"na cika ku da surutu ko"? Girgiza mashi kai su ka yi alamar a'a.



Hankalin Zahra Ya?i kanciya, bakomai ne yajawo hakan ba face Unaisah, ko kwanto takeyi kamar tasan ta, sai dai takasa gane a ina tasan fuskarta, sai yanzu ta samu damar kare mata kallo daga inda take azaune, duk wani motsin unaisah akan idon zahra, ta kwallafa rai akan son yin magana da ita dama kawai take jira....



Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin nauyin haWa ido da chief ba, tun da suka zauna ta sunnar da kanta tana wasa da yatsun hannayenta, ?amshin turarensa gaba Waya ya cika mata hanci,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? duk wannan abun da take yi chief owais na lura da ita, da yake suna fuskantar juna da shi, wayarsa ce ru?e a hannunsa da yake daddanawa cikin nutsuwa.



Ga jerin kayan abinci da aka sha?e masu table da shi amma takasa ci, ga yunwa tana ji.



Gyaran muryar da Hajiya Malikat tayi masu ne yasa suka dago a tare suka kalle ta, tana daga zaune gefen chief



"Nasa an kawo maku abinci kun ?i ci, meyasa?"cikin kulawa tayi ma su maganar.



Murmushi suka dan saki suna faman no?e kai.



"Ko dai Kunyar Chief ku ke ji" kamar ta shiga zuciyar su, murmushi tayi ma su



"Ku ci mana, hankalin shi ba akanku Yake ba"



Batool ce ta fara cin abincin ganin zata sanya hannu yasa hajiya malikat cewa"ki Wauki tsokali" muryarta na dan rawa tace"ban iya ci da shi ba"



"Okey, nagane ki sanya hannun"

Hannu tasa ta soma ci, unaisah kuma ta Wauki glass na lemu tana Wan kur6an shi sama sama take satar kallon fuskar chief owais da zarar taga zai Wago da idanunsa take yin saurin kau da nata gefe Waya, bakomai ne yaja hankalin ta gare shi ba, face kamanninsu da Danish, kusan komai nasu iri Waya banbancin su kaWan.



Mai girma sharafudeen ne ya nufo wurin su, fuskarshi da fara'a Ya samu wuri ya zauna yana dubansu, da sauri suka gaishe shi cikin girmamawa ya amsa masu.



Duban owais yayi"baka cika min alkawari na ba" ya faWa yana Wan haWe fuskarshi.

Dagowa chief yayi tare da kallon daddyn nasa, da alama bai fahimci me yake nufi ba

"Maganar da mu kayi dakai Wazu da safe"

Sai yanzu ya fahinci inda zancen daddyn nasa ya dosa.



A hankali ya Waura idanunsa kan Unaisah dake kur6ar lemu.



Murmushi hajiya malikat tayi



"tubarakallah Masha Allah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina da lafiyana, gani ga second in-law Wina, yarinya mai hankali da nutsuwa, ni dai surukan nawa duk kyawawa ne, ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa...." amsa mata yai da ameen.



Ga dukkan alamu unaisah bata fahimci takan zancen ba, ta dai ji ana zancen suruka, Ru?o hannunta daddy Sharafuddeen yai a cikin na shi fuskar shi dauke da murmushi yace"I'm so happy to meet you, my daughter-in-law, I don't even know how to describe the joy I feel just from seeing you today"



murmushi tasakar masa har dimple din ta lotsa, duk da batasan wanene shi ba, ranta yana bata cewar Mahaifin Chief ne saboda kamannin su da ga gani.



Muryarta cike da jin nauyin shi ta furta"nima naji daWin haWuwa da kai,"



"Shekarunki nawa ne"? ya jefa mata tambayar.



"Sha shida amma na kusa shiga ta sha 17"

A wayance Daddy sharafuddeen yace"Wonderful, Now, what about your studies?



Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta amsa mashi tambayar da yayi mata ba.



"Sorry kada daddy ya takura maki da tambaya ko"? Murmushi ta Wanyi masa.



"Inaso ne nasan me yakamata mu fara yi don tallafa ma rayuwar ki, ko ba haka ba" cike da rashin fahimtar kalamansa take duben shi, Hajiya malikat dake kallon ta murmushi ne dauke akan fuskarta, yarinyar ta kwanta mata aranta.



Chief owais ya nutsu yana sauraron su.



"Aure ko karatu wanne kika fi so a yanzu" waro mashi gray eyes dinta tayi da sauri ta sanya tafin hannu ta rufe fuskarta alamar taji kunya, hakan da tayi ba karamin dariya ya basu ba, hatta chief saida yayi murmushin gefen fuska.



Hankalin batool gaba Waya baya akansu tun da ta samu abinci take ta aikin ci.



"Kinyi shiru baki ban amsa ba" ya ?ara tambayarta, ?asa ?asa da murya chief ya furta"dad..." dakatar da shi daddy sharafudeen yayi"no kada ka shiga tsakanina da surukata, baby Angel ke nake sauraro," tayi mamakin jin ya ambaci nickname dinta, ba tare data buWe fuskarta ba tace"Aure zanyi kafin na cigaba da karatu"



Murmushin fuskarsa ne ya faWaWa da zolaya yace"ta kwana gidan sau?i, yanzu faWa min kina da saurayin da zaki aura ne ko babu"



da sauri hajiya malika tace"haba dan Allah, kabarta mana, miji ay ta riga da ta samu ko ba haka unaisa"? ?aga mata kai tay alamarh.



Duk wannan abun dake faruwa a tsakanin daddy sharafudeen da Unaisah akan idanun Nazli wadda tuni tagama cika ta batse ranta yayi mugun 6aci tamkar ta Waura hannu bisa kai tayi ihu, wani irin kishine Ya ziyarce ta ganin yadda chief owais yayi zaman shi a wurin yarinyar, tun zuwan su hall din bai tako yazo inda take ba, kamar ma baisan da zamanta ba.....

Bazata juri kallon su ba, mi?ewa tayi da niyar tabar hall din kamar daga sama muryar Faryat ta katse mata hanzarinta.



"sister Nazli, Ina zaki je ne bayan ba'a kammala taron ba"!



Ba tare da ta kalli faryat ba tace"bazan juri zama ba, sai nake ga kamar ba don mu aka shirya dinner din nan ba, because everyone's attention is focused on them. Daddy Ya tafi da wani wanda bamusan wanene shi ba and the chief is only paying attention to that girl." ta faWa tana nuna saitin inda unaisah ta ke da hannun ta.



Ru?o hannunta faryat tayi a cikin nata" Sister, ba ke ya kamata ki bar hall din ba! They are the ones who should leaves"



Girgiza kai Nazli tayi"no ni bana son hatsaniya, barina shi yafi min kwanciyar hankali"



Ta faWa tana kokarin kaucewa rukon da faryat tayi mata.



Sai dai taki bata damar tafiya

"Nasan menene ya 6ata maki rai sister, ba ke kaWai ba, mu ma ran mu ya 6aci da zuwansu saboda babu alkhairi atattare dasu, gaba Waya hankali Ya koma kansu, Amma ni na maki alkawarin zan kawar da yarinyar can daga hall din nan, indai hakan zai kwantar maki da hankalin ki, amma bai kamata ki tafi ba, ba zamu ji dadi ba" shiru Nazli tayi na Wan wani lokaci kafin ta Wan sauke ajiyar zuciya.



"What are you going to do to her I hope you won't hurt her."?



Shu'umin murmushi faryat tasaki,



"Don't worry sister, I won't hurt her. I'll just keep her out of sight until the dinner is over."



"Bana so a samu matsala faryat!"



'kawai kibar komai a hannu na, abun da nake so dake da zarar kinga babu yarinyar kiyi kokarin jan hankalin Yaya owais"



A hankali Ta furta Okey, fasa fita tayi da sauri ta juya ta koma wurin zaman ta.



Faryat kuwa ba karamin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login