Showing 195001 words to 198000 words out of 391264 words

Chapter 66 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2612

da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"?



Sunnar da kanta ?asa tayi

Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba"



GyaWa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya.



Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi.



Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye...



Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faWa maku, sannan ku ka kuma ?aurace wa saSon Allah toh ha?i?a Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haWi dayi mashi godiya

Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen...

Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun Waya da zai dinga kula da marwa"



shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki.



"Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ?yamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...."



cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ?yamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...."



Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.."



"Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..."



mi?ewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin....



Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin.



Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata.



"Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace"



tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ?irga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin.



Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata le?en asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta neW'



Amma duk da haka bata makaro ba, ta Wauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita!



"Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula

"Kiyi hakuri Kinji yar uwata, bana son ganin hawayenki, nasan kina jin yunwa bari na kawo maki abinci in kika kammala ci sai in taimaka maki kiyi wanka..." kifa kai marwa tayi jikin pillow ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita, zuciyarta ta karaya, a halin yanzu ba rayuwarta ta ke jima tausayi ba, rayuwar hajjaty itace abun tausayi....dakyar hajjaty ta shawo kanta har ta samu marwa ta daina kuka, da sauri ta mike taje kitchen donta haWo mata abunda zata ci.



___________________________________
'?





*Hajiya Saratu*



A zaune take kan mirror chair jikinta sanye da sleeping gown ta manyan mata, fuskarta sam babu walwala ta zabga tagumi da hannunta Waya bata jima da farkawa daga bacci ba, ko wanka ta gaza shiga tayi, saboda rashin kwanciyar hankali, duk bayan yan mintuna saita duba wrist watch din hannunta, lumshe idanunta tayi yayin da acan ?asan zuciyarta take tariyo maganganun da suka tattauna ita da Hajiya laurat a jiya, bayan ta taso daga office tsoro da fargaba suka hana ta dawo gidan, tace ma driver dinta ya wuce da ita aso villa acan suka haWu da hajiya laura tun daga kan yanayin fuskar Hajiya saratu ta fahimci babu lafiya akwai wani abu da yake damunta, bayan sun zauna a pool yard masu yi masu hidima suka kawo masu coffee da kayan marmari tace mata bismilla su fara sha, girgiza kai tayi alamar bazata sha ba, hajiya laura tace wai meke damunki ne? kiyi magana mana, a shirye nake da in taimaka maki don mu shawo kan matsalar, ajiyar zuciya hajiya saratu ta sauke tana faman yamutsa fuska ta kwashe komai daya faru dangane da ciwon marwa ta sanar da hajiya laura.



"Wallahi ina cikin tashin hankali, zama gidan ma ya gagareni, yanzu haka da kika ganni daga office ko gida ban wuce ba nayo nan don in fada maki halin da nake ciki"



Shiru hajiya laura tayi jim da alamun ruWani akan fuskarta tace"ni abunda bangane ba, kina nufin dare Waya ta farka da lalurar"?



Waga mata kai hajiya saratu tayi, al'amarin ya Waure mata kai

"Kuma an kaita asibiti?

"Bani da masaniya, amma bari na kira baba naji halin da ake ciki" tay maganar tare da curo waya ta danna ma baba obie bayan ya Waga, ta tambaye shi awani hali marwa take a ciki, ya sanar da ita abun da likitoci suka ce, tayi mashi sallama ta Wago ta kalli hajiya laura da tayi zugudum tana kallonta, ta sanar da ita abun da baba obie ya faWa mata, ga mamakinta sai taga hajiya laura ta saki murmushin gefen fuska takai hannu ta dauki cup of coffee ta kurba still da murmushi akan fuskarta, hakan ba karamin Waure ma hajiya Saratu kai yayi ba fuskarta a Waure tace"bana son iya shege meye abin murmushi aciki?



Yar dariya laura tayi"kwantar da hankalinki mutuniyata, kinsan wani abu"? Girgiza kai tay alamar a'a



"Wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba yarinyar nan marwa silar ciwonta yana da ala?a da aikin le?en asirin da kika sanya ta!! Hankali atashe Hajiya saratu ta zaro ido tana kallon laura aruWe ta furta"ban..ban gane me kike nufi ba?



"Ke yanzu har sai nayi maki bayani? Yakamata ki gane mana, kiyi amfani da brain dinki, ciwon yarinyar nan aikin asiri ne, wlh ture akayi mata, in ba haka ba taya za'a ce rana Waya mutun ya tashi da cutar kuturta sannan ba baki, ai ke daga ji kinsan Waura mata ciwon akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata le?en asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...."



Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba Waya tabi ta ruWe.



Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi Wan adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....."



Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"!



hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika ?iya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya Wauko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma Waga mata hankali, bata ta6a jin faWuwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita.



Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa sukuni wani irin tsorone Ya kamata babban tashin hankalinta kada hajjaty tayi silar kassara rayuwarta kamar yadda ta kassara rayuwar marwa ya ilahi abin ya Waga hankalin ta, ba ita ta runtsa ba adaren jiya har saida pravin ya dawo ya fara mata faWa akan rashin dawowarta da wuri, baiwar Allah saboda tsoro ta kasa mayar mashi da martani saima ta rungumeshi ta ?an?ame shi hakan ba karamin daure mashi kai yayi ba, yaja hannunta suka zauna gefen gadon ya tambayeta meke damunta cikin sanyin murya tace mashi bata jin dadin zuciyarta tsoro take ji saboda abun da ya faru da marwa shiyasa taki dawowa gidan..



murmushi pravin yasaki har cikin ranshi yaji dadin tsoratar da tayi saboda shi agurinshi damace ya samu da zai dinga juyata son ranshi, tun da ya gano lagwon ta, a daren ranar sai da ya biya bukatar shi da ita, son ranshi ta sakar mashi jiki yayi abunda yakeso dama ya kwana biyu bata bashi hakkin shi ba.



Bayan ta dawo daga duniyar tunanin ta mi?e tana zagaye Wakin tana tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin dole ta Wauki mataki! Ta tsani hajjaty fiye da yadda ta tsani mutuwartaW'



__________________________________
'?







Lokacin da Benazir ta farka daga bacci, da wata irin kasala ta buWe idanunta wadanda suka kaWa jawur muryarta na rawa ta fara ambaton sunan Angel mikewa zaune tayi kan gadon, hannunta Waya dafe dakanta, ga wata faduwar gaba da take ji



"Babyna! Where are you? Mami Ina Angel dina? Bata nan ne? dakyar ta iya saukowa daga kan gadon tayi mi?a haWi da yin hamma kafin ta fara baza ido tana neman Unaisah, ita kadai ce adakin, hajiya layla taje office din dr jazz domin amsa kiran da yayi mata.





"Angel! Angel! Can't you hear me calling you? Where are you?" Da karfi tayi maganar tare da nufar kofar toilet ta kwankwasa"pls idan kina ciki, Ki amsa min babyna kinji..." ta fada tare da kanga kunnanta jikin kofar, shiru taji ba a amsa mata ba, da alama babu mutun aciki, hakan yasa tay pushing door din ta shiga ciki tana bin ko'ina da kallo kwata kwata bata ga kowa ba, ji tayi kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu, gaba Waya tabi ta rude dama saida ranta ya bata cewar ba lallai ta ganta ba

Fitowa tayi daga toilet din, ta nufi bed dinta, ta zukunna tana le?en karkashin gadon don taga ko anan ta buya



Adai dai lokaci hajiya layla ta shigo dakin hannun ta ruke da takardar sallama kaitsaye idonta suka sauka akan benazir.



rass taji gabanta Ya faWi ganin yadda tabi ta ruWe tana ambaton sunan babynta, tuni taji hawaye sun ciko idonta sam takasa karasa shiga ciki saboda fargaban amsar da zata ba benazir idan ta tambayeta Ina babynta, batasan ya zatayi da ita ba, ga tsananin tausayinta da take ji.



"Mommy"! Muryar dr shurieim ce ta katse mata zancen zucin ta, aWan firgice ta juya baya tana kallonsu, a jere suka nufo ta su uku ne, Shureim da Alhaji ubaid tare da hajiya sarah fuskokinsu dauke da murmushi, dakyar ta haWiye damuwarta ta nufe su tana fara'a suka rungume juna ita da hajiya sarah bayan sun raba jikinsu, shureim Ya matsa kusa da mommynsu Ya rungumeta tare da manna mata kiss gefen fuskarta.



"Sannun ku da zuwa"



hajiya sarah tace"ay min afwa wlh banji dadi ba, jiya banzo na duba jikin benazir ba, ban kuma kira naji ya kuke ba" murmushi hajiya layla tay"kai haba ba komai wlh, ay kinama kokarin zuwa dubata, wlh kada kiji komai benazir tana cikin koshin lafiya.." tai maganar tare da kallon Alhaji ubaid dake kallonta, harara ta Wan watsa mashi afakaice saboda taji haushin rashin kiransu da baiyi ba jiya, cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri jiya bana jin dadin jikina ne shiyasa ban kira ba, naso ma inzo dubaku" ta6e baki tayi"ay kwara da kukazo gaba Wayanku, ga Benazir can tana neman yarta, kuma yarinya masu ita sun dauki abunsu, dama likita ne ya bada maganin bacci aka bata tasha kafin aka rabata da yarinyar yanzu gata can ta hargitsa dakin tana neman yarta"



Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Dr shureim yace"baiwar Allah, na tausaya mata, wlh dama saida naji fargaban zuwan ranar nan, gashi sun shaku da yarinyar"



Alhaji ubaid yace"yanzu ya zamuyi jama'a? ay ni nayi zaton ma zamu taras da su ashe har sun tafi, gaskiya banji dadi ba, ban ta6a haduwa da yarinyar ba balle inmata godiya ita da iyayenta da sukai mana halacci.."





Hajiya layla tace"wannan duk mai saukine tunda aneelah tasan gidan iyayenta, wata rana saimuje muyi masu godiya, yanzu dai muji da maganar benazir! Menene mafita"!



Hajiya sarah tace"ni nama rasa ta cewa wlh, amma ni aganina, abun da yakamata shine mu lalla6ata mu fada mata cewa daddyn yarinyar yazo ya dauke ta sun tafi mall, da anjima zai dawo da ita, saboda mu samu mu bar hospital Win da ita, in ba haka ba dakyar zata amince ta bi mu" gaba daya sunyi amanna da maganar hajiya sarah, atare suka nufi dakin, suna shiga suka isketa zaune gefen gado duk ta yamutse gashin kanta kamar na mahaukaci, ga fuskarta sharkaf da ruwan hawaye.



Atare suka hada baki gurin yi mata sallama, da sauri ta mi?e tana kallonsu, muryarta na rawa ta furta"mami! Ya shureim! Daddy! aunty Sarah! Ina babyna? Tana ina? Na duba ko'ina banganta ba! Dan Allah ku fadamin waya daukar min babyna? Wlh in har ba'a dawo min da itaba, zuciyata zata buga in mutu kowa ya huta"!



kusan atare suka haWiyi yawu kowa yasha jinin jikinshi, dakyar hajiya Sarah tayi karfin halin furta"haba Benazir? Meyasa zaki daga hankalinki akan yarki? Waya isa Ya rabaki da ita? Ki kwantar da hankalinki, Yarinyar nan takice halak malak.."bubbuga kafafunta tayi saika rantse da Allah batasan me take ba, bayan da hankalinta tsabar pretending ne



"Ni kawai ku fadamin tana Ina? Meyasa banganta ba"?



"Benazir, daddynta ne ya dauke ta, sunje mall zasuyi maki siyayya da anjima zai dawo da ita gida..." cike da fargaba hajiya layla tayi maganar, shiru tayi jimm na Wan wani lokaci kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya fuskarta ayamutse tace"mami dagaske Taj yazo nan? Shi ya dauki Angel dina"? Murmushi suka sakar mata, dr shureim yace"kwarai kuwa dagaske shiyazo ya dauketa.."



"Amma bai tambayeni ba? Ko ya daina sona? Ta fada tana zare masu eyes dinta



Alhaji ubaid yace"ya tambayeki mana, ay saboda ke sukaje yin siyayyar, yana son ya faranta miki rai.." wani irin tsallan murna ta daka tana dariya.



kallon kallo su hajiya layla suka jefawa junansu hankalinsu atashe, wato akwai gwarama idan suka koma gida taji shiru taj baizo mata da yarta ba.



"Mommy zamu jiraku a mota" dr shureim ya fada tare da kallon daddynsu atare suka fuce,

Badajimawa ba, saiga su sun fito tare da benazir har ta canza kayan jikinta ta maida kayan da aka kawota asibitin da su, a backseat na motar dr shureim ta zauna, yana agaba tare da alhaji ubaid, Hajiya layla kuma a motar hajiya sarah ta zauna, a jere motocin suka fuce daga asibitin.


Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.


Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright ? 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe page 40 Complete
by
Novels Elite Admin
September 03, 2024
Sponsored Link
Takun ?arshe
Ex-Prisoners=ؓ?

Gaba Wayan su suna zaune kan sofas na falo.

"Aunty ummi wai yaushe angel dinmu zata dawo gida ne? Jemimah ce ta faWa tana faman haWe fuska.



Sajeed yace"ni ma na damu da rashin dawowarta gashi tun jiya ko awaya bata kira munji muryarta ba.."



Batool tace"dan Allah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login