Showing 102001 words to 105000 words out of 391264 words

Chapter 35 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2591

damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ?ADDARA!




Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita, tasan halin mutumin nata.



Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A ?afa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake kaWawa



"Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"? da mamaki Tace A'a daddy menene"?

"Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" aWan ruWe ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye.



Har saida gaban ta ya faWi idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa harWe akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen ?afafuwansa ko takalma babu.





Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba.



Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai"



?ar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"?



"mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna"



kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai ?yale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ?ura.



A haka suka jera har suka ?araso ?ofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin kaWan ne amma fa Ya haWu, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An ?awatashi kamar A dubai.



Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata



Sai ?ara kallon ko'ina take tana Wan jinjina kanta, har cikin ranta ta ?ara jin ?aunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta.



"Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs.



A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna.



"Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa



"Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta faWa tana kwa6e masa fuska



Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba



"Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"?



"Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa



Ru?o hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau



"Shi ne Ya baka wannan"? ?aga mata kai yai alamar eh,



Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"?



Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya Waga muryar shi.



Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba.



"My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..."



kafin ta ?are maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya mi?e zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba daWewa zanyi ba"



Taj dake kallon su murmushi yai tare da ?arasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,'



Kamar kuwa yasan sbd shi Ya mi?e zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs.



A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nannaWe cikin bargo sai sharar baccin ta take yi.



watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba Waya ta ?an?ameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna"



Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta buWe idanunta waWanda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su kan fuskar Unaisah ta ?ura mata ido tana kallon ta, da tsantsar ruWani take binta da kallo, Itama unaisah kallonta takeyi cike da kewarta, ba zata ta6a mantawa da fuskar denejo ba, ta ?ara haske fara jawur da ita kamar ba'indiya saboda kyau, ga gashin kan nan nata mai tsayi baki wulik har gadon bayanta..



Muryarta aWan tsorace ta furta"wacece ke"? Mutun ko aljan"!



Dariya unaisah tayi cike da nishadi tace mata"Baki gane ni na"?



Waro idanu waje danejo tayi da ?arfi ta furta"ANGEL"



tuntsirewa unaisah tai da dariya tare da faWa mata ta sake rungumeta, daura hannayenta biyu tayi akan bayanta tana fadin"Ni ce, Angel dinki, ashe da rabon zamu sake haduwa danejo na" mamaki Ya hana danejo magana, da sauri ta tallabo fuskar unaisah da tafukan hannayenta, ta kura mata ido tana kallon ta batare da ta kyafta idanunta ba, ko amafarki taga fuskar Angel sai ta shaida ta, duk da ta ?ara girma a yanzu ta zama yar matashiyar budurwa, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta, da sauri ta kwantar da unaisah kan kirjinta, itama kukanne Ya kubce mata, sautin shesshekar kukansu duk Ya cika dakin, a hankali take shafa sumar kanta tana faman sauke ajiyar zuciya, Allah ne kadai Yasan irin kaunar da take Yi mata, taso unaisah, tayi kukan rashinta kamar zata zauce, muryarta kasa kasa ta furta"Alhamdulillah Ya Allah, nagode maka wallahi bazan Iya misalta farin ciki da nake aciki ba, Ya Allah nagode maka daka bayyana min Angel Wina, Ya Allah nagode maka...." cikin shesshe?ar kuka ta faWa, tama rasa inda zata tsoma ranta saboda murnar ganin Angel.



Wagowa unaisah tayi tasanya tafin hannu ta goge mata hawayen cikin sanyin murya tace"Aunty Danejo, naji dadi da Allah Ya sake haWa ni dake a matsayin matar daddyna, I can't thank you enough saboda halaccin da kikai min arayuwa Allah ne kadai zai Iya biyan ki, kin so ni kin kuma kaunace ni tsakani da Allah, duk da bakisan koni wacece ba a lokacin amma kin taimaki rayuwa, kiyi hakuri ki yafe min laifin da nayi maki....' tana faWa tana matsar kwalla.



"Angel laifin me kikai min? Ni ay baki min laifin komai ba...."

Girgiza kai tai hawaye nabin kuncin ta tace"nayi maki laifi, bayan mun sha?u da juna, na gudu daga rugarku kina ji kina gani har biyo ni ki ka yi kina kiran sunana don in tsaya amma naki sauraronki, ashe da rabon in sha wahala" idanunta acikin na danejo takeyin maganar



"duk da bana danasanin ?addarar rayuwar da ta riske ni saima farin ciki da nakeyi saboda a kowani rashi da nayi toh akwai nasara acikin sa" tun da tafara magana danejo ta nutsu tana sauraronta, har cikin ranta tana mai mamakin girman yarinyar da kaifin basirarta, komai nata na dabanne shiyasa take da saurin siye zuciyar mutune.



"Aunty danejo, Kinga ikon Allah ko? Bayan na tafi sai gashi Allah Ya hada ki da daddy na har kun yi aure, amma baki takura kanki ba babu danginki a kusa, ki bani labari ya kikaji da kika fara shigowa cikin burni" yar dariya danejo tayi kafin ta fara bata labarin irin yadda ta tsinci kanta farkon shigowarta birni, ta tabka ?auyanci taj ba karamin hakuri yayi da ita ba, saboda tsoro da rashin sabo da irin rayuwar birni.



Gaba daya suka kama yin dariya kamar wasu zautattu, Yadda kasan wasu aminnan juna.



"Amma dangin ki fa? Shikenan ba zaki sake haduwa da su ba"?



"Ay Yayi min al?awarin zai kaini rugarmu nan badajimawa ba" murmushi Angel tayi"amma naji dadi watakil nima in bi ki muje, in gano su hasiya da bawuro"



"Baki manta da sunan su ba" jinjina mata kai unaisah tayi"ban manta ba, na haddace su akaina"



"Dama kece bakuwar da zanyi"? Waga mata gira tai alamar eh.



"Daddynki Ya faranta min raina, naji dadin ganin abun da banyi zato ba, amma lokacin da kika gudu ina kika je ne , tayaya akai aka gano ki? Ta fada cike da son jin karin bayani.



"Ki manta kawai, nadai ci wahala amma komai Ya wuce, bana son tuna baya" jinjina kai tay alamar ta fahince ta.



"Ina daddyn naki yake"?



"Nabar shi a falo su biyu ne tare da Wan uwana Danish"



Ru?o hannunta tayi"muje falon" saukowa sukayi daga kan gadon atare suka fito



A lokacin Taj Yana zaune kan sofa tare da Danish, tun bayan tafiyar Unaisah hankalinsa Ya?i kwanciya, musamman da yaji ta daWe bata fito ba, taj Yaso Yaja shi da fira sai dai Ya?i bashi hadin kai, Jin motsin saukowar su down, yasa shi saurin kai idonsa ga dubansu, lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya ganin Angel dinsa.



Fuskar taj Wauke da murmushi yake kallon su, danejo kuwa tun da ta daura idonta kan fuskar danish gaban ta Ya fadi rass har sai da ta Wan dakata da tafiya saboda taji fargaban ganin masifaffan kyan dake gare shi, ganin ta dakata da yin tafiyar ne yasa unaisah yi mata gyaran murya tare da cewa"Shi ne dan uwana danish, kada kiji komai atare da shi muka zo"



jinjina kai tay kafin ta bi ta suka karasa saukowa down asaman sofa dake fuskantar su taj suka zauna, kowan nan su murmushine akan fuskarshi banda danish wanda hankalinsa ke akan unaisah.



"daddyn Angel, inatayamu murna cikin ikon Allah sai gashi Allah ya bayyana mana ita, amma meyasa baka fada min anganta ba"?



"Saboda inaso na baki mamaki" yar dariya tayi"wallahi ka bani mamaki kuma ka faranta min raina, ubangiji Allah Ya ?ara tsare mana ita daga sharrin makiya da mahassada dama duk wani abun cutarwa" har cikin ranshi yaji dadin kalamanta"ameen ameen, ga dan uwanta nan ku gaisa da shi" tun da tafara magana taki yarda ta kalli danish saboda tsoranshi da take ji, kallo Waya da ta masa kafin su sauko down ta gane ba shi kaWai ba ne.





Muryarta na dan rawa ta furta"eh ta fada min sunan sa danish, ya kake dan uwan angel, Ina fata kana lafiya" muryarsa kasa kasa Ya amsa mata da lafiya, ba tare da ya dube ta ba



"Amma daddy Angel ya kuke da shi"?

Taj yace"yanzu ba lokacin tambaya bane idan na samu time zan maki bayani, tashi muje kitchen mu dauko masu abunda kika shirya masu"



mikewa tayi taj yabi bayanta suka nufi kitchen





A hankali unaisah ta sanya idonta a cikin nashi, Murmushi tasakar mashi har dimple dinta Ya lotsa, sai yai tamkar baisan tana yi ba.



"Ba dai fushi kake da ni ba? Fadamin ko na bata maka rai na"? Ta fada tana Wage mashi gira wani kallon kasan ido mai kama da harara ya wurga mata



"Na fahimce ka, nasan bai wuci saboda na tafi na barka bane, ni narasa gane kishin da kakeyi akaina, sau biyu kana dukan daddyna, na farko ka jefa masa pillow daga upstair saboda yayi hugging dina, na biyu kuma ka Naushe shi da wannan kafcecen hannun naka saboda ya gyara min mayafina, next time inaga hannayensa zaka karya idan Ya ?ara ta6ani..." ta faWa tare da Waura kafa daya bisa Waya tana jifar shi da harara kallon kawai yakeyi bai tanka mata ba.



"?wara tun yanzu ka fara yi masa biyayya kana kyautata masa, saboda daddyna shi yake da ikon mallaka maka ni, Idan ba haka ba wallahi kana ji kana gani zai aura min...."



kasa ?arasa maganar tayi ganin yana nannaWe hannun rigarshi, ay tuni tasha jinin jikinta, damtsen hannunsa Ya fito fari sol ga zanan tattoo na tambarin kurkukun kaddara, adan tsorace tace"my man yanzu saika buge ni akan wannan maganar" banza yayi da ita babu alamun zai tanka mata.



Murmushi tayi tare????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? da kai hannu ta Wauki wayarta dake a jiye kan sofa inda tabar ta, a fakaice ta soma daukar shi video ba tare da sanin shi ba, saboda yayi mata kyau he looks so sexy cikin sleeping dress expecially da ya naWe hannun rigarsa zanan tattoo dinsa ya bayyana.



A tare Taj da danejo suka shigo falon hannayen su ruke da trays na kayan abinci, kafin su karaso tayi saurin ajiye wayar, ta yi ma danish alamar ya gyara hannun rigar sa, hannu yasa yaja hannun ya rufe damtsen nasa, bayan sun ?araso saman lallausan carpet din falon suka sauke masu farantan.



"Bismillah My daugher, inaso ki ba auntynki mamaki, Ki zauna Ki cinye abincin nan ke da dan uwanki Danish" murmushi unaisah tayi kafin ta sauko ta zauna.



"Malam Danish bismillah" ya faWa Yana nuna masa carpet din, sam baiyi niyar ci ba, amma saboda unaisah Ya sauko Ya zauna, shima taj din da danejo suka zauna suna fuskantar su, tuni kamshin abincin Ya karaWe hancin su, wani haWaWWen dambun Shinkafa ne ta zuba masu a plate, Yaji kayan kamshi ga nama manyan yanka da ta jera masu asaman dambun, ta tsiyaya ma su juice mai sanyi a cups, tun da suka fara cin abincin, Ta lura da yadda danish yake ci kamar zai fasa ?aramin bakinsa, da alama dambun yayi masa daWi, hatta taj da danejo satar kallon sa suke yi su kansu ba suyi tsammanin zai iya cin abincin har haka ba, bayan sun kammala cin dambun ta sake zuba masu farfesun ?an ciki, kamar masu fama da yunwa haka suka tasa shi gaba suka lamushe, ta kuma ?ara zuba masu gurasa haWi na musamman taji kuli kuli da kayan lambu da aka yayyanka ga mai dake kyalli asamanta tare da tsiren nama, danish bai ta6a cin gurasa ba sai Yau, kai harta dambun shinkafar yaune karo na farko daya fara cinshi, yaji dadin abincin har ?warar cikinsa yayi, Angel dake kallonsa sai faman sakin murmushi takeyi ba tare da ya lura da ita ba, bayan sun kammala cin abincin kowa yayi kulu wash rabu hani'an danejo ta kwashe kayan abincin ta nufi kitchen da su

"Daughter, dare yayi muje na raka ku gida, Kada chief Ya tuhume ni, kinsan yanzu bani da hurumin daukarki tun da a karkashin kulawarshi ku ke har zuwa time da zamu kammala bincike"



"Bakomai daddy, na fahince ka," shafa gefen fuskarta yai, danish dake kallon su tuni ya hade ransa, shi fa har yanzu bai daina kishi da taj ba, saboda baisan ala?ar dake a tsakanin iyaye da dansu ba.



Fitowa danejo tayi daga kitchen, ganin su tsaye yasa tace"ya akai nagan ku a tsaye ku zauna mana muyi firar yaushe rabo"



Taj ya ce"Zasu tafi ne" Waure fuska tay"bangane me kake nufi ba, nayi zaton ta dawo gida kenan," girgiza kai yai"ay tana a gidan amma a part din chief suke da zama, zata dinga zuwa kuna gaisawa da juna...." dakyar ya samu ya fahimtar da ita, atare suka raka su unaisah har gida kafin sukayi masu sallama.



Lokacin da suka shiga falon babu kowa har sun koma bedrooms dinsu alamar time din bacci yayi, kamar kar su rabu da danish har saida ta raka shi bedroom dinsa kafin ta dawo ta nufi nasu dakin, tana shiga ta samu deeja kwance kan gadon su sai jan minshari takeyi, murmushi tasaki tana kallon ta, har yanzu kwalliyar dazu ce akan fuskarta duk ta ca6e kamar ?ar mahaukaciya, ta jima tana kallon ta, kafin ta fara cire kayan jikin ta, ta musanya dana bacci, fuskarta dauke da annurin farin ciki, ta hayekan gadon, bata damu da rashin ganin batool ba, tasan bazata wuce dakin aunty ummin su ba, huggin pillow tai, Allah ne kadai yasan dadin da take ji sam ta manta da zancen kiran aunty pretty gaba daya tunaninta akan abun farin cikin daya faru yau ne



______________________________________
'?





Zaune ya ke kan sofa ya Waura ?afarsa Waya bisa Waya, yayin da idanunsa ke akan laptop din gabansa da yake operating lokaci Waya ya Wan dakata Ya jingina bayansa jikin Sofa haWi da lumshe idanunsa zuciyarsa a cike take fal da tunanin prettynsa har yau jiran hajiya laurat yake yi don jin amsarta, tun jiya bayan kammaluwar dinner din hateem ziyad ya nemi alfarmar yin magana da ita bayan sun ke6e cikin girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa daga bisani ya fara kora mata jawabi game da bukatarsu, lokaci Waya yanayin fuskarta ya canza zuwa 6acin rai kamar bata son zancen Benazir da yake yi mata, acikin ranta tayi mamakin jin cewa a hannun Zaki ta faWa ita sam ta manta da rayuwar benazir tamkar ma ba'a halicce ta adoron duniya ba, saboda tun fil azal hajiya laura basa ga maciji da hajiya layla wata irin gaba ce atsakaninsu shiyasa bata shiga shirgin abun da ya shafi layla, a lokaci shi kanshi ziyad ya lura da 6acin ran da take a ciki amma sai ta waske ta ?a?aro murmushi tana fadin Allah sarki benazir ashe dama zaki ne ya taimake ta? Alhamdulillah wlh nayi murna ziyad, sai dai abun da ya daure min kaina babu wanda Ya kirani daga gidan Ya fadamin cewa anganta amma in sha Allah zan fidda lokaci inje can gidan da kaina don in tabbatar ta dawo in yaso daga bisani zan tuntu6i shi zaki din...." akan haka suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login