Showing 24001 words to 27000 words out of 391264 words

Chapter 9 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2553

saurin tarar umfashinta da cewa"Karki kuskura ki?ara gigin Waga min waya idan an kira ni, babu ruwanki da wayata" lamarin ya Waure mata kai adabarbarce ta furta"laifine idan an kiraka na daga? Anya pravin kana da gaskiya kuwa saboda kawai na Waga wayarka shi ne ka fito tsirara daga toilet da ruwan kumfa a jikin ka"!

Harara ya galla mata"wannan bai shafe ki ba, Nidai ina ?ara jan kunnanki babu ruwanki da wayata, ban yi maki iyaka da komai nawa ba, amma banda wayata," Kallon tuhuma take jefa mashi, ba tun yau ba ya tsani yaga ta ta6a wayarshi kamar ta tsunkuli ranshi ne.

"Kallon Ya isa haka, ki tashi kije ki yi wanka" ta6e baki tayi kafin tace"ba yanzu ba, sai zuwa anjima idan zamu je dinner din Hateem"



?aure fuska yayi babu annuri ya furta"ay na faWa maki, bazan bari ki halarcin dinner Win nan ba"



"Amma dai dawasa kake min ko"?

"Na ta6a yi maki wasa irin wannan"?

"Amma meyasa zaka hanani zuwa bayan na riga dana kwallafa raina"? fuskarta a yamutse ta jefa mashi tambayar

Shiru yai bai tanka mata ba, taci gaba da cewa"bazaiyiwu ba pravin, matan family din nan gaba Waya zasu halarci taron sai ni kadai zaka hana zuwa"?

Gaban mirror ya tsaya yana gyara jikin shi,

"Dakai fa nake magana"?

Sai da ya mula yasha iska tukunna yace"abun da nakeso ki fahimta, zuwanki dinner din baida amfani! Saboda matan family din nan ba kaunarki su ke yi ba, iyakaci suci maki mutunci su zazzageki ni kuma abun da banaso kenan, sannan ni ina kishin kije wadannan dattawan masu gemu su kalle min ke"



Kwantar da kanta tayi jikin pillow

"Wannan ba hujja bace pravin, meya kawo maganar cin mutunci a taron bankwana da hateem kaima in banda abun ka, sannan kishi da kake ji ay bani kadai bace matar da zanje dinner din ba muna dayawa...." kafin takare magabar ya tari numfashinta da cewa"Amma ay ke kadai ce ba'asan da igiyar aure akanki ba, kowa kallon bazawara yake yi maki, uwa uba kuma surar jikin ki dake jan hankalin su"



Saukowa tayi daga kan gadon ta nufe shi, ta tsaya daga bayanshi tare da Waura kanta saman bayanshi.



"Hubbyna, dan Allah kada ka hanani zuwa, wallahi na ?wallafa raina akan dinner din nan, ka taimaka min pls nayi maka alkawarin zan kare mutunci na, indai ka yarda dani pravin kabarni inje' da shagwa6a ta ?are maganar tare da zagayo hannayenta kan waist dinsa tuni yafara jinshi a wata duniyar, ta san duk wata hanya da zata canza mashi ra'ayin shi.



Lumshe idanunshi yayi, yayin da yake kallonta ta cikin mirror, tsantsar sonta da kaunarta yake ji,

?ago dakanta tayi daga bayanshi ta daura kan kafadarsa ta hagu.



Suka ci gaba da kallon juna.



"Inaso ka faWamin tsakanin ni da kai waya fi kama da Wan mu"



Shiru yayi tamkar baison furta maganar ya ce "kin fi kama da shi"



Murmushi tasaki har dimple dinta ya lotsa



"Allah ya ji ?an shi" ya amsa mata da ameen.



Sumbatar wuyanshi tayi, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba

"Zaka barni inje babyna"?

Baiyi niyar barinta taje ba, amma yanayin da tayi mashi maganar yasa shi amincewa batare daya shirya ba.

Wani irin farin cikine ya lullu6eta shi kanshi ya shaida hakan

"Atare dakai zamu je ne"?

"No,ni ba lallai naje ba,"

"Amma yakamata kaje kaima zaiji daWi, kaga daga yau shikenan gobe ba lallai ka samu danar ganawa dashi ba may be tashin asuba jirginsu zai lula"

Janyo hannunta yayi ya dawo da ita ta gabanshi, yadda zaiji dadin kallonta dakyau

"Nima zanje in sha Allah"

"Bari na taimaka maka ka idasa shiryawa, nasan hajiya Saratu tana can tana dakonka, daga zuwa sallar asuba ka gudo dakina"

"Matar da bata damu dani ba, ni fa banda amfani awurinta... " bata bari ya karasa maganarba ta rufemashi baki, don bata son yana aibata hajiya saratu awurinta.



Shirye shiryen sun kankama, Don tun wuraren ?arfe tara na safe Zungureriyar motar kamfanin su zahra mai Wauke da tambarin Zahra World of beauty ta karaso estate din, kafin shigar motar sai da Security officers su ka yi mata wankan tsarki ciki da bai suka bincike komai da na'urorin tsaro, hatta Interior designers din dake a cikin ta ?an matasa mata sai da Sojoji suka bincike su from head to toe, suka tabbatar ba su shigo da wani abun cutarwa ba, kafin suka bar motar ta shiga ciki, Hajiya saratu ce ta tsara lokacin da za'a fara aikin decoration din dakin taron saboda friday ne kurarran lokaci kwara ay komai da wuri acewar ta



Masu aikin gidan kuwa tun asuba suka fara Waura girke girke, saboda uban aikin dake gare su, abinci ne za'a girka kala kala, Na ?abilu daban daban, kafin kace me cikin ?an?anin lokaci ?amshi ya gauraye ko'ina na gidan baba obie, don anan ake aikin girkin....



Hajiya zahra kuwa yau tsabar murna kamar wadda akaiwa albishiri da gidan Aljana, tun jiya akayi mata saloon da kunshi na jan lalle kamar amarya, taci buri akan dinner din nan kamar ranar auranta, Saboda son ta dau gayu na kece raini motar Aneelerh ta ara da yake tafi tata motar tsada da kyau, Tuni taba mahboob motar ta hada shi da ?an canji ya tafi kai ta wurin da za'a wanke ta don ta ?ara kyau, kowa na gidan sai da yasan da zancen zuwan Zahra Obie estate saboda ta addabi kowa duk bayan ?an mintuna sai ta kalli agogo burinta lokaci kawai lokaci ya ci ka....



?arfe 9 na safe, Zeenatu tana a zaune kan mirror chair, tana ?an shafe shafen ta, bata jima da fitowa daga wanka ba, jikin ta sanye da bathrobe mai kyan gaske, ta Waure gashin kanta

Fitowa benazir tayi daga toilet da alama itama wankan tayo, ta yi daurin gaba da towel, fuskarta babu walwala ta kumbura jawur da ita saboda kukan da tayi adaren jiya da abun nan ya faru

Ganin zeenatu dake ta shafa powder yasa ta Wan saki face din ta da zolaya tace"uhum su baby shuriem wa ake ma kwalliya" kunyar maganar Benazir yasa tayi kamar bata ji me tace ba

Gyaran murya benazir tayi still bata Wago ba, saima ta Wauki jan baki tana shafawa

"Wato kinyi imanin sai kin zautar min da yaya na"? Cak zeenatu ta tsaya da shafa jan baki, cike da jin kunyar benazir ta sunnar dakai ?asa

"Duk hasken da Allah yayi maki zeenatu har sai kin ?ara da powder in ban da asara, so kike ki koma zabayyana ne'? dariya ce ta kubce ma zeenatu har fararen hakoranta suka bayyana masu kyau da tsari

Muryarta ?asa ?asa tamkar ta mai yin raWa ta furta"aunty benazir mommy ma tana shafa powder in zata ma daddy kwalliya, shiyasa nima nake shafawa" dariya benazir tayi hadi da Wan girgiza kanta..

Wucewa wurin closet din dakin tayi domin shirya kanta, within minutes benazir ta fito asanye da riga da skirt sun Wan kama jikin ta

Gaban madubin ta tsaya daga gefen zeenatu tana fadin"naga abun naki bamai karewa bane, ki tashi ki je ki sanya kaya, kafin darling din naki ya farka daga bacci" cike da jin kunyar maganarta, zeenatu ta mi?e tana faman sakin murmushi sai da tafara daukar hijab dinta dake ajiye bisa gado kafin ta nufi hanyar fita dakin don taje nata dakin ta sanya kaya

Fitarta ke da wuya suka yi kici6us da dr shureim wanda ke kokarin doka sallama, tun da ya sauke idonshi akanta ya kasa janye su, cikin jin kunyarsa ta sunnar da kanta kasa tana faman no?e kai ta furta"yaya shurem Wina ina kwana, fatan ka ta shi lafiya.. ' ta faWa la66anta na dan kerma without looking at him

Gogan naka ya kasa magana saboda kyanta da ya dauke ma shi hankali

Muryar ta da shagwa6a ta furta ya shureim ina magana ka share ni...

Lumshe idanunsa yai yayin da yake shakar kamshin turaren dake fesowa daga jikin ta

Muryarshi can ?asa makoshi ya furta" nabd alqalb (F(6 'DBD() kin yi min kyau ban yi tsammanin idanuwana za suyi min tozali da kyakkyawar fuskar ki ba..." arude ta maimaita kalmar nabd alqalb ta dago tana zare mashi blue eyes din ta, muryarta na Wan rawa ta furta"ya shureim bansan me kake nufi ba"

Side smile ya sakar mata, tare da matsawa dab da ita, tamkar zaiyi mata raWa a kunne ya furta"Bugun zuciyata" farfari tayi da idanunta wani irin farin ciki Ya lullu6eta

Batai wanai aune ba taji ya manna mata sumbata saman soft cheek din ta' waro idanu tayi a ruWe ta watsa da gudu ta nufi hanyar bedroom din ta

Bin bayanta yayi da kallo tamkar yabi ta haka ya ke ji

"Yaya Shureim kaine? Yaushe ka zo shine baka min sallama ba" kamar daga sama yaji muryar benazir firgigit yai tare da dubanta

Yana kokarin bude baki yai mata magana karaf idanunsa suka sauka akan shatun yatsun hannun dake akan wuyanta ruWu rudu fatar wurin tayi dabra dabra jawur, gabansa ne yayi wani irin mugun faWuwa ji kake rass

Benazir bata lura da abun da yake kallo ba, gaba Waya ta faWa kirjinshi ta rungume shi haWi da manna mashi peck kan kuncinsa, irin gaisuwarsu ta larabawa

Idanunsa a zare yake kallon fatar wuyanta, kafin ya daddage ya Waura tafukan hannayensa kan kafaWunta ya Wago da ita

"Benazir! " da karfi Ya ambaci sunanta

"Me nake gani akan wuyan ki"? Ya jefa mata tambayar

Farat Waya ta gane me yake magana akai, da sauri taja hannun shi suka shiga dakin gudun kada wani yajiyo su

"Tambayarki nake yi kinyi shiru baki ce komai ba!" adan tsawace ya furta maganar

Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba, cikin shesshe?ar murya ta labarta mashi abun da ke faruwa tun daga rana ta farko da aka fara kawo mata hari

Ranshi yayi mugun 6aci na kin fada mashin da batayi ba,

In a breaking voice ya furta"shi ne baki faWa min ba"?

"Yaya shureim bansan wanene yake son rabani da rayuwana ba, bansan meke shirin faruwa dani ba, na 6oye maku ne saboda ban dauki abun serious ba, da farko nayi tsammanin mafarki ne, ashe ba haka bane so ake akashe ni yaya shureim bansan zunubin dana aikata ba.... ' ta ?arasa maganar tana faman shesshe?ar kukan, Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, ya gaza yarda da abun da idanuwanshi suke gane mashi

?aura yatsun hannayenshi yai akan wuyan nata ya shafa shi a hankali, runtse idanunta tayi saboda raWaWin da taji, ganin hakan yasa shi janye yatsun sa

Yama rasa tunanin da zanyi dangane da bakon al'amarin nan

Ruko hannayensa tai acikin nashi tana cigaba da kuka take fadin"yaya shureim ka tayani da addu'a, bana son in mutu ban hadu da mijina da ?ata ba, yaya shureim ka taimaka min idan ba haka ba wata rana za'a iya farkawa ataras da gawata, jiya ba don kiran da akayi min ba har sautin karatun al'kurni ya fita da tuni na jima da mutuwa... Bai bari ta ?are maganar ba, Ya toshe mata bakinta da tafin hannunsa

Kwantar da kanta yayi kan chest dinsa muryarsa kasa kasa yake ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un yayin da zuciyarsa ke dakan uku uku!!!

"Yaya shureim ko dai aljanune suke son kashe ni? Idan ba su ba to waye zaiyi min hakan a gidan nan? Babu wani bare a cikin mu, sai house maids da security officers, babu abun da ya ta6a haWani da wani daga cikin su, bansan su ba, balle har ace na aikata wani abu ne da zaisa a nemi rabani da rayuwana...... ' cikin jin kunar rai ta furta maganar.

"Yaya shureim dan Allah mubar gidan nan, dama saboda mu haWu da aneeleerh ne yasa na ?wallafa raina akan zuwa, tun da ban samu hanyar da zan hadu da ita ba, mu koma gida zai fi min kwanciyar hankali na...."

Tuni idanun dr shureim sun cicciko da hawaye, yai matu?ar girgiza da jin abun da ke faruwa da yar uwarsa tabbas yana ji aranshi wani abu ne ke shirin faruwa da ita, dole ya mi?e tsaye don ganin ya ceci rayuwarta



*(Mu haWu Jibi Alhamis Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya, Don jin Yadda zata kaya)*





*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


Kurkukun Kaddara
Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 11 Complete
by
Novels Elite Admin
May 26, 2024
Sponsored Link


_ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_

3,F 'DB/1=؋?
'

~Takun ?arshe=?%?~







B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??Best gifts for your loved ones





An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?Best gifts for your loved ones







Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'







__________________________
'?













Shafa sumar kanta ya soma yi cikin sigar lallashi ya furta"Allah yana atare dake, duk wani mai neman ki da sharri kanshi zai koma, bi'iznillahi bazan bari wani cutar min dake ba a karo na biyo, zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baki kariya da ayar Allah, zan iya hana idona bacci don inyi gadin ki a kowani dare kafin lokacin da zamu bar gidan, Inaso ki kwantar da hankalin ki, bana so ki sanya damuwa aranki, mu bi komai a hankali don ganin mun gano wanene ke yi maki hakan, bana son jin maganar nan abakin wani, kibarta kawai daga ni sai ke!!" kwantar mata da hankali yaci gaba dayi, tare da karfafa mata gwiwa har ya samu ya shawo kanta....



*=؋?CHIEF OWAIS=ت?*



Kasancewar Jiya bai samu isasshen bacci ba, sakamakon nafilfilin da ya tsaya yi, hakan ya haifar mashi da jin matsanancin bacci mai nauyin gaske, tun wuraren ?arfe bakwai na safe Daddy sharafudden yake ta faman zarya zuwa room din shi don ganin koya farka amma shiru har ya tafi office dinsa dake anan cikin Villa.....



Wayarsa ce ta soma yin ringing, da zarar ta katse wani kiran ke shigowa, da wata irin kasalar bacci ya buWe eyes dinsa wadanda suka canza launi, addu'ar ta shi daga bacci ya ambata aransa kafin ya mai?a hannu ya dauko wayar dake kan nightstand, ba tare daya mi?e daga kwancen da yake ba ya soma duba me kiran nashi, missed calls ya gani har shida, Uku daga Prime minister, biyu daga boss man, lumshe idaninshi yayi kafin ya aje wayar ya sauko ya nufi bathroom, ?an mintuna ?alilan Ya fito waist dinsa Waure da towel fari ?yal, gaba Waya ?irar ?arfinsa ta ?ara baiyana, ?irjin nan nashi acike ya ke da albarkatu.



A gaban mirror ya tsaya tamkar mai nazarin wani abu, A lokacin da baiyi tsammani ba kwatsam yaji An rungumo shi ta baya, A ruWe Yakai idaninsa ga hannun wanda ya rungumo shi, nan take ya sauke ajiyar zuciya dama sai da ranshi ya bashi cewar shi ne.



"Daddy ba sallama, har kasa gabana Ya faWi"

Tuntsirewa sharafudeen yayi da dariya ba tare daya raba jikin shi daga na chief ba


Muryarsa da tsantsar farin ciki Ya furta"Nayi kewar ka ne sanyin idaniyata, da tunaninka na tafi office, nagaza ta6uka komai shiyasa na dawo don inga ko ka farka, Ina fata ka yi breakfast din ka" cikin kulawa yai maganar yana leken face din sa ba tare daya raba jikin sa daga na shi ba

"Ban kaiga yin breakfast ba, saboda ban jima da tashi daga bacci ba"

"Hakan na nufin baka samu isasshen bacci ba daren jiya, bana hana ka kaiwa dare kana aiki ba"? ya faWa yana Waure mashi fuska'

Chief owais dake kallon daddyn nashi wani irin sanyi ne ke ratsa heart dinsa

"Ay min afwa dad, zan kiyaye hakan, nagode da kulawarka agare ni"

"Good, yanzu faWa min me kake son ci insa a haWa maka"

"Bazan samu damar yin breakfast ba, gida zan wuce"

juyo da shi Dad sharafudeen yayi suka fuskanci juna

"Yau ma kana nufin bazan samu damar cin abinci a tare da kai ba? Saboda kai na hana kaina yin breakfast duk don saboda muci atare, shi ne yanzu kake fada min tafiya za ka yi"?



fuskarshi babu annuri Ya furta maganar,

"Nayi jiran banza kenan, Bari na koma office, Allah ya kiyaye hanya"

Juyawa yayi cikin takun sauri Ya nufi door room

Kafin ya buWe kofar, Chief owais yai hanzarin bin bayan shi, Gaba Waya yayi hugging dinshi ta baya

"Am sorry dad, kasan bana son Bacin ranka, sannan bansan ni ka tsaya jira mu yi breakfast ba"

Lumshe ido dad sharafuddeen yayi, yayin da yake sauraron shi

"Lokaci na naka ne daddy, duk wani abu mai mahimmanci yabiyo bayan naka, Idan ma kace kada na fita, wlh ba inda zanje zan tsaya tare da kai ne"



daWaWan kalamai chief owais yake furta mashi, cikin ?ankanin lokacin zuciyar sharafudeen ta sassauto daga fushin da yayi.



Juyawa yai suka fuskanci juna ido cikin ido



"Idan na tuna yadda Dan uwana hateem yake kukan rashin Wa da Allah bai bashi ba, Ni kuma Allah Ya bani Wan sai dai bamu da lokacin juna, abun ba ?aramin karya min zuciya yake ba, bana so na bata maka lokaci, Ka tafi kawai, ay zamu hadu ne a wurin dinner da anjima"




Girgiza kai chief owais yayi, calmy ya furta"ba zan iya fita ba daddy, idan har banyi breakfast tare dakai ba, ka yi hakuri, ka bari mu yi kawai, daga ni har kai zamu fi samun kwanciyar hankali"



Dafa broad shoulder dinsa yai da hannu Waya"Ina alfahari dakai bugun zuciyata, kaga kuwa yadda ka kara girma da kyau? Ya fada yana duban jikin shi from head toe,

"Da gaskiyar mutane da suke fadin na iya haihuwa" murmushin gefen fuska chief ya dan saki har dimple dinsa na chin ya lotsa wani irin madarar kyau.



"Amma dai yau zanga Surukata ko"? ya tambaya yana Wage mashi gira

Jinjina mashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login