Showing 183001 words to 186000 words out of 391264 words

Chapter 62 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2636

dirshan, taci gaba da kuka"wallahi saida raina ya bani wani abu zai faru da su, tun lokacin da muka bar gidan nan naketa jin faduwar gaba, ashe wani abu ne zai faru da junaid dina, na shiga uku mami ku taimaka mun! Ku nemo min Ana ta kawo junaid dina.."!! Da sauri Zahra ta rungumota a kirjinta, ta cigaba da lallashinta..ita kanta zahran kukan ne ke shirin kubce mata.



"Haba Anila meye abun kuka? Kamar dai bakiyi tawakkali ba? Wayace maki wani abu ya faru da su? Uncle Wan iyane ya fara mata magana cikin tausasa harshe.



Ummi tace"ni abunda nake tunani kodai Mahboob ne Ya fita da su yakamata akira shi aji" da sauri Abie ya zaro waya ya danna ma mahboob kira yana dagawa ko sallamar shi abie bai amsa ba yace"mahboob kana ina"?



On the other hand mahboob yace"ina akan hanyar dawowa gida..."



"Ana tana atare dakai"?



Da mamaki mahboob yace"ana kuma abie? Ba tana agida ba? Ko bata nan ne"?

Katse kiran Abie yayi, tare da kallon su mami dake kallon shi

"Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ?ara karaWe kunnuwansu...

Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ?ara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matu?ar Waga hankulan su


fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun."



Ummi tace"Anila raba kanki da Wan adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"?



Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina waWannan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu Wanyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi



Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba.



Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali



"Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi"



Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta buWe baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" faWa sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru.



Mi?ewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai raWaWi da tafara ji, gaba Waya suka bita da kallo ganin ta mi?i hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta.



da sauri Abie yabi bayanta ya dam?i hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin ?wace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..."



Tana cikin yin magana ta sar?e kwatsam ta yanke jiki zata faWi da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar kiWima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya faWi ?asa.



La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh?



dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da buWar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na Wauko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta buWe min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun Wazu, sai na mi?a mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai Waga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba Waya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe.



"Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr, duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi.





Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows ?asa dressing mirror dinta ya kife ?asa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ?ara jefasu a rudani...."



Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta Wauko robar ruwa a fridge mai sanyi ta buWe murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta buWe idanunta waWanda suka kaWa jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su da?yar ta iya motsa la66anta da suke bushe ?amas ta furta"mami ina junaid Wina? Ana ta dawo min da shi"



shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta...

Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harWewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su.



"Zahra kun kira layin Ana Win"? Waga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ru?e qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaWe kunnuwan su

Uncle Wan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki"

__________________________________
'?



*=؋?UNAISAH ANGEL=ؓ?*



Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ?ara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ?atutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faWo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani.



Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya Wauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab....



Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa..



"Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita...



"Ya jikin naki? Wazu naga kamar kin samu lafiya.."



shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka..





Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta Wan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buWe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta Wan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"?



"Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faWa tare da saukowa daga kan gadon ta fara Waga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya.



Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta.



"Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya Waurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat Waya ta nuna bata ganta ba.



Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruWe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta

"Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ?atuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaWe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta.


"Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba.



"Mami kinyi shiru..." murmushi ya?e ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba.



Ringing Win wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun Wan kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta Wan firgita kaWan.



"Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta.



"Babyna..."
Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse.



kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse.

Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"?

On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri"



"Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani"

Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan

"Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..."



"Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta"



"Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun Wan jima suna waya kafin sukayi sallama.



Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya buWe kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun



Daya bayan Waya ta fara karanta shi.



_Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_



Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani ?aramin yarone ya Wauki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta...



Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ?ara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci Waya taji gabanta yaWan faWi ganin kamar nick name dinta wato Angel



_My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_





Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi.



"Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna



"Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta



Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta ?wallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya"



ta faWa tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba"



Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu Waya, sai yaji ta bashi tausayi.



"Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"?



"Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gyaWa kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin.


______________________________
'?



Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta mi?e kwata kwata babu kuzari kamar zata faWi kasa da sauri zahra


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login