Showing 285001 words to 288000 words out of 391264 words

Chapter 96 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2630

bakin kofar dakin sunyi shiru suna jiran ya bude masu ?ofa..

daga bisani ya ru?o hannunta suka shiga toilet, Ya wanke mata fuskarta, suka fito daga toilet din still hannun shi ruke cikin nata suka zauna kan gadon shi..

"Daddy, bazan kara kuka ba,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? zanyi maku addu'a, Allah ya kare min ku ya dawo min daku lafiya" tsananin tausayinta ya kama shi damuwar shi a haka zai tafi yabarta gashi yaji alamun zazza6i a jikin ta.

"Yawwa my daughter, yanzu kin share min kokwantona akanki, ni dama nasani, ?ata mai biyayya ce, zatayi abunda daddyn ta yake so.."

ya faWa tare da shafa gefen fuskarta data kumbura jawur, wlh shi kadai yasan irin yadda yakeji azuciyarshi duk in ya tuna inda zasuje da kuma yarsa tilo da yake da ita, bayason wani abu ya faru kawai dai yayi imanin komai zai faru da su mai kyau ko mara kyau mukaddari ne daga Allah, Bawa bai isa ya guje ma kaddararsa ba.

"Banaso sauran Yan uwanki, su gane wani abu, pls kija baki kiyi shiru, ko da sun tambayeki me yasa kike kuka, ki fada masu wani abun daban, nasan kina da wayau basai na maki bayani ba "

jinjina mashi kai tay,

Rungumota yayi akan kirjinshi, ya fara janta da fira Yana tariyo mata kuruciyarta duk da halin damuwar da take aciki saida taji sanyi aranta.

"Nan dakina ne, Zaki Iya zama aciki kafin mu dawo, ga toilet ki shiga kiyi wanka.." amsa mashi tayi da toh..

Sumar kanta yaci gaba da shafawa, yadda ya sabayi mata tuntana yar kankanuwarta, ahaka yake samu tayi bacci, aiko cikin sa'a yaji alamun bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke a hankali Ya kwantar da ita kan gadon, sai da yayi mata addu'o'i kafin Ya mike da baya da baya yake tafiya yana kallon ta idanunsa cike tab da kwalla.

Jiki asanyaye yajuya tare da buWe room door Win Ya fito su ummi na ganin shi suka kewaye shi kamar yan jarida suka tsare shi da tambayar meya faru da Unaisah...


"bata Jin dadin jikinta ne, zanyi magana da dr, zai zo ya duba ta, yanzu bacci takeyi pls idan ta farka ummi ki taimaka mata tayi wanka taci abinci sannan ki sanya mata ido sosai.." basu kawo komai aransu ba, Ummi tace in sha Allah zanyi duk abunda kace.

Kallon Danejo yayi"My wife, Pls ki taimaka ma Ummi, Ku kula da su, " fuskarta dauke da murmushi tace"toh, daddyn Angel, kaima ka kulamin da kanka" sallama yayi masu, kafin fitarshi daga part din a ?alla ya shafe mintuna biyar yana tunani kafin Ya fuce..=ؔ?


_______________________________
'?


*CHIEF OWAIS*


A Hankali Motar shi ta kunno kai cikin wani katafaren Resting Home na mai girma sharafudeen, tun kafin SA din dake driving dinsa yayi parking ta window glass din motar Ya hango Jami'an DSS kewaye da Courtyard din gidan dama kafin su shigo yaga sojoji tsare da gate din gidan hakanna ya dinga jin faduwar gaba.

Motarsu nayin parking bai jira an bude mashi car door ba saboda sauri da kanshi ya bude ya fito, with respect Dss din dake tsaye suka sara mashi, ko kallo basu ishe shi ba Ya nufi main door din falo.

Walking quickly ya haura Uptairs a gaban ?ofar katafaren Master suite na mai girma sharafudden ya Wan dakata da yin tafiyar.

"Come In" daga cikin Wakin Ya juyo muryar daddynsa

Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing.

Madaidaicin table din gabansa na Wauke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya.


Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa

"have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba.

Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi..

Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka Wauka kasha naka ne"

yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.."

?iris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ruWe yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa.

"Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"!

Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..."

Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi.

"hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"?

ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi.

"Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Ya?i ne?

"Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi

"Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine Wa namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada.

Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala.

"Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya faWa

Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko Waya, dan leken asiri nane ya fada min"

"why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"!

Ya fada rai abace

"Naji Ubana Obinna, zan dakatar da Wan leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ru?e hannayensa acikin nashi.

"Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice.

"pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...."

Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta.

Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba.

"Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda Wan le?en asirin nawa ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Ya?i a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_

ya faWa babu wasa akan fuskar shi, harya buWe baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar Waga mashi hannu"na gama magana Owais," ya faWa tare Ya duba agogon hannunsa

"I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce.

Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu ?addamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karanS'

Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi.

Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba.

Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace.

Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci Waya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint Win daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking Winta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana.

Gwiwowin ?afafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta Webe shi gaba Waya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi.

Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking.

"My baby boy, how are you"?

Kokari yake ya buWe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy."

yana faWan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi.

Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne?

Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ?ara sanin inda kan shi Ya ke ba..

(TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA>??S')

__________________________________
'?

Yayin Da Chief Owais ke a gar?ame Cikin Wakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa ?arfe biyar na maraice dai dai ba ?ari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuWe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan ya?i sun shirya tsaf.

Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform.

Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a al?awari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a Wauki abun da mahimmanci ba ne.

Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka Waga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu"

ya faWa idanun shi akan screen Win wayar shi dake ru?e a hannun shi..
Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"?

"Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..."

Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa"

"Har layin daddyn nasa na kira baya shiga"

"To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta Waga"

"Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran

Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number..

BuWe sakon yayi tare da karantawa

_Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_

(Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta maya?an, Na soke kai farmakin)

Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaWa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa.

jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin BuWe kofar main Falon, zumbur Ya mi?e Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu...

Waya bayan Waya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna..

Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"?

Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu

gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi

"Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai Waci Ya haWiya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira"

Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba.

"Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon..

Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi"

"Na kira layin shi baya shiga"

"Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy.

Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi.

kallon big guy yayi

"Har yanzu baka same shi ba"?
Jinjina mashi kai yai alamar eh..
Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ?ara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki"

"Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita"

ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna.

ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba.


"chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai aWan bace Yai maganar.

Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su"

"Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka Waga kaji me zaice maka"!


Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa
General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira"

yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama.

Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi

"Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau"

wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau"


Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi Wayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya ?wara muje villa din.."

Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci.

gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwaWawa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su buWe masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama.

wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke.

"Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya buWe mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba.

Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun Waya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku..


"Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya.


Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa.

"Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi
Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi.

dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince.

boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login