Showing 210001 words to 213000 words out of 391264 words

Chapter 71 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2549

kasa, Waya saman Waya an jera su daurin Waurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin Wakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne.



A hankali ta Wauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai.





tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mari?i dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata ma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????su jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faWa kamar ba ita ba.



da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta.



ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ?amas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta.



juwa ce ta kwashe ta gaba Waya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faWi ?asa a sume..



Saurari Littafin Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.


Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haWi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki.



cikin mawuyacin hali ta Wan yi karfin halin buWe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba.



Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya ji?e makoshinta nan da nan ta fara kwankwaWarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!!



"Ki sha A hankali kada ki sha?e" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana.



Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi bu?atar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi.



saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ru?e da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa



*KHALA* dattijuwar arzi?i, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana Waya daga cikin Elders na kurkukun ?addara sune masu fada aji, tana da ?arfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin suI ?



Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruWani



kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta.



la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba.





"Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faWa arude tana tararraba idanu.



Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar.



Ta Wan dakata tana kallon gabriella.



"Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta.



"naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna"



Saurari Littafin Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
ta fad'a fuskarta Wauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta





"Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! AruWe Gabriel take kallonta, harta buWe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murWa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..."





Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta Wauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne.





Ta Wauko bowl Waya ta juyo tare da kallon Gabriella





"Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ?are maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta mi?a mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu WanWano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta Waga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buWe wani kwano mai Wauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta Wauki gorar ruwan ta mi?a mata, ta kar6a ta sha.



Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji Wan dama dama a cikinta.



Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruWe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake?



"Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki al?awarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba.



Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel



"Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki ?etare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta faWa tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita.





"Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta Waga sandar hannunta tayi mata nuni da wata ?ofa



Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta faWa still da murmushi akan fuskarta.



Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve Win ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su.



"su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data Wauka a coma..



Ru?e hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh.



"Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a



"Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki"



"Toh,"



"Good girl" ta faWa tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta.



"Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta buWe su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata.



ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta buWe ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala.



ta mi?e tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet ta cika kwamun da ruwa mai Wumi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske.



Ta daWe acikin ruwan tana Wumama jikinta kafin tayi wanka ta maida rigarta, ta fito ta zauna kan kujerar, ta dauki storybook ta fara karantawa.





Murmushine ya bayyana akan fuskarta, da alama labarin da take karantawa ya faranta ranta, babi huWu ta karanta, ta fara jin kasalar bacci, mi?ewa tayi tare da kwashe books din ta nufi book shelves din dakin inda taga khala ta dauko mata su, tana kokarin ajiyesu ta hankaWe wasu jerin littattafai dake a shelves tana kokarin tallabe su biyu suka rikito ?asa, wani irin faduwar gaba ta ji, tsoro ya kamata tunawa da gargadin da tsohuwar tayi mata akan kada ta ta6a komai na dakin, jikinta na kerma ta zu?unna tana kokarin tattara books din kamar diary suka an kulle su da makulli tayadda baza'a iya buWe su ba.



Akan laps dinta ta daura books din kamar ance ta kalli covers dinsu karaf tayi tozali da hoton abunda ke akan diary na farko, zanan kananun yara ne su uku sanye da jajaye kaya, mata biyu sun sanya namiji a tsakiyar su, kayan matan rigace dai dai gwiwa launin ja, shi kuma namijin riga da wandone jajaye, abun da ya Waure mata kai da hoton cover din, duka yaran an daure masu hannayensu da igiya, an toshe bakinsu da jan kyalle, ga hawayen jini kwance kan fuskokinsu, da rubutun larabci aka rubuta sunan books din kokarin karantawa tayi A hankali ta furta sunan shi *sijill al-sujn* bata san menene ma'anar sunan shi ba, janye na farkon tayi ta dubi sunan Wayan diary din *tr+kh sijnil qadar* mi?ewa tayi da sauri ta maida su gidan da suka fadowa, ta gyara su dakyau ta yadda ba azagane dun faWo ba, da sauri ta nufi matakalar gadon ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta.



___________________________
'?



*HAJJATY*



Safa da marwa takeyi atsakar dakinta, Hannun ta ru?e da wayarta, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita, saboda fargaba da tashin hankalin ciwon marwa jiya taga abunda ya rikitar da ita, kusan kwana tayi adakin marwa tana kokarin shawo kanta saboda kukan da takeyi abun yayi yawa kamar zata kashe kanta, hajjaty ga tsoronta da take ji amma ahaka ta daure ta zauna adakinta har saida ta shawo kanta ta hanyar kunna mata karatun kur'ani kafin ta samu jikin marwa yayi sau?i har bacci ya Wauke sannan ta dawo daki, yau tun da safe ta buga ma sheikah imam kira awaya ta sanar da shi halin da marwa take aciki, tace mashi ta kasa gane meke damunta, sheikh imam Win yace zai shigo in sha Allah.



A yanzu haka shi take jira, ta kasa shiga dakin marwa saboda bata jin dadin ganin ta a mawucin hali, yarinyar ba karamun tausayi take bata ba.





Kira ne ya shigo wayar da sauri ta duba screen din wayar ganin sunan sheikh imam ne yasa ta daga da hanzari ta daidata nutsuwarta gurin yi mashi sallama bayan ya amsa mata yace"na iso gidan" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta dauki mayafi ta rufawa kanta, ta zura flat shoes a kafarta, ta fito ta nufi main falo din gidan tasan anan yake tsayawa idan ya shigo.



Tunkafin ta karasa ta hango shi zaune kan sofa as usual cikin shiga ta magadan annabawa.. masu aikin gidan dake ta kai komo cikin girmamawa suke gaishe da shi, har abunsha sun kawo mashi da snack, har ya fara shan lemun ya hango hajjaty, mikewa yayi tare da tunkararta, da fara'a tace"barka da safiya malam, ya gida ya iyali" murmushi yayi jin ta tambaye shi ya iyali.



bayan sun kammala gaisawa tayi gaba yabi bayanta har zuwa dakin Marwa saida ta fara shiga kafin tayi mashi iso ya shiga daga ciki, a lokacin marwa tana kwance kan katifarta, bacci mai nauyine ya dauke ta sai faman jan numfashi take yi, daga gani awahalce takeyin baccin.





"Malam, ni dai narasa gane kanta cikin kwanakin nan, in ta fara kuka kamar ranta zai fita, kuma wlh ina kiyayewa gurin bata maganin kamar yadda ka ce.." tay maganar tana kallon shi.





Matsawa yayi daga gaban mattress din Ya zu?unna Yana kallon yatsun hannayen marwa da fatar fuskarta, farat Waya ya gane babu lafiya, ciwon nata ma ?ara ha66aka yakeyi babu alamun sau?i, lamarin ya Waure mashi kai, a kalla ya shafe mintuna yana kallonta yana nazari akan yanayin ta.



Hajjaty dake kallon fuskarshi sheikh imam tuni tasha jinin jikinta ganin yanayin shi ba walwala.



mikewa yayi tare da kallon hajjaty"anya kuwa kinbi sharuddan bata maganin dana fada maki dai dai? Ko dai kinyi kuskure ne" arude ta girgiza kai"wallahi ban ta6a kuskureba, ina kokarin kiyayewa kamar yadda na fada maka..." bayani tayi mashi yadda take bata maganin, dalla dalla kamar yanda ya fada mata, tabbas ya yarda da maganarta, abunda bai gane ba ta ina matsalar take! Shiru yayi jim yana kara bin marwa da kallo

Muryar hajjaty na rawa tace"malam akwai matsala ne"?




Ya fahimci hajjaty bata lura da habbakuwar ciwon marwa ba ..

Numsafawa yayi kafin ya furta"ina maganin nata yake"?



Jikinta na 6ari tace"ga su can akan mirror, bari in dauko maka" dakatar da ita yayi da hannu tsayawa tayi, tana faman zare idanunta, juyar da kai sheikah imam yayi tare da kallon gaban mirror din marwa A hankali Ya nufi gaban madubin Ya tsaya tare da kallon robobin maganin, Waya ya Wauko ya buWe ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi.



Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya haWe rai sosai, Waya bayan Waya ya buWe murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta



"Ya akai haka"? Ya faWa yana dubanta



Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" haWe rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya faWi ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata.



Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba Waya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma

Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da Wan aiken shi ya kawo mata maganin tabbas


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login