Showing 315001 words to 318000 words out of 391264 words

Chapter 106 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2559

hawayen ta, Waga hannayenta tayi sama Cikin harshen larabci ta fara karanta addu'o'i duk akan Danish dinta.


Lumshe idanun shi yai a hankali ya sake bude su kan fuskarta, ya jinjinama irin kaunar da take ma Danish yayi fatan ace shi ya samu soyayyarta, saboda samun mace tagari irin ta zaiyi wuya a fadin duniyar nan, yarinyar da zata iya tashi in the middle of the Night tayi nafilfili don ta yi maka addu'a Omg=??


A hankali Ya zukunna ta gefen ta, Ya zuba mata lumsassun idanun shi masu Wauke da bacci.


Bakomai yake kallo ba fa ce eye lashes dinta da soft lips dinta dake kerma sun jiku da hawayen ta sometime har tongue take zurowa ta lashe su baisan ya akai ya tsinci kan shi da kallon ta ba.

A hankali ya mayar da eye balls dinsa kan kwantaccen gashin forehead dinta dark brown ya nannade gwanin ban sha'awa kai komai nata abun ban sha'awa ne.


Kasa yi mata magana yai cos yai tunanin she may feel uncomfortable if she sees him in front of her.

Slowly ya mi?e tare da juyawa ya nufi hanyar fucewa daga dakin
Kamar daga sama yajiyo muryarta a cikin kunnan shi"Wanene" dan dakatawa yai ba tare da ya juya ba, Zumbur ta mike gabanta na faduwa cos tajiyo motsin tafiyar shi.

waro idanu waje tay lokacin da tay arba da faffadan bayan shi, wlh sai taga kamar Danish ne yanayin tsayuwarsa banbancin Danish yafi sa tsayi da kuma doguwar sumar kai, uwa uba launin fatarsu ba daya ba.


"Wanene"? Ta ?ara faWa cike da fargaba, gudun kada ya tsoratar da ita yasa shi juyowa a hankali suka fuskanci juna tana ganin chief tay saurin share hawayen ta saboda ya hanata kuka, tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin a cikin dakinsu, arude ta furta"barka da dare" ya fahimci rudani dake akan fuskarta hakan yasa shi cewa"I'm sorry na shigo dakin ku batare da izninku ba, na fito ina zagayawane najiyo shesshekar kukanki, Hankali ya tashi sau uku ina yin sallama ba'a amsa min ba, har knocking nayi shiru shiyasa na yanke shawarar shigowa ciki amma ba halina bane"


Cikin sanyin murya ta furta"na fahimce ka, kuma nagode da kulawarka agare ni, ka damu dani sosai"

Sam taki bari su hada ido tun kallon farko da tay mashi ta kawar da idanun ta.

"Kin manta sharaddun da dr ya gindaya maki? I thought I would find you sleeping, although you are doing good thing, but you should continue resting until you've fully recovered, ban hana ki masa addu'a ba, zaki iya yi masa addu'a aduk lokacin da kikai sallah, amma yanzu dare ne Unaisah"

with respect ta amsa mashi da toh.

Shiru suka Wanyi na wani lokaci, takun tafiyarsa taji da sauri ta dago matsowa yai dab da ita..

Ta sadda kanta kasa tana dan jin faduwar gaba.

In a cool voice yace"a ranar da mu ka kwana a sansanin mu, Danish ya nemi in yi masa alkawarin ko bayan ransa In kula da rayuwarki data mahaifinki da yan uwanki, and I vowed to fulfill his request"

jin wannan maganar yasata kusa fashewa da kuka jikinta ya kama kerma.

"Ban fada maki don in fama maki raunin dake a cikin zuciyarki ba, sai don inaso ki taimakamin Unaisah, Ki bani hadinkai gurin ganin na cika masa alkawarinsa, in har kika bani dama duk da ina shiga busy saboda aiki zan yi kokarin ware mana lokacin da zamu dinga ganawa da juna, in sha Allah I'll support you in overcoming the pain that's troubling you."

dakyar ya ?are maganin ganin yadda hawaye ke yar tseral kan kuncinta aranta ta ayyana wata irin kauna Danish yakeyi mata? Ya Ilahi, Shi damuwar shi wanda zai kula da rayuwarsu in baya nan wayyo Allah hakika tayi babban rashi arayuwar ta.

batai aune ba taji safkar yatsun chief kan fuskarta gently ya soma share mata hawayen ta.


Muryarsa tamkar ta me yin raWa ya furta"If you give me a chance, I will replace him, despite knowing I may never fully replace him in your heart" ya Wan dakata yana mayar da numfashi, ta nutsu tana sauraron shi.

"Na riga shi sanin ki amma ya riga ni haduwa dake, nasan da ace tun lokacin na bayyana kaina agurinki da nima na samu gurbi acikin zuciyarki, sai dai kash na makaro amma har yanzu ina da sauran dama Unaisah, nasan kun shaku da juna ke da shi, kun sha wahala a tare, kun yi rayuwa a guri Waya, kun san sirrin juna, nikuma bansan komai dangane dake ba, amma idan kika bani dama nayi maki alkawarin zan canza maki rayuwarki...."

da wata irin siga ta jan hankali yai mata maganar, har saida taji wani irin yanayi atare da ita, kalamansa sun ta6a zuciyarta.

?agowar da zatay keda wuya karan hancinsu ya gogi na juna razanar da ta Wanyi ne yasa ta Waga ?afa zatay baya aikuwa gaba daya ta tafi zata kife kasa saboda rashin kwarin jikinta.

Cikin zafin nama yai hanzarin damko waist dinta Ya janyota gaba daya ta fada kan broad chest din shi, wani irin faduwar gaba taji, She could feel his heart beating rapidly, lumshe idanunta ta danyi sam ta kasa motsawa daga jikin shi, ta rasa gane me take ji? Amma tabbas taji wani irin sanyi da kwanciya hankali yana ratsa zuciyarta.

har ga Allah bai janyota da wata manufa ba, gudun kada ta fadi yasa shi rukota sai kuma abun ya nemi ya jefasa a wani yanayi mara misaltuwa, nutsuwa yai yana kallon fuskarta tay lamo a jikin shi kamar jinjira.

Damuwar rashin Danish ta fara affecting brain din ta, komai ya faru Danish take gani a yanzu haka ji take kamar a jikin Danish ta faWa shiyasa ta kara narke masa.

abunka ga mabukacin dake bukatar duk wani abu da zai sanyaya mashi zuciya.

"Unaisah" shiru bata amsa mashi ba.

"are you sleepy? Ya tambaya yana leken fuskarsa.

Still bata motsa ba, Batool ce ta fara mutsu mutsu kamar zata farka, hakan yasa shi raba ta daga jikin shi ya Wan jijjigata dakyar ya samu ta buWe idanunta wadanda suka kaWa jawur kamar an watsa masu barkono.

"Muje ki kwanta" kamar gunki tay shiru babu alamun zata Waga ?afarta, kamar bata jin me yake cewa.

Sungumarta yai kan Shoulder inshi Ya nufi bed da ita, Cikin kulawa ya kwantar da ita..

"Kada Ki kwana Da hijab a jikin ki, Ki cire sannan ki yi addu'a" sai lokacin ta dan jinjina ma shi kai.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin Yai hanzarin juyawa ya fuce daga dakin.


Sai bayan daya fitane ta samu kanta, maganganunsa ne suka dinga yi mata yawo akai a haka har bacci mai dadi yai awon gaba da ita.

"ANEELEERH
ba ita ta tashi farkawa ba sai wuraren ?arfe huWu na dare dayake tasa abun aranta har mafarki saida tayi, idanunta biji biji ta buWe su ta dubi agogo, kafin ta curo wayar daga chargy harta cika, Kunna wayar tayi Haskenta na kawowa taga abunda ya karya zuciyarta hoton Ana ne da baby junaid akan wallpaper dinta sunyi murmushi a hoton.

Bata samu wayar da password ba, lalube ta cigaba dayi mata ta shiga whatsapp dinta, tana tsaka dayin scrolling ta fada Archived anan taga wani Group da Ana ta bude ita da sisters dinta,, Shiga ciki tayi ta soma karanta firarsu.

_sister, ke da kike zaune cikin rufin asirin Allah, meyasa kika ce kin gaji da zama gidan? Bayan irin sabon da kikayi da Aneelerh, gashi muma ta silarki mun samu taimako a gurin ta_

_ba zaku gane ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, bawai don son raina nakeso In bar gidan ba, kawai hankalina ba akwance Yake ba, ni dai kawai inaso nabar gidan ne_

_kinga in wani abu ke damunki, ki fada mana, mu nemi mafita a tare_

_kada ku Waga hankulanku, babu komai, kawai inaso nadinga ganinku kullum akusa dani, saboda kuka dai ne dangin da kuka rage min a duniya_

_idan kina so mu dawo kusa dake, toh ki sama mana aiki anan abujan mana, sai mu dawo, muma munfiso mu zauna kusa da ke_

_bazan bari ku dawo nan ba, sai ni kusa ma min aiki in dawo nan_

_meyasa_

_nafison zama a Jos din fiye da nan_

Dakatawa Aneelerh tayi da karanta sakon, aranta ta ayyana meyasa Ana take gudun zama abuja? Bayan kafin zuwansu tafi kowa daukin zasu dawo nan"! Girgiza kai ta danyi kafin ta yanko wata firar tasu ta ci gaba da karantawa..

_janet tace"Ana! Kina cikin hayyacinki kuwa? Meyasa kike magana kamar wata musulma"? esther tace"Na fara zarginta, cikin kwanakin nan kullum in zakiyi magana a group chat dinmu sai kin sanya mana abun addinin musulunci bayan mu ba musulmai bane_

_Voice note ta tura masu"nagaji da 6oye maku da nake yi, ku yan uwana ne babu wani sirri atsakanin mu, nasan zaku goyi bayana" su kace muna sauraronki"Na musulunta, Yau wata biyu kenan, amma babu wanda ya sani, ko Aneelerh ban fada mata ba, A boye nake yin sallah ta"_

_"Dagaske kike ko wasa" janet ce ta fada_

_"Na ta6a maki wasa irin wannan"?
Janet tace"a'a"_

_Ana Tace"toh, Dagaske nake Ana Winku Yanzu musulmace ni, na yi imani da Allah kuma nayi imanin cewa Jesus da muke bautamawa bawan Allah ne kuma manzon sa ne"_

Esther tace"nagaza yarda Ana, kamar dai kin haukace, taya zaki bar addinin iyayen mu da kakannin mu"?


_Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta kaWaitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_

wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta raWa masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi.

Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar.

taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi.

yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala.

Bayan ta sallame sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta.

Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta mayar da hankali akan videon..

wani irin faWuwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati...

tsabar kiWimar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi.

Yana buWe idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun kaWa jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..."

Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba.

"Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe.

lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin.

da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da Wan mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya Woke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye.

Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka"

Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito"

gaban faucet taje ta wanko fuskarta ta buWe kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ru?e qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum.

"Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata haWo min wani kuma ma zata dafa min noodles..."

"Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta Wauki junaid ta shiga toilet da shi.

da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dau?e da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet.

Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa.

Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido..

"Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya?

"Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou"

"Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon.

"Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta faWa tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne?

Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya

"In sha Allah next week zai koma"


Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafaWi a duniya

Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci.


sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da le?a fuskar ta, gabanta ne ya faWi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaWa jawur.

Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba.

Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruWe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta..

"Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake"

dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..."

murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaWa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late"


"Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin.

Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa"

"Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin..

Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su.

tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ?wama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ?aramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matu?ar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login