Showing 180001 words to 183000 words out of 391264 words

Chapter 61 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2569

Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka mi?e suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci Waya daga cikin su ya fara bayani,



"Duk da irin ?o?arin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana Wan girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya Waura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ruWe Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ruWe jin bayanan Docs.

"Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana Waya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai Waya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace ?arara akan fuskokinsu..



"Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar ?walla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba Waya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare Waya ba tare da dalili ba.....

"Dr ba yadda za'ay ku buWe mata bakin ta? Baba obie ya faWa yana kallon docs Win,

Girgiza kai Waya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ruWe ga tashin hankali......



Dafa kafaWar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sau?i, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar,

numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan Waya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin bu?atar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata ?arin ruwa da wasu allurai da zasu ?ara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji daWin hakan, Baba Obie ya ro?esu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi ?o?arin hakan. Su Hajjaty sunso su ?ara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ?ara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi.



Suna a kan hanyarsu ta komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam Win ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, ?an hanjinshi suka motsa, wata irin kiWima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....!



_______________________________
'?





A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba.



Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya..



yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ?ara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai faWo mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu



Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ru?o hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna



"In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a"



Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da Waukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake!



kallon zarah tayi"na kira baya shiga!"



Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari Wan anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta



"Anila ya kamata ki kira mahboob ki tuna mashi kar ya manta yaje da wuri ya dauko baby junaid, kinsan bayasan jira muma yanzu zamu tashi mu tafi yamma tayi"dariya sukayi su duka ummi tace"gaskia kam" tashi Anila tayi ta koma gefe Waya ta kira layin mahboob yana Wauka tace" please karka manta kaje ka dauko baby junaid da wuri...

Katse ta yai da cewa "ohhh Aunty Aneelah saikace karatu kusan kullum sai an tunamin inje dauko sa? to ki kwantar da hankalinki baby junaid tun ?arfe 2 yana a gida, yau da wuri aka tado su, saboda za'ayi wani taro a school dinsu, nima abokina ne dake koyarwa a school din ya kira ya fada min an tada su shine naje na dauko shi, halan bakuyi waya da Ana bane"?



Wani irin bugu zuciyar Anila tayi rass! Taji gabanta ya fadi zuciyarta ajagule ta furta"wai kana nufin tun karfe biyu junaid yana agida"?



"Kwarai kuwa, naga kamar kin daga hankalin ki, idan ma don saboda shine kada ki damu kanki yana atare da Ana ita na damka ma amanar shi"

Still hankalin ta bai kwanta ba tace"mahboob na kira layin Ana a kashe, pls ko zaka duba min su"?

voice dinta kamar zatayi kuka ga wani faduwa da gabanta keyi "ki sake kira kiji ni yanzu bana agidan na tafi kallon match" sallama sukayi ta kashe wayar hannunta har kyarma yake wurin kiran layin Ana still dai a switch off, cikin sauri ta koma falo ta gayama su ummi yadda tayi da mahboob mikewa mami tayi tare da kallon su uncle abdallah "to mufa baki zasuyi halinsu" ta fada tare da yar dariya, hajiya adama tace"wlh kamar ku kwana banso ku tafi Allah, kun Webemin kewa yau, Anya bazan biku ba" da zolaya uncle dan iya yace"shi kuma abdallan ina zamu kai shi? aikuwa su duka suka sa dariya, Aneelarh kamar jira take ta yafa mayafinta zarah ma haka gaba Waya suka fito compound din gidan inda sukayi parking car dinsu...

"Allah ya kiyaye hanya, mungode sosai, in sha Allah zanzo ganin jikana, agaida min shi..." Uncle abdalla yayi masu sallama akan idon su motocin suka fuce daga gidan hajiya adama hada kwallarta saboda bataji dadin tafiyar su ba, ruke hannunta uncle Abdalla yayi a cikin shi, suka koma cikin gidan su...

Nima na ru?e hannun al?alamina
'?

(Mu haWe Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya=?%?)

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*

Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.


Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright ? 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe chapter 36 complete
by
Novels Elite Admin
August 31, 2024
Sponsored Link
Takun ?arshe
DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?

tun da motocinsu suka haura kan titi Aneelerh take ta tsuma ji take kamar ta ?wace driving din daga hannun Abie don gani take kamar bai sauri, tsigar jikin ta sai tashi take, gaba daya ba ta da kwanciyar hankali..

Tsawon mintuna kafin suka ?araso anguwar su, baba mai gadi ya taso ya buWe masu gate, motar abie ce farko ta uncle Wan iya na abiye da bayan su, abie nayin parking hannunta na kerma ta buWe motar ta fito ta nufi cikin gidan.

Mami tace ohni Aneelerh ko irin alkunyar nan babu, baka lura da yadda ta Waga hankalin ta ba tun agidan hajiya adama..." mami ce tay maganar tare da buWe motar ta fito abie na dariya yace"ya'yan zamani kenan, ay su ba ruwansu da wata kunya indai akan ya'yan su ne idon su rufewa yakeyi.

Da sauri zahra ta fito tabi bayan Aneelerh, bayan ummi da uncle sun fito baba mai gadi ya karaso inda suke yayi masu barka da dawowa...

Lokacin da Aneelerh ta shiga falon ko sallama batayi ba saboda idon ta ya rufe, yaronta kaWai takason gani muryarta na rawa ta furta"Ana! Ana! Ana...! Shiru ba'a amsa mata ba, a kan sofa ta wurgar da handbag dinta, ta nufi bedroom dinta da sauri don taga ko baby junaid na anan tana shiga ta iske dakin wayan babu kowa, fitowa tayi a fujajen ta nufi kitchen"Ana! Ana! Wai ina kika shiga ne?...." tana shiga kitchen ta taras babu kowa ranta ne ya bata kodai yana adakin Ana suna bacci"? Hakan yasa ta juya da sauri ta nufi hanyar dakin Anah



"Aunty Anila..." zahra ce ta kira sunanta, shigowarta kenan ta hango Aneelerh ta nufi dakin Ana da sauri tabi bayanta, kafin ta karaso Aneelah ta ture kofar dakin, cike dasa ran zata gansu kwance kan gado, zura kafarta keda wuya idanunta suka sauka akan gadon Ana babu kowa akai, dakin gaba Wayanshi a haukace yake kamar anyi dambe a cikin shi, fululluka har biyu ta gani kan floor, ga zanin gado a yamutse yayi uban squeezing, wani abu da ya ?ara rikirkita Anila, dressing mirror din dakin data gani ya kife ?asa, Wa'iyazubilla wani irin jiri jiri ta fara gani a cikin idanunta da wani irin azababban faduwar gaba ta ?arasa shiga ciki kamar wadda aka zare wa laka, zahra tana abiye da bayanta sai faman zare idanu sukeyi cike da tashin ha???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nkali, tun daga kan yanayin dakin suka fahimci wani mugun abunne ya faruW'





"Mun shiga uku Aunty Anila! Meya faru da dakin Ana? Ta ina? Ina baby junaid..."? AruWe zahra take magana ita Anila gaba daya rudani Ya hana ta furta kalma, jikinta na kerma tasa hannu tayi knocking toilet door din dakin cike da sa ran Ana zata amsa mata, almost 3 times tana kwankwasa kofar toilet din babu alamun za'a tanka mata ko za'a buWe kofar, da iya karfinta na karshe ta bangaje kofar da kafadarta nan take door din ta buWe a slow ta bada wani sauti kiiiiiiiiii!



Da wani irin faduwar gaba ta zura kafarta cikin toilet din, A hankali take bin ko'ina da kallo, bata ga kowa ba, sai shower da tagani a kunne ruwa yana ta kwararowa ya malale kan floor, ga faucet ma a kunne ruwan dake 6ul6ulowa ta cikin shi Ya cika sink din harya fara gangarowa ?asa.



Hankali atashe Anila da zahra suke karewa toilet din kallo..

Muryar Anila na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zahra na shiga uku? Bangan su ba! Banga baby junaid ba! Ina Ana takai shi? Ina suka shiga!...





Ru?o hannunta Zahra tayi"Auntyna ki kwantar da hankalinki, muje mu duba sauran dakunan watakil taje gyara dakin wani a cikin mu, ko kuma sun fita backyard.



Da sauri suka fito daga dakin, adai dai lokacin Su mami sun shigo suna zaune a falon suka hango zahra da Anila zasu gifta ta falon

Muryar Mami ce ta katse su"Kai Ina zuwa haka? Kusan atare suka juyo muryar Anila na rawa ta ce"mami ba mu ga Ana da baby junaid ba, su muke nema..." jin wannan maganar Yasa ummi da su Abie suka mike tsaye

Ummi tace"kun duba ko'ina"? Zahra tace"yanzu zamu karasa dubawa..." ta fada tare da ru?o hannun Anila suka nufi hanyar dakunan su Abie...



Abu kamar wasa sai da takaiga ko'ina na gidan sun duba sa?o da lungu amma ba su gan su ba, nan fa hankulan mutanan gidan Ya tashi, hatta su abie saida suka tayasu neman Ana, kowan nan su Ya hada uban gumi kan fuskarshi, sai da suka tabbatar babu su agidan sannan suka dawo falo suka tsaya cirko cirko.



Fuskar mami A yamutse ta furta"to ina suka shiga ne? Ko dai sun fita daga gidan ne? Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, watakil ta fita da shi"





Abie ne Yace"bari nayi magana da baba mai gadi, in ma fitar su kayi zamuji a wurin shi, A hanzarce Ya fuce daga falon Uncle dan Iya yabi bayan shi da sauri.



Baiwar Allah Aneelarh, tafi kowa jin jiki, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita gaba Waya ta gama sarewa, tana zaune kan sofa, hannayenta biyu daddafe da kanta, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta.



Zahra dake a gefenta itama damuwarce akan fuskarta, ta dafa kafaWar Anila tana kokarin kwantar mata da hankali, ganin yadda ta canza fuskarta tayi jawur cheeks dinta har kerma suke, dama abunda take ta zullumi kenan, tunkafin barinsu gidan hankalinta bai kwanta da yanayin da taga Anah ba! shiyasa take ta jin faduwar gaba dama sau dayawa in wani abu zai faru da bawa Allah na bashi haske kan al'amarin.



Mai gadi na zaune kan kujera Ya kure sautin radio dinshi, sam baiji Kiran da su Abie suke kwala mashi ba, har saida suka karaso gaban kujerar tukunna ya lura da su, da sauri Ya kashe radio din Ya mi?e yana kallon su



"Bayan fitar mu daga gidan nan! Wani ya ?ara fita ne"? Abie ne ya jafa mashi tambayar, girgiza kai yayi"yalla6ai babu wanda Ya fita..." can kuma yace au na tuna Mahboob ya dawo tare da junaidu, bayan shigar shi ina zaune sai ga mahbob ya fito ya shiga mota ya fuce, bayan shi babu wanda Ya ?ara fita...." bai kare maganar ba Uncle Wan iya ya tari numfashi shi da cewa"kana nufin baga ka lokacin da Ana ta fita da junaid ba..." girgiza kai baba mai gadi yayi yace"a'a gaskiya ni banga gifcinsu ba, Ina zaune na kasa na tsare ko sauro bai isa Ya haura gate din nan batare dana kama shi ba..." hankali atashe Abie da uncle dan iya suka kalli Juna.



"Yalla6ai wani abu ya faru ne"? Baba mai gadi ne yayi tambayar ganin kamar damuwa akan fuskokinsu...

Abie ne ya zayyana mashi abunda ke faru, baba mai gadi yace"ikon Allah! Amma yalla6ai kun duba ko'ina? Saboda wallahi ni banga fitarsu ba, Allah shine shaidata, ko gyangyadin bacci banyi ba, lokacin sallah kadai ke tada ni, kuma sallar ma abakin gate din nayita...." ba su tsaya jin karashen maganar shi ba, da sauri suka koma falon gidan, su mami na ganinsu suka mike har suna hada baki wurin tambayar abunda me ganin yace Abie ne ya kora masu jawabi.



Kaf a kunnan Anila lokaci Waya ta rushe da kuka tana fadin"inna lillahi wa'inna ilahirraji"un..." daga kan sofa ta sauko kan floor ta zauna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login