Showing 63001 words to 66000 words out of 391264 words

Chapter 22 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2592

da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi?

Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hankaWe garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci.



Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma Waura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu



Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa.



Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka daWe suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa

Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri Waya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin Wan mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya Waga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba Waya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka Waure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi ?an dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi....



Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan ?arsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba,



A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time Win kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya ?afe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa.



Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya ?i komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya haWa mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai bu?ata......



Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba Waya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba Waya hankalinshi baya akanta....



Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta.



Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta.....



Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba.



Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta.



Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar ha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????usar ke fita irin ta ?an koyo.



Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa



Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta Webe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira kaWan kaWan saboda rashin sabo, da kuma ?arancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba.



Tun daga ranar daya haWu da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, ro?ansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ?ara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta ?walla rai akanta ne?



Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da buWar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu na neman wuce gona da iri.



Cikin kwantar da murya yace masu su yi hakuri, su daina bugunta indai saboda shi ne yanzu zai tafi yabar masu rigarsu" sam basu fahimci me yake cewa ba, sai ma wani irin kallon tsana da suke jifar shi da shi, har ya juya zai tafi danejo ta ru?o hannunsa, a fusace gidado ya ru?o hannunta, suka riketa don kada tabi shi.



Sautin kukanta ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, shi kanshi baya son rabuwa da ita, ba don yaso ba sai don ba yadda zaiyi ne...



Har yayi nisa da tafiya, ya Wan dakata zuciyarshi na raya mashi ya juya ya kalle ta, watakil bazai sake haWuwa da ita ba, har zuwa lokacin da zai bar dajin,



Juyawar da zaiyi keda wuya, kwatsam idanunsa suka sauka akan rigar Angel dake shanye kan Waya daga cikin bukkokin su, daga gani wanke ta akayi aka shanya don ta bushe, da farko bai tantance abunda idanunsa ke nuna masa ba, sai da ya Wan kara ?ura idanunsa tukunna Ya shaida itace rigar baccin da ke a jikin Angel aranar da ya gudo da ita, sune kayan jikin ta, was wasi yafara yi a cikin zuciyarsa tayaya akai rigar unaisah tazo dajin a hannun fulani? Ko dai suma suna da irin rigunan gayu ne"? Farat Waya zuciyarshi ta bashi amsa da cewa me zai kawo irin wannan suturar a hannun mutanan da ke rayuwa a daji? Sai dai idan tsintar ta su kayi...' muryarshi na rawa ya furta"idan har dagaske ne abunda nake hasashe tabbas Wani ya ceto rayuwar Angel Wina bayan na jefata a cikin ruwa tun da gashi har rigarta ta bayyana...



Ba zato ba tsammani, suka ga mutumin da suka kora ya watso da gudu ya dawo wurin rigarsu, har sun har zu?a zasu fara dukanshi da sandunan su sai kuma suka fasa ganin Ya dam?o rigar da danejo ta shanya kan bukka, ru?e rigar yayi a hannunshi zuciyarshi na bugawa da matsanancin karfi ya soma ambaton sunan Angel Angel, Lokaci Waya su bawuro da su hasiya suka kalli juna da mamaki jin yana ambaton sunan yarinyar da danejo ta tsinto a cikin ruwa, tambayar shi suka soma yi wanene shi? Ya akai yasan yarinyar?



Hawaye na zuba daga idanunsa ya dago rigar yana nuna masu yace" wannan rigar ta ?ata ce Angel, da hannuna na jefa ta cikin ruwa, dan Allah ku fada min a ina kuka samu rigar? Ko dai kune kuka ceto rayuwarta....." kukane yaci karfinsa, gaba daya ya rikice masu, su kansu so suke son san me yake cewa don suji ko shine mutumin nan da yarinyar take nema don bazasu ta6a mantawa ba da irin kukan data dinga yi masu tana kaisu bakin ruwa donsu nemo mata daddynta tun basu fahimtar me take cewa har suka gane cewa wani nata ne take nema..



Danejo ce kaWai ta fahimci me Yake cewa, nan take ta fashe da kuka Cikin harshen fulatanci ta sanar ma sauran ?an uwanta abun da taj Ya ke faWi nan suka gane cewa shine mahaifin Angel, yarinyar data tsaya masu aransu, har yau har gobe basu cireta aransu ba, hakika sunyi farin ciki mara misaltuwa da ganinsa.



Tsabar farin ciki yasa danejo ta watsa da gudu ta fada kan kirjinsa ta rungume shi tana kuka, ta soma tambayarshi ina Angel? Ko ya ganta"? Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, a ruWe ya tambaye ta me take nufi? Ba su suka taimake ta ba" cikin sanyin murya danejo ta labarta mashi komai daya faru tun daga lokacin da ta tsintota a cikin ruwa har zuwa time da ta gudu daga rigar su.



Wani irin jiri yaji yana shirin kwasarshi saboda kuncin dayaji, bakomai ne ya jawo mashi jinkirin da yayi ba nazuwa daukarta face loosing memory din da yayi.



Zubewa yai kan gwiwowinsa zuciyarsa a hautsine tamkar zata buga, gaba Waya suka kewaye shi, suna kallon shi gwanin ban tausayi, ganin yadda ya ke matsar kwalla.



Saboda son da suke ma Angel yasa suka yi mashi kyakkyawar tarba, a kalla ya shafe wata a rigar su, kafin Yaji bazai iya cigaba da zama a dajin ba, kwara ya koma gida watakil idan yaje can ya sameta ta koma wurinsu Aneelerh.



Ranar da taj ya shirya tafiya, zai bar rigar, ya yi masu bankwana kamar karsu rabu, yace masu zai fara zuwa wurin mutanan da suka taimake shi kafin ya wuce garin su, guzurin tafiya suka hada masa, kowa ya kawo abunda yake dashi, suka bashi sannan sukace mashi idan Allah yasa yaga yarsa angel ya fada mata sunyi kewarta, zuciyarshi cike fal da kewarsu ya kamo hanya zai bar rigarsu, harfa yayi nisa yajiyo takun gudunta sai faman kwala mashi kira takeyi, a hanzarce ya juya yana kallonta, danejo ce hannunta ru?e da kullin kayanta, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, ganin ta biyo shi.



Karasowa tayi tana haki tace"dan Allah ka tafi dani inason ganin Angel"

Girgiza mata kai yayi"kiyi hakuri bazan iya tafiya dake ba, meyasa kika yarda dani har haka? ki yi hakuri ki koma wurin ?an uwanki" fashewa tayi da kuka.



Ana cikin haka, yajiyo sautin takalman yan uwanta kusan gaba dayansu ne suka biyota.



Fuskokinsu babu walwala, ru?o hannunta kakansu yayi tare da mika ma taj, da mamaki yake kallonshi don bai fahimci me yake nufi ba, har saida yayi mashi da kurmanci Ya nuna mashi cewa ya tafi da ita, sun bar mashi ita, saboda tace in har basu bari tabi shi ba, to zata kashe kanta ne, shiyasa suka yanke shawarar kwara su bar mashi ita, don ko sun barta ba lallai su iya shawo kanta ba.



Babu yadda taj baiyi da su ba akan subar yarsu, hankalinsu sai yafi kwanciya idan tana akusa da su amma suka sanya kafiya akan dole ya tafi da ita, ganin ya turje ne yasa suka fada mashi cewa marainiyace, tun kafin ta mallaki hankalin ta iyayenta suka rasu, bata ta6a neman wani abu daga gare su tarasa ba, don haka sun bashi amanarta, yaji tsoron Allah ya rike masu ita amana su je can su yi aure, hawaye ne suka wanke fuskarshi, jiki asanyaye yasa hannu ya ru?o hannun danejo,yayi masu alkawarin bazai ta6a bari ta nemi wani abu ta rasa ba, zai dauki dukkan wani nauyi nata zai bata kulawa, sunji dadin abunda ya fada masu a karshe sukayi bankwana da junansu, yaja hannun danejo suka nufi rigarsu Habu.



har sun fidda rai da sake ganin shi, tsawon kwanakin da yayi a rigarsu danejo kusan kullum sai sunzo neman shi a yar bukkarsa, sunyi mamakin ganin ya dawo masu tare da yar matashiyar budurwa, cikin harshen fulatanci danejo tayi masu bayanin komai dangane da taj...."



labarin tajudden da Angel ya ta6a zuciyoyinsu, har hawaye suka zubda masa saboda tsananin tausayin shi da suka ji, bayan komai ya lafa ya sanar da su zancen tafiyar shi, ba don sunso ba sukayi mashi fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa yaga yarinyarsa, kafin tafiyarsa saida suka hada mashi shatara na arziki, bayan haka suka yi masu rakiya har zuwa bakin titi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login