Showing 291001 words to 294000 words out of 391264 words

Chapter 98 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2606

naji kace kaji kamshin mutun bayan ni kadai ce mutum da ke rayuwa a cikin dakin nan.."

"baki saba min karya ba, Amma yau kinyi min, kinsan na tsani makaryaci, saboda alamace dake nuna mutun zai Iya cin amanarka wata rana"

idanunta ne suka ciko tab da kwallo, cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, na gane kuskurena, kasan ba halina bane, dama yarince daga cikin prisoners, inason yarinyar ne shiyasa na taimake ta..."

tun kafin ta kare maganar Ya daka mata tsawa a faWace Ya furta"meke damunkine? Kina cikin hayyacinki kuwa? Kin manta gargadin da nayi maki?

Kamar ?aramar yarinya ya rufe ta da faWa.


"Ki rasa wa zaki kawo cikin dakina sai ?as?antacciya Prisoner? ?akin Elder? kefa sirrina ce, sai da na fada maki banaso kowa ya rabeki in bani ba"

kokarin bashi hakuri tayi, ko kallo bata ishe shi ba, saukowa yayi daga kan gadon da kakkausar murya ya furta"Tana ina"! Jiki na rawa tsohuwa Khala ta sauko daga kan gadon.

"Pls kada ka rabani da ita, Inasonta, wallahi bada wata manufa na ajiyeta adakin nan ba.." magiya ta dinga yi mashi amma dayake zuciyar irin ta fir'auna ce ko kadan bai saurare ta ba.

Tsoro Ya hana Gabriella fitowa, kirjinta kamar ana luguden ta6are..

"Zaki fito da kafafuwanki, ko kuwa Ni kikeso In fito dake..." cikin karyayyar murya khala ta kira sunanta..

Jiki asanyaye ta fito daga karkashin gadon, wani dan iskan kallo Elder yabita da shi, farat Waya Ya gane ?ar wacece.

Dariyar sha?iyanci Ya saka kafin Yace"wannan Ay yar gurin Jan wuya ce, sadaukarwar Jini ce, bazan Iya barmaki ita ba, dama wata ce daban, Ko ubanta Yaji kin dauke ta sai yazo ya kar6eta ya mayar da ita cikin prisoners, kinga kuwa babu amfanin boyeta agurin ki...."

Gabriel ta ruWe da jin maganar shi, ta fashe da kuka, idanunta akan fuskar Khala dake kallon ta.

cikin shesshekar kuka tace"kada ki bari arabani dake, kashe ni zasuyi, bana so na koma gurin su, kada ki manta da alkawarin da kikayi min pls...."

Da kallon tuhuma Elder Ya dubi Khala"wani alkawari ne kikayi mata"

"Zan hada ta da Wan uwanta" ta fada rai a6ace..

"Ku shigo ku dauke ta" suka ji ya fada, kafin wani Ya furta kalma sai ga Giants biyu karfafa sun fado cikin Wakin, wani irin faduwar gaba Gabriella taji, jikinta na bari kamar mazari ta la6e bayan Khala, ta rurruke hannunta tanayi mata magiya kan kada ta bari su tafi da ita.

shiru khala tayi jikinta yayi sanyi lakwas, Zuciyarta ta karaya.

"Ku maida ta, Cikin ?an uwanta,"

Duk yadda Gabriella taso ta kubce masu abun yaci tura, tana ji tana gani suka nuna mata fin karfi akan idonta Giants suka fuce da Gabriella...

Jiki asanyaye ta koma kan kujera ta zauna, idanunta suka cicciko tab da kwalla...

Matsawa yayi kusa da ita tare da sunkuyar da kanshi gab da fuskarta"fushi kike dani"? Ya faWa tare da Wage mata gira..



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________
'?=?%?=؋?=ؔ?>???

Yar dariyar takaici ta yi, "Elder kenan, ka jima kana nuna min fin ?arfi, wlh tun ranar dana gane asalin wa nene kai, na ji ka fita araina, wlh na tsaneka kamar mutuwa, babu abunda nake kwaWayi da ya wuce inga bayanka, dan Allah ka mutu mana, na gaji ! na gaji !! da irin ba?incin da kake ?unsa mini, wai kai wani irin mutunne? ko sau Waya baka ta6a jin nadamar irin zunubban da kake aikatawa ba? Na jima ina kokwanton anya kai mutunne? Saboda babu zuciyar imani a ?irjinka... "

Bata ?are maganar ba, ya daka mata tsawar da tayi silar rikicewarta tuni tasha jinin jikinta, nuna ta yayi da yatsan shi, "Bansan a ina kika samu ?warin gwiwar gaya min magana cikin idona ba, koda yake dama haka kike da kafiyar tsiya, ke kin sani bada son raina na jefa ki cikin kurkukun nan ba, kece sila, shisshiginki da bin kwakkwafinki ne suka ja maki, naso mu dawwama acikin farin ciki amma kin 6ata komai, wallahi ba don son da nake maki ba da tuni najima da kashe ki, amma saboda ?aunar da nake maki shiyasa na killaceki anan saboda kada ki tona min asirina..."

Cike da taikaici ta yi murmushi haWi da Wan girgiza kai ta ce, "Ai ni tuni kajima da kashe ni, me kuma ya rage? Tsawon shekaru ashirin rabona da inga hasken rana, tsawon shekara ashirin rabona da inga wani dangina, dan Allah ka kashe ni in huta, na ro?e ka Ka kashe ni mana...!" cikin jin kunar rai ta faWa.

Lumshe idanunshi yayi akan fuskarta tare da buWe su, da wata irin siga ta jan hankali yace,

"Idan na kashe ki, kamar na kashe kaina ne, nafison in ma mutuwar zakiyi mu mutu atare."

"Elder kenan, makomarmu ba zata ta6a zama Waya ba, ni da nake so In mutu Cikin rahamar ubangiji, taya za kai min fatan mu mutu atare?"

Tuntsirewa ya yi da dariya, cike da tsana take kallon shi....

"Bazan bari ki 6ata min ranata ba, yau ina cikin farin cikin zagayowar ranar da muka kafa gidan kurkukun ?addara, ko murna baki tayani ba..."

Wani kallon rainin wayau ta jefa ma shi a cikin ranta ta furta, "In Sha Allah yau ce rana ta ?arshe da zaku yi black night a duniya, Ubangiji Allah Yasa su kawo maku farmaki su tarwatsa tawagar azzalumai..."

"Me kika ce?" Firgigit ta kalle shi cike da fargaban kada ace Yaji ta, duk da ta dai san a zuciya tayi maganar amma tasan yana iya karantar abunda take sa?awa acikin zuciyarta.

"Kaji nayi magana ne?" Girgiza mata kai yayi.

"Ni zan Shiga fadata, ko zaki raka ni?" Banza tayi da shi,

"Ki kula min da kanki." Bai tsaya yaji amsarta ba, Ya 6ace ma ganin ta..

Me ya faru bayan Giants sun tafi da Gabriella?

Tana ta kuka tana tirjewa, a haka suka mi?i hanyar komawa cikin Kurkukun da ita, adaidai zasu karya wata kwana kwatsam saiga Tsohuwa Inno ta fito daga fadar elders karaf idanunta suka hango mata Gabriella...

A sukwane ta dakata da yin tafiya ta zuba mata idanu, yarinyar da take nema ruwa ajallo sai gata yau Allah Ya haWasu..

Dariyar mugunta ta saki mara daWin ji kamar haniniyar jaki, A firgice Gabriella ta kai dubanta ga tsohuwa Inno jin sautin dariyarta, Lokaci Waya yanayin fuskarta Ya canza ganin matar da ta tsana fiye da mutuwarta.

?arasowa Inno tayi gaban su da sandarta ta tsaya cike da sha?iyanci ta ce, "Wanake gani kamar Gabriella? Yarinya mai ran ?arfe, ashe rai kanga rai? dama saida raina ya bani baki mutu ba, Kina nan da ranki, kai! amma fa nayi mamakin tayaya akai kika rayu bayan tiyatar dana sa giant yayi maki? Wani mai imanin ne yayi jinyarki?

Banza tayi da ita, ta6e baki Inno tayi tare da kallon giants din dake a ru?e da ita, "A wace Bola kuka tsunto sharar nan"? Wannan kalma ta ?ona ran Gabriella, ta ?ulu sosai.

?aya daga Cikin Giant Winne Ya ce, "Daga Wakin Khala, Elder ne ya bada Umarnin mu dawo da ita cikin yan uwanta." Ta6e baki Inno tayi, "Dama nasani, duk cikin kurkukun nan babu mai zuciyar imanin da zai iya jinyarki in ba ita khala Win ba, amma fa na tayaki ba?in ciki, da kin mutu da kin huta."

Ta faWa tana le?en fuskarta, warin bakinta duk Ya cika hancin Gabriella, wani irin yun?urin amai ta fara Ji..

Bin ta da kallo tayi daga ?asa har sama, saboda tsabar fitsara hada sanya hannu ta Wage rigarta ta tura kai tana le?en gabanta don taga aikin da akai ma wurin, duk tayi shiru bata hanata ba...

?agowa tayi fuskarta dauke da shu'umin murmushi ta ce, "Kin Winku da kyau, wuri fa yayi kyau, naji dadi kinga yau Manyan Ba?in mu zasuyi badago a kanki..." ta faWa tana sakin dariya.

?ululun ba?in cikine Ya tokare makoshin Gabriella sai huci take kamar zakanya, kashe mata ido tsohuwa Inno ta yi kafin ta kalli giants din dake a ru?e da Gabriella ta basu Umarnin su tafi.


Kamar jira take Giants Win subar wurin dama zuciyarta ta kawo wuya, aikuwa tayi wani irin kukan kura da iya ?arfinta na karshe ta daka uban tsalle tayi zaman yan bori akan Tsohuwa Inno, kamar Allah ya aikota ta dinga gartsa mata cizo da yakushi tsohuwa inno ta dinga kokarin Kayar da ita ?asa amma takasa, sai da ta kekketa fatar ?wal?walin kanta, duk ta ciccisge mata yar hurhurar dake a kan, tayi ma kwallan kan rantali da akaifarta duk ya yi jaga jaga da jini...

Wa'iyazubillah! Wata irin kururuwa tsohuwa inno ta saki tare da jijjige jikinta silar hakan yasa Gabriella ta kundumo ?asa timm! nan take Inno ta rikiWa ta zama wata mummunar halitta mai razanarwa, gurnaninta kaWai Ya isa ya rikita kwakwalwar mutun.

Da mugunta ta durfafi Gabriellah, a lokacin so tayi ta kasheta ta hanyar handameta, aikuwa ta watsa aguje ta nufi wata doguwar hanya mai duhun gaske, bin ta Halittar ta yi aguje duk inda ta taka sai floor Win gurin ya girgiza saboda girman halittar, gaba Waya Gabriella ta rude ta razana ta rasa ina zata boye kanta, don tasan muddin Tsohuwa Inno ta kamata Sai dai buzunta...

Sa?o da lungu ta dinga bi, tana tsaka da yin gudun ta faWo cikin wani ke6a66en wuri mai tarin komatsai ga shi babu wadataccen haske,

Gurnanin dabbar da ta jiyo ne yasa ta furgice ta soma ja da baya, cikin rashin sani tana ?ara Waga kafarta ta taka wani wuri gaba Waya ?asan gurin ya rubza da ita ta zurma cikin wani rami wanda bakomai ne a cikinsa ba face zallar jini mai ?arnin gaske ga Woyi, shi wannan tafkin asalin samuwar shi daga Wakin fiWa ne na gidan kurkukun ?addara, jinin mutanan da suke feWewane idan ya gangaro ta cikin pipe kai tsaye yake shiga cikin tafkin anan ya ke taruwa in suka tashi amfani da jinin zuwa suke su dibe shi a cikin tuluna.

Wa'iyazubillahi! kamar zata haWiye zuciya saboda azabar ?arnin da ya toshe ?ofofin hancinta, jinin ya mamaye jikinta Iya wuyanta ne awaje sai ihu take tana kokawar fitar da numfashin ta.

Ko da tsohuwa Inno ta faWo wurin ta hango Gabriella tana ihu cikin jini, nan take ta RikiWa ta dawo ainihin suffarta ta mutane, wata irin mahaukaciyar dariya ta saki, ganin ha?arta ta cimma ruwa, Saboda zalunci maimakon tabarta haka sai da tayi mata sihiri ta ?arasa nutsar da ita cikin jinin kanta ya shige gaba Waya, tasan bazata rayu ba, sai dai a fito da ?asusuwanta in namanta ya gama zagwanyewa.

A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Ya?i kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin Wakinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ?ara tashi ganin har dare yayiW'


_______ &?=?y? &?BLACK NIGHT=؀?=?y? &?_______


?arfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun ?addara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun ?addara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya karaWe ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda kiWan ke tashi..

takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya ?addamar da gidan kurkukun ?addara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna Wokinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ?ara ?arfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu le?a muga meke wakana adaren Black NightW'S'

?aya bayan Waya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ?ure kuri adakansa, ?arshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne.


Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na ?asar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban san?o dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye.

A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu ?aton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da ba?i a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai ?yan?yami in ya kallesu sau Waya bazai sake marmarin kallon su ba.


Tawagar matsafan kurkukun ?addara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu ba?a?e har ?asa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar ?warangwal.

Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini.

Gaba Wayansu sun hallara a tsakar kurkukun, ?wansu da ?war?watar su ko'ina ka kalla sune birjik.

Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun sa?o da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya ?arfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su.

Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka daWe suna she?e ayar su.

Surutunsu Ya karaWe ko'ina, da wani irin Yare mara daWin Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nishaWi.

Daga kan ground floor Win gurin wani haWaWWen red carpet ne aka shimfiWa tun daga fadar mai girma Elder har zuwa ?arshen bango inda aka ?awata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an ?awatasu da kayan ado.

Daga can gefe Waya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne Wauke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu haWarin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table Win, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman Wawisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan ma?walashe.

Yayin da makaWan suke ta yan kiWe-kiWe da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe ha?ora suna kallon su..

Gaba Waya sun ?agara a fara shagalin, fitowar Elders kaWai suke Jira..


Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba Wayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ?ari.

Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya faWa yana bin su da kallo..

"Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin gaWar makaho bace, ?ananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sau?i ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su ?etare ba, mune masu ?arfin iko, da izinin mu komai ke wakana, in muka so Da kalma Waya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!"

Gaba Waya suka tuntsire da dariyar sha?iyanci, bayan sun tsagaita da yin dariyar Elder Ya dubi wanda yayi maganar Jan Le6e, "Na ji daWin bayanin ka.." Ya faWa tare da maida dubanshi kan Elder din dake zaune gefen Jan Le6e ya ce, "Mutumina Jan wuya, Ko akwai labari? Ko kuwa sai mun sha mun bugu don nasan halinka da miskilanci kafi sakin baki idan ka hau kan network..." Cike da sha?iyanci ya furta, "Musamman in akwai mata da giya anan linzamina yake kwancewa..." Dariya suka saka gaba Waya....

"Baka da matsala mutumina, yau ranarmu ce, saika za6a ka darje," ?asaitacciyar dariya jan wuyan ya saki.

"Jan kunne na ji ka yi shiru baka ce komai ba"? Ya faWa Yana duban shi.

Muskutawa ya yi ya gyara zaman shi, "Elder, Ni bani da abun cewa, Hankalina Ba a kwance Yake ba, ban ta6a tsintar kaina a yanayi na jin faWuwar gaba irin na yau ba..." gaba Waya suka maida hankali kan shi.

Da kakkausar Murya wani mai zafin rai a cikinsu wanda suke kira jan harshe Ya ce, "Wannan wani irin zancen banza ne? Ka kuwa san me hakan Yake nufi? FaWuwar Gaban Elder yana nufin mummunar ?addara zata Iya afka mana, tun wuri Ka dakatar da zuciyarka, ba'asan Elder da raunin zuciya ba..."

Yana ?are maganar Jan Wuya Ya ce, "Ka gafarce ni, kaima kayi kuskure a maganarka Jan harshe, Elders sunfi ?arfin mummunar ?addara, ita kanta ?addarar tsoron mu take ji, shiyasa bata ta6a gigin afka mana ba..." Da gadara suke magana.

(Duniya budurwar wawa, Wanda Ya 6ace Ya 6ace.....)

"Jan wuya, kai Win na dabanne, namijin duniya, wanda bai ta6a karaya ba, ina son ?warin gwiwarka mutumina..." Ya faWa tare da yi masa alamar jinjina da babban yatsansa, kafin Ya dubi Jan Kunne "Kai kuma, kada na kuskura na ?ara jin ka ambaci faWuwar gaba, nasan me ke damunka, da zarar kaga mata masu manyan mazaunai zaka wartsake..." Dariya suka saka gaba Wayan su.

Kafin wani ya ?ara furta kalma a cikinsu, Evil Giants masu ?irar samudawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login