Showing 51001 words to 54000 words out of 391264 words

Chapter 18 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2570

farkawa ba, may be har yanzu baka gama dawowa normal ba, a hakan ma na samu kwanciyar hankali, ganin ka da nakeyi ba karamin faranta raina yayi ba" ya fada yana Wan murmushi sama sama.



"Nasan kana jin yunwa bari nayi magana akawo mana abinci" wayarsa ya zaro daga aljihunsa har time din yana lura da kallon da danish ke jefa mashi har ya fara jin shakkar ko dai ifritan dake jikinsa ne suka motsa, dauriya ce kawai irin ta Hateem



"Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya faWa tare da mi?e ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya mi?a ma Hateem wayar, Cike da zumuWi ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi

Har saida gabanshi ya Wan faWi ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka dam?i waya.



da sauri ya dago suka haWa ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske.



Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya.



"Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba.



Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne.



Bugu uku Chief yayi picking call din



"Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"?



"Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun Wazu ya?i yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"?



muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar.



Da buWar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki.



"Babu, Mu kaWaine"!



"Uncle ka sanya sojoji su yi maku ?awanya saboda yaron ba shi Waya bane, bana so asamu matsala"



"In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar



Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais.



"Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka Wauka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ?ara ha?uri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran.



Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ru?e da faffaWan faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu bu?aci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci.



Ya Wanyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba.



Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu faWo ?asa.



"Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"?



Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfiWar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi.



ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message.



_I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_



Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata"



Tuni ?amshin soye soyen da aka kawo masu ya buWe hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba.



Farantin farko yana dauke da ban?ararrun kaji anyi masu jar suya sai mai?o sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, Wayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun haWo masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu bu?ata......



'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman haWiyar yawu.



Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us.



Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,.



Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya Wan buWe kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya haWiye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya Webo sakwarar ya mi?a mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba...



Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya faWo masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane.



BuWe baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su...



Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne Wauke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna...



Bayan sun gama da plate din sakwarar, Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna.



Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan coconut milk da fresh juice.



Sauke farantan hateem yayi can gefe Waya ?asa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi Waya dafe da bayan shi, Wayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu waWanda zai dinga gani yana Webe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba Waya hakan ba karamin Waga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma ?asa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya buWe idanunsa, dakyar ya samu ya Wan buWe su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma ya?iya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai Wan tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani Wan cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma.



Kafin ya gama Wauke Wauken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ?an?ame shi da hannayensa da farko ya Wan ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai daWi yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya ?an?amesa kamar wani yace zai ?wace masa shi.



Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda daWin da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa.



Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar raWa yayi mashi magana.



"Do you feel what I feel about you?"



Ya faWi hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa.



Kamar daga saman yajiyo daddaWar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think"



wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai haWiye sa.



"Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ?ara jin muryar shi.



"No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba



"Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar

Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara Yin tozali dakai, Naji na kamu da matsananciyar kaunarka, duk da bansan wanene kai ba, amma naji ka kwanta min araina, ka sace min zuciyata, bab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ban abinda yafi jan hankalina gare ka shine kama da muke da juna, Ina jinka tamkar ni na haifeka, Allah ne kadai yasan son da nake maka Danish, wallahi bana son rabuwa dakai, bana son in tafi in barka, don bani da yarda zaniyi da natafi da kai" Kalaman da yake furtawa daga cikin zuciyarsa suke fitowa, abunda ke ransa ne yake bayyana masa ko ya rage radadin da yake ji na kaunarsa .



A hankali danish ya Wan buWe idanunsa yana satar kallon fuskar hateem dake a dab da tashi, wani irin kallo yake jifar shi da shi mai wuyar fassaruwa batare da prime minister Ya ankara ba.



"Bansan su wanene Iyayenka ba, bansan dalilin dayasa sukayi watsi da rayuwarka ba, amma bana tsammanin akwai wanda zai samu Wa kamarka ya jefar sai dai idan da wani dalilin"



Runtse ido danish yayi sam baya son anayi mashi maganar iyayen sa.



Muryarshi na dan rawa ya furta"ka daina yi min magana akan iyayena, bana son su bana son duk wani abu daya shafe su, If I could see them, I would kill them."



A ruWe prime minister ya dubi fuskar danish da tsantsar mamakin yadda kalaman suka fito daga bakinsa, har kokwanto yayi anya shi yayi maganar?



Ko da yai yunkurin tambayarshi meyasa yace haka, sai jinshi yayi shiru alamar wani baccin ya dauke shi....

Ha?i?a furuncin da ya yi akan iyayen su sun tada masa hankali, sun tsaya masa a ?ahon zuciyarsa, duk da baisan dalili ba amma yaji fargaba aransa, musamman da ya ambaci Idan ya gansu zai kashe su .......

Lumshe idanunsa yayi, tare da ?ara janyo danish ajikinshi, yaci gaba da Wan bubbuga bayansa kamar mai lallashin ?aramin yaro a haka harshima baccin yayi awon gaba dashi, wata irin iskace mai ni'ima taci gaba da kaWa wurin da suke.......



gaba Waya abun da ke faruwa akan idanun Yazrin, sai dai basu samu damar jin komai da suke tattaunawa ba atsakanin su saboda akwai tazara.



Nannauyar ajiyar zuciya Gimbiya mujeedat ta sauke tare da kallon Yazrin dake a gefenta"gwanin ban sha'awa, sun burgeni, a yadda suka kwanta kamar Uba da Wansa, ban ta6a jin zafin rashin Wa bamiji ba sai ayau dana kalli Hateem da yaron nan, wallahi sunyi min kyau sun tafi da imanina ......." Cikin sanyin murya Gimbiya mujeedat tayi maganar.



Jikin Yazrin yayi sanyi lakwas tamkar wadda aka zarewa laka, idanunta sun ciko tab da kwalla ta soma magana ba tare data janye idanunta daga kan shimfiWarsu Hateem ba.



"Daddy ya bani tausayi, na tausaya masa mommy, daga shi har matashin nan, Ina kaunarsa Ina jinshi kamar Wan uwana na jini... " da raunatacciyar murya tayi maganar.



"Mommy abun da yafi ta6a zuciyana, yaran ba su da kowa a daji aka tsince su kamar yarda naji akhi owais Ya faWa, wallahi banji dadin yadda Su oum saratu suke jifarsu da munana kalamai ba, ni abun da ya daure min kai Yaran sunyi kama da family din daddy sosai"





Jinjina kai Gimbiya mujeedat tayi ba tare da ta iya furta komai ba, Ta yun?ura ta mi?e Cikin takun nutsuwa Ta nufi shimfidar su hateem, Yazrin na zaune bata bi bayanta ba, bakomai zuciyarta ke tariyo mata ba, face lokacin data haifi baby boy din su da suka rasa, ha?i?a taji bakin cikin da bata samu damar ganin ko da gawarsa bane, taso ace ko da fuskarsa ne ta gani, tuna wannan yasa taji hawaye sun taru cikin idanuwanta



Adai dai bakin shimfiWar ta Wan zu?unna tana kallon danish from head to toe, yayin da zuciyarta ke azalzalarta da kaunarsa, sai kallon shi takeyi babu kyaftawa, ranta ne ya raya mata wani abu da bata da tabbaci akanshi, hakanan taji tana son ta jaraba gwadawa, Mi?ewa tayi da sauri ta zagaya ta dayan bangaren da farantan abincin da aka kawo masu suke, ta zaro ?aramar wu?a ta yanka fruit, ta dawo bangaren inda danish Yake ta zu?unna duk akan idon Yazrin da mamaki yagama cikata, zuciya da sake sake arude ta furta me mommy zatayi wu?a"? hankalin ta yadan tashi tsoron ta kada ta aikata wani abu duk da tasan hasashenta bazai ta6a zama gaskiya ba...



A hankali ta Waura ziraran yatsun hannunta kan sumar danish ta ru?o ?asanta, Cike da fargaban kada su farka, tana yi tana kallon fuskokinsu cikin kwanciyar hakali suke fitar da numfashinsu, bacci yayi dadi



Yatsun hannunta na kerma ta yanki sumar kan danish da wu?ar, ajiyar zuciya ta sauke tare da mi?ewa ta mayar da wukar cikin kayan abincin kafin ta juya tana faman sauke ajiyar zuciya ta nufi Yazrin tunkafin ta ?arasa yazrin ta mi?e tana tana fadin"mommy! Meyasa kika datsar mashi gashin kai"! Idanunta azare ta fada tana nuna ziraziran gashin danish da gimbiya mujeedat ta cira daga kanshi



Fuskarta dauke da murmushi tace "Ki kwantar da hankalin ki, kinsan dai mom dinki ba matsafiya bace," dariya yazrin tayi"ina kyautata maki zato a koda yaushe Rabin raina" lumshe ido gimbiya mujeedat tayi"ki ajiye min gashin nan a wurinki, Idan muka koma gida zan tambaye ki shi" da sauri Yazrin ta kar6i gashin daga hannun mom mujeedat, ta cire cover din wayarta ta Waura gashin abayan wayan kafin ta mayar da cover din sosai ta matse shi ta yadda bazai ta6a faWowa ?asa ba.



"Yanzu ki zo mu koma dinner hall, kada aji shiru babu ni babu hateem bayan saboda mu akayi taron" amsa mata yazrin tayi da toh" a jere suka nufi hanyar fita daga garden din, suna tafiya Yazrin na waiwayon shinfidar su danish, har saida ta 6ace ma ganinta tukunna ta dauke idanunta daga gare shi.



*Dinner Hall*



Bayan zahra ta kammala yin wayar, Jiki na rawa ta dawo Ciki tana nema unaisah, kamar zata zauce sai ?an waige waige take yi babu ita babu alamarta, kusan sau uku tana zagaye tsakar hall din wurin neman unaisah amma babu ita, zuciyarta ba ?aramar karaya tayi ba, Har cikin ranta bata ji dadi ba, saboda taso su sake ganawa da juna, Yarinyar ce ta kwanta mata aranta, musamman yadda ta sakar mata fuska har ta amince mata su kayi hutuna, dabara ce ta faWo mata, ganin Waya daga cikin matasan ?an matan a tsaye tana kallon masu yin rawa akan dance floor sai murmushi take saki, da sauri Zahra ta nufe ta, muryarta da sanyi ta furta"sannu baiwar Allah" firgigit batool ta dubeta da alama ta razana don bata tsammaci jin muryar wani a kusa da ita ba



"Kiyi ha?uri na baki tsoro ko"? da fara'a zahra tayi mata maganar, batool kuwa sai kallon bakuwar fuskar takeyi ta?i tanka mata, gani take kamar zata cutar da ita ne tun da ta fahimci basa son su



Mi?a mata hannu zahra tayi"ni suna zahra, ke fa"? Cike da rashin yarda ta furta"batool" muryarta da Wan rawa tayi maganar, ba tare da ta Waura hannunta asaman na zahra ba, nan take zahra ta fahinci tsoron ta take ji hakan yasa tace"ki kwantar da hankali yar uwata, Bana Waya daga cikin waWanda suka ci muku mutunci Wazu...." still bata saki fuskarta ba



"Shikenan, yanzu ki faWa min ina ?ar uwarku Unaisah? Muna cikin magana da ita Wazu aka kirani awaya sai naje amsa kiran kafin nadawo na taras bata nan, Ko kinsan inda take"!?



Sai da ta ambaci sunan Unaisah batool tafara kyafkyafta idanunta tana bin dakin taron da kallo, sai yanzu ta tuna da tsawon lokacin da bata ga gifcin unaisah ba, kuma bata cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login