Showing 333001 words to 336000 words out of 391264 words

Chapter 112 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2650

kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ru?e cikin na juna.



Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba.



"To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a Waki."



Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana."



Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne."



"Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki."



Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba"



"Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku daWe dan Allah, zan ma kira Abie dinku in faWa masa"



"Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba."



A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, buWe motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, ?arar horn din motar da ya ji ne yasa shi Wan dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan.



Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta buWe backseat, ta Wauko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School.



"Yaya Shureim ina wuni?" Ta faWa da fara'a akan fuskarta,



Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?"



"Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"?



"Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school."



Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta faWa tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna.





Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta.





"Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?"



Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya."



Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo."



Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya."



Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?"



"Yaya Shureim mu je zamu faWa maka."



Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi.





_____________________Obie Estate=?%?




Koda suka ?araso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga.



Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa Win Owais, Tunkan su ?arasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta.



Officers shidda ne suka yiwa motar tasu ?awanya,



Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" Waya daga cikin su ne ya umarta.



Bayan sun fito suka fuskance su.



"Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?"



Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya faWa fuskarsa a haWe don shi baya son abunda zai haWa shi da masu kaki...



"Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya Waga ba."



Benazir ce ta faWa idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta.



Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba, ta ji haushi ita da ta yi kwalliya don Taj ya gani sai gashi wasu na nema su riga shi gani.



Almost 3 times Anila tana doka masa kira baya picking, hankalin su ba ?aramin tashi ya yi ba..



"Ya zamu yi Benazir! Ya ?i Wagawa wlh"



"Keep trying, idan ba haka ba wadannan masu fuskar shanun ba bari zasu yi mu shiga ba."



Cikin harshen larabci ta yi maganar..



Murmushi Dr Shureim ya yi tare da Wan girgiza kanshi jin abunda yar'uwarsa ta fada, jami'an kuwa sun baza kunne da yake ba arabi da ace da hausa ko da turanci ta fada da taci na jaki.



Taj na ?o?arin fitowa daga toilet yana ta gungura wheelchair dinsa ya jiyo muryar Batool tana kwaWa masa kira,"Daddy, wayarka tana ringing, wani ne ke kiranka"



Har ya nufi ?ofar dakin sai gata ta faWo ko sallama babu, tana ta haki ta mi?a masa wayar tana fadin, "A falo ka barta saman hannun kujera."



Bai kar6i wayar ba sai cewa ya yi ta karanta mashi sunan me kiran, Wan zare ido ta yi kafin ta dubi sunan da ya bayyana akan screen din wayar.



"An..An..Antin Yu.. nai..sah.." da?yar ta ?are karatun a lokacin har kiran ya katse, Murmushi Taj ya sakar mata, "Auntyn Unaisah ne, kin yi kokari daughter, Allah ya yi maki albarka."



Ya faWa tare da kar6ar wayar, sai faman sakin murmushi ta ke yi, tana son taji an yabeta in ta yi abu.



"Ina ?ar uwar taki ne?"



"A Waki na barota kudundune cikin bargo."



"Bacci ta ke yi ne?"



Girgiza kai ta yi, "Waya ta ke yi da Chief, Daddy baka ji yadda take kashe mishi murya ba hada shagwa6a fa," fashewa yayi da dariya har fararen hakoransa suka bayyana.



"Sha?a mini in ji me take ce masa?"



Da biyu ya yi maganar saboda yana son yadda Batool take kwaikwayon maganar Angel dinsa, aiko da yar shagwa6a ta ce, "Shine ka tafi baka jira na tashi daga bacci ba, pls kada ka daWe ka dawo gida bazan jure zama batare dana sanyaka a idanuna ba"



Tuntsirewa Taj ya yi da dariya, Itama dariyar ta kama yi yadda kasan uba da ?arsa.



"Daddy, ka ji daWi?" ?aga mata kai ya yi, "Sosaima, kema da kika bani labarin ga wannan" Ya fada tare nuna mata robar peanut din da ya aje kan drawer bai kaiga fara ci ba, da sauri taje ta dauka tare da yi ma shi godiya.



Fitowa ta yi daga Wakin jikinta a sanyaye, kwata kwata babu walwala, a saman stairs ta zauna hawaye cike tab da idanunta take kallon Peanut din da daddy Taj ya bata, A hankali ta soma Webowa tana afkawa a baki tana ci, hawaye na sintiri kan kuncin ta, Allah kaWai yasan me ke damun ta.



Fitar Batool ke da wuya, wani kiran na Anila ya sake shigowa wayar tasa, picking ya yi tare da kara wayar a kunne.



Bayan sun gaisa ne Anila ta fada masa gasu a bakin gate na gidan security sun hana su shiga ya taimaka ya yi masu hanya su shigo.



Shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai dakile shigowarsu saboda baya son suga halin da yake a ciki, ga Chief ma baya nan, bayan haka ba'a son ma kowa yasan wani abu dangane da farmakin da suka kai, in har su Anila suka gan shi zaune kan wheelchair dole hankalinsu zai tashi harma su nemi jin me ya faru da shi..



"Taj na ji ka yi shiru baka ce komai ba?" Muryar Anila ce ta katse tunanin da ya ke.....

Muryarsa a dabarbarce ya furta, "Anila meyasa baki kira kin fadamin zaku zo ba?"



"Banyi tunanin yin hakan ba, saboda na ga Almost weeks kona kira bana samunka."



"Anila, sai dai ku yi hakuri ku koma gida, yanzu bama nan mun je yin meeting a headquarter Win mu."



On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help."



Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka.



Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan,



"Okay, ku Wan jira"



Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya Waga kiran..



"Yalla6ai mun yi ba?i, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faWamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su."



Koda jin wannan maganar Chief Win ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki.



Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa.



A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su.



"Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ?etare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu.



"Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daWe."



Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ?arasawa ?ofar ta zuge suka shiga bakinsu Wauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi.



Time da suka buWe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ?arasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa Win ma da?yar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da Wayar ?afarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta.



Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi.



Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta.



Har saida suka ?araso kafin ya Wan Wago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya Wan ji gaban shi ya faWi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haWe rai tare da kawar da idanun shi.



Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake.



Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a da?ile ya amsa mata..



"Ku zauna."



A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi....



Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ?walla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba..



"Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har sa?o na tura maka akan ka taimaka ka haWani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..."



Hannu ya Waga mata tuni ta haWiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?"



?asa-?asa da murya Anila ta raWa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi ha?uri mu yi abinda ya kawo mu, kinga da?yar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu.



Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan."



Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh.



Dakatawa ta Wan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ru?e da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ?arshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruWani...



"Zan iya ganin Videon??"



Da sauri tace "Eh," Ta faWa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta mi?e taje gaban shi ta mi?a ma shi.



Bayan ya kar6a, lokaci Waya hankalinsa ya tashi matu?a, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya Waure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya Wan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle Win Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada.



A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?"



Idanunta cike tab da ?walla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din"


Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaWa sun Wan yi ja,



"Ku sha lemun" Ya faWa yana nuna masu drinks din..



Mi?a hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye..



"Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya ?an-iya shine full name na uncle dinki ko?"



Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ?arashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa.



Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi...,



"Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?"



Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously."



A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe Waya.



"Ina sauraronki! FaWamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta Wan yi tana haki kamar wadda tasha gudu.



Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta Wan kur6a.



Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari..



*bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ?arshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ?asa rabin jikinta a cikin toilet=?G?*





Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci Waya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haWi da yi mata magiya akan ta bude amma ta?i saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ?walla.


"Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta.





Da?yar ta iya tattara ?arfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta.



A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba Waya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ?arta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta.



Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ?ura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, mi?a hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ?arya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ?ara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ?arfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ?o?arin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ?arfinta na ?arshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba Waya gangar jikinta ta dawo cikin toilet Win kanta ya daki floor, A zabure ta mi?e ta watsa a guje ta nufi ?ofa sai dai me? Kafin ta ?arasa ?iiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ?ara ta yi da ?arfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ?a??arfa jikinshi sanye da ba?a?en kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login