Showing 282001 words to 285000 words out of 391264 words

Chapter 95 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2646

motarsu..

Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish..

"Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su

"Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..."

yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay"

"Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su..

"Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su.

"Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi..

Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.."

kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..."

Wan zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar Wan aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi."

Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku"

ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi"

murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face Wan uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba.

tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa.

A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa.

Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa.


"Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking Winta already.."

dafe kai yayi da hannu Waya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah..

"Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota"

"Okay, sai naji daga gare ka"

Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka.

Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown Win jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse.

Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ?ankance...

Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba

A faWace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki"

Make mashi kafaWa tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba, anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba"

?aure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka ?yaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..."

Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba kaWan ba.

________________________________
'?=ؔ?


Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist Winsa Waure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom Win nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki..

Yatsun kafafunta Ya hango ta ?asan labulen daya Wage sai kerma suke ...farat Waya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa bayan kwanakin da suka shafe batare da sun nemi junan su ba, kome ya kawota bedroom dinsa? Aransa ya ayyana hakan.

Yi yayi tamkar baisan da zamanta adakin ba, shaf shaf Ya shirya kan shi, Cikin Singlet fara da short.. kafin Ya koma gefen gadonsa Ya zauna tare da maida hankalinsa kan breakfast din da Taj yasa aka kawo mashi..

A tsanake Yake Cin abincin ta wutsiyar idanunshi Yake satar kallonta yayin da take buWe labulen Tana le?ensa ji take kamar taje garesa tayi hugging dinsa sai dai ina wani irin shakkar tunkararshi takeji, saboda maganganun data gaggaya masa marasa dadi ita kanta bata tsammaci zai dyauki tsawon kwanaki bai kula ta ba ko kiranta awaya bayayi..

Gajiya tayi da tsayuwar, ta fito daga bayan curtain din tayi tsaye tana kallon shi.

Tayi zaton baiganta ba, cikin sanyin murya tace"My man, fushi kake dani?

Banza yayi da ita hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.


"Baka ga halin damuwar dana shigaba, saboda kai ko bacci bana iyayi,nasan komai ya faru laifina ne, nina ja ma kaina amma ka yi hakuri ka yafe mim, I don't know if we'll meet again, maybe this will be our last meet, duk da bansan date da zaku tafi ba, amma inaji araina yau ne, shiyasa daddyna yace mu tafi part dinsa mu zauna, ni kuma na boye saboda inason muyi bankwana kafin mu rabu..."

ta faWa idanunta cike tab da kwalla, So hana ganin laifi, duk yadda yaso Yaki jin tausayinta hakan ya gagare shi, kalamanta sun ta6a zuciyar shi.

slowly ya dubeta daga kasa Ya fara kallonta, Hankalinshi ya tashi da ganin irin ramar da tayi, daga gani bata samun isasshen bacci ko bata cin abinci yadda ya kamata ga shi babu gyara a jikinta, kamar zai zubda mata kwalla saboda matsanancin tausayinta dayaji yasan duk akan shine ta shiga halin Damuwa...

Da spoon din hannun shi ya nuna mata gefen shi, cike da rashin kwarin jiki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya batare da ta kauda ido daga kallon shi ba..

Cup din tea Ya dauko Ya kanga mata abakinta, ganin taki buWe baki yasa shi furta"kisha" la66anta har kerma suke da sauri take kur6ar shi, nutsuwa yayi yana kallon throat dinta dake moving slowly.

sai da ta shanye shi kaf kafin ya dauki fork duk tana kallon shi Ya nannaWo noodles ya tura mata abaki, kamar yasan yunwa take ji, sakin jiki tayi ya dinga bata tana ci saida ya tabbatar taci ta koshi kafin ya aje spoon Win.

Ya ruko yatsun hannayenta a cikin nashi, bata ta6a jin kunyar hada ido da shi irin na yau ba, saboda rashin mutuncin data zazzaga mashi, sunnar da kanta kasa tayi

Cikin nutsastsiyar muryarsa ya ce"Ni ban ru?e ki a zuciyata ba, baki min komai ba, amma yanzu kin min abunda banji dadin shi ba..." a rude ta kalle shi

"Meyasa zaki takura kanki akaina"?

Cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, nasan nina tursasa maka akan kaje aman wallahi ni kadai nasan radadin da zuciyata keyi min saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya idan ka tafi, wallahi bana so na rasaka, kuma wallahi bada son raina na gaggaya maka magana ba, nayi ne kawai don in fahimtar dakai amma kaima kasan irin son da nake maka zan iya rayu wa dakai ahaka yadda kake, koda kuwa zaka makance ne ka kuturce, ka gurguce wlh zan rayu dakai bazan ta6a canza maka ba"

bata kare maganarba, ya rufe la66anta da yatsan shi, hakan yasa ta haWiye sauran maganar da bata amayar ba..

Nutsuwa yayi yana kallon siraran hawayen dake sintiri kan kuncin ta..


"Basai kin yi min bayani ba, na fahimce ki, ina jin abun da kike ji..." lumshe idanunta tayi tana jin wani iri aranta...


"Listen to me carefully, now I need your peace of mind because that way, I'll have the confidence to do everything, maganganun da kika gaya min tabbas banji dadinsu ba, amma ta wani bangaren sun taimakamin gurin Farfado da tunanina..." Ya Wan dakata Yana duban fuskarta, sill bata bude idanunta ba.

"Abu Waya da nakeso Kiyi min al?awari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, and even if I don't come back, be patient, Endure a life without me"

(sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba)

bai ?are maganar ba, ta katse shi cikin shesshekar kuka tace"Bazan iya daukar maka alkawarin nan ba, saboda bazan iya jurewa ba, bazan ma iya rayuwa batare dakai ba.."

fuskarta ya tallabo da tafukan hannayensa"meyasa zaki karaya Unaisah? Kin manta abunda kike ce? ...girgiza kai tayi"ka manta da abunda ya wuce, ba acikin hayyacina na fada ba.." murmushi takaici yayi

"Ki sama ranki zan dawo da raina da kuma Lafiya na, Nayi maki alkawarin hakan, zan kare kaina bazan bari na mutu ba.." bai kare maganarba tay saurin furta"baka ce In sha Allah ba"? Shiru yayi bai amsa mata ba.

Gyada kai tayi"tunda ba zakace ba, ni zanyi maka addu'a, Allah ya kare mun kai, Allah ya dawomin dakai da ranka da lafiyarka, in sha Allah, ko bayan kun tafi zan raba dare na biyu, rabi inyi baccin awanni kadan rabin In tashi tsakar dare inyi maku addu'a...." har cikin ranshi yaji dadin maganarta, kuma, Har time din bata buWe idanunta ba.

Batai aune ba, Taji safkar Yatsunsa agaban rigarta, a firgice ta bude idanunta, wata irin kunyace ta kamata ganin Yana maida mata front buttons Win rigarta, sakamakon gudun da tayi Wazu gaban rigar ya buWe batare da ta ankara ba, tun da yafara bata abinci yake ta kokarin gyara mata rigar saidai ya kasa saboda gudun masifarta.

Sunkunyar da kanta kasa tay, tasan yaga abun da take 6oye masa..

"Ranar dana dawo, what will you do when you see me?"

Ya fada tare da zame yatsunsa daga gaban rigarta ya maida tafukansa kan shoulders din ta kamar kanwarsa.

"I can't imagine how happy I'll be, I'll cry for joy and hug you tightly"

ha6arta Ya Wago da hannun shi"shi kadaine abunda zaki min"? Jinjina mashi kai tay,

"That won't be enough for me.."

"FaWa min me kake so"?

Kunnanta ya ruko tare da yi mata raWa bai ?are maganar ba, tay sauri toshe bakin shi da tafin hannunta, kamar wadda taji wani mugun abu, jikinta har rawa yake, His shyness enveloped her, and his sexy words made her burn with desire he also set his soul on fire, lumshe idanun shi yayi tare da ware su cikin nata, harara ta Wan watsa mashi tare da murguWa mashi small lips din ta.., kashe mata ido Waya yai tare da Wage mata gira batasan sa'adda ta saki murmushin gefen fuska ba, wato son da takema Danish irin unconditional love ne, idan tana tare da shi takan manta da komai, kamar dai yanzu da suke atare ta manta ma da hudubar da daddyn ta yayi mata kan hada jiki da sukeyi indai tana tare dashi mantawa take da komai shi kadai take gani kuma takeso ta kasance dashi.

Yana kokarin janye hannunta daga bakinshi, ba zato ba tsammani suka ji anyi knocking Win kofar, kallon juna sukayi wani irin faduwar gaba taji, sam ta sha'fa'a ta manta da daddynta da ke neman ta.

Muryarta nawa tace"nasan baiwuci daddyna bane, ni bana so naje part dinsa nafiso Inga tafiyarku tukunna, pls kada ka fada masa ina aciki, Ni zan boye..." wani irin kallo yake binta da shi, jikinta na kerma ta mike da sauri ta boye bayan curtain

Daga waje sukajiyo muryar Taj Yana fadin"Danish, Ka bude min ?ofa" mikewa yayi yaje gaban room door din Ya bude mashi.

shigowa yayi fuskarshi babu walwala Yace"Unaisah tazo nan"? Danish dabai Iya karya ba, Ya nuna mashi Curtain din da hannun shi"tana ciki" cike da takaici Taj Ya nufi labulen Ya Wage shi, wata irin gigitacciyar ?ara ta fasa kamar zata zauce, ta dinga ihu tana fadin daddy bazanje ba, Ka kyale ni, kabarni inga tafiyar ku"!


ga tausayinta yanaji amma ji yake kamar ya rufeta da bugu.

bai bata lokaci ba, Ya sungumeta kan kafadar shi, Ya juya ya nufi kofar dakin kuka ta dinga Yi tana mika ma Danish Hannu don Ya kawo mata dauki bawan Allah Yana ji Yana gani Taj Ya fuce da ita, baisan ko wannan zai kasance rabuwarsu Ta karshe ba, yana jiyo sautin muryarta daga waje cikin shesshekar take sambatu

_"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_

Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....

Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin jikinta duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________
'?=?%?=؋?=ؔ?>???

Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....

Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..


Agaban kofar shiga falon part dinsa, Ya danna Password din ?ofar, ta bude kafin Ya shiga da ita ciki, adai dai Lokacin Yan uwanta sun kabbara sallar La'asar da ake ta kira, anan falo Danejo ta shimfiWa masu prayer mat sun daidaita sahun su.

Kwatsam su ka jiyo kukan Unaisah hakan Ya Waga hankulansu a rude suka katse sallar, gaba daya suka kai dubansu ga Taj, sun firgita da ganin yadda Ya daukota a saman kafadarshi, sai hauka ta ke yi mashi, har suna hada baki gurin tambayar Taj meya faru da Unaisah.

bai bi takansu ba, Ya nufi bedroom dinshi da ita, adai dai lokacin Ummi da danejo sun sallame sallamarsu kusan atare suka mike tare da bin bayan shi.

Sai dai kafin su ?araso Taj ya datse ?ofar Wakin.

A saman gadon shi Ya wurgar da ita gaba Waya ta kife kan mattress din gashin kanta ya tarwatse

Yana huci Yace"shashasha, wlh kin bani kunya, wlh badan kaunar da nakeyi maki ba da yau saikin yabawa aya Zakin ta, bugun tsiya zanyi maki, wawuya kawai, ban ta6a zaton za ki min haka ba, har yanzu kina nan da kafiyarki ta kuruciya, saboda soyayya bakya ganin kowa da gashi, shi kadai kike tsoron ki rasa, na fahimci ma kinfi damuwa dashi akaina, nima fa hadani za'aje kurkukun, amma kwata kwata bata ni kike ba..."!


Da?yar ya ?arasa maganar saboda ?ululun ba?in cikin daya tokare makoshin sa.

A hankali Hawaye masu Wumi suka wanke fuskarsa.

Dagowa tayi agalabaice tana kuka ta girgiza mashi kai muryarta ashake ta furta"daddy ba haka bane, ka fahimce ni, kaifa mahaifina ne, wallahi na damu dakai, har abada bazan ta6a samun madadinka ba..."

bata kare maganar ba, Ya juya zai bar dakin yana huci, durowa tayi daga kan gadon da gudu ta nufe shi harya ruke handle din ?ofar, tay saurin rungumeshi ta baya ta zagayo da hannayenta kan stomach dinsa, ta ma?yal?yleshi cikin shesshekar kuka take lallashin shi tare da bashi hakuri..

su ummi sai bugun kofar sukeyi don ya bude masu.

Hakan da tayi masa ba karamin sanyaya zuciyar shi tayi ba, tuni ya sauko daga kan dokin zuciyar da ya hau, A hankali Ya ruko hannunta tare da janyo ta ya dawo da ita ta gaban shi, Yayi hugging dinta tightly, a hankali yake shafa sumar kanta, duk da halin damuwar da take a ciki sai da taji sau?in radadin da take ji a cikin zuciyarta.

cikin sanyin murya yace"komai ya wuce Unaisah, na daina fushi dake, raina ne ya 6aci amma yanzu na fahimce ki, kiyi ha?uri dukkanmu addu'arki muke bukata, amma kukan nan da kike yi da sanya damu aranki bazai ta6a canza mana kaddararmu ba, saboda addu'a ce kadai take canza kaddarar bawa, Ki yi mana addu'a Unaisah In sha Allah, zamu dawo cikin koshin lafiya.."

cikin kwantar da murya yakeyi mata nasiha, su Ummi dake tsaye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login