Showing 309001 words to 312000 words out of 391264 words

Chapter 104 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2601

zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci.


Abu Waya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci rabi ta tashi tayi nafila, wani sa'in in ta fara tsayuwar daren Har sai kafafunta sun fara raWaWi tukunna take dakatawa.

mafi yawan lokutta akan prayer mat bacci ya ke yin awon gaba da ita, Unaisah da Aunty Umminsu sai batool ne kadai sukasan da tafiyarsu kai farmaki sauran yan uwanta babu wanda ya sani abu daya da suka sani shine har yanzu suna shirye shiryen tafiya amma basu tafi ba, kamar yadda Unaisah ta sanar da su, tayi masu hakanne don kada su daga hankulansu yayin da ita kuma hankalin nata ba akwance yake ba, sai dai suna yawan tambayar meyasa Danish baya le?o su? kuma su an bar su anan ko nan zasu ci gaba da zama ne kuma yaushe ne zasu je kai farmakin, dakyar suke samu su shawo kansu ita da ummi, harta Danejo batasan komai ba dangane da kai farmaki ta dai san zasu je yin wani aiki kamar yadda Taj ya faWa mata, abunda yafi damunsu babu wanda ya kira su awaya balle su san awani hali suke a ciki....=ؔ?


A daren jiya ne ta farka tsakar dare da matsanancin faduwar gaba sakamakon wani mummunan mafarki da tayi, Hankalin ta ya tashi matuka jin yadda tsigar jikinta da zuciyarta ke tashi, gaba daya tarasa samun nutsuwarta saboda tana ji aranta wani mummunan abu ya faru da su, a lokacin idanunta sun makance burin ta kawai ta ganta a part din Chief don taga idan sun dawo ko basu dawo ba, hijab ta zura a jikin ta, batare da sanin kowa ba ta fito daga dakin daddyta dama anan suke kwana ita da Batool bayan tafiyar su.

Ta sauko down ta nufi main door ta falo, ta dinga ?o?arin buWe ?ofar ta kasa saboda security din dake a jiki, batasan menene password din kofar ba, har jaraba sanya numbers tayi sau biyu ana nuna mata wrong code tare da warning message.

zukunnawa tayi bakin kofar tafukan hannayenta toshe da bakinta don kada yan uwanta sujiyo ta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sai da ta gama hasala can zuciyarta ta ayyana mata me zai hana ta jaraba sanya kwanan watan da aka haife ta, cos ta sani tuntana karama mahaifinta baida password da ya wuce date of birth inta, cikin hanzari ta mi?e ta danna numbers din fortunately ?ofar ta buWe batai wata wata ba ta fuce aguje ta nufi part din Chief, ko tsoro bata ji dare ne fa sosai donma akwai hasken Electricity tamkar rana.

Fitarta keda Wuya Batool ta farka sakamakon fitsari daya matseta Bayan ta fito daga toilet din ta dawo dakin Sai lokacin ta lura babu Unaisah, hankalin ta ya tashi tana fitowa ta hango ?ofar Falon abude kasancewar Unaisah bata datse ?ofar ba, nan take ranta ya bata fita tayi cikin sauri ta nufi kofar harta kusa Isa kwatsam Ta tsinkayi muryar Ummi cikin Kunnanta.

"Babe Ina zuwa" cak ta tsaya da tafiya, Ummi ta nufo ta cike da mamaki take duban kofar falo data gani abuWe.

"Ina zaki haka da tsakar dare ko mayafi babu akanki? Wanene kuma Ya buWe kofar nan? Ko wani ya shigo ne?

cikin rawar murya ta fada mata babu Unaisah adaki, Da jin haka Ummi ta ruko hannunta suka bi bayan Unaisah, fitarsu keda wuya kofar falon ta datse silar bangazar da sukai mata..

Suna fitowa suka hango Unaisah tsaye agaban Security officers din gidan ta ru?e qugu, ashe sun ganta lokacin da take gudu tana kokarin karasawa ga kofar shiga bangaren Chief.

a hanzarce suka kewata suna tambayarta ina zataje da tsakar daren nan? Gaba daya sun fahimci bata acikin hayyacinta sai haki take muryarta na rawa ta furta wurin Chief zataje.

Officers din sukace mata ay basu dawo ba, don haka ta koma inda ta fito, ta fashe da kuka tana fadin ba inda zataje, ita ta gaji da zama cikn fargaba kawai su kaita inda suke.

rigima ta saka masu duk yadda suka kaiga zare mata ido da yi mata tsawa akan ta koma takiya har takaiga wani Soja yai kokarin kai hannu da niyar ya Wauke ta aikuwa ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa mashi fata, ranshi ya 6aci matu?a harya daga hannu zai kwasa mata mari cikin zafin nama officer din dake a gefen shi Ya dam?i hannunsa da kakkausar murya yace"karka kuskura, In har ba so kake ka rasa aikin ka ba"

Yana huci Ya fusge hannun shi ya juya yabar wurin, lallashin ta suka cigaba dayi don su samu ta koma tace masu in har suna so ta koma su bude mata kofa ta shiga ta dauko wayarta data bari, Officer din yace ta fada masu inda ta ajiye wayar zasu kawo mata zuwa gobe yanzu dare yayi taje ta kwanta, kin fada masu tayi tace itama batasan inda ta ajiye wayar ba sai ta shiga zata duba, kuma a yanzu take son wayar"

Ba yadda suka iya da ita adole suka kira Layin Agent zahra saeed daya daga cikin na hannun Chief amintattunsa, saboda ba wanda zai iya bude kofar idan ba su din ba.

Saboda rigimar Unaisah yana bacci tare da iyalinsa yayi recieving call din su, bayan sun sanar da shi abunda ke faruwa yace su dauke ta su mayar part din, Officern yace mashi yalla6ai ba fa yadda zamuyi da ita, abokin aikinmu da yai gigin ta6a ta cixo ta gartsa mashi har saida ta fasa Fatar shi, yana can yana jinyar kan shi" da jin hakan agent zahra yace"tafi karfin ku ne? wai ma wacece acikin yaran" kallon ta officern yayi meye sunanki" muryarta ashake tace Unaisah..

"Sir sunan ta Unaisah, tana launin ido ruwan toka" da jin hakan okay yace su jira shi.

Adai dai lokacin su ummi suka karaso tayi mamakin ganin Unaisah tsaye gaban Security Officers, Hijab din jikinta ta jike sharkaf da gumi ta hade rai kamar bata ta6a dariya ba, tambayarsu tayi meke faruwa ne, anan officers din suka sanar dasu komai daya faru, batai mamaki ba ta riga tasan halin kayanta in taso abu kamar zawo take bata da uziri ko kaWan.

Batool ta tausaya mata sosai, ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su...

Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buWe ta.

Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buWe kofar daga can inda yake.

Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa Wauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba Waya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su.


Suna shiga Wakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faWo kan floor, cikin sauri ta dau?i hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta"

Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruWu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta.

Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer"

"To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ?awarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"?

Da mamaki Unaisah ta ?ara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba.

"Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar..

"Zan faWa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba..

Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya Waure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ru?e fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call.

"Kin tabbata shine"?

"Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.."

lamarin ya Waure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta.


Kafin wani ya ?ara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne.


Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faWa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke"

kafin Ummi ta shigo Wakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu.

Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta.


Morning

Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi.

"Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faWa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faWa, sai uban kasusuwan wuya..

In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.."

Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi..

"Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ?are maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haWiye shi.

"Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daWi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faWa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba,

Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"?


Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su.

A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba Waya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy.

"Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaWan.

mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su.

Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru"

Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira.


zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buWo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta Wauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya.

Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call Win tayi tare da kara wayar a kunnanta..

"Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya.

"I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita"

On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School.

basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?"

yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma ya?i kulani ay da tuni mun yi maki ?ani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari.

tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki"

murmushin ya?e tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faWa maki yana da au..." bata ?are maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call Win tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata Wauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuWi, kafin ta ?arasa Ummi da Batool suka bi bayanta da Wan gudun su.

At same time motocin su ka yi parking, a gaggauce Officers dake tsaron gidan suka Yi masu kawanya tare da yin hanzarin buWe cardoors, Adai dai lokacin Unaisah ta zuro kofarta waje wani burki Taci idanunta azare take Kallon motocin Cike da fargaban wa zata fari gani.

CO ne Ya fara fitowa cikin hanzari ya zagaya bayan motarsu ya buWe boot ya cure folding wheelChair ya ajiye ta kasa ya fara kwancewa sai da ya daidaita wheelchair din kafin Ya furta"zaku iya fitowa da shi"

Wani irin faduwar gaba taji gaba daya tabi ta rude jin ya furta za'a iya fitowa da shi ko wanene? sai faman rarraba idanu takeyi akan motocin, lokacin da idanunta su kayi mata tozali da mutumin da SA suka rurruko daga backseat na Waya daga cikin motocin, jikin shi sanye da patient uniform blue yar riga ce mai tsayi, Cinyar kafarsa Waya gaba dayanta a nannaWe take da bandage daga gani aiki akayi masa a tsakiyar cinyarsa, A hankali suka zaunan dashi kan wheelChair din sai nishi yake yana fitar da numfashi mai huci daga gani babu lafiya atattare da shi.

Cike da tashin hankali ta zare idanunta, la66anta na kerma ta furta"inna lillahi wa'inna Ilaihirraji'in! Daddy"! Da karfi ta furta sunan shi, bawan Allah a firgice Ya dubi inda take har rama yayi saboda azabar ciwo, suma Jami'an suka maida hankali akan ta..

watsawa tayi da gudu tana karasawa gaban shi a slow ta zube kan gwiwowinta, ta fashe da matsanancin Kuka tamkar ranta zai fita Cikin shesshekar kuka ta furta nashiga ukuna! daddy Meya faru dakai? Meya faru da kafarka?

tsantsar tausayinta ne Ya kama shi, Ummi da Batool sun kasa motsawa saboda tashin hankalin da idanunsu suka gane masu, daya bayan daya sauran dake acikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login