Showing 207001 words to 210000 words out of 391264 words

Chapter 70 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3577

COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.


Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US

OPINION
FACEBOOK

COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.

Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job

LATEST POSTS

ADVERT
Novels Elite
Copyright ? 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more

Accept !
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite

Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun ?addara Takun ?arshe chapter 42 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 05, 2024
Takun ?arshe

Boss Bature

A kishingiWe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya Waura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haWe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest

Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you"

Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest, naji dadi saboda abun alfahari ni agare ni"



sun Wan jima suna tattaunawa kafin daga bisani su ka yi sallama da juna.



Fitowa baba obie yayi daga toilet, jikinshi sanye da jallabiya fara, ya dago da ido ya dubi owais fuskarshi da fara'a yace"jikallena, nabarka zaune kana jira na, uziri ne ya ru?e ni a ciki" dagowa chief yai tare da kallon shi suka haWa ido da juna"barka da fitowa,"



"Yawwa owaisu na, fadamin me kakeson ci insa akawo mana, yau atare zamu yi breakfast.."



ya faWa yayin da yake nufar bedside drawer chief yace"duk abunda kakeson ci nima shi zan ci "



Landline din kitchen baba obie ya kira, bayan an daga kiran ya isar da sakon abunda za'a kawo masu na breakfast bayan ya ajiye wayar



Ya samu guri kan lallausar rug din ya zauna haWi da daura kan shi saman laps din chief yadda kasan uba da Wansa.



ya Wago ya kalli fuskar Owais dake kokarin saita shi da phone camera"me zaka min haka"?



"Hoto zan Wauke ka, naga ka yi min kyau"



murmushi baba obie ya sakar mashi"duk kyau na nakai ka"?



"Eh mana, mu da mukai gado agurin ka, gaba Waya kamanninka muka Wauko"




Saurari Littafin >>>>Kurkukun ?addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun Wora.
"Na tsufa owais, yanzu babu wannan kyan da kake faWin ina da shi"

"Kai kake ganin haka, ni tun da na taso rayuwata ban ta6a ganin mutumin daya tsufa da kyan shi irinka ba" ?ayataccen murmushi baba obie ya saki yana kallon fuskar chief, yaji dadin kalaman shi sun faranta ran shi.



"Baba, Wazu kace zamuyi magana, ya fada bayan ya kammala daukar shi hoton.



shigowar hajjaty dakin ne ya katse firar su, ta Wauki wankan material, hannunta ru?e da tray na kayan breakfast dinsu agabansu ta ajiye tray din cikin girmamawa ta gaishe da su suka amsa mata har ta juya zata fuce daga dakin muryar baba obie ta dakatar da ita.

"Ya jikin marwa"?

"Da sau?i baba,"

"Okey, ubangiji Allah ya bata lafiya" ta amsa mashi da ameen bayan ta fuce daga dakin chief ya dubi baba obie"wacece marwa"?



Ba halinsa bane tambayar abunda bai shafe shi ba, just saboda yaji ya ambaci ya jikin ta.





"?aya daga cikin masu aikin gidan nan ce, bata da lafiya" iya abunda ya fada masa kenan saboda baison ya Waga mashi hankali, kamar yadda su twins sukai hijra saboda kyamar marwa.





"Allah ya bata lafiya" ya amsa mashi da ameen



Tea pot baba obie ya dauka ya tsiyaya masu shayi a kananun kofuna suka dauka suna sha





"Ka tambaye ni dangane da maganar da nace maka inaso muyi ko" Waga mashi kai yai alamar eh



"Nasan bazaka ji dadi ba, amma kada ka hanani tafiya" janye cup din hannunsa yai daga kan lips dinsa"tafiya zakayi"! Jinjina mashi kai yayi"lagos nakeson zuwa gurin aminina, kasan na daWe ban ziyarce shi ba, kuma shi yana kokarin zuwa akai akai ya dubani har gida" jinjina kai chief yai"yaushe ne zaka tafi"?





"Karshen watan nan, 3 weeks zanyi in dawo" Waure fuska chief yayi"har sati uku baba, ina laifin one week" murmushi yayi"dama sai da nayi fargaban fada maka nasan da wuya ka kyale ni, indai bazaka barni ba to saidai muje atare" girgiza kai chief yayi"ba zan iya binka ba, naso muje atare amma ayyuka sunyi min yawa, amma fa bazan bari ka tafi kai kadai ba,"! Yamutsa fuska baba obie yai"to ni da wa zan tafi owais? Kowa yana da aikin yi, bana son in takura masu"



Shiru yayi jim kafin yace"zanyi magana da pravin, ya Wauki hutun aiki Ya bika ku tafi, don gaskiya ni bazan bari ka tafi kai kadai ba"





"Haba owais kamar wani karamin yaro, sai kace bakasan wanene kakan naka ba, waWannan kafafuwan nawa ba inda basu taka ba, har birnin sin sunje, nafa yi yawan duniya fiye da tunaninka, tun ina matashina nake fita kasashen waje ni kadai abuna."



Murmushi chief yayi"da da yanzu ba Waya ba, ka manyanta sosai ga tsufa, shiyasa nake tattalinka bana son wani abu ya same ka, duk da nasan Allah ke tsare bawansa."



kalaman chief sun kara faranta ranshi murmushi yayi yana kallon fuskar shi"anya akwai wanda yakaini dacen jika a duniyar nan"? chief yace"ni yakamata nayi wannan tunanin, cos bana tunanin akwai wanda yayi dacen kaka irina, ina alfahari dakai," dariyar farin ciki baba obie yasaki idan owais na yabon shi dadi yake ji kamar ya zuba ruwa kasa ya sha.



"Owais Mu fara cin abincin nan kada ya huce.." Chief ne yayi serving dinsu atsanake suke cin abinci ya lura duk dagowar da zaiyi sai sun haWa ido da baba obie wani kallon so da kauna yakeyi mashi.



"Naga kana kallona, ba zan canza maganata ba, zanyi magana da pravin din atare zaku je nasan zai baka kulawa ta musamman kuma zai dinga sanar dani duk wani motsinka" dariya baba obie yayi"oh Wan leken asiri zaka hada ni da shi kenan" Waga mashi gira chief yayi"bakomai nasan saboda kaunar da kake yi min ne, naji na amince muje atare da shi din" ya fada yayin da yake tura abinci abakin shi.



Knocking room door din akay daga waje, baba obie yace shigo ciki"



muryar hajiya saratu ce ta katse masu cin abincin nasu, atare suka dago suna kallonta, shugowa tayi jikinta sanye da swiss code lace, idanunta sanye da farin glass, ta aza veil a kafadarta, ta kashe daurin ture kaga tsiya, hannunta na aruke da handbag dinta.





Kwata kwata babu annuri akan fuskarta saida taga chief ta Wan saki fuskarta.



"Shalelena barka da safiya, har anyi shirin xuwa office.. " murmushi ta sakar mashi"barka da safiya babana, ina fata ka tashi lafiya" tay maganar tare da samun guri ta zauna tana fuskantar su..

"Lafiyalou auta,"



"Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"?

Yace"Alhamdulillah"



"I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi.



"She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya"



"Masha Allah, naji dadin jin hakan"



tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa.



gaba Waya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya faWa yana kallon su

Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba?

Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani Wan arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa"



tattausan murmushi sukayi

Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta faWa tana kallon shi



"Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu.



"Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa"



A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu.



Mi?ewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"?





"I'm sorry, Grandpa. I'll come back later"



ya faWa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata.





Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba.



"Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi.



"Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan.



Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? Waure fuska tayi

Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara le?awa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faWa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba.




"Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haWe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su.





"Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. "





Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata mi?e da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a...

Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haWe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi.





Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba.



"Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba"

"Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin.



__________________________________
'?



Lokaci Waya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ?arfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ?asa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaWaWdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buWe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi.



A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ?arfafa kanta donta samu damar buWe idanunta, ta ko'ina ba sau?i, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta.



La66anta dake a bushe ?amas fatarsu ta faffashe hada busasshan Wigon jini, da ?yar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta.





Lokaci Waya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta mi?e zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buWe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matu?ar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau.

Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take.





A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye Wakin har saida ya karaWe cikin sa tamkar da rana.



Idanunta suka washe, amatu?ar ruWe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ?arfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna



Gaba Waya ta ruWe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba.



Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ?o?arin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta le?a ?asa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta Wan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta Waura ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata mi?e aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba Waya ta kundumo ?asa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta mi?e tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu



mi?ewa tay tsaye tana kallon katafaren Wakin mai girman gaske, gado Waya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login