Showing 87001 words to 90000 words out of 391264 words

Chapter 30 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2593

wace irin musiba ce? Cikin karyayyar murya yace"Ni yakamata ku hukunta saboda ni nayi maku laifi, na ro?e ku ko dan sanayyar dake a tsakanina daku....."



Wata irin mahaukaciyar dariya suka tuntsire da ita jikinsu har jijjiga yakeyi kamar ana bugun ganguna, wani daga cikinsu ne ya kuma cewa"Ba sani, ba sabo a tsaka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nin mu, saboda ka tabka babban kuskure salsabeel ka yi ha'inci, don haka dole ka fuskanci hukunci mai tsanani daga gare mu"



Sunan Allah Ya ci gaba da ambato acikin zuciyarshi, duk addu'ar da tazo mashi yinta yakeyi ba ?a??autawa, har jaraba Yin amfani da sihirin shi yayi don ya ku6utar da kanshi da kuma Gawawwakin amma abun yaci tura, ?arfin sihirin shi bai kai na su ba, sun riga da sun yi mashi mugun Wauri na sihiri ba zai iya ta6uka komai ba.



Ja da baya ya soma yi ganin suna tunkaro shi, cikin matsanancin tashin hankali, kafin ya ?urema bangon Wakin tuni Waya daga cikinsu yai zazzafan taku ya dam?i wuyan salsabeel da kafcecen hannun shi, nan take numfashinsa ya soma ?o?arin Waukewa, Waga shi yai sama tun Yana kiciniyar ?wace kanshi harya fara gazawa idanunsa sun kaWa jawur sun fiffito waje, nan take ya soma bleeding ta baki ta hanci, wani irin raWaWin azaba ne Ya ziyarci salsabeel tamkar ana yi mashi Waskanan wuta a jikin shi, fuskarsa tayi jawur jini ya kwanta a fatarsa, hawaye da gudu suke kwararowa ta cikin idanunsa bakomai zuciyarshi ke tariyo mashi ba A lokacin face kalaman mahaifiyarsa Tamira, Idanunsa na akan gawarta.... Numfashinsa na kiciniyar Waukewa gaba Waya ya gama jigata har ya fidda rai da rayuwa, a lokacin da basuyi tsammani ba suka jiyo sautin dirar wani abu a bayansu, da sauri giant Win daya sha?e wuyan salsabeel ya sake shi jiki ba ?wari ya kife ?asa kan shi Ya daki ?asa da?yar numfashin sa ke fita da hucin zafi, kusan atare Giants Win suka juya baya don ganin menene Ya faWo cikin Wakin da har Ya bada sautin mai kuwar gaske.



Da wani irin tsantsar Al'ajabi suke kallon shi, yadda kasan saukar aradu Haka Ya faWo masu Yana huci kamar Mayunwacin Zaki, kwata kwata babu riga a jikin shi sai dogon wandon kakin Giant, jikin shi sai tsuma ya ke yi tsabar fusata, ta ko'ina zufar 6acin rai ce ta ke tsastsafo masa, harta tsokokin jikinsa motsi su ke yi, da wani irin hucin zafi numfashin sa ke fita.





Shin Wanene Wannan? To bakowa bane face GARKUWA, dalilin dayasa shi dawowa kurkukun saboda hankalin shi ya?i kwanciya yasan mawuyacin abu ne Salsabeel ya samu fita daga cikin kurkukun tare da gawawwakin salin alin, ranshi na bashi cewar wani mugun abun zai iya faruwa da Salsabeel Win, shiyasa lokacin da su ka shiga cikin makewayin bayan ya buWe ma su Angel kofa ya?i bin su yace su fara yin gaba shi zai taho da Akwatin kayan su tare da back pack Win su, za su tarar dashi a bakin ?ofar da zasu 6ulla idan sun ?arasa, yayi hakanne don ya samu damar dawowa ya taimaki rayuwar salsabeel saboda baya son ya rasa shi ko dan saboda halaccin da ya yi mashi a rayuwa bazai ta6a mantawa ba, yaji mutuwar tsohuwa Tamira don haka bazai bari rayuwar salsabeel ta salwanta baW'






Kallon kallo su ka soma jefawa junan su tsakanin Giants da Garkuwa, wato gaba da gabanta, Aljani Ya taka wuta, banbancin Danish da sauran Giants shi ?arfin sa Na Evil giants ne masu Star Uku kai ko a cikin su Ya zarce su Power, babban kuskuran da Elders sukayi shine dam?a amanarsu gare shi saboda ya zama garkuwarsu a duk lokacin da za'a kawo masu hari, ba su ta6a tsammanin garkuwarsu zai Iya cin amanarsu ba, shiyasa suka bashi sihirin da ya fi na kowani giant na gidan kurkukun ?addara, a halin yanzu babu mai iya karawa da shi sai Elders wato Leaders Win su, Danish Yana da kwatankwacin ?arfin giants Wari a jikin shi, ba?a?en shaiWanun dake a jikin shi wani irin ?arfi ne da su na fitar shari'a, kuma basa ji basa gani umarnin shi kaWai suke bi, hatta su kansu elders ba su isa su hana shaiWanun bin umarninsa ba, kuma su sukayi kuskuren Waurashi akan turbar da yake ashe da rabon su yi danasani mai girman gaske,



Duk da Salsabeel baya acikin hayyacinshi Hankalin shi ba ?aramin tashi yai ba, ganin Danish Ya dawo! Muryarshi na rawa ya furta "meyasa! Meyasa Danish? Meyasa ka dawo? Ina ka baro su Angel? Sautin muryarshi ko fita batayi shi kaWai yake sambatun shi ba tare daya iya Wagowa da kan shi ba, saboda raunatar da yayi.





?aya daga cikin giant dinne Ya ambaci sunan shi"Garkuwarmu"! Yana huci Yace"Ni ba garkuwarku bane! Garkuwar su ne! idan har kuna son zama lafiya to ku ?yale salsabeel da gawawwakin nan, Idan ba haka ba, zanyi maku abun da baku ta6a tsammani ba"! da kakkausar murya ta majiyi ?arfi ya faWa yana nunasu da yatsan hannun shi.



A lokacin kusan suman tsaye sukayi saboda mamakin kalaman shi! ha?i?a yayi matu?ar Waure ma su kai sun firgita da jin furucin sa.



"Amma dai wasa kake mana ko"? Girgiza kai yayi "na ta6a yi maku wasa makamancin wannan!?



"Idan kuwa har dagaske ne, Elders sunyi kuskuren yarda dakai maci amana! Ka bamu mamaki! Ina ka samu ?warin gwiwar da har ka Iya gaya mana magana a gaban idon mu ba tare da jin shakkarmu ba?" Shiru yayi baice masu komai ba.



"Tun wuri ka yi gaggawar Janye ?udurinka, Saboda kai namune baka isa ka juya mana baya ba, har abada kai mallakin gidan kurkukun ?addara ne, kuma garkuwarmu, Idanma mafarki ka ke yi to ka farka tunkafin lokaci Ya ?ure maka, duk wani abu da zakai ta?ama dashi anan ka same shi, kuma da zarar elders sunji maganar nan, kasan me zai biyo baya......" wanda yayi maganar Ya faWa yana mai yi mashi kashedi.





"Har abada ba zanyi danasanin bijiremaku ba, Shawarar da zan baku shine kuyi gaggawar barin wurin nan idan kunaso ku tsira da rayukanku saboda ni banzo da niyyar na cutar da wani ba, Wan uwana kawai nakeso na ku6utar daga sharrin ku."






Babu yadda Danish bai yi da su ba akan subar salsabeel amma suka sanya kafiya, dama su giants basu da tsoro kuma basa karaya sai dai komai zai faru ya faru, Kafin kace me faWa ya kaure tsakaninsu tamkar a filin Ya?i, tuni ?ura da kururuwa sun karaWe cikin da?in, bakajin komai sai gurnaninsu mai matu?ar firgitarwa, gaba Waya sun rikiWa sun koma dodanni masu ban tsoro sai kaima juna farmaki su ke yi kamar abokan gaba, Kakin Giant Win dake jikinsu Ya faffasa saboda garkuwa ne agare su, idan har ba ciresu yayi ba to bazai iya yin galaba akan su ba balle har Ya yi nasarar kashe su, wani irin bahagon naushi ya soma sakar masu akan idanuwansu duk wanda ya nausa nan take ?wayar idanuwansa ke zazzagowa cikin Jini Ta faWo ?asa, gaba Waya Ya zautar dasu Ya nakaWa masu lugudan wahala, Har saida numfashinsu Yabar gangar jikinsu tukunna Ya zu?unna Yana huci batare daya canza halittarsa ta mutane ba Yabi su Waya bayan Waya ya farke ?irjin kowannan su ya 6an6aro zuciyoyin su Ya tura abaki Yana ci saboda Ya ?ara ?arfin sihirin shi.



?akyar Salsabeel Ya samu ?warin gwiwar mi?ewa numfashinshi na fita sama sama, muryarsa da rauni Yace "Danish meyasa ka baro su Unaisah Ka dawo don ka taimaki rayuwata, Idan wani abu ya same su fa"?



Danish bai tanka mashi ba, har Sai da Ya gama abunda Yakeyi tukunna Ya girgiza jikinshi ya rikiWa ya dawo ainihin suffarshi ta mutane.



Ruko hannun salsabeel yayi acikin nashi yana faman fitar da huci Yace"Saboda rayuwarka tana da mahimmanci, bazan bari na rasa ka ba, nasan cewa zasu iya farmakar ka shiyasa na dawo don na ceci rayuwarka, Inaso na cika maka burinka na ganin ka binne gawarwakin su tsohuwa tamira sannan in ku6utar da kai.



Girgiza kai Salsabeel yayi hawaye cike fal da idanunsa yace"Danish ka tafi kawai, Zasu Iya riskarka, wallahi ba zasu ?yale ka ba, ni kuma bazanso ka ?ara shan wahala arayuwarka ba, Yanzu lokaci ne da yakamata kayi rayuwar yanci Danish, inaso kayi farin ciki kafin kabar duniya, Hakkin ka da aka tauye maka na rayuwa shi nakeso ka samu Danish dan Allah ka tafi, kabarni kawai, ka koma wurin su Unaisah ni basai na rayu ba, rayuwarku tafi mahimmanci agareni nasan zaku haWa gwiwa don ganin kun kawo ?arshen elders...." magiya ya dinga yi masa akan ya tafi ya ?yale shi amma ya?iya har saida ta kaiga Ya daka mashi tsawa a faWace Yace"Ka tafi ka ?yaleni!! nace maka ka tafi! ka tafi !kabarni kawai..."





Cikin sanyin murya Danish yake faWin "bazan tafi ba salsabeel, Idan kaga na bar wurin nan to na kubutar da kai ne..."



Gaba Waya sun Harzu?a, faWa ne ya kaure atsakanin su kamar zasu bugi juna, kwatsam a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin tarin Deeja Ya cika kunnuwansu, kamar an dasa masu aya suka dakata dayin sa'in sar da suke yi, kusan atare suka kai idanunsu ga duban inda take a kwance da tsantsar al'ajabi, babu wanda yayi zaton akwai me rai acikinsu, da sauri Danish Ya nufe ta Yana dubanta, idanunta a runtse take sambatu cikin fitar hayyaci take ambaton sunan haris da Angel tana faWin "ku taimaki rayuwata kuna ganin za'a cutar dani........" kallon juna sukayi shida salsabeel, kafin Ya mayar da dubansa ga sauran gawawwakin dake baje ?asa da sauri yakai hannu ya Wan ta6a ?afar Rubina wani iko na Allah nan take Taja Numfashi da ?arfi ta fesoshi batare da ta bude idanunta ba, sai la66anta dake kerma, Waya bayan Waya yake farkar da su babu wanda yake a cikin hayyacin sa duk sun jigata sun galabaita, sai sambatu su ke yi suna ambaton ruwa ruwa za su sha, ?i shi suke ji.






Maimakon salsabeel yayi farin cikin farfaWowar su, sai ya fashe da kuka yana faWin "wallahi banso suka rayu ba, saboda bani da yadda zanyi da su, mutuwar ita ce hutunsu, ga shi babu yan uwansu sun riga sun tafi...."



Cikin tashin hankali ya ru?o hannun Danish yaci gaba da faWin"ka taimakamin Mu binne su kawai, su ?arasa mutuwa acikin ?abarinsu, ni banga amfanin suci gaba da rayuwa a wannan duniyar ba, wahala zasu sha idan mutanan nan suka riske mu zasu kashe su ne bayan sun gama wula?anta rayuwarsu....", kafin Ya ?are maganar Danish Yace"bazai yiwu ba, kamar yadda yan uwansu suka rayu suma haka zasu rayu, bazan ta6a bari su rasa ransu acikin gidan kurkukun kaddara ba, ko da kuwa zan jefa kaina cikin hatsari ne sai nayi musu hanyar da za su gudu" da ?warin gwiwa ya furta kalaman tare da fucewa daga dakin tsohuwa yaje ?asan gadon Batool inda suke ajiye robobin ruwa ya dauko su ya wuce toilets din dakin su ya samo masu ruwan da zasu sha, bayan ya dawo yabi su daya bayan daya ya basu ruwan suka soma sha.



Salsabeel dake kallon shi tsabar ?ululun bakin ciki baisan sa'adda ya fashe da kuka yana fadin "Danish ka tafi kawai, idan har bazaka taimaka min mu binnesu ba, dan Allah ka tafi zaifi min kwaciyar hankali, Ka rigada kasan bamu da wata hanya da zamu iya ceton su...." Cak Ya tsaya da yin maganar ganin babu danish Kamar walkiya Ya 6ace ma ganin shi, Shiru yayi yana faman haWiyar yawu cike da zullumin ina Danish Yaje? Ko dai Ya tafin ne ...? Tuni ido Ya raina fata sai kace ba shi bane yake korarsa akan Ya tafi ba, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, hankali atashe yake kallon su Dija dake zazzaune a ?asa cikin fitar hayyaci suke ambaton sunan ?an uwan su musamman sunan Unaisah da na Danish, gaba Waya sun zauce, gawar mahaifiyarsa ya kalla tuni wani kukan ya kuma zuwa mashi cikin matsanancin tashin hankali Ya soma ?walawa Danish Kira don Ya dawo ya taimake shi ko ya samu ya binne su.





Jin shiru babu alamun zai dawo ne ya sa shi zubewa kan gwiwowinsa Yana ta faman yin shesshekar kuka kamar ransa zai fita.



Kamar daga sama Yaji motsi a Wakin, A firgice Ya Wago da idanunsa azazzare ya kai duban sa ga Bookshelve Win Wakin tsohuwa tamira dake Ta motsi, Kafin yai wani yunkuri gaba Waya Ya rikito Ya rubza ?asa, Jikinsa na 6ari Ya mi?e yana kallon ?ofar da ta 6ullo, da matu?ar mamaki akan fuskar shi.



Ta cikin ?ofar Danish ya fito, fuskarshi sharkaf da gumi Ya dubi Salsabeel.



"Zamu Iya tafiya" wani irin farin Cikine Ya lullu6e Salsabeel.



A ruWe ya furta"Danish tayaya akai ka gano ?ofar nan? Ban ta6a sanin akwai ta ba, kuma bana tsammanin ko ita tsohuwa tamira tasan da zaman ta" ya faWa cike da son jin ?arin bayani.



Yana faman huci yace"Kada ka manta, ka riga ni tsintar kanka acikin kurkukun ?addara ni kuma nafi ka sanin komai na cikin sa, duk wata ?ofar sirri dake a kurkukun nan nasan da zamanta, tabbas tsohuwa bata san da wannan kofar ba, tsohuwar hanyace da aka jima da toshe ta, ni da kaina na sake ha?a ta da sihiri na, Idan muka bi ta cikin ta, zata 6ular da mu cikin wani kogon dutse dake wajen kurkukun nan, dalilin dayasa na za6i ku raba hanya da su Unaisah saboda nasan zasu iya farmakar mu idan har suka gano abunda ke wakana, inaso na raba masu hankali ne watakil in mukayi hakan wasu su rayu daga cikin mu"




Bazai iya jure kallon Danish ba, Yaron Ya burge shi, Ya yi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba, ya taimake sa a lokacin da rayuwarsa take akan ga6ar salwanta, da sauri ya janyo shi ya rungume shi yana kuka, kafin ya raba jikin su cikin sanyin murya yace



"Amma danish su Angel fa? Yakamata ka koma wurinsu suna bu?atar ka, bana so wani abu ya same su"



Girgiza kai Danish yayi "kada ka damu, babu abunda zai cutar da su, saboda na rigada na Waure hanyar da suka bi da sihiri babu wani mahalukin da ya isa ya iya tsaga kofar ya shiga balle har ya cutar da su, kafin nazo nan sai da na kiyasta awannin da za su yi kafin su ?arasa kofar da zata 6ular da su waje ni kuma zan riga su komawa bayan na taimake ku"



Murmushin farin ciki salsabeel ya saki,

Basu tsaya bata lokaci ba suka yi kokarin taimaka ma su Hibba don su mi?ar da su tsaye, saidai mutun biyu daga ciki kafafunsu sun kasa Waukar su sakamakon abunda tsohuwa Zafreen ta yi ma su, bayin Allah sai ihun azaba suke saki, da sauri Danish Ya sungumi deeja ya goyata a bayan shi, ya sanya mayafin daya Wauko a ?asa ya Waureta tamau, kafin ya Wauki Rubina ya Waurata a kafaWar shi dama su biyune basu iya tafiya.



shi kuma Salsabeel ya yi amfani da bargon tsohuwa tamira ya nannaWe gawarta aciki ya Waurata a kafadarsa.



A haka suka bi hanyar mai duhun gaske ga zafi tamkar ana rura garwashin wuta, sunci ba?ar wahala su sarah kamar numfashinsu zai Wauke. Cikin awanni takwas da su Angel sukayi suna rarrafawa akan hanyar su duk wannan abun Ya faru, baifi awa biyar ba su salsabeel sukayi nasarar fita daga cikin gidan kurkukun ?addara hakan na nufin sun riga su Angel ku6uta saboda tasu hanyar batai nisan wadda su Angel suka bi ba.



Bayan su Salsabeel sun 6ula cikin kogon dutsen, Danish Ya sauke deeja da Rubina daya Wauko, shima Salsabeel ya sauke gawar tsohuwa tamira, su hibba duk suka zube agajiye har lokacin bakunansu basu gushe da ambaton sunayen ?an uwansu.



Kallon juna sukayi kowan nan su na haki, da sauri salsabeel ya ru?o hannun Danish, cikin sanyin murya yace "Danish, bazan ta6a mantawa da halaccin da ka yi min ba, kayi min abunda har abada bazan ta6a mantawa dakai ba, kaine silar ku6uta na daga Gidan kurkukun kaddara kuma kaine silar cikar burina na ganin na cika al?awarin mahaifiyata dana Waukar mata akan in rufe gawarta kada in bari ta wula?an ta, Danish ko a mafarki ban ta6a tunanin akwai ranar da zan bar gidan kurkukun kaddara ba, nasha jaraba guduwa nida mahaifiyata amma mun kasa saboda karfin sihirin mu bai kai ba, sai gashi a sanadiyar ka nayi nasarar fita...." tuni hawaye sun wanke fuskarshi.




"Danish, Koda ace ban rayu ba, ni ka gama min komai wallahi, koba komai na sha?i iskar duniya bayan tsawon lokaci da na kasance a kulle" ya faWa yana duban cikin idanunsa "ni dai burina ka yi rayuwar farin ciki tare da yan uwanka, ubangiji Allah Ya kare min ku ya tsareku a duk inda zaku kasance, bani da tabbacin zamu sake haduwa wata?il ma ba lallai mu rayu ba....." bai ?arasa maganarba ya fashe da kuka mai cin rai, da sauri Danish ya janyoshi suka rungume juna sosai suka kankame jikinsu.



Bubbuga bayanshi Salsabeel yai da hannunshi "Wan uwana, ka kula min da kanka, wallahi ina mutuwar sonka tun farkon ranar da aka kawo ka gidan kurkukun ?addara a cikin tsumman ka, naso ka Danish, zan tafi da kewarka, Allah ya rayamin kai Danish, Ina fata wata rana kaima ka zama cikakken musulmi, ka yi rayuwa kamar kowa kayi Aure ka hayayyafa....."



Lumshe idanu Danish yayi cikin sanyin murya yace"ina sonka Wan uwana, nima zanyi kewarka, ka kula min da kanka, ina fata mu sake haWuwa" Yana faWa Ya raba Jikin shi daga na Salsabeel, A hankali ya soma tafiya yana ja da baya yana duban Salsabeel da ?an uwan shi waWanda kwata kwata basa a hayyacin su, wasu irin zafafen hawaye ne suka cika idanuwan Danish bai daina kallon su ba har saida yayi nisa kafin Ya 6ace ma ganin su.





Bai dira a ko'ina ba sai a bakin kogon bishiyar da su Angel zasu 6ula, adai dai lokacin su kuma har sun ?araso bakin kogon bishiyar suna ta faman ambaton sunan shi.



Bayan tafiyar Danish A cikin Dajin salsabeel Ya samu wuri a gefen wata bishiya ya binne gawar tsohuwa tamira, ya zu?unna gaban ?abarinta yai mata addu'o'i yasha kuka kamar ba gobe, har shaida sai da yayi ma kabarin nata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login