Showing 312001 words to 315000 words out of 391264 words

Chapter 105 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2548

motocin suke fitowa, Chief owais ne jikin shi sanye da Singlet fara sai short, gaba Waya goshinshi bandage ne, fuskokin su duk sun 6aci da tabonnin raunukan da suka ji, Wa'iya zubilla, dafe kirji ummi tayi cike da tashin hankali ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool kuwa Fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita musamman data lura babu Danish a cikin su, daga cikin sauran da suka fito daga cikin motocin U.s armies din da suka rage ne su Biyar, babu cikon Wayansu, sai wasu daga cikin na hannun daman Chief wadanda ba'aje Kai farmakin da su ba.

Akace labarin zuciya atambayi fuska, tunkafin suyi masu bayani suka karanci komai daga yanayin su, Dakyar Taj yai karfin halin janyo Unaisah Ya rungumeta akan kirjin shi, tare da shafa sumar kanta yana faman sauke ajiyar zuciya, har cikin ranshi yaji dadi da Allah yasa ya rayu ashe da rabon zai sake ganawa da yarsa? sai dai abu daya da yake ma fargaba.

hannun Ummi ruke dana Batool suka karaso Gurin su Chief, Fuskokinsu sharkaf da hawaye Murya Na rawa Batool ta furta"Ina Danish din mu"? Shiru sukayi don basu shirya komawa asibiti da wanin su ba.."dan Allah ku faWa min Ina danish? Meyasa bangan shi ba..." cikin shesshekar kuka tayi maganar, Sunyi shiru suna kallon ta, Chief ma Hankalinsa baya akan su, saboda matsananciyar damuwar data mamaye zuciyarsa.

Unaisah data kwantar da kanta a kirjin daddynta, Hankalinta Idan yai dubu toh ya tashi, tin da taji muryar Batool tana tambayar Danish ta fahimci babu shi su ka dawo! Babu!!babu!! Hasbunallahu wa'ni imal wakeel, acikin zuciyarta ta dinga maimaita duk wata addu'a datazo cikin bakin ta.

Ummi kuwa Jikinta yagama mutuwa Cikin sanyin murya ta wanda Ya kara tayi masu Chief barka da dawowa da tambayar ya jikin su, fuskokin su kwata kwata babu walwala suka amsa mata, Kafin Commender james ya nemi su shiga ciki saboda majinyatan jikinsu da suka jigata, dakyar Chief yake Tafiya saboda rashin kuzari, bawan Allah shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyarshi bazai ta6a mantawa da Danish ba Har abada ya kafa tarihi acikin zuciyar shi, gaba daya abun da suke jima fargaba yadda yan uwan shi zasu kar6i abunda zasu fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu.

"Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"?

Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani"

yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki.

mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta.

"Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba...

Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."?

Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo...

"Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi ?addara..."

wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada.

ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya.

hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye.

Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"?

"Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar"

jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.."

ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin.

Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su.

saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"!

"What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya Wan lafa, cikin sanyin murya ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.."

yana faWan hakan Ya mi?e cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa.
Yana shiga Ya faWa kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Ya?in Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan.


abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya dam?a mashi saboda ya cancan ta.

A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya Wan numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi


aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa.

Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa..

_______________________________
'?

"Dan Allah ku faWa mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya...

Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba"

A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba"

Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi ?asa.

mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne"

gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta faWa tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne"

"Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu"

Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka kaWa jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta faWa kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi.

Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta ..

_"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_

_"Abu Waya da nakeso Kiyi min al?awari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_


"Meyasa zaka yi min haka? Ta fada acikin ranta

"Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta"

Lokaci Waya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta.....=ؔ?

Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"?

ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga...

Lokaci Waya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba=ؔ?


*Bayan Wani Lokaci*

*OIH*

Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su.


A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun kaWa jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta.


Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital)


gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta.

Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya..=ؔ?

Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya.

Hankalin su Ya tashi matu?a sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba.

(Get well Soon Unaisah Angel)


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?=?%?=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: =?%?=؋?=؞?=ؓ?=ؔ?=؞?>???

~<><><><><><><><><><><><><><><>
'?~

~__________________________________~



gajiya tafari yi da tsayuwa charging kwata kwata baya sauri, zama tayi gefen gadon su ta dan fara gyangyadi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba da ita.


A hankali ya ke saukowa down ya zuba hannayensa Cikin aljihun wondon baccin sa, sam ya kasa runtsawa saboda tunanin a wani hali Unaisah take a ciki? Ta yi bacci ko idonta biyu? Ya damu sosai akan ciwonta, direct ya nufi bedroom dinsu Yana gab da zai shiga ya jiyo shesshekan kukan ta kasa kasa.

Almost 3 times yana kwaWa sallama shiru tare da knocking door din, ba'a amsa mashi ba Har zai juya sai kuma ya kasa jurewa saboda baya son damuwarta ga kuma kukan da ya ji ta na yi.

A hankali ya tura kofar Wakin Ya shiga da sallama abakin shi, babu wadataccen haske a dakin sai na bedside lamp da suka bari a kunne, Batool ya hango a kwance kan gadonsu tana ta sharar baccin ta ita kadai abun ta.


Wurga eye balls dinsa yai saitin inda yake jiyo shesshekar kukanta, wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi ganinta a cikin prayer corner tana a zaune kan prayer mat, jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ruke da prayer beads tana lazami, yayin da idanunta ke akan qur'anic stand din data buWe.

tabbas tajiyo kamshin turaren Chief sai dai bata kawo aranta cewa shine ba kuma kwata kwata ba ta ji motsin shigowar mutum ba saboda tayi nisa a cikin ibadarta.

Unaisah ta yi Namijin kokari ba lafiya gare ta ba, amma saboda ta nema masa rahama gurin Allah yasa ta hana idonta bacci ta tsaya tsayin daka don ganin tayi masa addu'a dama alkawari ta daukar masa zata raba daren ta biyu rabi ta yi bacci rabi ta yi addu'a, samun masoyi mai sonka tsakani da Allah da zai iya yi maka addu'a batare da sanin ka ba zaiyi wuya a duniyar nan.


Hakika ta burge shi sosai, Har ya zagayo ta gabanta bata lura da shi ba, saboda ta Wan lumshe idanunta, dogayen eye lashes din ta sun ji?u da ruwan hawayenta.

Kyakkyawar fuskarta ta 6aci da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login