Showing 144001 words to 147000 words out of 391264 words

Chapter 49 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2634

kabbara sallah,......"

Sallamar su Alhanji ubaid ce ta karaWe kunnuwansu, da gudu Zeenatu ta diro daga kan gado ta fuce kamar walkiya, tunkafin ta karaso dr shuriem Ya hangota, murmushi ya saki tare da bude mata hannayenshi ta faWa kan kirjinshi tana dariya

"Yaya shureim sannu da dawowa, naji dadin ganinka, dama ina ta zullumin kada kaki dawowa gida.." bata ?are maganarba, Alhani ubaid Yayi mata gyaran murya, waro idanu tayi don gaba daya ta manta da shi awurin cike da jin kunyarshi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta

Dariya Alhani ubaid Yayi"zeenatu, meya hanaki yin bacci..." muryarta da yar shagwa6a tace"yaya shureim nake jira ya dawo..." kafin ta kare maganar Alhaji musa Ya shigo falon Ya nufe su cikin takun nan nasa na isa

"Sannunku da dawowa, ya mai jikin"?

Alhaji ubaid Yace"da sauki, kafin mu dawo ta farka sai dai bata ahayyacin ta...." cikin nuna tausayawa ya furta"Allah Ya bata lafiya, gobe zanje asibitin, Ina Hajiya laylan ne"?

Dr.shureim yace acan zata kwana" shiru yayi bai ce komai ba.




wani abu daya daurewa dr shureim kai tun da ya dawo gidan zeenatu bata tambaye shi Ya jikin benazir ba, kwata kwata kamar irin ta manta da zancen ta, bayan tafi kowa nuna damuwa akanta, har magana yayi mata banji kin tambayin auntynki benazir ba, sai tayi shiru bata tanka mashi ba kamar bataji me yace ba, kusan sau uku yanayi mata maganar tana share shi, amma idan yayi mata wata maganar daban saita amsa mashi.



Bayan shigar shi daki, kasa runtsawa yayi, har saida Ya kira mommynsu a waya ya tambayeta awani hali suke ciki? Ta tabbatar masa da komai lafiya kafin ya samu nutsuwar Yin bacci.



*EX-PRISONERS*



Around ?arfe 10 na dare, ummi ta sauko down, har ta shirya cikin kayan baccin ta,

Tunkafin Ta karasa Ta hango wasu daga cikin su kwance ka lallausar carpet din falon suna bacci, tun da zu tabarsu suna ta shan fira atsakaninsu tayi tunanin in sun gama zasuje su kwanta sai kuma ta taras da su kwance suna sharar bacci, wasu asaman sofas wasu akan carpet



Murmushi tasaki haWi da girgiza kanta, tama rasa tayaya zata fara tada su,duk sun sanya kayan baccin su..., Waya bayan Waya ta fara farkar da su



"Batool My baby, wake up, Parveen! Hannah ku tashi dan Allah....! Ni bansan ya akai kuka bari bacci Ya dauke ku a falo ba, salon kawai ku wahalar da auntyn naku..." dakyar ta samu batool ta mi?e tana ?an soshe soshe



"Wuce kije daki" ta amsa mata da toh,

"Praveen ku tashi..." cikin magagin bacci ta buWe ido bakinta cunkushe da apple din da bata karasa cinyewa ba, bacci yayi awon gaba da ita, mi?a tayi tare da yin hamma ta nufi dakin su, ganin tana tangal tangal kamar zata fadi ne Yasa ummi yin saurin cafko hannunta, a lokacin ta samu hannah ta mike, ta ruko hannayensu a cikin nata har Waki takaisu, sai da taga sun kwanta kan gadonsu kafin ta dawo falon

Taci gaba da tada su"sajeed! Naufal ku tashi dan Allah, Mubeen Haris! Javed! Wai baku ji ina magana ne"? da wata irin kasalar bacci kowan nan su Ya mike har kwara mazan da kwarin su, suka nufi bedrooms dinsu



Wurinsu jemimah ta nufa, sun cunkushe kan sofa mai mazaunin mutun biyun yadda kasan kifin gwangwani, hannu biyu tasa ta dauki jemimah, ta daurata a kafadarta, kafin ta sa Wayan hannun ta Wago Azeeza, ta daurata a dayar kafadar ta, ahaka ta nufi dakin su, ta kwantar da su kan gadon su, sai da ta kashe masu switch din dakin kafin ta fito ta koma falon,

"Sarah! Wake up, rubina! Hibba! Pls ku tashi! Mana, Yasmin"! Har ta fara gajiya da tada da su, mikewa sukayi kamar babu laka ajikinsu, raka su tayi bayan sun kwanta ta dawo tana kallon waWanda suka rage, Eve ce kwance kan rug tare da Deeja..Sai unaisah dake a naWe kan sofa,

"Deejatun haris, Ta shi muje ki kwanta..." cikin magagin bacci ta fara sambatu tana fadin"wai meye haka ne? Ni ku kyaleni wallahi kada wanda Ya ?ara min magana..." Hannu ummi takai da niyar ta dago da ita, aikuwa ta daddage takai mata naushi a gefen bakin ta, tsabar zafin da ummi taji ne Yasa tayi saurin dafe bakin, ta lalla6a ta koma kan sofa ta zauna tana faman yarfa hannunta, ranta ya 6aci taji haushin naushin da khadeeja tayi mata, hakan yasa ta yanke shawarar barin ta a falon ta kwana, gudin kada ta lahantata garin tada ta daga bacci

Mikewa tayi ta nufi hawwa ta dan bubbuga kafafunta, cikin sa'a ta farka

"Ki je daki ki kwanta" amsa wa tayi da toh, bayan tafiyar hawwa ummi ta nufi unaisah

Bata tada ta daga baccin ba, daukarta tayi akan kafadarta, ta nufi bedroom dinsu da ita, tana shiga ta kwantar da ita akan gadonsu, ta kashe mata switch dakin,

Bayan ta fito falon, Ko kallon inda deeja take akwance batayi ba, don ranta Ya 6aci, kaitsaye ta nufi hanyar komawa dakinta, har ta kusa shiga taci karo da Batool kwance kan matattakar benan sai faman sharar baccinta take Yi

da alama zamewa tayi awurin ta faWi cikin magagin watakil tayi azan gadone shiyasa taci gaba da baccin ta

?aukarta ummi tayi da hannu biyu ta cucci6eta, ta haura da ita upstairs, bayan ta shiga dakin, ta kwantar da ita kan gadon su kafin itama ta haye ta kwanta tare da rungumota a jikin ta....





*d'
>?y?UNAISAH ANGEL=ؔ?*



Around ?arfe 1:30 na dare, ta farka da matsanancin ciwon mara mai azababben zafi, hannayenta dake kerma ta Waura su akan cikinta, sai faman murzarshi take yi, sai faman yin birgima take akan gadon, da?yar ta buWe idanunta waWanda suka kaWa jawur da su, cikin mawuyacin hali ta kai hannu jikin bedside lamp ta kunna fitilar haske ya gaure zagayen gadon da take, wani irin gumi ke tsastsafowa ta jikin ta, hatta pajama din dake a jikin ta sun manne ma fatarta,

Yun?urawa tayi da?yar ta sauko daga kan gado ta shiga toilet, ta haye kan toilet seat, tayi fitsari anan taga jinin da ya dawo mata jawur yana gangarowa ta tsakantsakin cinyoyin ta, runtse idanunta tayi da karfi duk irin Waukin da take na son ya dawo mata sai da taji abun ya fita ranta saboda raWaWin da mararta ke yi mata

Bayan tayi tsarki ta fito, babu wandon ajikin ta, can ta baro shi a toilet....a gaban drawer chest na wardrobe din kayan su ta zukuna ta buWe tare da sura hannu ta Wauko pad daya, ta haWo da pant, akan mattress ta Waura su tana faman sakin nishi kamar mai na?uda,

"Can I give you a hand ."! kamar daga sama ta tsinkayi muryar mutun a kunnanta, sai tayi tsammanin gizo muryar shi keyi mata...kwatsam hasken Wakin ya dauke Wuff duhu ya gauraye ko'ina, a firgice take kallon duhun daya mamaye idanunta, gashi bata ?arasa sanya pad din ba, cikin duhu tafara laluban gefen gadon don ta kunna fitar, ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun akan mararta, a matu?ar firgice ta zare gray eyes dinta, muryarta na kerma ta furta"de...deeja? deeja? Shiru ba'a amsa mata ba...tasan su biyu suke kwana dakin shiyasa ta ambaci sunanta, tunani tayi kadai batool ce

"Batool ke ce? Shiru ba amsa,"dan Allah wanene? A tsananin tsorace tayi maganar.

"Daddy...." bata kai ga ?arasa maganar ba, Taji gaba Waya anjayota, ta faWa kan kirjin shi, farat Waya ta gane koma wanene namiji ne kuma kakkarfa, Kware baki tayi zata fasa ihu yayi saurin haWe bakinsu guri guda, jikinta ya fara kerma tafara kiciniyar kwace kanta, kamar yar dambe ta dinga Wuma masa dundun da hannayenta waWanda ke abayanshi, tayi kuka tayi haukan ko gizau baiyi ba har gartsa mashi cizo tayi wuri uku a kirjinshi amma babu alamun yaji zafinda zai sake ta

Fashewa tayi da matsanancin kuka"wayyo Allah daddy na, Aunty ummi, my man kana ina? Kana gani za'a cutar dani, na shigo uku wayyo Allah..." da iya karfinta na karshe ta bangaje shi gaba Waya ta kife kan floor, bata iya ganin komai da rarrafe tana laluban hanyar fita daga Wakin, ?afafunta taji ya ru?o da hannayensa biyu ya Wago bai direta a ko'ina ba sai akan gadon ta

Ta yunkura zata gudu Ya hambareta da gwiwar hannunsa, kanta ya daki pillow, kafin tayi yunkuri sake mikewa, mutumin ya toshe mata baki da tafin hannunsa gaba daya ya sakar mata karfi, ta yadda ko yatsan hannunta bazata iya motsawa ba, numfashinta dakyar yake fita, wani iri danshi danshi ta fara ji agabanta kamar ana zu?e jinin dake fita ta farjin ta, runtse idanunta tay zufa ta fara tsastsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, ga wani azababen zafi da matsananciyar kasala da suka rufeta a lokaci Waya, ta fara jan numfashi tana nishi, hawaye masu Wumi suka wanke fuskarta, gaba daya ta zauce ta rasa tunaninta, lamarin kamar a amafarki take jin afkurwarsa, ta kasa ta6uka komai, sunan danish dana daddynta da aunty ummi kadai take iya ambato cikin zuciyarta a karshe raci gaba da ambton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....... W'



Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Shin wanene Yayi ma unaisah wannan aika aikarS'



_____________________________
'?



A zaune Yake kan darduma, Cikin shiga ta farar jallabiya, Hannunsa ru?e da qur'ani Ya nutsu Yana karanta shi,



"Assalamu alaikum"! Cikin kunnanshi Ya tsinkayi muryar abbansu, sai da yakai aya kafin daura kur'ani kan prayer mat din Ya dago da ita Ya dube shi,

Yana asanye cikin kakin shi, zama yayi daga gefen gadon shi Yana duban fuskar dan nasa dakyau,



"Ina kwana daddy, Kun tashi lafiya"!



"Meke damunka"? Kai tsaye Ya jefa mashi tambayar,



Sunnar dakai kasa yayi kafin ya furta me ka gani daddy"?



"Abubuwa da dama! Na farko kwata kwata baka acikin nutsuwarka, tun zuwanka Nigeria na lura da akwai wani abu dake damun ka! Bayan haka me ya hana ka komawa bakin aikin ka!?



Shiru yayi ba tare sa ya furta kalma ba, baiso daddynsu Ya fahimci halin da yake aciki ba, saboda baya son Ya Waga hankalin shi,



"Kada ka 6oye min komai, duk duniya baka da kamata, kasan tsakanina dakai babu sirri, Idan wani abune ke damunka, ka sanar dani, in sha Allah zan taimaka maka mu sami mafita atare..." Ya faWa cikin nuna kulawa



Bayajin zai iya 6oye mashi damuwar shi,tun da harya riga daya gano da kan shi, kwara kawai ya fada mashi gaskiya,

Cikin sanyin murya ya zayyana mashi komai, tun farkon haduwarsu da Benazir, da irin rayuwar da sukai har izuwa rabuwar su..." dagowa yayi idanunshi jawur cike tab da hawaye ya kalli daddyn nasu



"Daddy ka tayani da addu'a, Allah Ya jarabceni da sonta, ko baccin kirki bana iya yi saboda rashin ta atare dani, bansan awani hali take a ciki ba, nayi jiran hajiya laurat shiru har yau bata neme ni ba..., bana jin zan iya barin kasar nan in har ban hadu da ita ba....."



Tsananin tausayin shi ne Ya kama Daddyn nasa,



"Meyasa baka fada min ba tun farkon zuwan ka"?



"Banyi tunanin yin hakan ba, na bari sai in na hadu da ita sai in sanar dakai..."



Murmushi sir mubarak yayi aranshi yana mai mamakin zaki, mutumin da bai ta6a ganin wata ?a mace Ya nuna yana son ta ba, Aikinsa kadai Yasa agaba, al'amarin so da girma ya ke...



A hankali Yasa hannu ya zaro wayar shi daga aljihu, ya Wan daddanata, zaki dake kallon shi bai son me zaiyi ba.



Kara wayar yayi a kunnansa, kafin Ya furta"Assalamu alaikum mutumina, Ina fata kana lafiya"?

On the other hand muryar mutumin ta amsa masa da cewa"wa'alaikum salam! lafiyalou, Ina fata kaima haka"?

"Alhamdulillah, naji muryarka kamar daga bacci ka tashi .."

"No na jima da tashi, ya iyalin naka"?

"Suna nan lafiya lou...Tambaya ce nake so inyi maka..." gaba daya zaki ya nutsu yana kallon sir mubarak, baisan dawa Yake magana

"Ina sauraronka..."

"Yar wurin Yayanka benazir da ta bace, ta dawo gida ko hanyar yanzu ba labarin ta .."?

"Meyasa ka tambaye ni?

"Ka fara bani amsar tambayar da nayi maka..."

"Ta dawo gida..." azabure Zaki Ya mi?e tsaye da alamun rudani yake kallon daddyn nashi

"Nagode mutumina, Idan muka hadu zamuyi magana"

"Okey saina jika" katse kiran yayi, fuskarshi dauke da murmushi Ya kalli zaki, zubewa yayi agaban daddyn nashi, ya dafe gwiwowin kafafunsa da tafukan hanneyansa



"Daddy wanene ka kira a waya.. "?

"Uncle dinta ne Alhaji musa, baka san cewa shi mutumin mu bane, ay da tunfarko ni ka fara tuntu6a da maganar ta, da baka sha wahalar yi ma hajiya laura magana ba..." wani irin annurin farin cikine ya bayyana akan fuskar zaki,

"Idan har kana so In haWaka da ita, sai ka bani cin hanci" ya fada da zolaya

"Daddy me kakeso na baka? Ka fada min koma menene...." dariya sir mubarak yayi

"Farin cikin ka da kwanciyar hankalin ka nakeso .." dariya zaki yayi

"Ka bani mamaki son, ji bi yadda soyayya ta jigata ka, kamar ba dan sir mubarak ba...." sunnar da kanshi kasa yayi cike da jin kunyar daddynsa

"Ni kamarma na ta6a ganin yarinyar? Halan 6oye ta kake yi idan naje canada don kada na ganta ." girgiza kai yayi"a'a daddy, bana 6oyanta zaka iya saninta, duk wanda yaje gida sai yayi tsammanin yar aiki na ce, shiyasa baku ta6a lura da shakuwar dake atsakanin mu ba..."

"Gaskiya zanso inji meya faru da ita? Meyasa ta gudu tabar Yarta? Amma kaima da laifinka, fisabilillah ina maka kallon uztaz ashe har mace kake 6oyo agidanka, almost 16years haba zakina! Kunyi ma kanku adalci kuwa? Da hankalin ka ka ajiye matar aure kuma kasan guduwa tayi daga gida bakayi yunkurin neman danginta ka fada masu ba!meyasa"?



Ya faWa fuskarsa adaure alamar baiji dadi ba



"Daddy sonta ne Ya rufe min ido na, nasan na aikata babban kuskure amma nayi nadama, kuma ni harga Allah ban ta6a neman ta ba, abun dayasa ban nemi kowa nata ba saboda ta faWamin ta tsani danginta, bata son ta dawo Nigeria, nayi kokarin shawo kanta donta amince in dawo da ita amma sai tace idan na matsa mata zata kashe kanta ne, shiyasa na kyale ta, daga baya mijinta ya turo mata sakon saki ta wayarta, daga ganin hakan saina kara samun kwarin gwiwar killace ta agidana saboda in mallake ta........." cikin sanyin murya ya kare maganar yana kallon daddyn nasa,

"Kayi kuskure da baka sanar dani ba, ay da nayi maka hanyar auranta, yanzu koda ka hadu da ita zata iya bijire maka ta koma ma tsohon mijinta...." dafe kanshi yayi da hannu Waya"daddy ka tayani da addu'a, Allah yasa rabona ce..."

"In sha Allah zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ka samu abunda kakeso.." ajiyar zuciya ya sauke, kafin wani ya kara magana a cikin su,

Sallamar hajiya turai ta katse su, atare suka amsa mata, ta shigo fuskarta dauke da murmushi"i'm sorry na katse maku firarku, my son barka dai, fatan ka tashi lafiya" da fara'a ya amsa mata"lafiyalou mommy,

Kallon sir mubarak tayi"na kammala shirya mana breakfast, ka taso muje kaci kada ka makara" ruko hannun zaki yayi acikin nashi atare suka mike suka nufi dining din



Adai dai lokacin, dr Jazz ya fito sanye cikin black trouser da shirt, Ya daura lapcoat akan kayansa, idanunsa manne da farin glass

"Barka da safiya daddy..."

"Yawwa Son, Harka shirya kenan"

"Eh,"

Ya faWa tare da samun wuri kan dining chairs suka zauna, turai ta fara yin serving nasu

"Big bro Ina kwana.." murmushi ya sakar mashi kafin yace"lafiyalou, ina fata kaima haka" ya Waya masa kai alamar eh,

Har sun fara cin abinci, Ibad Ya fito daga shi sai Wan short,

"Mommy ni an manta dani, shine ba a kirani inzo inci abincin ba . " ashagwa6e yayi maganar

Turai tace"sorry babyn zaki, Ay nayi zaton zaka jira ne Ya kammala in ya rage sai ka ci.." murmushi sukayi

"Oh wai har yanzu bai daina wannan Wabi'ar ba"? Sir mubarak ya tambaya yana kallon zaki

"Daddy bai daina, abun nasa kullum ?ara gaba yakeyi, bansan ya zanyi da shi ba, har friends dina sun gane halinsa, Na cin sauran abincin da na rage...."kallon shi sir mubarak yayi da sauri ya juya baya yana faman noke kai

"Daddy pls kada kamin faWa, ni wlh na saba, kuma nafi jin dadin cin ragowar abincinsa, daWi Allah" dariya suka sanya gaba dayansu



"Calm down Your mind, kai fa last born ne, shalelan mommy da daddy, ba wanda zaiyi maka faWa, kayi abunda kakeso" yaji dadin maganar turai,

"Zo ka zauna in zuba maka abinci.." da sauri ya samu guri ya zauna, Yana satar kallon daddyn su da jazz wanda tun ya zauna, hankalin shi baya atare da su, gangar jikinsa ce kadai atare da su ruhinsa yana wurin faryat daya kwallafa rai akai.



"Jazz kaci abinci mana! Salon sai ka makara ko"? Cikin kulawa Sir mubarak yayi masa magana

Kamar baisan cin abincin Ya dauki cuf of tea mai zafi Ya Wan kur6a

"Daddy dan Allah kace ma yaya zaki mu koma toronto, ko dan saboda karatuna, in ba haka ba zaija amaida ni baya..." da damuwa akan fuskarsa yayi maganar

Harara zaki ya dan watsa mashi"kada na sake ji kayi magana!..."

Sir mubarak ya katse shi da cewa"ba haka yakamata kace mashi ba.." ya faWa tare da maida dubansa ga ibad wanda Ya haWe rai.



"Next month zaku tafi, in sha Allah"

Murmushi ibad yayi"yawwa daddy thank you.."



"Wato na lura gudunmu kake Yi ibad..

"No momy wlh saboda school, kuma na manta bibina a gida..." Yana nufi magensa, mi?ewa jazz yayi"zan wuce" atare suka haWa baki wurin yi mashi Allah kiyaye hanya, sai da yabi kowan nan su ya manna masu peck kafin ya tafi......



________________________________
'?



Tun da garin Allah ya waya, Aneeleeh ta rasa kwanciyar hankalin ta, ta kasa tsaye taka zaune kamar mai fama da ta6in hankali, tayi matu?ar kagara ta kosa hajiya Saratu ta kira zahra, duk bayan yan mintuna sai ta le?a dakin zahra don ta ji ko ta kirata shiru har yanzu babu wani labari, kamar yadda ta matsu haka hajiya layla ta matsu suzo da yarinyar, itace ta fara farkar da ita daga bacci da sanyin safiya ta kira ta awaya, tana kara jaddada mata akan kada ta manta tayi kokari su yi magana da iyayen yarinyar, ta rasa ya zatayi gaba daya ta daura ma kanta damuwa, daren jiya dakyar ta runtsa..



"Aunty Aneelerh"muryar zahrce ta ratsa kunnanta, Jiki na rawa ta juya da sauri ta nufi zahra dake shugowa dakin, tana sanye da hijab, hannunta ruko da wayarta...

"Zahra ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login