Showing 81001 words to 84000 words out of 391264 words

Chapter 28 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

3614

babu alamun zata motsa ne yasa shi yin gyran murya, kamar wadda aka zungura da sanda a Wan firgice ta dube shi tana faman zare idanu

"Lafiya? Ko bakisan ta ba ne"?



Muryarta a harmutse tace"abie, na kasa yarda ne da abun da gani, wannan sakon da aka turo min daga benazir ne aminiyar nan tawa, matar da yau tsawon shekara goma sha wani abu da 6atan ta...." kafin ta ?are maganar abie yace"kina nufin Benazir yar gidan Alhaji ubaid? Wannan ?awar taki ta ?uruciya" jinjina mashi kai tai alamar eh.




"To ki kira layinta mana sai ki ji idan itace da gaske" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta mi?e ta fuce daga Wakin a falo ta tsaya kafin ta danna call, jikin ta har kerma yakeyi tsabar zumudin taji idan banezir ce take neman ta. ......





*DAULAR ALHAJI MUSA*



Gaba Wayan su sun Hallara a kan dining chairs, Tani da lami ne suke dawainiyar yin serving din su, an shake masu table da lafiyayyan abincin breakfast.



Tun da suka zauna babu mai magana acikin su, zeenatu da benazir abayane a jikin su, sun daure kansu da head scarp, yayin da Hajiya sarah ta sanya fitted gown ta atampa, kayan sun bi shape din jikinta, sam babu Wankwali akanta sai zallar gashin kanta da ya sauko har kan kafadarta, mom layla ma atampar ce ta sanya, Alhaji Ubaid da shureim jallabiya ne a jikin su, Alhaji musa ne kadai ya Wauki wankan tsadaddiyar shadda launin blue sky, kayan sun zauna mashi abunka ga namijin duniya, yayi kyau sai dai babu annuri akan fuskarshi kamar kullum Ya haWe rai kai kace bai ta6a murmushi ba, tsabar yadda ya Waure fuskarshi yana faman shan kamshi kamar wanda iska ke yi ma wari.



Abinci yake ci kamar baisan tauna shi, hajiya layla dake kallon shi ji take kamar ta sha?e shi saboda haushin shi da take ji.



Dr shureim dake cin abinci a tsanake ranshi ne ya bashi cewar Ana kallon shi a hankali ya dago da idanunsa kai tsaye suka shiga cikin na zeenatu, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido Waya, da Wan mamaki akan fuskarshi Ya zaro mata ido da sauri ta sunnar dakai kasa tana cigaba da sakin murmushi, girgiza kanshi yayi kafin ya maida hankalinsa akan abunda Yake yi.



Gaba Waya Hankalin benazir baya atare da su, ta tasa plate din abinci agaba ta kasa ci saboda tunanin Yarinyar da ta kira ta a daren shekaran jira, tun washe garin jiya take ta kiran layin baya shiga hankalin ta ya?i kwanciya.



"Benazir Lafiyar ki kuwa? ko wani abu na damunki ne? Tun dazu na lura dake kin kasa cin komai" cikin kulawa mom sarah tayi mata magana.



Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace"ba abu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nda ke damuna mommy, lafiyana qalou"

"Okey, ki fara cin abincin kada ya huce, ba lallai yai maki dadi ba"

Amsa mata tayi da toh

Spoon ta Wauka ta soma cin abincin zuciyarta cike fal da tunanin Unaisah



Wayar dr shureim ce ta soma ringing daga cikin aljihunsa, Hannu ya zura ya curo ta yana duban me kiran nasa.



"Ka tsaya ka kammala cin abincin, Inya so daga baya sai ka yi picking call din"



Muryar Alhaji ubaid ce ta katse masa hanzarinta.




"Daddy, kira ne mai mahimmanci,"

"Shikenan je ka daga" mikewa yai a hanzarce yabar dining din



Tafiyarsa keda wuya Hajiya layla ta dubi Alhaji Ubaida dake a zaune gefenta tace"ya maganar da mukayi dakai jiya"?

Murmushi yadan saki Yana duban fuskar Alhaji musa Yace"ay na fada maki, Ki ?ara hakuri"



girgiza kai tayi"bazai yiwu ba, ni bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba! Wannan ay abun kunyane ace muna zaune gidan kaninka....." maganar na dira kan kunnan Alhaji Musa Ya ajiye spoon din hannunsa, fuskarsa a murtu?e Ya ke duban Hajiya layla, yasan tayi maganar ne don Yaji ta.

Gaba daya hankulansu mom sarah ya dawo kanta.



"dan Allah ki yi shiru ya isa haka! Muje Waki mu yi magana" galla masa harara tayi"wallahi babu inda zanje, ko na bika bai wuci ka bani hakuri ba, Ni nagaji da zama acikin gidan nan, gaba Waya a takure nake, Kai ko gudun surutun mutane ba ka yi? tsawon kwanaki kana zaune agidan kaninka tare da Iyalinka"?

Hankali atashe mom sarah tace"dan Allah kiyi hakuri, mu kammala cin abincin sai muyi magana...." kafin ta ?are maganar Alhaji musa Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tuni taja baki tayi shiru.



Jikin zeenatu harya fara yin kerma saboda batason tashin hankali arayuwarta, abun kaWan ke rikitata, ita dai benazir ba ta ce komai ba ta zuba ido tana kallom mommyn nasu dake ta faman tada jijiyoyin wuya.



A gadarance Alhaji Musa Yace"Bana son haniya"



Harara ta watsa mashi"ay idan baka fita harkar mijina ba, hayaniya yanzu ka fara jin ta, wallahi bakaso zaman lafiya ba, akan me zaka dinga juya mutane son ranka sai kace wasu bayin ka, komai sai dai ka bada umarni abi, to wlh bazan lamunta ba! Hakuri na Ya ?are, idan shi ka rufe masa baki to ni baka isa kayi galaba akaina ba!" ta fada tare dakai hannu ta bugi gaban table da karfi, kafin ta yunkura ta mike tare da kallon Alhaji ubaid.



"Ni zan tafi, tun da naga kai baka da niyar barin gidan," mayar da dubanta tayi ga benazir"tashi mu tafi" jiki asanyaye benazir ta mi?e, nan take zeenatu ta fashe da kuka tana fadin"Inna lillahi mom layla dan Allah kada ku tafi, wallahi banso, mommy kada ki bari su tafi, daddy kace masu su su yi ha?uri su zauna, ko kuma su tafi da ni" Hankalin Tani dana lami ba karamin tashi yayi ba, ganin rikicin dake shirin 6allewa.



Wani irin tausayin ta ne ya kama benazir sam batason ta rabu da yarinyar sai dai ba yadda zatai dole tabi umarnin mahaifiyarta.



Da sauri Alhaji Ubaid Ya mike muryarshi da 6acin rai Yace"haba layla menene haka? Yanzu abun ki kai kin kyauta? Mutane suna zaman su lafiya kin tarwatsa masu farin cikin su"



Dakatar da shi Alhaji musa yai, Cike da isa Ya mike tare da kallon fuskar Hajiya layla dake huci.



"Ga hanya nan ki tafi, Allah Ya raka taki gona" bayan ya furta hakan Ya juya azafafe Ya nufi bedroom dinsa Yana shiga ya dauki wayarsa, Call Ya danna tana fara ringing akayi picking

Muryarsa akausashe Yace"kada ku bar kowa ya fita daga gidan nan Idan Har bani na baku umarni ba"!



On the other hand Muryar wani basamuden mutun ta amsa mashi da cewa "Angama Yalla6ai" sauke wayar yayi





"Haba dear, why ba zaka bari su tafi ba, na fa ji kiran wayar da kayi, meyasa zaka rike su? Tun da matar nan ta nuna bata son tafiya to ka ?yale su su tafi mana," muryar mom sarah a kule tayi maganar tana duban bayan shi...



Tamkar tayi magana da bango, babu alamun zai juyo ya fuskance ta balle harya amsa mata, Rai a6ace ta dawo ta gaban shi ta tsaya idanunta cike tab da kwalla ta furta"magana fa nake yi maka....."



da buWar bakinsa sai cewa yai"Toh Uwata Ina sauraron ki" ya fada yana ru?e qugunsa, Idanunsa akan fuskarta, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin shakkarshi, sam takasa cigaba da yin maganar.



Gefen wuyanta ya shafa da tafin hannun sa"sau nawa zan ja maki kunne akan ki daina shiga abun da ya shafi dangina!" cikin sanyin murya tace"bazan ?ara ba"



Jinjina kanshi yai, kafin ya ?ara furta wata maganar, Muryar zeenatu ta karaWe kunnan su.



Shigowarta kenan dakin ko sallama babu, Muryarta da shesshekar Kuka take fadin"daddy dan Allah kada ka bari su tafi, ni ban gaji da ganin su ba, ko kuma ka bari na bi su mu tafi a tare"



Juyawa yayi tare da daura idonsa akan ta, fuskarta tayi jawur hawaye na sintiri kan kuncinta.



Mi?a mata hannu yai da sauri ta nufe shi, hugging dinta yai tare da Waura hannunsa kan bayanta yana dan bubbuga shi cikin sigar lallashi.



"Ya isa, Ki daina kuka My daughter, ko dan saboda ke bazan bari su tafi ba, dolensu ne su zauna gidan nan ko suna so ko basa so" sauke ajiyar zuciya zeenatu tayi jin abunda yace, Hankalin ta ba karamin kwanciya yai ba, Hajiya Sarah ta kasa furta komai, Jikin ta yai mugun sanyi musamman yadda Taji Alhaji musa Yana magana da gadara babu Wa'a a kalamansa....



A fusace Layla Ta nufi dakin ta, bayan tace da benazir taje ta haWo kayanta su tafi, bin bayan ta Alhaji ubaid yayi kamar zai rufeta da bugu sai faWa yake yi mata, Ko kallo bata isheshi ba, trolley din kayanta ta Wauko Ta fara kwashe kayanta dake a cikin closet tana jerawa a akwatin.



Dawowa dr shureim yayi aWan rude yake kallon dining din ganin babu kowa, da sauri Ya nufi dakin Benazir Yana shiga ya sameta, zu?unne gefen gadon ta tana kuka, ga trolley din kayanta da ta gama haWawa.



a ruWe ya furta Benazir? Lafiya? Meya faru naga hawaye akan fuskarki"?



Jiki asanyaye ta mike tare da kallon shi, fuskarta tayi jawur da ita.



"Yaya shureim bayan kaje amsa kira, mommy ta fara faWa akan ita bazata cigaba da zama gidan nan ba, shine tace min inzo in hada kayana mu tafi, ni kuma bana son tafiya saboda ban cimma burina ba, na ganin na haWu da Aneelerh...."



Share mata hawayen ta ya somayi da hannayensa cikin sigar lallashi Yace"kiyi hakuri ki daina zubar da hawayen ki, bana so kina sanya damuwa aranki, amma ni kaina na goyi bayan ku tafi benazir! Ko dan saboda abunda ke faruwa dake agidan nan, Ina jin tsoron na rasa ki, kwata kwata hankalina bai kwanta da zamanki ba'



"Yaya shureim idan na tafi tayaya zan haWu da Aneelerh"?



Harya buWe baki zaiyi magana, kwatsam Wayarsa ta fara ringing, a hanzarce Ya duba sunan mai kiran nashi, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, arude benazir tace yaya shureim lafiya naga kana murmushi"



"Alhamdulillah, Kiran da muke ta jira ne sai yau Allah Ya nufa zamu gana da su, kar6i kuyi magana, abban Aneelerh ne Yake Kiranki...." Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin picking call din kamar zata zauce tsabar murna



Muryarta da zumuWi ta furta"Assalamu alaikum Abie Ina kwana...."



Kafin ta ?are maganar unexpected Muryar Aneelerh ta ratsa kunnanta da wani sauti mai karfi ta furta"BENAZIR!! Mafarki nake ko gaske"? Fashewa da kuka benazir tayi jin muryar aminiyarta da kunnuwanta sukai maraicin ji na tsawon shekaru.



Cikin shesshekar kuka tace"Wallahi nice Aneelerh, nice benazir din da kika sani..."



Kafin ta ?are maganar, Itama Aneelerh ta fashe da matsanancin kuka tana fadin"Benazir baki kyauta ma kanki ba! Meyasa? Meyasa? Meyasa kika gudu na tsawon shekaru? Idan wani abu ke damunki ba zaki faWa mana ba? Kinsan irin kunci da radadin da muka ji bayan tafiyarki? Kin kama hanya kin gudu kin bar jinjira acikin kwamin wanka, Da ranki da lafiyarki baki ta6a kira kinji awani hali Yarki take a ciki ba, wai dan Allah meyasa kikayi haka benazir meyasa.....?" kasa ?arasa maganar tayi saboda kukan da ya sar?e makoshin ta.





Tsananin tausayin su ne Ya kama dr shureim, tun dazu yana atsaye yana kallon Banazir kuma yana sauraran komai da suke tattaunawa.





"Dan Allah Aneleerh Ki nutsu inyi maki bayani..." Aneelerh bata bari tayi mata bayanin ba rai a6ace tace"me zaki faWa min benazir? Ni meyasa ma kika kirani ne? lokacin da yakamata ki kira baki kira ba sai yanzu da lokaci ya kure...." hankali atashe benazir ta ke sauraron ta idanunta sun kaWa jawur da su la66anta na kerma ta furta"meyasa kikace haka"?



?uff taji Aneelerh ta kashe kiran, hawaye na sintiri ta dago tana kallon shureim wanda tuni jikin shi ya gama yin sanyi.



"Yaya shureim ta kashe kiran, dama nasani ba lallai ta kula ni ba..." tsananin tausayinta ne Ya kama shi, hannu yasa ya kar6i wayar, Ya sake Kiran Aneelerh ta?i Wagowa.



Text message Ya tura mata



_Aneelerh ki Waga kiran, Ba benazir bace yayanta dr shureim ne Ina son Yin magana dake_



A 6angaren Aneelerh, Jiki amace ta sulale kan carpet ta zauna dirshan sai kuka takeyi, bakomai take tunawa ba face Angel da tajuddeen, Taji takaicin yadda Benazir tayi watsi da rayuwarsu gashi Yanzu ita benazir din ta dawo su kuma sun 6ata babu su a doron duniya

Muryar Angel ta soma tariyowa kalaman da saba fada mata tuntana yar ?an?anuwarta



_Aunty aneelerh wai meyasa Mommyna bataso na? gani yar kyakkyawa dani kowa rububina yakeyi amma ita, bata damu dani ba, shine ma ta haifeni ta bar ni acikin kwamin ka, idan bata sona to meyasa ta haife ni ay da ta sani ta kashe ni acikin ta_



?arar shigowar sakon ne Ya fargar da ita daga zurfin tunanin da ta shiga, zuciyartace ta dinga tunzurata akan kada ta duba wayar ta ?yale ta kawai, saboda ta bata haushi, Taji zafin abunda tayi.



Wayar sai ringing takeyi taki dubawa, kasa jurewa tayi, saboda ita kanta tayi kewar aminiyartata, bazata taba mantawa da ?awancensu ba, duk da taci wahalar banezir saboda rashin jin maganarta.



Yatsun hannunta na kerma ta ru?o wayar ta duba sakon, bayan ta gama karantawa, a kagare ta soma kokarin bin kiran don taji me dr shureim zai faWa mata, aranta tana mai mamakin bayyanarsu lokaci Waya.



Video Call ta kirasu don ta ?ara tabbar da cewa su dinne, bayan sunyi picking call din kallon kallon suka soma jefawa junansu, kowa yasha kuka, hakika sunyi mamakin canzawar da sukayi, duk sun fara manyanta...

Cikin sanyin murya ta furta"ya shureim! Dama kana nan"!

Jinjina mata kai yai alamar eh, kafin Ya soma magana cikin nutsastsiyar muryar shi.



"Aneelerh, inaso ki nutsu ki saurari abun da zan fada maki" amsa mashi tayi da toh, saboda tana ganin girma dr shureim.



"Abun da Ya faru da banezir bayin kanta bane, mu kanmu bamu san da hakan ba sai lokacin da ta dawo, bata a cikin hayyacinta gaba Waya alamomin da muka gani ajikinta ya tabbatar mana da cewa Kurciya akayi mata, shiyasa ta gudu tabar yarinyarta batare data tuntu6i kowa nata ba......" atsanake shureim ya fayyace mata komai, Ita kanta benazir din batasan da abun da suke zargin anyi mata ba sai yanzu da taji abakin dr shureim, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, aneelerh kuwa jikinta yagama mutuwa, cikin tashin hankali take ambaton inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.



Dr shureim Yace"hakuri zamuyi da abunda Ya riga ya faru, bana so muna tuna ba....." nasiha ya cigaba dayi masu har saida Yaga hankalin su Ya kwanta, kafin Ya bar wayar a hannun benazir Ya basu wuri don su gana da junansu

Kamar yau ce rana ta farko da suka fara haWuwa, sai bin kansu suke yi da kallon kurulla, Allah ne kaWai Yasan irin kewar juna da su ka yi.



"Benazir bansan yadda zan misalta maki farin cikin da nake a ciki ba, Allah shine shaidata, Naji dadin ganinki da ranki da lafiyarki"



Cikin sanyin murya tace"nima haka Aneeleerh, ashe da rabon zamu gana bayan tsawon lokaci"? Ta fada tana matse kwallar da ta cike idununta.



"Aneelerh, Ina Yarinyata dana bari? Ina mijina Yake? Mommy ta fada min basa kasar nan amma ni ban yarda da maganarta ba, dan Allah ki fada min gaskiya, saboda nasan ke kadaice zaki fada min"



Fuskar Aneelerhh Wauke da matsananciyar damuwa take kallon benazir dama sai da tayi fargaban tambayar da zatai mata, tuni taji zafafan hawaye sun cika mata idanunta.



"Aneelerh kinyi shiru baki ce komai ba? Pls ki yi min magana wlh ji nake kamar zan zauce saboda ?agarar da nayi na son ganin su ..." ta faWa tana dubanta



"Kada ki ji komai, Ki faWamin kawai ko da ace sun mutune zan rungumi ?addara..." cikin karfin hali ta faWa, tun da tafara maganar Aneeleeh ke kallonta gwanin ban tausayi.



bata jin zata Iya sanar da ita a yanzu, ko dan gudun kada zuciyarta ta buga, ?wara ta kwantar mata da hankalin ta.



?a?aro murmushi tayi akan fuskarta



"Abun da mami ta faWa maki gaskiya ne, suna nan cikin koshin lafiya, sun yi tafiya zuwa south korea inda Uncle dinsa abdalla ke zaune, amma ina ji araina sun kusa dawowa"



Tsabar farin ciki yasa banezir sakin dariya har fararen hakoranta suka bayyana, Aneelerh dake kallonta tsantsar tausayintane Ya ?ara kamata.



"Dan Allah Aneelerh idan kina da hotonta ki turomin inason ganinta, Idan ma kina da number taj din ki bani sai muyi magana da shi, wlh na?agara da son ganin su"



Murmushi Aneelerh tayi"kada ki damu zan tura maki da hotonta har ma dana yaro na, sai dai bani da layin taj bansan da wanne yake amfani acan kasar ba"



Da mamaki tace"Aneeleerh dagaske kin haihu? Ya'yan ki nawa yanzu"?



"Shi kadai Allah Ya bani, baki ganshi ba, kyakkyawa kamar Angel dinki.."



Muryarta na rawa tace"Allah sarki, Aneeleeh, na tayaki murna, Ina mijin ki ko shima hada shi suka tafi korean"?



"Atare suka tafi" murmushi benazir tayi kafin ta kuma cewa"ki bani labarin Yarinyata, inason jin kuruciyarta, Ina fata dai bata dauko halina ba.." dariya aneelerh tayi da zolaya tace"like mother like daughter, Har tafi ki rashin ji magana," waro idanu banazir tayi hada sanye hannu ta dafe kanta Waya"indai kuwa hakane nasan ba lallai ta yi min da sauki ba, watakil ma ta tsane ni, bata son ganina" ta fada tamkar zata fashe da kuka



"Ki ma daina wannan tunanin, taya Wa zai ?i jinin uwarsa, ay bata da abu mafi soyuwa da yawuce mahaifiyarta, ni nasan Angel bazata ta6a gudunki ba"



kwantar mata da hankali taci gaba dayi, har ta bata labarin unaisah, taci dariya wani wurin kuma ta matse kwalla.



"Allah sarki tajudden na barshi da dawainiyar yarinya, abunda yakamata ace ni nayi bansamu damar yi ba..." in a cool voice tayi maganar," shiru suka danyi na wani lokaci kafin Aneelerh tace"Har yau babu labarin Aisha! Baiwar Allah taga rayuwa, gaba daya ?addarace ke bibiyar rayuwarmu lokaci Waya ?awancenmu ya tarwatse nayi takaicin rasa farin cikin amintarmu' hawayen dake taruwa acikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta....



Shiru banezir tayi zuciyarta cike fal da jimamin halin da suka tsinci rayuwarsu.



"Inaso nazo gidanku Aneelerh, ki kirani da layinki, sai inyi saving contact naki" amsa mata tayi da toh, sunjima suna waya kafin sukayi sallama da junansu..



Meya faru bayan Ummi Ta fuce daga dakin su Unaisah?



Da gudu ta nufi dakinta, tana shiga ta bude toilet ta tsaya agaban Sink tana kwarara amai, idanunta sun kada jawur da su, shatun jijiyoyin goshinta sun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login