Showing 354001 words to 357000 words out of 391264 words

Chapter 119 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2574

Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba.

ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.."

bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?!!...."

Dakyar ya ?are maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid.

Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci.

Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naWeta.

Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi.

Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"?

Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya mi?a ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka"

Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa.

Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu.


Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya dam?i ?eyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka.

Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faWa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma.

"Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha.

"Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"W'



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*



*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM]  Amin@ M Yusuf Yol@: =?%?=؋?=؞? &?=ؔ?=؞?>???





~___________________________________~



A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu Wauke da damuwa.

"Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faWa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ?ona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......"

da?yar Benazir ta ?are maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa.

Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin.


"Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda ba?in cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan"


Aneelerh ta Waura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faWa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki.... "

Aneelerh bata ?arasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba Waya Wokin ganinki mu ke yi"

Babu alamun zata tanka masu.

"Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita"

Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaWa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake sa?awa a cikin Zuciyar shi.

Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su.

"Pls ina son insan meye ala?arku da Aisha ne? A nan take zaune?"

Murmushi Taj ya Wan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar.


A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ?ara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..."

Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita.

A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!"

Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faWa min meke damun ki?"

dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..."

sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruWewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa.

"Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ba?" ta faWi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi.

Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta mi?ar da ita zaune saboda karfin hali irin nata..

Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest Winta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haWu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya Wauka har a jikinta tana jin shi.

RuWewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. "

ta faWa tana ?o?arin ?wace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faWa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi ta?i bari ta motsa.

Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta.


Kafin Ta Waura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke Wan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya.


Ji ta yi inama ace Batool ce Wiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daWewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne.

Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ?ara tabbatar da hasashen ta.

"Aunty Ummi da sauki?"
Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh .


Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu Waya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ?afarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arzi?i ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ?afa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sau?i, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faWa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ?o?arin mi?ewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi.


__________________________________
'?

Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ?urawa ceilling idanunta da suka kaWa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ?ona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta?

Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai ma?ura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara.

_______________________________ '?


Around ?arfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari Waya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit.

With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi

"Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo.

Cikin sauri SA Win ya buWe tan?ameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ru?o handles dinsu ya bi bayan Chief da su.

Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su.

Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin ya fuce.

Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka.

Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down.

tun kafin ya ?araso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi.

A hanzarce suka mimmi?e tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya Wan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna.

With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu.

Gaba Waya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai.

Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da mi?a masa hannu suka gaisa da juna.

Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim..

"A yi mini afwa, na barku kunata jirana." ?an murmushi suka yi gaba dayansu.

Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba"

Fuskarshi a sake ya Wan jinjina kan shi,

Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da mi?a masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana Wan jinjina kan shi.

Lamarin ya Waure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo Waya dana Taj.

Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi.
Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa.

Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,

A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ?ara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaWai ya sani, bayan haka yanzu an Waga ?afa da kawo min harin."

Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruWani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ?asa.

"Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?"

Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin.

Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba Waya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant Win kurkukun ?addara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya Wago ya dubi Benazir suka haWa ido cikin na juna.

"A lokacin baya, kafin ?addara ta rabaki da gidan mijin ki,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login