Showing 264001 words to 267000 words out of 391264 words

Chapter 89 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2567

masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?"

Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi ?arfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ?ara ganin ta ba"!

Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata.

Giant Win dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin buWaWWiyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita Wakin fiWa kamar yadda kika bani umarni, ban ?ara bi ta kanta ba"

Murmushin gefen fuska ta saki, "If she dies, I will be sad because I want her to witness the black night,
Even though I know even if she is alive, she will not be useful anymore."


Cike da sha?iyanci ta faWa kafin ta sake ce ma giant Win,

"Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita Wakin fiWa ka tabbatar sun feWe sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar.

"Bayan na kaita Wakin fiWar, ban ?ara komawa ba, saboda ba hurumina bane"

Bata tsaya taji ?arshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya.

bata nufi ko'ina ba sai dakin fiWa, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici Win dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta.

Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta.

Wani irin ?ululun ba?in ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani haya?in huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa..


A matu?ar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya Wauke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo.

da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta.

_"FaWa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yun?urin yi min rashin Wa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_

waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya ?arfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi

_bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_

Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata.

Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta faWo dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta dam?i wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke faWa mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell!

cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta ?arasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta Wauka gurin yin jinyarta ba, har Winki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji.

Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu.

Kamar zasu yi dambe ita da Khala, saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da ?arfi kamar doki, da ?yar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa Wagowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin Wan uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas.

Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar ?arama dake sai ba?ar zuciya kamar ta kafuran farko! Dame kike ta?ama ne? Ina karfin naki yake uhm!"? Nishi ta dinga yi tana huci kamar zata iya ta6uka wani abu.

Sassauta murya Khala tayi, "Ba duka muka taru muka zama Waya ba, kasancewata a gidan kurkukun ?addara, ba hakan yana nufin nima muguwa bace, kamar yadda kika zata, kinyi min mummunar fahimta, amma nayi maki uziri saboda bakisan komai dangane dani ba..."

ta faWa tana kallon idanun Gabriella da suka kaWa jawur.

Numfasawa tayi kafin ta Waura da cewa, "Da ace ni muguwa ce da ban taimaki rayuwarki ba, nasan yanzu tunaninki ya dawo, dama abunda na ke gudu kenan saboda nasan za'a rina, yanzu da ban zo Wakin nan ba da tuni kin jima da kashe kanki saboda Wamsil basira, idan kina tunanin mutuwa mafita ce a gareki toh ki daina, shi jarumi ba'a san shi da karaya ba, kada ki zama raguwa ki zama jaruma mai iya tankwara zuciyarta me kuma burin Waukar fansar zaluncin da aka yi mata.

Tana jan nishi da ?yar ta furta, "Who are you? Where did you find me? and Why did you help me?"


"Sanin wacece ni baida amfani, iya abunda zan iya sanar dake shi ne ba a haife ni a gidan kurkukun ?addara ba, bada son raina na kasance a cikin shi ba, ta karfi da yaji aka kawo ni nan, bazan iya misalta maki ?unci da raWaWin da na ji a lokacin dana buWe idanuna na tsinci kaina a gidan kurkukun nan ba, na ga musiba da bala'e da idanuna, abunda ban ta6a zaton ko a mafarki zanga makamancin shi ba, zuciyata a karye take saboda anci amanata an yaudare ni, bayan haka an nuna min fin karfi ba yadda na iya,...." idanunta ne suka ciko tab da kwalla.

"Kamar yadda kika so kashe kan ki, nima nasha yin yunkurin yin hakan amma idan na tuna menene makomata? Sai inji na gaza! Mutuwa bazata hana su cigaba da aikata fasadi ba, saboda su Win 6atattu ne in har bamu haWa hannu mun kawo ?arshen su ba, babu abunda zai canza na daga zaluncin da suke aiwatarwa, bayan haka babban abunda yasa nake so na rayu shi ne ya'yana inason na sake ganin su ko da da numfashina na ?arshe ne".

muryarta na rawa ta ?are maganar, hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, Gabriella dake sauraran khala, itama hawayene kan fuskarta, tana da wuyar sha'ani a rayuwarta bata yarda da mutane amma karo na farko ta yarda da tsohuwa Khala, maganarta ta karya mata zuciya.

A hankali ta zame tafinta daga kan Gabriella, hakan ya bata damar mi?ewa ta zauna da ?yar tana duban fuskar khala da tausayawa

"Ke Wan uwan ki Waya ne, ni kuma jikokina da suka salwanta agidan kurkukun ?addara yawa ne da su, inaji ina gani ban iya tsinana masu komai ba saboda an nuna min fin ?arfi...." fashewa ta yi da kuka kamar ?aramar yarinya.

Itama Gabriella din kukan ta fashe da shi saboda tausayin khala da ya mamaye zuciyarta ashe ita bata ga komai ba tayi mamakin ha?uri da juriyar tsohuwar da har ta iya kai tsawon lokacin nan bata haWiyi zuciya ta mutu ba.

"Yau kimanin shekara ashirin cuf, rabon da in sha?i iskar duniya saita gidan kurkukun ?addara, bani da burin da ya wace in tona masu asiri, kullum ne sai na ro?i Allah dare da rana ba fashi, duk da har yanzu ba wani sauyi, ban ta6a gajiyawa ba, saboda nasan Allah ne kadai zai iya cika min burina kuma yana sane dani, wani jinkirin Alkhairi ne kuma ina ji araina ?arshen kurkukun nan ya zo" ta faWa tana jan magina.

"Kin tambayeni Ina na tsinto ki?" A ranar bayan na fito daga fadar Elder naji ina sha'awar in kewaya kurkukun duk da bana so nayi tozali da abunda zai hanani kwanciyar hankali, har zan gifta na hango tsohuwa inno tare da giant din da ya Wauko ki babu sutura a jikin ki raina ya 6aci ba kaWan ba, nayi zaton ma kin mutu ne, kwatsam idanuna suka hango min yatsun ?afarki na motsi, wani iko na Allah ni da bana shiga huruminsu bansan ya akai zuciyata ta azalzala min akan in taimaka maki ba, cikin sanWa na bi bayan su, har suka aje ki a Wakin fiWa, tafiyar su ke da wuya, nayi 6adda kama ta hanyar amfani da sihiri na, na shiga cikin Gigantes Medici din batare da sanin su ba saboda hankalinsu ya karkata akan aikin fidar da sukeyi, kafin su zo kanki cikin abunda bai fi da?i?a talatin ba, na sace ki na kawoki Wakina, na fara kokarin tsayar da bleeding din da kike yi kafin na dinke raunukan jikin ki...." tiryan tiryan khala ta zayyana mata komai, wani irin son tsohuwar ne ya kamata har batasan sa'ar da ta faWa kan kirjinta ba, ta rungumeta cikin shesshekar ta furta, "Ki yi ha?uri nayi maki mummunar fahimta, ki yafe min"

?an murmushi khala tayi kafin ta daura da cewa, "Tun kafin ki dawo hayyacinki na ji kina ambaton sunan Wan uwanki Gabriel, na kwallafa rai a kan son sanin wanene shi? a cikin bookshelve Wina ina da littafin register na fursinoni (Sijil al-sujna) a cikin littafin na buWo ina bincikawa don inga wanene me suna Gabriel, ban sha wahala ba, saboda nayi nazari na gane cewa ku Win ba tsoffin prisoners bane cikin waWanda aka kawo ne a ?arshen shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, cikin sa'a na ga sunayen ku, a fahimtana Wan uwanki ne ko?..." cikin sanyin murya tace, "twin brother Wina ne."

"Zaki iya tuna tayaya akai kuka tsinci kanku a gidan kurkukun ?addara?" Girgiza kai ta yi har lokacin bata raba jikinta daga na khala ba.

"Bazan iya tuna komai ba, Wan uwana kadai na sani, pls ki taimaka min in gan shi..." Shiru tsohuwa khala ta yi saboda tasan me zai biyo baya in har ta faWa mata cewa baya a cikin kurkukun, cos ta ga sunan shi cikin list na escaped prisoners, ta lura da yadda take mugun son shi in har ta faWa mata, zuciyarta zata karaya ne kuma zata ga kamar ya manta da ita ne shiyasa ya tafi ya barta batare da ya taimaki rayuwarta ba"

?agowa tayi da kanta, "kinyi shiru baki bani amsa ba, bana so na rasa Wan uwana, nasan yana cikin wahala kuma yana nemana, pls ki Wauko shi ya dawo nan mu rayu atare"

Dafa kafadarta khala tayi, "Zan iya jefa rayuwarmu da tashi cikin haWari, abunda yasa nake 6oyenki saboda a yanzu haka dattijuwar da ta kusa kashe ki, nemanki take ruwa ajallo, amma in har Allah yayi mana tsawancin kwana gaba na yi maki al?awarin zan hadaki da Wan uwanki..."

cikin karyayyar murya ta ce, "ya mutu ko"? Girgiza kai tsohuwa khala ta yi, "A'a yana raye, "

"Ta ya kika san yana a raye"?

"Zan nuna maki"

?aga mata kai ta yi alamar toh, saukowa suka yi daga kan gadon, ta Wauki sandar ta, ta nufi gurin furannin dake a Wakin, Gabriella tana a biye da bayanta, da sandar ta nuna mata fure kore shar da shi a cikin wata tukunyar shi mai kyan gaske.

"?an uwanki yana a cikin ?oshin lafiya, kin gan shi nan" aruWe ta dubi khala, "tayaya hakan zai yiwu! Mutun ya zama fure??"

Dariya khala tayi, "It's a magic trick kema idan naso sai in mayar dake fure, Ko kina da ja ne?" Ta faWa da zolaya, da sauri ta girgiza kai,

Zu?unnawa tayi a gaban furen ta ?ura ido tana kallon shi, cikin sanyin murya ta furta sunan shi abun mamaki sai ta ga furen ya motsa ganyayyakinsa kamar iska ta kaWa shi.

Murmushi ta saki,"Da gaske kaine?" again ya ?ara motsa ganyen shi, wani daWine ya lullu6eta har ta buWe baki zata ?ara magana kwatsam ba zato ba tsammani taji kamar an jeho mata wu?a a kirjin ta,

dafe shi ta yi da hannun ta, radadi ya hana ta motsa, nan take ta fara yin aman jini,

Hankalin Khala kwata kwata baya akanta batasan meke faruwa da ita ba, saboda tayi zurfi acikin tunanin ta, sai kokari Gabriella take ta ru?o rigarta amman ta kasa saboda kermar da yatsunta ke yi....>?z?

__________________________________
'?

*BENAZIR=ؔ?*

Suna a zaune kan darduma su biyu ita da Zeenatu, sun haWa baki suna karatun kur'ani da suka buWe akan qur'an stand

Wayar tace ta fara ringing, bayan takai aya ta dakata da yin karatun ta mi?e da sauri ta nufi wayar dake ajiye saman gadonta

"Aunty Benazir, Azeezaty ne?" Zeenat ta tambaya tana kallon ta

Bata ba ta amsa ba, har saida ta dauki wayar, ta dubi sunan me kiranta, tayi mamakin ganin sunan Uncle ya bayyana yau wata rana Alhaji musa ya kira ta, a ranta ta furta Allah yasa alkhairi ne.

?aga kiran ta yi ta kara wayar a kunnanta, tana kokarin yi mashi sallama ya katse ta da cewa, "Ki same ni a garden yanzu" amsa mashi ta yi da toh.

Aje wayar tayi gaban mirror, ta juya suka haWa ido da Zeenatu ta ?ura mata ido tana kallon ta.

"Daddynki ne ya kira ni, ki cigaba da yin karatun yanzu zan dawo" tace toh"

Bayan fitar Benazir, cike da zumuWi ta mi?e, ta Wauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura.

Lokacin da Benazir ta ?araso Garden Win tunkan ta ?arasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi.

bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ?irjinta da hannu Waya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!"

Yana Jin muryarta da sauri ya Wago ya kalle ta, zumbur ya mi?e tare da ambaton sunan ta "Benazir!"

Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba..

Gaba Waya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruWe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta.

Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce,"

Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi.
Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi.

"Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faWa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ru?o hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare.

Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buWe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka ?urama juna ido kamar yau suka fara haWuwa, sunyi kewar junan su sosai.

"Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?"

Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan sha?uwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita..

"Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba?

"Ka manta wayata tana a hannunka?"

"Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ?asar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?"

Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ?asa, tasan bata kyauta mashi ba..

"Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ?aunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ?aramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta.

Da ?yar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ?ara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buWe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login