Showing 66001 words to 69000 words out of 391264 words

Chapter 23 - Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

2580

ba su tafi ba sai da sukaga ya samu motar hayar da zata shigar da shi cikin garin joss tukunna sukayi mashi bankwana.



Tun da suka shiga motar, danejo ta kankameshi, kamar wani yace zai kwace mata shi, wani irin mugun tsoron mutane take ji, mutun Wayane ta yarda dashi ta kuma damka amanarta agareshi saboda tasanyawa ranta cewa bazai ta6a cutar da ita ba.



Kafin su karasa cikin garin, tuni bacci yayi awon gaba da ita, a yayin da kanta ke asaman kirjinsa, hankalin taj sam ba akwance yake ba, saboda fargaban kada miyagun da suka kai mashi farmaki su gansu, yasan muddin sukasan cewa bai mutuba, to kuwa zasu nemi hanyar da zasu kashe shi ne kamar yadda suka kashe dan uwansa uzair, mutuwar da tayi matu?ar girgiza shi, dabara ce ta fado mashi da sauri ya sanya hannu ya cire gyalen danejo da take daure qugunta da shi, ya lullu6e fuskarsa, Idanunsa ne kadai suke a bude.



Bayan isarsu joss, motar ta sauke su a tasha, driver yace ina kudin mota, sai lokacin ya tuna da baida ko sisi, sai dai kayan da fulanin nan suka bashi, hakuri ya bashi ya hada shi da katon dawon fura, mai motar baiyi gardama ba ya kar6a, ruko hannun danejo yayi suka soma tafiya atare har ya sama masu abun hawan da zai kaisu unguwar da su ke, kafin isar su tuni dare ya ritsa da su.



Da farin cikinsa Ya zo unguwar, amma lokacin dayaga gidajensu a kulle, nan take murnar ta koma ciki, tunkafin ma yaji abunda ya faru hankalinsa yai mugun tashi, baisan ina zai tsoma kanshi ba, ga yar mutane da yake ta yawo da ita, harta fara yi mashi kukan yunwa take ji, tausayinta ne ya kama shi, da ya san hakan zata faru dabai yi kuskuran tafowa da ita ba..



A bun hawa ya kuma tsaida masu, suka nufi gidan uncle abdalla da ita don ya ga ko sun dawo daga south korea, tunkafin me abun hawan da ya kawo su ya sauke shi ya hango gate din gidan a kulle alamar basa nan, tamkar ya daura hannu aka ya fasa ihu haka yaji.



Tunawa da amininsa muhsin wanda Angel ta ta6a sace ma matarsa waren takalmi yasa shi yanke shawarar zuwa gidan shi tare da danejo, yasan acanne zai ji komai daya faru bayan 6acewarsu





Basu sha wahala ba, cikin sa'a suka same shi agida, tare da matar shi, lokacin dayaji sallamar taj a firgi ce ya mike zaune yana kallon kofar shigowa falon, bai gane shi ba har saida ya cire mayafin danejo dake akan fuskarsa tukunna ya shaida shi, muryarshi na rawa yace taj! Dama kana araye? Tsawon lokaci muna ta neman ku babu kai ba uzair duka an nemi ku an rasa"? A rude yake jefa mashi tambayoyin, matarshi da sauri ta nufi danejo ta ruko hannunta suka zauna kan sofa, kafin ta mike ta shiga ciki ta kawo masu abinci da ruwan shi.



"Dan Allah abban muhsin kabarshi Ya huta, bakasan daga ina yake ba, sannan bakasan meya faru dashi! Idan har bai samu nutsuwa ba tayaya zai iya fayyace mana abunda ya faru da su"? Fuskarta a yamutse tayi maganar, jinjina kai yayi fuskarsa da tsantsar al'ajabi yace da taj su shiga ciki yayi wanka ya canza kayan jikin shi, yaga duk sun jigata kamar na almajirai,



Bayan sun huta, sunci sun koshi, har bacci yayi itama danejo ta dan runtsa, wuraren karfe shabiyu na dare yafarka ya taras da muhsin ya zabga uban tagumi yana kallon shi, mamakine yacika shi.



"Ka yi hakuri taj, kada kaga na takura maka, wallahi na damu da rashin ku, hankalina bazai ta6a kwanciya ba har sai ka fadamin meya faru da ku da har kuka gudu aka neme ku aka rasa......"



Mikewa zaune taj yayi, kafin a tsanake ya labarta masa komai daya faru, wani irin matsanancin kuka mai cin rai muhsin ya fashe dashi, bakomai ya firgita shi ba ya kuma bashi tsoro face mutuwar amininsu uzair ta yi matu?ar girgiza shi, cikin shesshekar kuka ya ke fadin"taj dama abunda ya faru daku kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un wannan wata irin masiface, Uzair ya mutu, Angel ta 6ace, rana Waya an tarwatsa farin cikin zuri'arku, in sha Allah sai Allah ya saka maku wannan zaluncin da akayi maku....."muhsin ya yi kuka tamkar ransa zai fita,

Lallashinshi taj ya somayi yana fadin yayi hakuri komai ya riga daya wuce, yanzu shi damuwarshi ina aneelerh take matar uzair"?



Da?yar muhsin Ya samu nutsuwa, ya fara mashi labarin abunda Ya faru bayan 6acewarsu,

Yaji dadin jin cewa Aneelerh tana agidan iyayenta, abun da ya faranta ranshi, Yaron da yaji ta haifa masu, tunkafin ma yaganshi Yaji Ya kamu da kaunarsa, kaunar da yake yima uzair gaba daya ta koma akan yaron da bai ta6a ganinsa ba......' acikin labarin da muhsin ya fada masa abu Wayane bai sanar da shi ba, rasuwar iyayensa gudun kada zuciyarsa ta buga, kwara idan ya samu nutsuwa ya sanar dashi daga bisani.



A daren ranar kafin muhsin yabar dakin taj, Sai da taj ya gargaWesa akan kada ya sanar ma wani cewa yagansa saboda rayuwarsa tana acikin hatsari, idan mutanan da suka kashe uzair suka san da zaman shi tabbas zasu cigaba da bibiyarsa har sai sunga bayan shi.

Cikin sanyin murya muhsin yace in sha Allah babu wanda zaiji zancen dawowarshi, zai rufa masa asiri yaci gaba da zama a gidansa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mashi mafita....



Tsawon wata guda suna agidan muhsin, a cikin kwanakin da yayi baya iya runtsawa saboda damuwar rashin angel, duk daren Allah Sai yayi nafilfili saboda angel dinsa, duk ya fita hayyacinsa sam baya da koshin lafiya ciwon kafarsa tamkar ana fama masa shi abu ya?i ci ya ?i cinyewa, muhsin yaso ya bi shi suje asibiti a duba lafiyarshi gudun kada ya rasa ranshi amma yaki yarda saboda bayason wani yaga fuskarshi, ya ?wammace idan ma mutuwarce ta dauke shi agidan muhsin zaifi mashi sau?i akan wadannan azzaluman mutanan su kona shi.



A daren wata rana ne, Yana cikin Yin nafilfilin dare, Yajiyo dirar motoci a cikin gidan muhsin, A firgice Ya mike daga kan darduma Gabansa na faduwa, baisan su wanene sukazo gidan muhsin ba, a irin wannan lokacin karfe kusan sha biyu na dare, zuciyarsa na bugawa ya nufi falon gidan don ganin su wanene,

Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, ganin matasan samari masu jini ajika suna shigowa kowannansu sanye cikin shiga ta bakake kaya sun rufe fuskokinsu da facemask.



Bakomai ne ya tsoratar da shi ba face tunawa da wadannan body guards din da suka budewa alhazawannan motocinsu, nan take ranshi ya bashi cewar sune, hakan na nufin muhsin Yaci amanarshi, bayan yayi mashi alkawarin zai rufa masa asiri shine yabi ta bayan fage ya tona masa asiri, zuciyarshi ajagule ya furta meyasa zaiyi min haka! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankalin shi danejo kada suce zasu haWa da ita su kashe...



A lokacin zuciyarshi ta riga ta gama hasala, Jininsa akan akaifarsa yake, tunkararsu yayi muryarshi a fadace yace"kun biyo ni nan dinma donku kashe ni? Laifin me nayi maku ne? Da Waci aransa ya furta maganar, kamar daga sama yaji muryar muhsin daga bayan shi yana fadin"taj, ka tsaya zanyi maka bayani" a sukwane ya juya ya kalle shi a fusace yace"wani irin bayani zakayi min muhsin? haka mukayi dakai? ka cuce ni muhsin, ba zan ta6a yafe maka ba, yanzu dakai za'a hada baki don akashe ni"? Hawaye cike tab da idanunsa yayi maganar, fitowa danejo da matar mushin sukayi daga dakin duk suka tsaya suna kallon su....

Matasan da suka tsaya abakin kofar falon sun harWe hannayensu akan kirjinshi suna kallon shi, babu alamun zasuyi magana..



"Taj bazan ta6a cin amanarka ba, abun da ya faru da kai ba kai ka Wai ya shafa ba, hada ni kaina saboda ina jinka tamkar Wan uwana na, waWannan matasan da kake gani, ba su zo da niyar su cutar dakai ba, sai don su taimaki rayuwarka, Idan ka basu hadin kai in sha Allah zakuyi nasarar nemo Angel dinka data 6ata, bayan haka zasu tayaka daukar fansa akan mutanan da suka kashe uzair"



"Har yanzu ban fahimci inda zancenka ya dosa ba .." murmushi muhsin yayi kafin yaci gaba da cewa"su Win jami'an hukumar ISOD ne, nasan ba zaka rasa sanin CHIEF OWAIS ba, Wan gidan Sharafudeen Obinna......" wani irin al'ajabi ne ya kama tajudden muryarshi na rawa ya maimaita sunan Chief Owais da tsantsar mamaki yace"muhsin dagaske kake min ko wasa? Tayaya akai ma su kasan da zamana"



Kafin muhsin Ya bashi amsar tambayarshi, Chief owais Ya shigo bakin shi dauke da sallama cikin shiga ta kakin isod, da sauri matasan nan suka buga kafa tare da sara mashi, muhsin kamar zaiyi mashi sujjada tsabar yadda yake washe baki yana yi mashi sannu da zuwa yalla6ai, shi dai taj ya gaza yarda da abunda idanunsa suke gane mashi, kai ko a mafarki bai ta6a tsammanin zai haWu da chief owais ba, mutumin da a tv kadai yake iya ganinsa, sai gashi yau a zahiri Allah Ya nuna masa shi.



Cike da qasaita, Chief Ya nuna masa sofa alamar Ya zauna" jiki na 6ari taj yaje ya zauna yana ta faman bin shi da kallo a lokacin shima ya zauna kan sofa din dake fuskantar ta shi.



Cikin harshen turanci yace"nasan zaiyi wuya ace baka sanni ba, amma duk da haka zan gabatar maka da kaina, da farko sunana owais sharafudeen Obinna, chief na hukumar Isod...." ya faWa tare da Wan dakatawa yana dubansa, tun anan taj ya fahimci ba karamin mutunne bane mai ji da kansa.



"Malam taj, kamar yadda kake mamakin ganina nima haka nake mamakin kasantuwana acikin rayuwarka, ko a mafarki ban ta6a tsammanin akwai ranar da zan hana idona bacci saboda damuwa da mutumin da bansan wanene shi ba...." kalaman chief owais sun girgiza shi matu?a, har dai ya gaza jure wa yace"dan Allah ka fadamin meyasa ka damu dani bayan baka sanni ba"



da buWar bakinsa sai cewa yai"?arka ce sila" waro idanu waje taj yayi da tsantsar mamaki yake binsa da kallo fuskarsa da rudani yace"meyasa kace haka"?



Numfasawa yayi kafin ya soma magana muryarshi tamkar ana busa sarewa saboda dadin sauraranta....



A washe garin ranar dana dawo Nigeria daga U.S anyi min wani kira da ya tsaya min araina....



Fitowa yayi daga cikin bathroom waist dinsa daure da towel, yayin da dayan hannunsa ke a ruke da wani short towel yana tsane sumar kanshi, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, wayarsa dake akan nightstand ta soma ringing, dakatawa yayi da tsane sumar kan da yakeyi a hankali ya nufi wayar ya dauko ta yana duba number din da aka kirasa da ita, yayi mamakin ganin bakuwar number, A matsayin shi na jami'in sirri komai nasu asirrince suke yin shi, harta phone number dinsa special ce, bakowa yasan shi da ita ba, sai mutun yakai yake samun damar mallakar ta, bai yi niyar picking call din ba saboda a ka'idarsa baya Waga bakuwar number, ko kiransa akayi indai ba family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi......



Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa...

Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba.



Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"?



Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce,"



Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa,

"kinsan dawa kike magana"?



"a'a," ta bashi amsa atakaice



"Ur age"?



"7yrs" voice Win shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?



"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaWai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"



Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa



"Can i call u video"?



Da sauri tace eh,



Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka Wana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba Waya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta...



"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ?ananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon ?urulla kamar zai haWiyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba...



Zuciyarsa ba ?aramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta....



Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin yaWa aikinsu na ?an jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba.



Gaba Waya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance Waya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........



Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar.



Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba ....



Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya ?walla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ...



Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su...



A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel.



Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a.



Muhsin yana Waya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi Wayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji Wuriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba...



Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take,

"Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi,

Da sauri chief ya ruko hannunsa acikin nashi, cikin sanyin murya yace"ka yi hakuri, ni banzo don na fama maka raunin dake acikin zuciyarka ba, nazo ne don na tallafi rayuwarka, idan har ka bani hadin kai nayi maka alkawarin zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baka kariya, na kuma tallafa maka da duk abunda nake da shi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login