Showing 27001 words to 30000 words out of 346625 words

Chapter 10 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

xan da6a maki wukar nan kowa ya huta" Tsit tayi jikinta na rawa hawaye na sauka idonta, can karshen kwalta suka kai ta, wani kuturun uncompleted house da Surajo ke ginawa, sbda rashin wajen kwana yake kwana a haka, Salmanu yace "Shikenan sai ku tare nan daren yau kafin gobe da safe Hansai taje tayi mata jere a shagon naka" Iliya yayi wani dariya ya sauka daga adaidaitan yana kallon Jiddah da ko kukan ta kasa sbda fargaba da shock, ya daure fuska yana kallonta da jajayen idonsa yace "Sauka mu shiga Amaryata ta kaina" Da kyar ta sauko daga adaidaitan ya tisa keyarta har cikin gidan wanda duk dogayen ciyayi ne, Surajo yace "To ko 'yar kifi da ruwan leda ba a siya mata ba ai" Iliya yace "Ai akwai wasu daren masu xuwa da yawa bayan wannan, idan bata ci yau ba xata ci gobe" Surajo yace "Da akwai lemo daya ma da na siyo da rana ban sha ba sai ka bata ta sha kawai" Dariya duk suka dinga kyalkyalewa da, Can jikin bango jiddah ta rakube kusa da yar katifar dake kwance a dakin da wani karamin fitila da bbu hasken kirki, ko siminti bbu a kasa, banda warin ta6a da wiwi bbu abinda dakin ke yi, ta runtse ido tana jin abubuwan kamar a mafarki, sallama su Surajo suka yi ma iliya suka fita dakin suna dariya suka yi masa sai da safe, Ya mike ya kulle kofar ya dawo ya xauna ya fiddo kwalin ta6arsa ya kunna ya fara xuka yana kallon Jiddah da ta takure ko ina na jikinta na rawa, yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri amaryata cikin bacin rai na bubbuge ki, raina ne ya baci ba kadan ba, kinsan idan raina ya baci bana ganin komai idona rufewa yake, har mutum ina iya kashewa, yo sau nawa ma aka yi hakan, kawai garbati ya ce min kusan kullum sai an xo an tafi dake an dawo a katuwar mota.... Shi ma shegen dake tafiya dake a motar ya ci sa'a bamu hadu ba wllh" Ita dai Jiddah bata ce komai ba jikinta sai bari yake, ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana xukan hayakinsa yana murmushi ya rungumota kusa da shi, ta runtse ido xuciyarta na bugawa da sauri sauri, yace "Inji dai baki jin yunwa ko Amaryata?" Ta girgixa masa kai da sauri, ko kallonsa bata son yi kar ta saki ihun da take hadiyewa, ya wurgar da guntun taban hannunsa ya mike ya fara cire kayan jikinsa, Abuturrab ne ya fado mata, hawaye me xafi ya fara silalowa idonta, Bata san lkcn da ta fasa wani ihu a mugun tsorace ba ta rufe fuskarta da gwiwanta... Ya hade rai ya buga mata dundu a baya yace "Kee, ki kiyayeni fa, so kike ayi tunanin fyade xan maki bayan ke halaliya ta ce, dubu sha uku na biya jiya jiyan nan, har yanxu Babata bata san yanda aka yi da tinkiyarta ba, shine xaki kawo min iskanci, to idan xaki saki jiki ki saki, don muna nan da ke har sai an kira assalatu wllh...." Ta kallesa cikin dakiya amma muryarta na rawa tace "Fitsari xan yi" yyi murmushi yace "To ko ke fa, amaryata, ai gwara kawai ki saki jikin ki" Ya mike ya yace "Mu je in raka ki" Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace "Aa wllh sanyi nake ji" Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace "Mu je kiyi fitsarin" Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace "Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya" Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d'an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace "Tass xa ki shanye lemon nan" xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace "Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane" A wangale ya ga d'an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace "Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni" Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace "Daga ina suka dauke ki?" Tace "Can cikin gari" Ya girgixa kai yace "Yanxu ina xa ki?" Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace "Cikin gari xan je don Allah" Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace "To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace "Don Allah kana da waya?" Yace "Ehh" tace "Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah" ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace "Pick ur call" hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace "Hello" Hawaye ya silalo idonta tace "Ni ce" Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace "Ohk ina ji" Ta fashe da kuka sosai tace "Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka...." Abuturrab ya dago da sauri yace "Xuwa ina?" Cikin kuka tace "Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi" Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace "Kina ina yanxu?" Ta bi inda take da kallo tace "Mai adaidaitan yace min kano road ne" Abuturrab yace "Ba sa wayar" Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace "Ehh a dai dai wajen muke ma" bayan few seconds mai adaidaitan yace "Toh shkkn xan jira in sha Allah" Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace "Abba xan d'an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it's urgent" Abba yace "Alright sai ka dawo" Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din.....


07087865788✍🏻💖💖 *Jiddatul Khair* 💖💖





_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻





9.....

Abuturrab yayi parking yana bin wajen da kallo ya dau wayarsa yayi dialing number da suka kirasa da shi, yana fara ring mai adaidaitan dake hira da wani me d'an kiosk a wajen ya daga, Abuturrab yace "Ka duba wani bakar mota a wajen da kace" Mai adaidaitan ya mike yana dube duben wajen, can ya hango motar Abuturrab ya kalli Jiddah dake xaune cikin adaidaitan har sannan ta takure waje daya yace "Ga sa can ya iso" Dago kai tayi da sauri sannan ta sauka daga cikin adaidaitan, tare suka tsallaka titi da shi xuwa daya side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa ya mika masa yace "Nagode" Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace "Shiga" Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace "Bayan na tafi sai me ya faru?" A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe, ganin yanda take kuka ya kalleta yace "Ya maki wani abu ne?" Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d'an kalleta yace "Yanxu babu wanda kika sani nan cikin gari?" Ta girgixa masa kai tace "Ba kowa" ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace "Barka dai ranka shi dade..." Abuturrab yace "Ya aikin?" Mai gadi yace "Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?" Abuturrab ya d'an shafa kai yace "A'a, wani d'an alfarma nake nema gun ka" Cike da natsuwa yace "Toh ina saurarenka yallabai" Abuturrab yace "Erm... Mai dakinka na nan ai?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki wllh" Abuturrab ya kalli Jiddah yace "So nake don Allah ta d'an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da takura tunda daki daya ne ko?" Da sauri Mai gadin yace "Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai" Abuturrab yace "Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo" Mai gadin yayi murmushi yace "Baxa ayi hakan ba ranka shi dade" Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace "Sauka, sai da safe..." Yana fadin haka ya bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace "Mu je ciki to...." tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo, dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da sallah ta d'an ta6ata tace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab, bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace "Babu wani aikin da xa ayi?" Matar tayi murmushi tace "Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki" Jiddah bata ce mata komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace "Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki...." Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Aa xan taya ki" Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace "Maman Abdallah kun tashi lafiya" Ba tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace "Ba ita bace" Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da fara'arta, cike da ladabi tace "Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana" yana tafiya yace "Lafiya lau, Abdallah bai tashi ba?" Tace "Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu" yace "To a gaida min shi" Tace "Xai ji Dakta" Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali... Karfe takwas Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace "Tunda kinyi wanka mu shiga daga ciki mu gaisa da 'yan gidan in amso mana kumallon mu, ko" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Maman Abdallah ta goya d'anta tace "Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu" A hankali Jiddah ta mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da murmushi fuskarta tace "Bakuwa kika yi Shafa" Maman Abdallah ta washe baki tace "Ehh wllh Hajiya, bakuwa nayi da yammacin jiya" Cike da ladabi ta risina tace "Ina kwana Hajiya" Umma tace "Lafiya lau kun tashi lafiya?" Maman Abdallah tace "Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan" Umma tace "Suna ciki..." Jiddah na kallonta a hankali tace "Ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa.... ya sunanki?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Jiddah" jin footstep ta dago tana kallon direction din, Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace "Ahh me babban suna ce ashe" Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Maa sha Allah, sunan yayata gare ki, sannu da xuwa" Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace "Yar uwarki ce amma" Maman Abdallah ta sosa kai tace "Ehh kauyenmu daya" Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace "Tunda suna da bakuwa ki kara masu" Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace "Mun gode hajiya Allah ya kara girma" Umma tace "Ameen" Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo.... He looks so confused, sak tayi masa kama da mai awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace "Muna chatting kuma ka sauka" Abuturrab yace "Ehh i am driving now" Ahmad yace "To where?" Abuturrab yace "Aunty ta aikeni" Ahmad ya d'an ta6e baki yace "Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?" Abuturrab yace "Kai me ya dawo da kai during week day?" Ahmad yace "Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha Allah" Abuturrab yace "Ohk anjima xan shigo idan na dawo" Ahmad yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane, wani d'an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace "Abokina me ke faruwa a nan?" Saurayin yace "Wata amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama'a kuma na ta dannan shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kiyaye" Barin anguwar Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace "Kayi hakuri babu wani bayani na kawo maku yarinya..." Mai gadin ya katse sa da sauri yace "Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina.." Abuturrab ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace "Gashi ka rike wannan" Mai gadin ya girgixa kai yace "Aa kar mu yi haka da kai don Allah" Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan, Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login