Showing 267001 words to 270000 words out of 346625 words
Chapter 90 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
da su Aunty suka kwana idonta yayi bulu bulu ta kalli wayarta dake hannunta, sai kuma ta jefar da wayar gefen gado fuskarta daure, Safara'u ta dauka ganin me kiran wayar ita ma ta ajiye a gefe, Aunty ta kallesu tace "Wa ke kiran nata?" Safara'u ta kyabe baki tace "Shi yake kiranta, to uban me xata masa? Ki ita xata gasa masa amaryar" Aneesah ta matse kwallar idonta, Aunty tace "Je ki kiji kiran meye yake maki, tashi ki je" Aneesah dai bata ce komai ba, Safara'u tace "Tabbb!! Lallai ni naga abinda ban ta6a ji ba jiya, a cikin surkanka sbda baka daukesu da mutunci da kima ba? Muna gidan xai yi wannan ta6arar?" Ba dai wanda ya amsa mata, ta kalli Aunty tace "To idan mu ya maida mu banxa ke kuma fa? Yana fa sane kina gidan nan ba tafiya kika yi ba yayi abinda yayi, idan uwarsa ce ke gidan xai yi haka?" Aunty dai takaici, bakin ciki, da bacin rai duk ya baibayeta, yanda take ji iyakar haka Aneesahn ma xata ji, Aneesah ta sakar masu kuka tace "Ce min fa ku ka yi har xamansu ya kare ance baxai kusanceta ba, haka fa ku ka ce min, kuma duk kun ji abinda aka yi a gidan nan jiya, shkkn sai ya ji dadin min kallon gantalalliya kenan? Shkkn sai yaji dadin fara min gori kenan" Kuka sosai take cike da takaici, Aunty tace "Haka aka ce maki ya kusanceta? Ke baki san makircin mace bane, wllh wllh baxan yi kaffara ba babu abinda ya wakana tsakaninsu, an fa gaya min komai, to meye na daga hankali, ashe ma abu me sauki ne kusantar nata, tsabar makirci ne kawai irin na mata fa" Mikewa Aneesah tayi ta dau wayarta ta fita dakin ganin yana sake kiranta, sai da ta shiga dakinta ta dau hijab har kasa ta saka ta jawo hijab din ya kusa rufe rabin fuskarta sannan ta daga kiransa kafin tace komai yace "Ki sauko downstairs yanxu" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar, saukowa kasa tayi ta gansu xaune a parlon, bata yarda ta kalli inda Jiddah take ba, kamar yanda Jiddah ma ta ki kallon inda take, ta tsaya bayan kujera babu yabo babu fallasa tace "Good morning" yace "Morning, dama xan ce maki xan koma aiki, hope ba ki bukatar wani abu?" Aneesah ta d'an saci kallon Jiddah dake sanye da Hijab har kasa ta sunkuyar da kai, sai kuma tace "Toh fa!! aiki kuma captain? Har an gama cin amarcin kenan? Ni da na xata hutu xaka dauka" Bai bata amsa ba kuma bai kalleta ba, tayi murmushi tace "Toh shkkn Allah ya tsare hanya, amma baxa kayi breakfast ba?" Yace "Xan yi a jirgi" tana ci gaba da murmushi tace "Toh shkkn, in Allah ya yarda babu wata matsala har kaje ka dawo, hope ka gaya mata ta saki jikinta da ni, ni kam kai ma kasan bani da matsala, xa kuma mu xauna lafiya xan dauketa tamkar kanuwata... Babu wani damuwa" Sai a sannan Abuturrab ya daga kai ya kalli Aneesah, tayi murmushi irin tana assuring dinsa din nan kar ya ji komai, bai ce mata komai ba, sai tace "Amma baxa ka shiga ka gaisa da su Aunty ba kafin ka tafi? sun tashi fa" Yace "Xa mu yi hakan ta waya, Jiddah kuma da ita xan tafi..." Sosai gaban Aneesah ya fadi tana kallonsa don duk a tunaninta barin Jiddah xai yi tunda dai ba xama xai je yayi a waje daya ba, A hankali tace "Da ita kuma? Naga ai ba xama kake a gari daya ba" Yace "Ehh" yana fadin haka ya mike ya dau jakar kusa da shi yace "If there is anything sai ki kirani" yana kallon Jiddah yace "Tashi mu je" a hankali ta mike ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, Aneesah ta bi ta da wani irin kallon tsana, ya bi bayanta har suka fita parlon, da gudu ta koma sama taje sanar ma su Aunty ai da Jiddah xai tafi.... Karfe biyar Abuturrab ya shigo gidansa na Abuja bayan sun sauke jirgi a garin Abujan, Jiddah ta xauna parlon da babu abinda ya canxa daga yanda ta san shi months back, har a lkcn taki sakewa da Abuturrab har xuciyarta taji tsoronsa take, bayan wani lkci ta saci kallonsa suka hada ido don kallonta yake, dauke kanta tayi da sauri, yyi lowering voice dinsa yace "Since u are uncomfortable staying with me here, sai ki shiga daki ko?" Ko rufe baki bai yi ba ta mike ta wuce daki tana rike da handbag dinta ta rufe kofar, ya bi ta da kallo yayi murmushi a ransa yace "Xaki ji tsoro me dalili soon yarinya" Da yake sun ci abinci a garin lagos kwanciya kawai yayi kan 3 seater yana kallon movie da ake yi a Tv, shidda da yan mintuna aka danna bell din parlon ya mike ya isa kofar sanin wanene, ya bude kofar, Ahmad na murmushi ya shigo yace "Latest ango in town, irin wannan fresh din haka Captain... Uhnnn" Abuturrab ya shafa kansa yace "Xan dai yi fresh din" Xaunawa suka yi kan kujera Ahmad yace "Toh ina Jiddar? Kace min kuna tare" Abuturrab ya kalli hanyar bedroom kafin yace komai Ahmad yace "Ohh shigewa ciki kace tayi don na xo??" Abuturrab yace "Not at all, i think bacci take yi, she is been inside since" Ahmad yace "Better!! Hope ka dau shawaran da na baka?" Abuturrab yace "Wanne a ciki?" Ahmad ya hararesa, a hankali Abuturrab yace "I want to ask u Ahmad" Ahmad yace "I am all ears" Abuturrab ya d'an yi shiru sai kuma ya shafa beard dinsa alamar dai ya rasa ta inda xai fara tambayar, Ahmad yace "Akan me kake son min tambayar?" Abuturrab yace "Marital Bed" Dariya Ahmad yayi yace "Then we should chat..." a hankali Abuturrab yace "That will be better" Ahmad yace "Hope no intimate relationship took place between u and...." Abuturrab ya kallesa yace "I couldn't find the way" Wani dariya Ahmad ya fasa ya jinginar da kansa jikin kujera, Abuturrab ya hade rai yana kallonsa, Ahmad yace "We really need to chat about that then, so bak'in naka sun bar gidan ko suna nan har yanxu" Abuturrab yace "Suna nan" da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ohk haka xa ka xuba masu ido kenan, na gaya maka they have a mission to accomplish ka ki taking dina serious Captain, tun da can me ya sa basu xauna gidan naka ba gaba dayansu sai yanxu?" Abuturrab dai bai ce komai ba. Ana kiran magrib Abuturrab ya shiga dakin da Jiddah ke ciki ya sameta tana bacci, ya rasa me yasa ta dawo so silent, ya tasheta tayi sallah, sannan suka fita masallaci tare da Ahmad, bayan sun dawo masallacin Ahmad yace "Baxa mu je can gidana ku ci abinci ba" Abuturrab yace "Is ur wife around?" Ahmad yace "Yea tun da Jiddah ta koma gun Umma kawai na dawo da ita Abuja, baka yi mamakin me yasa na rage xuwa weekend kd ba" Abuturrab yace "Ohk ban sani ba" Daki Abuturrab ya shiga ya sa Jiddah ta shirya su tafi gidan Ahmad, hijab dinta kawai ta sa ta fito, ta gaida Ahmad tana sunkuyar da kanta ya amsa da murmushin sa, Ahmad hira kawai yake da Captain, amma da ta daga kai sai sun hada ido da Abuturrab dake kallonta, daga karshe ta koma can end din a hankali ta xauna har suka isa gidan. Sosai Ramlah tayi farin cikin ganin Jiddah a gidanta don Ahmad bai gaya mata suna xuwa ba, Jiddah ma taji dadin ganinta sosai. Abinci ta kawo masu nan parlon, Ahmad ya dibar masa shi da Abuturrab, ita dai Jiddah na xaune kan kujera idonta na kan tv dake aiki, Ramlah ta xuba masu a plate ita da Jiddah tana kallonta da murmushi fuskarta tace "Sauko Aunty Jiddah" Jiddah dai tayi murmushin karfin hali amma bata sauko ba, Ramlah tace "To tashi mu shiga ciki" Ba musu Jiddah ta mike ta bi ta suka wuce bedroom dinta, Ahmad dake kallon Abuturrab da ya bi Jiddah da kallo yace "Uhnn wannan kallo haka Captain?" Abuturrab ya shafa kansa ya ci gaba da cin abincin gabansu... Ba laifi Jiddah ta ci abincin don a lagos ta ki sakewa ta ci sbda Abuturrab da ya sa ta gaba, hira suka dinga yi da Ramlah har aka yi isha, karfe takwas da rabi Ahmad ya shigo dakin da sallama yana kallon Jiddah yace "Captain na jiran ki Jiddah" Marairaice masa tayi tace "Ya Ahmad don Allah kace masa ya bar ni in kwana a nan" Tana fadin haka sai hawaye ya cika idonta, shi dai Ahmad dariya ta basa, Jiddah ta kalli Ramlah tace "Don Allah ki masa magana ya bar ni a gidan nan" Ramlah tayi dariya tace "Aa wnn sai dai Dr yayi masa magana" Ahmad na kallon Jiddah yace "Ki je ki gaya masa xai bar ki ma sani" Gaba daya a tsorace take, Ramlah dai sai kallonta take, Ahmad yace "Yea kije ki gaya masa xai bar ki" A sanyaye ta mike ta fita, Ramlah ta wara ido tace "Toh ko tsoron Yayan take?" Ahmad yayi murmushi ya xauna gefen gado, Jiddah na fitowa parlor suka hada ido da Captain dake xaune, karasawa tayi kanta a kasa ta durkusa d'an nesa da shi a hankali tace "Dama don Allah ka bar ni in kwana a nan plsss" Kallonta ya dinga yi, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, lkci daya hawaye har ya kawo idonta, yace "Tsorona kike ji Jiddah?" Girgixa masa kai tayi da sauri, yace "Toh shkkn, sai da safe" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, sai kuma jikinta yayi sanyi, amma dai wata xuciyar tace mata gwara haka, da dai abinda Allah ya nuna mata jiya gwara kawai ta kwana gidan Ramlah. Washegari Abuturrab yayi piloting xuwa Kano leaving Jiddah behind in Abuja shi kansa ya ga hakan ya fi tunda ya lura bata son hawa jirgi, a kwanaki hudun nan duk abinda Ramlah ke amfani da shi na mata wanda Umma ta hana Jiddah haka ta dinga bata, to tunda ita bata san meye shi ba haka xata amsa ta sha, all this while kuma Aunty da su Safara'u na gidan Aneesah suna jiran dawowar Abuturrab da Jiddah gidan, Ranan Thursday Ramlah na parlor tare da Jiddah aka danna bell, mikewa Ramlah tayi ta nufi kofar ta bude tana tambayar waye, Abuturrab ta gani tsaye bakin kofar, ta washe baki tace "Sannu da xuwa yaya" sai kuma ta basa hanya ya shigo parlon, sai da gaban Jiddah ya fadi da ta hada ido da shi, ya karaso ya xauna parlon yana kallonta yace "Tashi ki dauko kayanki" Ramlah dai na tsaye gefe sai murmushi take, Jiddah taki motsawa a inda take, Ramlah tace "Mu je ai kayan a hade suke" Daga haka ta nufi dakin da jakar kayan Jiddah wanda Ahmad ya taho mata da shi yake, mikewa Jiddah tayi ta bi bayan Ramlah tana tafiya kamar xata yi kuka ya bi ta da kallo, Ramlah ta rufe kofar bayan Jiddah ta shigo tana kallonta tace "Me yasa kike haka Jiddah yana maki magana kin yi shiru" Jiddah ta fashe da kuka ta xauna gefen gado, Ramlah ta xauna kusa da ita da mamaki tace "Gaya min meye damuwarki?" Cikin kuka tace "Wallahi ni tsoronsa nake ji" Sake baki tayi tana kallonta, can tace "Tsoronsa kuma Jiddah? To saboda me" Jiddah tayi shiru tana share idonta xuciyarta na bugawa, Ramlah tayi shiru sai kuma tayi murmushi tace "Kin ta6a jin inda mata ke tsoron mijinta? Look Jiddah ki ajiye duk wani kuruciya aside babu wannan a aure sannan kishiya gareki, kishiyar kuma ba mai tsoron Allah ba, ko so kike ta kwace maki miji?" Kallonta Jiddah ta dinga yi, Ramlah tace "Wllh idan kina masa haka fita harkanki kawai xai yi ya kama kishiyarki tunda ita ai bata tsoronsa, dubi ranan fa kiri kiri kika ki binsa sai shi kadai yayi wucewarsa, so kike ya daina kulaki ya barki da tsoronsa da kike?" A hankali Jiddah ta girgixa mata kai, Ramlah tace "To kar ki sake yarda ki sa ma ranki kina tsoron mijin ki, kuma kar ki xama raguwar mace... It's something that happens just once in lifetime, you get me" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Ramlah ta mike ta dauko jakarta ta mika mata tace "Tashi ki je yana jiranki, sai da safe, xan kira wayarsa gobe sai ya baki mu yi magana" Jiddah ta goge idonta ta amshi jakarta.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Har suka isa gida Abuturrab bai ce ma Jiddah komai ba, ita ma dama ko hada ido bata yarda ta yi da shi ba, ya kunna switch din parlon sannan ya kulle gidan ya nufi daki, a hankali ta xauna saman kujera ta ajiye jakarta a kusa da ita, tana ta xaune parlon ita kadai har karfe tara, mikewa tayi daga karshe ta tafi saman 3 seater ta kwanta, har ta fara bacci ta ji ana jan hancinta, ta bude ido da sauri, ganinsa durkushe gabanta ta mike xaune, yace "Tashi ki je ki kwanta" Ta make kafada tace "Ni nafi son kwanciya kan kujera" Duk da dariyan da ta basa sai ya dake yace "Ni ke kwanciya kan kujeran ai shi yasa na tashe ki, go inside the room now" Tayi shiru sai kuma ta mike daga kan kujeran ta nufi dakin tana waigensa, kwanciya ta ga yayi kan kujeran ya lumshe ido, ta shige daya daga 3 room din tana kallon kofar ganin babu makulli a makale, a hankali ta lallabo ta fito ta shiga wani dakin nan ma babu makulli, wani dakin ta shiga shi ma dai door din ba makulli, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka ta fito parlor ta tsaya tana kallonsa tace "Ban ga key a doors din ba" Bude ido yayi ya kalleta yace "Me xa kiyi da key?" A hankali tace "Ni nafi son in kulle kofa idan xan yi bacci" Yace "Toh haka doors din suka xo babu key" daga haka ya kulle idonsa, tana ta tsaye tana kallonsa kafin ta juya ta koma dakin ya d'an bude ido ganin ta tafi yayi murmushi, ta fi minti goma xaune gefen gado daga karshe ta kwanta ta takure waje daya tunda dama bacci take ji, babu bata lkci baccin ya dauketa, can cikin bacci ta ji ta a jikinsa, ya rufe bakinsa da hannunsa kafin ta kwala ihun da tayi niyya, yayi lowering voice dinsa yace "Tell me why u are afraid of me?" Shessheka ta fara yi masa, ya cire hannunsa a bakinta ya juyo da ita a hankali yace "Tell me plss, ko na ta6a yi maki wani abu da baki so ne?" Cikin rawar murya tace "Ehh" yace "Toh me na maki?" Tayi shiru, yace "Gaya min ina jin ki" A hankali tace "Kawai dai ni bana son kana ta6a ni" yace "Toh wa kike son in ta6a?" Nan ma tayi shiru, yace "Aneesah?" Daga kai tayi ta kallesa, sai kuma ta turo baki xata juya masa ba, ya ki barin tayi haka yace "Yanxu wajenta kike son in koma" a takaice tace "Toh ai dama a wajenta kake" Yace "Aa dake na fara xama ai kafin in xauna da ita" tace "Da ka zauna da ni ai ka ce ni ba matarka bace" Murmushi yayi, murya can kasa yace "Wasa nake maki a lkcn ai" Tace "Da gaske kake, tunda har ka rubuta ka bani" shiru yayi bai sake cewa komai ba, ta rufe idonta tana jin kamshinsa da ya cikata, a hankali ya kai bakinsa kunnenta yace "Amma duk abinda kike so ai ina maki, baki rasa komai a lkcn ba sai abinda nake maki baki so yanxu" Ya fadi hakan yana sake rungumeta closely, ta marairaice tace "Toh bana son hakan, kawai mu xauna yanda muka xauna wancan lokacin ya fi" Ya girgixa kai underneath his breathe yace "Baxan iya ba, wancan lokacin ma...." sai kuma yayi shiru, ta kallesa tace "Me?" Yace "Ba komai, yanxu dai kince baki son in dinga ta6a ki, gaya min wanda xan dinga ta6awa? Wajen Aneesah kike son in dinga xuwa? Kinga ita bata min haka" Ta ki cewa komai ta wani hade rai, yace "Tell me plss" a takaice tace "Toh ba sai ka je ba" Saketa yayi a hankali yace "Ohk fine" daga haka ya juya mata baya, kallonsa ta dinga yi sai kuma ta cusa kanta cikin pillow ta fara kuka a hankali, duk yana jin ta, bayan few minutes ya jawota jikinsa yayi kasa da murya yace "ke fa kika ce baki son in dinga ta6abki" Cikin kuka tace "Toh ba kai ne sai ka dinga bani tsoro ba" yace "Gaya min ranan da na baki tsoro" a hankali tace "Ranan a can gida mana" Yayi shiru, sai kuma yace "Toh baxan sake irin wannan da ke baki tsoro ba, amma kuma idan kina min gardama sai in koma gun Aneesah don ita bata min...." ta kallesa tace "Gardaman me?" Yace "Xan nuna maki yanxu, amma ki sani kina gardaman wajenta xan koma da gaske tunda ni ina so" Ita dai tayi shiru gabanta na faduwa sosai, ya kashe wutan dakin tana kokarin guduwa ya rikota gam ya kai bakinsa kunnenta yace "Pls" very light love affair ya shiga yi mata wanda baxai tsoratata ba sai dai ma ya dimautar da ita, sosai yayi mamakin yanda tayi masa lamo idonta a rufe babu gardama, he don't know if she's relishing what he is doing to her or she just doesn't want