Showing 258001 words to 261000 words out of 346625 words
Chapter 87 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
all baka daukeni matsayin uwa ba, amma kuma babu yanda na iya hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, Idan ma ni baxa kayi shawara da ni ba kanwata na da ranta Aliyu kuma baxata ta6a cutarka ba ko bayan babu ni" Abuturrab da ya sunkuyar da kansa a hankali yace "Kuyi hakuri Ummi, in sha Allah xan gyara, nagode sosai... Allah ya kara girma" Ummi na kallon agogon dake nuna karfe takwas da rabi na dare tace "Toh a gaida Aneesah" yace "In sha Allah, sai da safe Ummi" daga haka ya mike ya fita parlonta, sai da ya tafi yayi ma Hajja sai da safe sannan ya bar gidan. Har wajen karfe sha daya Aneesah bata shigo bangarensa ba duk da ta ji shigowarsa gidan, tana can dakin da ya maidata takaici na neman hallaka ta, tuni ta sa aka kafa mata furnitures dinta tana ta tausan kanta dai, sosai dakin yayi kyau don shima din yana da girma enough, wanda ya rufe ma Jiddah ne kawai ya fi su girma gaba daya, Abuturrab ya fito bangarensa sanye da Pajamas dinsa ya nufi dakin nata, tana xaune tsakiyar gado sanye da wani kayan bacci shara shara tana chatting da wayarta, yana shigowa ta daure fuska kamar ta ga enemy dinta, yayi mata kallo daya ya xauna gefen gadon yace "Baki ji shigowata bane Aneesah?" A takaice babu yabo babu fallasa tace "Ban ji ba" Tana fadin hakan kuma sai ta tuna warning dinsu Aunty da Safara'u, sai kuma ta sake fuska tace "Da yake yanxu na cire air piece ban ji ba" shi dai yana lura da ita, kawai ya d'an yi murmushi yana bin dakin nata da kallo, sai kuma ya kalleta yace "Make me a cup of tea pls" Tace "Babu gas, nima har yanxu ban ci abincin ba" kallonta kawai yake don sarai yasan akwai gas da shi kuma Jiddah tayi amfani jiya, yace "Ohk, ina son maki wata tambaya" Tace "Ina ji" Yace "Gidan nan da gidana da Abuja which will u prefer staying?" Ta kallesa tace "Kamar yaya???" Yace "Ki xabi inda kika fi son xama a ciki" Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma tace "Ban gane in xabi wanda na fi so ba" Yace "Ohk, ko da yake ba ma ke ya kamata in fara tambaya ba, uwar gidan ya kamata a fara tambaya ta xaba, duk wanda ta bar maki kuma sai ki xauna a ciki" Aneesah ta sauka daga saman gadon da sauri tana huci tace "Kana nufin raba mana gida xa kayi?" Yace "Eh" Wani shewa tayi tana tafe hannu tace "Toh wllh baxai yiwu ba, duk mu taru mu xauna a nan din, babu xancen raba gida, duk girman gidan nan kace xaka raba mana gida, to wllh baxai yiwu ba, ta xauna nan nima in xauna nan, ai ba kanta xan xauna ba ita ma ba kaina xata xauna ba, wato ka raba mana gida don kuji dadin cutata ku dinga shiga hakkina to ban amince yau ba ban amince gobe ba...." Abuturrab kallonta ya dinga yi da mamaki cause he thought she will welcome the idea na raba masu gida da Jiddah, sai da ya jira ta gama tijaranta sannan ya mike yace "Baki isa ki gaya min abinda xanyi a gidana ba, idan na kai Jiddah Abuja sai ki bi ta can din ku xauna in gani" Daga haka ya fice mata daga daki ya kulle kofar, ta fashe da kuka tace "Wllh duk a gidan nan xa mu xauna duk abinda xai faru ya faru, babu xancen raba mana gida..." Sai kuma ta dau wayarta da sauri ta shiga kiran Aunty, Aunty dake kwance hotel room, Abba kuma yana bandaki ta daga kiran Aneesah tace "Lafiya??" Aneesah ta fashe da kuka tace "Kin ji wai raba mana gida xai yi Aunty" Aunty ta mike xaune da wani expression tace "Ya raba maku gida? A saboda me xai raba maku gida?? Shi har ya isa ya raba maku gida" Aneesah tace "Wlh he just finished telling me now and he is very serious about it...." Aunty tayi er dariya tace "Shine kike kuka kamar wata wawuya Aneesah, to sha kuruminki, battun dai gani ga ubansa kuma dama sai yanda nace, yi shiru ki saurari ikon Allah, gida daya kamar kun xauna, babu xancen raba gida" Abba na fitowa bandaki Aunty ta katse wayarta.
*pls wa enda na tura ma doc din Jiddatul Khair banyi saving digit dinsu ba, so I can't add dem to any group, pls su sake min magana so that i can do so, thank you*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari,_
Location Lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*Tested and trusted*
*if interested contact*
👇🏻
08052466875 Via WhatsApp
Ranan Friday as usual Abuturrab na shigowa garin kaduna da yamma ya nufi gidansu direct ta dalilin kiran da Abbansa ya masa jiya, babu kowa parlon ya fara shiga bangaren Abban nasa ganin motarsa da yayi a parking space, waya ya samesa yana yi, ya nemi waje ya xauna ya jira har ya gama sannan ya daga kai yace "Ina yini Abba" Abba yace "Sae yau ka shigo garin?" Yace "Ehh" Abba yace "Good, na samu labarin abinda kake son aikatawa na raba ma matanka gida isn't it?" Abuturrab ya daga kai yana kallonsa bai ce komai ba, Abba yace "Ko ba haka bane?" Abuturrab yace "Haka ne" Abba na kallonsa da kyau yace "Saboda haka kaga nima nayi ko??" Shiru Abuturrab yayi, Abba yace "At the first place wa ya baka wannan gurguwar shawaran?" Abuturrab yace "Aa kawai naga hakan xai fi xama alkhairi ne a tunanina" Abba yace "Toh ba me yiwuwa bane hakan, it's either ka ajiye su a Abuja gaba daya, ko Kaduna, amma u dare not separate der home, ba haka ka taso ka ga nayi a gidana ba, ni nasan wannan ba shawaran kowa bane banda Hauwa da Er uwarta don sune basu son xaman lafiya, ba kuma sa son wani ya xauna lafiya, to ni da nake mahaifinka nace ka hade matanka duk gida daya, final say din kenan, kuma in har xaka ci gaba a haka baka da decision din kanka sae wanda wasu can suka xartar maka to kuwa baxa ka dinga ganin dai dai lamarin ka ba, wannan a rubuce ma yake, tashi ka bani waje" Abuturrab ya kasa cewa komai ya kuma kasa tashi, bayan few seconds ya dago a hankali ya ga irin kallon da Abban nasa ke jefa masa, a hankali yace "Toh shkkn Abba, in sha Allah baxa a raba su ba" Abba yace "Tashi ka ban waje nace Malam...." Mikewa yayi ya fita parlon, ya tafi parlon Umminsa ya xauna, Ummi na fitowa daki ta gansa xaune, da mamaki tace "A'a, yaushe ka shigo?" Yace "Ban jima ba, ina yini" Ummi tace "Lafiya lau, ya aikin" yace "Alhmdlh" karasowa tayi ta xauna tace "What's wrong?" Yayi kasa da kai kamar baxai ce komai ba, sai kuma dai yace "Jiya Abba ya kirani ina wajen aiki.... Ummi ke kika masa magana a kan raba gidan da xa ayi?" Ummi tayi shiru da mamaki can ta girgixa kai tace "A ina na gansa xan gaya masa, jiya shi ma ya dawo ai... Hajja kuma na can gidan Ramlah balle ince ko ita ta gaya masa, balle ma bata san da xancen ba wllh" Abuturrab yace "Ce min yayi kar in kuskura in raba masu gida" Ummi tayi shiru tana kallonsa, can tace "Ikon Allah, ya fada maka dalilin nasa na cewa kar ka raba masu gidan?" Abuturrab yace "Kawai umarni ya bani without any reason" Ummi tace "Toh Allah ya sa hakan yafi xama alkhairi, bana son kayi disrespecting mahaifinka ka ki yin abinda yace, adhere to his instructions nd obey, sai kaga komai naka ya tafi dai dai da amincewan Allah, su kuma Allah ya hade kansu ya basu xaman lafiya, balle Jiddah naga bata da fitina ko kadan, baxa ta biye matarka ba idan Allah ya yrda" Abuturrab dai kansa na kasa, jin Ummi tayi shiru ya daga kai yace "Ummi goben xata koma can gidan?" Ummi tace "Xan kira Ramlan in ji, rabonmu da waya da ita tun jiya, bari ma dai in kirata yanxu" tashi tayi ta tafi daki ta dauko wayarta ta dawo ta xauna sannan ta shiga kiran Umma, Umma na dagawa bayan sun gaisa Ummi tace "Ramlah ya batun tarewan Jiddah gobe?" Umma tace "Ya raba gidan ne Yaya?" Ummi tace "Abbansa ya hanasa yin hakan...." Umma tace "Atoh kuma ae ba a so Jiddah ta tare ba kenan, ana nufin ta tare gida daya matsiyaciyar yarinyar nan warce bamu san xuciyarta ba? Gaskiya da sake yaya" Ummi tace "So kike ya tsallake umarnin mahaifinsa kenan ko me Ramlah?" Umma tace "Atoh Allah na tuba shi yana da wani umarnin da yake son abi bayan bai bi na tasa mahaifiyar ba, kiyi hakuri fa yaya ba rashin kunya nake maki ba, amma ke tunaninki bai baki cewar gun matarsa ya tafi kwana biyar din nan da yayi baya gida ba, to kuma wani umarni nasa yake son abi ga na mahaifiyarsa da yayi fatali da shi" Ummi tace "Kece wannan ya xama matsalarki ba ni ba, don ko kadan ban kawo a kai ba balle ya dameni, abinda na sani kawai gobe da safe aje ma Jiddah da furnitures dinta dakinta, da yamma kuma ta shirya mijinta ya je ya dauketa, that's all.... Sai anjima" daga haka ta katse wayarta, Abuturrab dai kansa na sunkuye, bayan few seconds ya dago yace "Nagode Ummi, Allah ya kara girma" Ummi tace "Ameen, amma kana ji na?" Yace "Ina ji Ummi" Tace "Xuwa yaushe xaka hada mata lefenta kamar yanda kayi ma daya matarka?" Ya sauke kansa yace "Sae dai in tura ma Umma kudi ta hada lefen" Ummi tace "Sae ka tura mata kamar nawa?" A hankali yace "1.5 yayi?" Ummi tace "Bai yi ba" Yace "Toh xan tura mata 2M" Ummi tace "Better" yace "I will send her in sha Allah, ana bukatan wani abun daban that i can assist with na kayan daki?" Ummi tace "Aa bama bukatar komai tunda ba maula muke ba, lefen dai da ya xame maka dole shi xaka yi, sauran duk dolenmu ne mu ya kamata mu yi mata don gudun gori wataran" Ya d'an yi murmushi ya mike yace "Xan karasa gida Ummi, daga kano nake yanxu" Ummi tace "Toh sae anjima" daga haka ya fita parlonta feeling much relieved. Kusan rabi da quarter din kudin lafiyayyun furnitures da aka yi ma Jiddah Ahmad ne ya bada kudin ba tare da yayi shawara da kowa ba, Umma ta cika sauran kudin, sannan ta hada mata lafiyayyun turarurrukan wuta da kwalabensu, Humra da Kulaccam... kai kace Maimoon xata kai gidan Miji sbda qualities din abubuwan da ta siya, Ummi kuma ta siyi komai na kitchen wares da ya mace xata bukata masu tsadan gaske, basu raga jiddah da komai ba na gatan da ake ma 'ya mace idan xa a kai ta gidan miji.... Aneesah na kwance dakinta da safe tana ta baccin da ta saba, wajajen karfe tara ta dinga jin kamar ana haurowa sama da kaya, hayaniyar ya sa ta mikewa ta saka Hijab dinta ta fito daga dakinta da sauri, tsaye tayi corridor tana xare ido, sai da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin ubansun kayan gadon da ake shigowa da su dakin da Abuturrab ya kulle madadin na Jiddah, Masu haurowa da kayan suka gaisheta, maimakon ta amsa masu cikin daga murya tace "Da izinin ubanwa xa ku dinga shigo ma mutane da kaya babu notice cikin gida? Uban wa ya aiko ku?" Tsayawa duk suka yi suna kallonta, cikin tsawa tace "Ba magana nake maku ba kun tsaya min kamar kurame? Daga ina wannan rubabbun kayan haka?" Daya daga matasan masu shigo da kayan yace "Easy Hajiya, babu wanda dai xai shigo wannan gida babu izini, mai gidan ma na kasa muke shigowa da kayan" Ta nufesa tana huci tace "Ni xaka yi ma rashin kunya ka gaya min maganar banxa?? Ni xaka daga ma murya?" Yace "Aa ba ni na kar xoman ba Hajiya, nima rataya aka bani..." Daga haka ya ci gaba da shigar da kayan da yake cikin empty room din, sai a sannan Aneesah ta lura da cewar an fitar da former furnitures din ciki babu komai a dakin, downstairs ta nufa kamar mahaukaciya, tana sauka taga Abuturrab xaune parlor, kallo daya yayi mata ya dauke kai, cikin rawar murya ta nufesa tace "Amma ai ina da hakkin a sanar da ni xa a shigo min gida ayi wani abu Captain, ba wai in ga katti a sama suna kokuwa da wasu tsinannun kayan gado can ba" Ya kalleta yace "Kina baccin asaran xa a sanar maki xa a kawo kaya, na xata har su gama abinda ya kawosu ma baxa ki tashi ba don lokacin tashin ki bai yi ba" Xata yi magana ya mike ya dakatar da ita fuska daure yace "Look Aneesah, bana son ki sa min ciwon kai da safen nan, gidanki ne nan din da xan sanar maki xa a kawo kaya? Ko kuma a kanki aka je xa a ajiye kayan? Do not provoke me Aneesah!!! Naga alamar ke baki son xaman lafiya a rayuwarki" Yana fadin haka ya koma balcony ya xauna ya bar mata parlon, wasu hawaye masu xafi suka shiga sauka idonta tana jin xuciyarta kamar xai fashe don bakin ciki, sai taji tsaf xata iya cinna ma gidan ashana duk ya kone da dai wannan kayan da ake shigowa da su, goge fuskarta tayi ta koma sama da sauri ta shige dakinta ta kulle ta dau wayarta tayi dialing number Aunty, bayan ta daga ta rushe mata da matsanancin kuka ta xauna a kasan dakin... Abuturrab na saukowa downstairs xai je masallaci yin Sallan azahar, har lkcn kuma masu aikin dake dakin Jiddah basu gama ba amma sun kusa, don ma su kusan shidda ne, yana stairs din karshe aka bude kofar parlon, kallonsu ya dinga yi har suka shigo, Aunty ce da Safara'u da Falmata, ya karasa shiga cikin parlon, Aunty ko kallonsa bata yi ba xata wuce sama, calmly yace "Sannu da xuwa, ina yini" kamar jiransa take dama, ta nufesa fuska a murtuke tace "Pardon??? Ka sha giyan wake ne kake gaisheni Aliyu? Or are u stupid? Ni xaka kalla kace ma sannu da xuwa?" Kallonta kawai yake, tayi wani kwafa ta nufi stairs kamar xata tashi sama, bai ko kalli su Safara'u ba ya fice daga parlon, Safara'u tayi wani murmushi ta bi bayan Aunty, Falmata ta rike ha6a tana biye da ita a baya tace "Ji fa tafiyarsa yayi bai gaishemu ba Aunty, dama d'an iska ne mijin Aneesan nan? In ni baxai gaisheni ba a matsayina na yayar Aneesah ke da kike matsayin kanwar uwarta sai ya ki gaisheki?" Safara'u ta juya ta kalleta tace "Meye abun damuwa Falmata, ai mutumin nan da kike ganin karshen d'an rainin wayo ne, ke dai mu je kawai xai shigo hannu ai, banda ma Aneesar da ta makale masa uban waye shi da xai min wnn walakanci da kimata da martabata" kwafa tayi ita ma, a haka suka haura sama tana ci gaba da bambaminta. Karfe hudu da yan mintuna motoci biyu suka shigo compound din gidan, Maimoon ce ta bude gaban mota ta sauka, Nafisah da Siyama da Safiyya, sai kanwar Yousuf Salima duk suka sauka bayan motar, Umma ce ta sauka daga cikin daya motar tare da mahaifiyar Yousuf Hajiya Rukayya, da wata kawarsu Hajiya Fatima, Su Maimoon suka bude booth din motocin suka dinga shiga da well packaged kayan turarrukan cikin gidan, da wasu kayan suna ajiyewa a main parlor, Umma na shigowa parlon da frnds dinta tace "Toh meye amfanin ajiyesu a nan, ba makullin na wajenku ba ku kai mun su can sama mana" Xaunawa su Umma suka yi a parlor har sai da su Maimoon suka gama haurawa da kayan sama xuwa dakin da aka jera ma Jiddah furnitures, Maimoon sai murmushi take don ba karamin haduwa dakin yayi ba kamar dakin gimbiya, Duk wannan abun Aneesah da falmata na kitchen suna girka indomie, su Aunty kuma ana can sama dakin Aneesah tare da Safara'u, tun da Aneesah ta leko taga su Maimoon ne ke shigo da kaya, wanda lkci daya kamshi ya gauraye parlon ta koma kitchen din da sauri xuciyarta na bugawa, takaici da bakin ciki kamar ya kar ta, Falmata dai sai cewa take "Ma ga ta yanda xa ayi xaman dai" kasa daurewa Aneesah tayi daga karshe jin ana ta shigowa da kaya anki gamawa, ta bar yayarta ta fito parlon tana tafiya cike da kasaita, ido hudu tayi da su Umma dake xaxxaune kan kujera suna hira, ta daure fuska ta dauke kai tayi wucewarta sama without greeting any of them, Hajiya Fatima da ta bi ta da kallon mamaki tace "Kar dai wannan fitsararriyar ce matar gidan?" Umma tayi wani murmushi tana girgixa kafa, sai kawai ta mike tace "Ku mu tafi mu yi abinda ya kawo mu yamma na yi" Tashi suka yi xuwa sama gaba dayansu... sai kusan karfe shidda da rabi suka gama jera turarrukan gaban madubi suka shimfida wani ubansun carpet a tsakiyar dakin, Maimoon ta shimfida tsadadden bedsheet saman gadon sannan aka cika ma dakin turaren wuta a burner aka sauke curtains, daki ya dawo sak na sabuwar amarya, kafin a kira sallah suka fito dakin bayan Umma kashe burner din, ta kulle dakin da makulli ta saka a handbag dinta, har lkcn Safara'u da Aunty suna makale daki babu wanda yasan suna gidan, su Umma na kokarin shiga motarsu Abuturrab ya shigo gidan da motarsa, can gefe ya tsayar da motar ya sauka ya karaso don gaida su Umma, kawayenta ne kawai suka amsa,