Showing 18001 words to 21000 words out of 346625 words
Chapter 7 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
kallo, ganinsu kadai taji xuciyarta ya fara tashi ta mayar da su da sauri ta cusa a ghana must go, duk ciwon da xata yi bata shan ko d'an paracetamol da Abbanta ke siyo mata lkcn da yake da rai, Hansai kuma ko kasheta ciwo xai yi bata ta6a cewa ta sha magani, muryar Bibalo ta ji tana kiran Uwarta tun daga bakin Zaure hakan yasa ta boye goran ruwan da ta sha ta rage, snn ta kwanta ta rufe idonta. Washegari da asuba jiddah ta kasa tashi kamar yanda ta saba, duk karfe biyar dama take tashi ta fita ta debo ruwa a borehole ta cika jarkunan tsakar gidan da ma bokiti, ganin gari ya fara haske Hansai ta leko dakin tace "Yau naga walakanci, Jiddah kece kwance har yanxu baki fito ba, uban wa xai debo ruwan yau? Bibalo me ciwon kirji ko ni xan fita debo ruwan?" Bibalo dake kwance tana bacci ta gyara kwanciyarta hade da rufe har fuskarta da xanin gadonsu, Jiddah ta dago da kyar muryata na rawa tace "Baabarmu kaina ke min ciwo sosai, idan na tashi juwa nake gani" Hansai tace "To a rayuwar nan yanxu waye baya fama da ciwon kai, ko digon ruwan alwala fa babu a gidan nan, ni kike son in fita in debo ko Bibalo da ba cikakkiyar lafiya gareta ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai tace "Ai ko daurewa xa ki yi ki mike ki debo ko bokiti uku ne, gida idan babu ruwa ai ba magana" Daga haka ta juya ta fita tana cewa "Idan ma xaki rufa ka kanki asiri ga bishiyar gwanda da mangwara can ki tsinko ganyayyekin su ki hura icce ki dafa ki sha kiyi wanka don sile na baxanyi amfani da shi wajen siyo maki magani ba" Da kyar jiddah ta mike tana dafa bango ta fita, ta dau bokiti, d'an makotansu ne ya taimaka ya kawo mata ruwan har kai uku gidan, ta dawo da kyar ko tafiyan bata iyawa ta shige daki ta kwanta ko ina na jikinta na mata ciwo... Har karfe goma na safe tana kwance, Hansai ta shigo dakin cike da masifa sosai tace "Ke ni fa babu ruwana ki tashi kiyi ta kanki ki tsinko abinda nace ki dafa uban waye xaki daura ma wahala bayan na ciyar da ke da nake yi" Jiddah ta mike ko ina na jikinta na rawa sbda sanyi, tace "Xan yi" tana magana ta jawo ghana must go dinta ta fiddo kudin jiya ta mika ma Hansai tace "Jiya wani ya kawo wai a baki" Hansai ta xaro ido tana kallon kudin ta karba tace "wani kuma? A ina kika gansa?" Tace "Aikawa yayi in xo, ina xuwa yace in baki" Hansai ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace "Amma gaskiya isuhu ya tare mana abubuwa da yawa a duniyar nan sanda yake raye, to da ya baki sai yace me??" Jiddah ta koma ta kwanta tana fidda numfashi da kyar tace "Cewa yyi in baki kawai" Shiru Hansai tayi tana kirga kudin har ta gama taga dubu talatin cif, ta kalli Jiddah da sauri tace "Ko dai mutumin da ya ta6a baki kwanaki ki kawo min kada mu fito sana'a?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh don girman Allah duk ranan da ya sake dawowa kice masa ya shigo in masa godiya" Jiddah bata iya ta bata amsa ba, Hansai ta mike murna fal cikinta tana murmushi ta nufi kofa tana cewa "In dai haka ne duk wani nawa amma banda Bibalo ya mutu a duniyar nan mana, daga mutuwa sai billowan alkhairi ta ko ina? Ashe dama akwai sauran mutanen kirki a duniya ban sani ba" Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta.
Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa, bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne, wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi Aunty" ta hade rai tace "Shine ni baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata, Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace "Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune, Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye, kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan, Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai maki sauki ba?" hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da xuwa Alhaji.... Ae da ta fito maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare" Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?" Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai" Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace "Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida, Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?" Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace "Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba" kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama da abincin tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba, girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka" Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen, suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace "Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?" Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan, he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a hayi?