Showing 234001 words to 237000 words out of 346625 words

Chapter 79 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ya fice daga dakin, Abuturrab ya dinga kallon kofar sae kuma ya dafe kansa ya lumshe ido... Washegari da safe Abuturrab ya gama shiryawa with so many restless thought in mind, he wish this is all but a dream, ji yake xuciyarsa is getting weaker day by day and he really need to go to the hospital, Amma kuma idan ba yanayinsa ka duba da kyau ba baxa kace ba shi da lafiya ba, sbda taurin halin da yake yi, ya kalli agogo dake nuna karfe tara snn ya kalli Aneesah dake baje saman gado tana ta baccinta, buga gadon yyi gently amma ko motsawa bata yi ba, ya tafi daya side din ya janye pillow din da take kwance kai a hankali, bude ido tayi sai kuma ta mike xaune da sauri tace "Haba Captain kai komai naka baka yin sa romantically or in a romantic manner? yanxu haka ake tashin mutum fisabilillahi?" Speaking calmly yace "Ina makullin motata?" Ta dauke kai hade da jan tsaki kasa kasa, sai kuma tace "Saboda makullin mota xaka min irin wnn tashin walakanci?" Yace "Kinyi sallah ne da xa a maki tashin da ya kamata? Kullum sai karfe goma bbu tsoron Allah xaki shiga bathroom kiyi alwala ki fito ki shimfida darduma kice xa ki yi sallah, who does that Aneesah?? Not even a 10 year old child" a fusace tace "Toh a je a banyi sallahn ba sae me? Ae ba kai ake ma sallan ba naga, balle ma ni nasan nayi sallata, kuma wllh ba laifinka bane nice na fita tsakar dare naje pharmacy na samo maka magani ka sha har ka samu karfi da bakin yi min walakancin da baka min ba tunda ka dawo kasar, for the pass 2 days da baka da lafiya waye ya ji kanmu, sae yau don ka samu kanka?" A hankali yace "Bani makullin motata malama" Tace "Ai kana ganinsa gaban madubi" Tafiya yyi gun mirror din ya dauka ya fice daga dakin feeling so irritated at her. Ramlah ce ta bude kofar parlon ganinsa ta koma gefe da murmushi fuskarta tace "Sannu da xuwa Yaya" Yace "Yauwa" tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya... Ahmad?" Tace "Ehh yana ciki ka shigo yaya" shiga parlon yayi ya xauna, ta wuce daki, Abuturrab na xaune ya jinginar da kansa da kujera bayan minti biyar Ahmad ya shigo parlon, ya xauna kujeran dake facing din nasa yace "Good morning" Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Ina ce idan kowa xai yi misperceiving dina kai baxa kayi ba, no not you Ahmad... and i was hoping u will understand me better then anyone, but do u mean i am mistaken?" Ahmad yace "U never wanted me to understand u, kana tunanin ni xan ki abinda kake so ne Captain?" Sai kuma yyi murmushi ya girgixa kai yace "Ka bani mamaki sosai, har gida na bi ka na sameka kan maganan Jiddah not long ago, kilan a lkcn ma ka koma kaje ka aureta ban sani ba, amma u almost blasted me telling me u have nothing to do with her, and u are leaving happily with ur wife, kana ganin ni xan maka bakin ciki idan ka kasance tare da Jiddah a matsayin mai dakin ka? Kana ganin i will also be against that bayan nasan komai tun daga farko har karshe? Da kuwa baka min adalci ba, coz i tried my very best tun farkon aurenka da Jiddah ka xauna da ita as ur wife, though i know u never bargained for that... amma nace ka dauka kaddarar ka ce a haka, kayi hakuri ku xauna, Aliyu sbda haka ka maida ni makiyinka, daga karshe kuma ka munafurce ni, Yes ka munafurceni, and you made me feel as if i am not trustworthy of, ban yi tunanin idan xaka boye ma kowa nima xaka boye min ba..." Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, looking so confuse yace "U misperceived me instead Ahmad, i never knew xan iya gathering courage lkci daya in fadi abinda ke raina kwana kusa, ban san xan iya ba, and abinda yasa bana involving dinka I don't want to look foolish after everything, ban san ta ina xan fara ba bayan abubuwa da yawa da suka faru, plss I don't want to go deep into this coz i am not okay Ahmad, but i am here to just say to u that.... i am sorry about everything, nasan a ko da yaushe kana sona da alkhairi fiye da kowa, kuma da na dau shawaranka tun farko abubuwan dake faruwa yanxu baxa su faru ba, i will accept all this in good faith in sha Allah" Ahmad dai bai ce komai ba yana sake mamakin Abuturrab, his pretence is just something else, ba a ta6a predicting dinsa, can yace "Allah ya tabbatar da alkhairi, ya Kuma kawo sassauci cikin lamarin" Abuturrab yace "Ameen, But i need a favour from u plss" Kallonsa Ahmad yake yana jiran jin favor din, a hankali Abuturrab yace "I want u to help me convince Umma" Ahmad ya girgixa kansa yace "I am sorry i can't involve my self in this because naga yanda suka dau issue din too personally, most especially Abba nd Hajja, sannan idan nace xan sa baki Umma cewa xata yi da sanina kayi komai kaga nima ka ja min kenan" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya mike, har ya nufi kofa sai kuma ya tsaya ya juyo yace "Thank you" sannan ya fita Ahmad dai ya bi sa da ido cike da tausayinsa, fuskarsa kawai xaka kalla kasan yana cikin damuwa sosai, jinginar da kai Ahmad yyi da kujera wishing he can help. Abuturrab na xaune parlonsa a sama yana rubutu saman wani plain sheet aka bude kofar parlon, juye takardan yyi upside down ya maida idonsa saman laptop din gabansa dake a kunne saman center table din kamar dai yana operating dinsa, Ta gefen ido ya kalli wanda ya shigo parlon ganin Ahmad ne ya ci gaba da rubutunsa a hankali, Ahmad ya karaso cikin parlon walking calmly yana kallonsa har ya iso ya tsaya gabansa yace "How are you feeling now?" Abuturrab bai ce komai ba idonsa na kan takardan da yake rubutu, Ahmad ya duka ya dauke takardan, Abuturrab xai kwace amma tuni ya koma baya yana kallonsa, Abuturrab ya mika masa hannu yace "Pass it to me..." Ahmad bai tankasa ba sai da ya gama karance abinda takardan ke dauke da shi tsaf, ya kalli Abuturrab da wani irin mamaki yace "What the heck... kana da hankali kuwa Captain?? Are u okay? what is this u are trying to do, are you even okay?" Bai jira me Abuturrab xai ce ba ya dauke har laptop din nasa, Abuturrab ya mike kafin yace komai Ahmad ya fita daga parlon... Aneesah dake downstairs tare da wasu kawayenta biyu da suka xo ta bi Ahmad da kallo ganin laptop din Abuturrab a hannunsa, sai bayan da ya fita kawarta Suhaila tayi kasa da murya tace "Ni dai ina son gayen nan wllh, sau biyu kenan nake ganinsa a gidan nan, d'an uwan captain ne??" Aneesah tace "Mijin kanwarsa ce fa" Suhaila ta hade rai tace "Toh ina ruwana, ni dai har raina naji ina sonsa wllh" Aneesah tayi kasa da murya tace "Toh xan tura maki numbersa" Rungumeta Suhaila tayi tace "Ko ke fa sweety" Gida Ahmad ya tafi direct, bayan yyi parking kofar gidan ya sauka ya shiga ciki, Umma ta fito daga dakinta kenan ta shirya xata fita ya shigo, Umma na kallonsa tace "Mu je ka ajiyeni gidan Yaya yanxu" Ahmad ya ajiye laptop din hannunsa ya mika mata takardan ta amsa tana cewa "Meye wannan din?" Har ta kai karshen content din sannan ta kalli Ahmad da mamaki tace "Did he send this?" Ahmad yace "Shi yasa na taho da laptop din, ni ban sani ba" Umma ta ma rasa abinda xata ce, haka ta bude baku, can tace "Toh ko bashi da hankali ne dai??" Bata jira abinda Ahmad xai ce ba ta bude jakarta ta nemi waje ta xauna ta shiga dialing numbersa amma ta ji a kashe, ta kalli Ahmad tace "Kana da number Aneesah ne?" Ahmad ya ciro wayarsa yace "Eh" Umma tace "Kira min ita kace mata ta kai masa wayar yanxu" Dialing kiran yyi Aneesah na dagawa yace "Pls ki d'an kai ma Captain waya, his phone isn't going through" Aneesah ta mike tace "Toh" bayan kusan minti biyar Aneesah ta kira Ahmad tace "Gashi nan Dr" Ahmad ya mika ma Umma wayarsa, Umma na amsa ta kai kunne da sauri tace "Aliyu??" Abuturrab yyi shiru jin muryan Umma, tace "Baka ji na ne?" Ya sauke kansa kasa yace "Ina ji" tace "Ka taho gida yanxun nan ka sameni" jin yyi shiru still tace "Ka ji abinda nace maka??" Yace "Toh" tace "Ba To ba, don't keep me waiting ina jiranka in 30mins time" A hankali yace "Ohk" daga haka ta katse wayar, buda baki tayi ta rike ha6a tace "Lallai ina ga ya fara xarewa ne yaron nan" Ahmad ya girgixa kai kawai ya xauna, yana ta tunanin ta ina xai fara yi ma Umma magana sai kuma yayi kasa da murya yana kallonta yace "Umma da banyi niyyar cewa komai a kan issue din nan ba don Aliyu really failed u all, ko kadan bai kyauta ba, amma yanxu ina rokon ayi masa afuwa don Allah Umma, he is really frustrated now, i know it's not going to be easy amma ki sa baki a sassauta masa Umma, kuma wllh Allah yana son Jiddah fiye da yanda ku ke tunani" Umma tace "Dama ina ta jiran wnn lokacin sai gashi Allah ya kawo, munafakai algungumai kawai, waye bai san bakin ku daya ba?? xaka ce kai baka san ya koma ya daura aurensa da Jiddah ba?? Ai duk iskancin da Aliyu yayi kana sane kuma kai ke mara masa baya, banda haka dubi yanda ka dinga watsi da batun yusuf a wancan lokacin, sbda baka ma son yana xuwa gidan nan yana ganin Jiddah ka dauketa ka mayar gidan ka, ashe da abinda ku ka kullala da shi, toh baxan sa bakin a sassauta masa ba, sae ya raina kansa wllh, kuma duk abinda iyayensa suka ga daman yi masa dai dai ne, yanda in his next life baxai sake daukanmu for granted ba, munafukai kawai" Ahmad dai yyi shiru yana kallonta ya ma kasa cewa komai, ta ina xai fara ce mata shi bai da masaniya a kan duk abinda Aliyu ke yi?? Sanin waste of time ne hakan don ba yarda xata yi ba ya sa yyi shiru, dama abinda yake gudu kenan ya ki cewa komai tun shekaranjiya sai gashi still bai fita ba... Kamar yanda Umma ta umarce Aliyu cikin 30mins din ya iso gidanta amma fa da karfin hali gashi driving yyi, he just saw his self a gidan, sae yanxu ya sake yarda ba shi da lafiya don har jiri yake ji sama sama, Umma ta dinga kallonsa har ya xauna yana kallonta a hankali yace "Ina yini" tace "Uban wa ka tura ma letter din nan da ka rubuta??" Yayi mata shiru breathing slowly, tace "Tambayarka nake malam" ya girgixa kai yace "Xan tura, amma ban tura ba tukun" Tace "Ohk wani aikin ka nema ka samu wanda mu bamu sani ba tunda dama baka maida mu a bakin komai ba?" Ya mata shiru, sai kuma ya jinginar da kansa da kujera, Umma tace "Ikon Allah, yanxu abinda ka fara sha ne ke gaya maka karya haka Aliyu? Ko dai hauka ka fara yi?" Ya dago yana kallonta yace "I don't want to risk my life and the life of more than 100 Umma... Hakan da nake son yi shine mafi alkhairi, my job isn't a anyhow job, nd i don't think i can continue with the situation i am in now, ni baxan iya ba, i just..." Shiru yyi ya sunkuyar da kansa, mikewa Ahmad yyi ya fice daga parlon ya bar su. Ahmad bai samu kowa cikin main parlor din gidan ba, direct ya nufi dakin Hajja, sallama yayi ya bude kofar ya shiga, Hajja na ganinsa tace "Toh kinga algungumin na biyu, tare suke komai in gaya maki.. shi ke xugasa kuma shi ya lalatasa, ya gantalar masa da rayuwa, wllh sanda na bar Aliyu xan je Masar ba haka yake ba, ba ruwansa da kowa ta kansa yake, bayan na tafi wannan mutumi duk ya lalatasa ya koya masa mugayen halayya" Aunty dake xaune dakin ta hade rai ta dauke kai ganin Ahmad, shi ma tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, Hajja tace "Ai wllh ina nan ina xuba ido inga hukuncin Usman a kan Aliyu, kuma duk mun yarda mu xama gantalallun... Allah sai ya sake sakinta, ai dai wnn karan idan ya saketa babu kuma aure tsakaninsu har abada, sai kuma yaje can ya ci kansa ya koma hayin rigasa ya nemo wata me siyar da awaran..." Aunty dai ta dauke kai saboda Ahmad dake tsaye, Hajja tace "Kinga ai ita narkekiyar can da yake sun san me suka tafka ita da yayarta ai har yau bata sake xuwa gidan nn ba, duk su suke xuga sa fa, kuma shawaran da kika bani na cewa a mayar da Jiddar Bauchi haka xa ayi wllh, ni ban ta6a sanin kin iya kawo shawara me kyau irin yau ba" Aunty dai tayi shiru, Ahmad yace "Ina yini Hajja?" Tace "Aa ni na yafe wllh, meye kuma ina wuni?" Yace "Ashe kuma dai abinda Aliyu ya aikata kenan?" Ta kallesa sannan ta kalli Aunty tace "Kinji munafuki koh? A gaskiya ya fitar min a daki kar ni in bar gidan, duk wani abu da ya shafi Hauwa ba son ganinsa nake ba gashi ta dalilinta da abinda ta haifa xa a fara tashin hankali tsakanin Bauchi da Kaduna" Aunty ta mike ta nufi kofa ta fice daga dakin, Ahmad yace "Wannan dai abinda ake ko kashe mutum Aliyu yayi sai haka, kuma da ba don shi din ba akwai wani da xai san Jiddah a cikin ku? Ya aureta domin ya ceci rayuwarta aka dinga samun me xugasa cikin gidan nan sbda tana da wani mugun kuduri a kansa har ya saketa ba don ransa ya so ba, ba wani ya xauna masa da Jiddah kafin su rabu ba, a xaunar da Jiddar a tambayeta ko ya ta6a cutarta dai dai da kwana daya duk xamansu har suka rabu?" Hajja tace "Ji algungumi Uban wa ke xugasa katon mutumi balagagge kace ana xugasa?" Yace "Aunty Hafsah ke xugasa sbda tana son aura masa er aminiyarta wanda gashi can ta hadasa da abinda ke cutarsa yanxu" Hajja tace "Aa bawan Allah na samu labari da kansa ya ga Nanisa yace yana so babu ruwan Hafsah, yau kwana uku kenan banda mutunci da girmamawa babu abinda ke hadani da Hafsah ko ita ce da girki ko ba ita ba nan take xuwa ta durkusa ta ajiye min abinci idan da akwai wani abu ta min kafin ta fita, da yake ni nace kada Hauwa ta sake shigo min daki babu ruwana da ita, toh ni ban ta6a sanin Hafsah na da hankali da mutunci ba sai a yan kwanakin nan, komai yi min take har wanki da wankin bandaki, yanxu idan xan kai Jiddah bauchin ma tace tare da ita xa mu kai ta, kuma ita ta kawo wnn shawarar me kyau" kallonta Ahmad yake ko kiftawa babu, Hajja tace "Ba ruwana xan nuna ma kowa ni er banxa ce har sai naji Aliyu ya saki yarinyar nan Jiddah, ita kuma Nanisa da kake cewa na fa je gidanta ranan tare da jiddan har muka kwana, baka ga kazanta ba kamar a fursin, gidan duk wari duk ya ru6e, ni dai da na dawo gida sai da na kwanta aka kara min ruwa wllh, ga gudawa da na dinga yi in gaya maka, ai ina jinjina kokarin Aliyu duk tsaftarsa har yake iya xama da ita har su kwanta, inaaaa shima kawai dai ya lalace da kazantar ne ba wani abu ba" Ahmad yace "Hajja kar ku tilasta Aliyu ya saki Jiddah wani abun yaje ya samesa, don a yanxu haka yana kwance tun shekaranjiya ba shi da lafiya, yau kuma ya rubuta resignation letter xai ajiye aikinsa" Hajja ta kallesa da sauri tace "Xai ajiye wani aikin? tukin jirgin saman??" Ahmad yace "Kwarai" Hajja tace "Ya ajiye a kan me bayan duk na fesa ma kawayena Larabawan Masar cewar jikana tukin jirgin sama yake, ba fa karamin aiki bane don ba kowa Allah ke ba ma ba sai turawa..." Hajja ta mike tace "Toh ya ajiye a kan wani dalili ana dai xaune qlau ba komai? Sannan wani rashin lafiya ce tun shekaranjiya kamar mara gata banga wani da ya shirya daga gidan nan yace xai je dubasa ba, kai ni wllh babu wanda ma yace bashi da lafiya banda kai yanxu, to uban me ya masu haka kamar wanda ya kashe d'an mutum? Kai tun fa fil'azal Usman ya fi son wancan shegen yaron Salim, gashi ya sallama ma en benue shi, Mu je ka kai ni gidan Aliyun yanxu ai ban ga ta xama ba, amma Allah wadaran Hauwa dai, d'an ki na fari baxa ki dinga jan sa jiki ki ji damuwarsa ba, wata uwar kirki ce d'anta ba lafiya xata yi shiru da bakinta kamar yaron banxa, wllh na gaji da wahalan matan Usman, duk en iska ne wllh" Daga haka ta suri katon jakarta ta fice daga dakin tana cewa "Mu je Ahmad, ai Allah yayi maka albarka kai da ka xo ka sanar min, wa ya sani ko asiri aka masa xai ajiye wannan aikin gwal din da yake yi, wllh ba kowa ake ba ma aikin ba sai turawa, to idan ba ikon Allah ba ta ya mutum xai iya daga ringimemen jirgi har sararin samaniya, ai sai irin su Aliyun da Allah ya ba" A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login