Showing 36001 words to 39000 words out of 346625 words

Chapter 13 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

wllh xai aika abinda ya fada, kwakwalwarsa ya ta6u da dadewa mu kuma bamu da halin kai sa ko ina a dubasa, har cewa aka yi mu kai sa dawanau a kano to ina kudin?" Wani mutumi a wajen yace "Alhmdlh abinda xan fada kenan ka riga ni Malam kabiru, gwara kawai a aura mata wani tunda uwar ma tace ba ji take ba yarinyar, kun ga tana dawowa sai a kai ta dakinta kawai..." Abuturrab yace "Akwai wani yaro na, ina son nema masa aurenta yanxu" Kallonsa duk suka yi, Mai Anguwa yace "Toh in dai kasan halinsa ina ga wannan ba matsala bace amma kafin nan ya kamata ka gabatar mana da kanka..." Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Ni sunana Aliyu Usman Umar... An haifeni nan cikin garin kaduna, ni matukin jirgin sama ne" Sake baki duk suka yi suna kallonsa kamar ranan suka ta6a ganin me tukin jirgin sama, yace "Gidan iyayena na nan Malali..." Mai Anguwa yace "Maa sha Allah Aliyu, to amma a ina kasan ita wannan yarinya da ake magana a kai?" Hansai ta amshe tace "Wllh daga siyan awara muka sa6a da shi, customer na ne shi da dadewa, da motarsa yake xuwa yyi parking ya siya har na dubu biyar dubu goma yana siya, toh shine jin rasuwar mai gidana sai ya kawo mana kudi dubi hamsin dubu dari, ta haka muka saba muna mutunci sosai da shi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah" Abuturrab dai bai ce komai ba, Mai Anguwa yace "Toh amma shi wannan yaron da kake son hada yarinyar da shi wanene, sannan a ina yake?" Abuturrab yace "A kano yake, yana aikace aikace ne a airport din kano..." Hansai tace "Shi ma jirgin yake tukawa?" Ya girgixa kai yace "Aa..." Wani datijo dake xaune wajen da baxai wuce shekara sittin da takwas ba yayi gyaran murya yana taunan goransa yace "Amma fa wata kusan ya fi wata kusan nake ji ai... Tunda haka ne ni yanxu xan bada sadaki sai a daura min aure da ita wannan yarinyar...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa, can ya girgixa kai yace "Haba Baba ai addininmu ma bai ce haka ba, da taxara sosai tsakaninku da yarinyar nan...." Dattijon ya hade rai ya katse sa yace "Toh kai idan taimako kake son yi ka aureta mana kai da babu taxara me yawa tsakanin ku, shi fa wannan yaron da kake son hadata da shi nasan ba kowa bane d'an goge gogen iyapot ne, ni kuwa kowa yasan babu rashin ci babu rashin sha a gidana, matana uku ko wacce kuma tana da yara shidda shidda, shi me anguwan ai yasan wanene ni, auren yarinyar nan da xan yi tamkar jihadi xanyi don ance bin maza take" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi with disgust, Dattijon ya ja tsaki yana ci gaba da taunan goronsa da jajayen hakoransa yace "Idan tsakani da Allah ne kai ka aureta mana yaro xaka wani kawo ma mutane fi'ili a nan, kaga mai anguwa a yanke min sadaki yanxu in bada a wuce wajen dama ina da niyyar auren kwanan nan" Yana fadin haka ya fiddo yan dari biyar biyar a aljihunsa, lokaci daya tunanin Abuturrab ya kwance, Hansai ganin 'yan dari biyar biyar tana d'an kame kame tace "Ai wllh tamkar taimako xaka yi Alhaji, wannan babban taimako ne, ni kaina da na haifeta bana shaidarta, kawai dai Allah ya shirya mana xuri'a" Alhajin ya murmusa yace "Babu komai ai tamkar jihadi xan yi, Ni mai anguwa ne waliyi na, ita kuma sai a samu wani...." Abuturrab ya rufe ido ya bude, yaji kansa ya fara juya masa ya dinga kallon tsohon nan da ya fara kirga kudin da ya ciro, rasa tunanin da xai yi yayi, he was totally lost, Hansai dake ta kallon kudin hannun tsohon tace "Kawai a daura tunda ga sadakin a kusa" Jibril yace "Wannan taimako ne me girma xaka yi Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, tana dawowa daga gantalin da ta tafi sai a wanketa a kai maka gida kawai" Abuturrab ya kalli mai unguwa after gathering much courage yace "Ni xan aureta, sai ka xama waliyi na" Ba Hansai ba kowa na wajen sai da yayi mamaki, mai Anguwa wanda da alama dama bai yi na'am da daurin auren da wannan tsoho me suna Alhaji Saleh ba yace "Toh Madallah Aliyu" Tsohon ya d'an ja tsaki ya mayar da kudinsa aljihu, A nan take kuma aka daura auren Abuturrab da Jiddah a kan sadaki dubu arba'in, su kenan kudin jikinsa da ya ciro daxu bayan ya siya ma Umma drugs, Xaune kawai Abuturrab yake a wajen amma gaba daya he is absentminded and lost ga wani sanyi da yaji yana shigarsa kamar xai yi xaxxabi, har aka gama komai aka raba dabino da alawan da aka siya a nan cikin layi, Hansai dai ta kasa gane ko murna xata yi ko akasin haka, Ya xa ayi babban mutum kamar wannan gashi har yace jirgin da bata ta6a gani ba duk tsawon rayuwarta yake tukawa ace wai ya auri Jiddah maimakon Bibalo, tunanin hakan yasa taji wani bakin ciki ya tokareta a kirji, lkci daya hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba ta dinga xufa daga inda take xaune, yanda take xufa haka Abuturrab ke xufan shi ma, tunda yake bai ta6a shiga rudani da confusion lkci guda irin wannan ba, wait!!! what did he just do now??? What have he done to his life?? A cikin lkci ba me tsawo ba aka gama komai, sama sama ya dinga jin albarkan da dattijan wajen ke sa masa na cewar ya rufa ma jiddah asiri duk da ga abinda aka ce tana yi amma hakan bai sa ya kyamaceta ba gashi ya taimaketa ya aureta domin nisantata daga cutarwan iliya, Abuturrab ya mika ma mutumin karshe hannu sannan ya mike a hankali ya nufi motarsa walking slowly kamar mara lafiya, yana shiga motarsa ya tada motar ya kashe Ac don sanyi yake ji sosai ya fara driving ya bar layin, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida lafiya cause blurry ya dinga gani ga kansa dake juya masa ya dinga ganin komai double, ko parking din kirki bai iya yayi ma motar ba ya sauka ba tare da ya rufe ba ya shiga ciki mai gadi ya bi sa da kallo, direct dakinsa ya nufa ba tare da ya kalli kowa na parlon ba, duk suka bi sa da kallo, Aunty ta kalli Ummi, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta mike ta bi bayansa da sauri, cikin bargo ta gansa ya lullube har kansa, da mamaki tace "Are you okay Aliyu???" Bai iya ya bata amsa ba, ta sauke bargon a hankali ganin he is shivering so much, da mamaki tace "Baka jin dadi ne?" Ya gyada mata kai kawai, tace "Subhanallah, let me switch off the Ac"



Nan na kawo karshen free pages na *Jiddatul Khair* in sha Allah, and the paid book is 500 Via

👇🏻
3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.....

And u show ur evidence of payment via my WhatsApp Number 👉🏻 07087865788.....


Plss just WhatsApp ban fiye son phone call ba, and i am begging you don't come to my DM without any concrete reason, it's tiring wllh....😓😰 just come, patronize, i save ur number, and i add u to my groups... Shikenan

Thanks and i love you all as u patronize.💖💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖





_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻






12...


Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?" Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace "Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday" Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace "Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah" Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah" daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son, Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran" Maman Abdallah tace "Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba" Maman Abdallah tace "Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai" Umma tayi murmushi tace "Toh sai kun dawo" Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn't comfortable, hakan yasa tace "Ko kuma ku tafi kasuwan kawai tare kada ta xauna shiru" Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace "Dama tare nayi niyyar xa mu je, da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya" Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman Abdallah tace "Toh taso mu tafi kasuwan" Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace "Tunda kallo take yi ki bar ta tayi kallonta mana" Kallonsa Umma tayi da mamaki, that's very odd of him, shi mutanen cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh tayi xamanta" Maman Abdallah ta fita parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace "Kilan ta manta ne bata kawo maka ba..." yayi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Kana son madara?" Ya girgixa mata kai, tace "Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad ma bai fiye shan madaran ba" Sama ta nufa tace "If u are done ina daki" Yace "Alright" Bayan few minutes da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace "Baki da wani damuwa a inda kike?" Ta dago ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace "Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a gida" Kallonta yayi a takaice yace "Toh a mayar da ke wajenta kenan?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa" Abuturrab ya hade rai yace "Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?" Bata ce komai ba, ya fara shan shayin hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace "Amma idan aka sauya maki shi wanda xai aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?" Kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Ko baxa ki amince ba?" a sanyaye tace "Toh ai ban san waye shi ba" yace "Toh ni nasan sa" Tace "Toh in dai baya shaye shaye" Ya dinga kallonta sannan yace "Kina dai son kiyi aure kenan dama?" Hawaye ne ya kawo idonta tace "Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana'a muke yi" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d'an kalleta yace "Wanda xan hada ku baya shaye shaye" A hankali tace "Toh" bude warmer din awaran yayi yana kallo yana d'an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya duk ya rufesu yace "Ki dauka ki kai maku can ki ci" Da sauri ta kallesa tace "Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne" Ganin babu spoon a wajen tace "Bari in kawo maka cokali" Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login