Showing 339001 words to 342000 words out of 346625 words

Chapter 114 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

kusan shekara goma kenN, Kishiyata Kulu ta dinga ciwo kamar dai ba na tashi ba, tun bayan haihuwar nan nata biyu dama kuma bata sake haihuwa ba, daya yaron nata rasu, dayan kuwa na garin Legas ko waiwayarta baya yi shekaranmu takwas kenan rabonmu da shi, komai dai na bukatar yau da kullum da ku ka sani kai hatta gidan da take ciki 'ya yana suka siya mata tunda Allah ya hore masu, tana dai cikin rufin asiri amma ciwo dai ya ki ci ya ki cinyewa, wai sai ana gobe Kulu xata mutu naje dubata da yake kullum sai an kai ni gidan a mota, shine take rokona gafara tana kuka, nace gafarar me kuma kulu, me kika min, nace mata ni baki min komai ba wllh kulu, lafiya muka xauna dake har xuwa yanxu... Hajiya Dada ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Wai a nan Kulu ke ce min ai ita ta ba ma kaninta Saleh Yusif ya kai sa garin kano kawai ya bar shi a kan hanya sbda kawai Malam Sanusi na yawan yi masa waka yana cewa ya mallaka masa gonarsa kwaya daya tak... Toh a daren ranan Kulu ta rasu, ni kuwa ya xan yi? Nace na yafe mata, a nan take kuma na sa yan uwan Yusif a buga gidan jaridu a kai labarin gidan radio har ma da talabijin ko Allah xai sa Yusif ya ji ya nemo mu, amma shiru kake ji, har snn kuma ina ji a raina Yusif bai mutu ba, ashe ma rai yayi halinsa...." kuka take sosai, Hajja tayi tagumi tace "Amma Allah ya tsine ma wannan mata kulu, Allah ya kara mata nauyin kasa, Allah ya matse kabarinta" Cikin Kuka Dada tace "Aa na yafe mata wllh, dena fadar haka na yafe mata" Hajja ta bude baki tace "Tabdi, yanxu ashe uban Jiddah da gatansa yayi ta galantoyi tun yana karami a kaduna, to kuwa wllh da yasan da wnn labari da kyar idan ya sa ma Jiddah wannan sunan da ya sa mata, don ita ma kulun ce ai, da yasan matar ubansa ce ta gantalar da rayuwarsa wllh baxai sa ma yar sa kulu, ni har naji na tsani sunan duk da sunan surkata ce dai" Dada na kallon Jiddah cikin kuka tace "Taho kusa da ni Hauwa..." jiddah ta goge idonta a hankali ta mike ta isa kusa da kakar tata ta xauna, Hajiya Dada ta rungumeta tana shessheka tace "Ko ba komai ai xan ganki in ji dadi, ko ba komai xan kalleki in tuna da masoyina Yusif, nayi farin cikin da Allah bai dau raina ba sai da na ga jinin Yusif" Hajja ta fashe da kuka tace "Allah ka tsine ma wnn mata dai kulu, ko ya xata yi da hakkin da da uwa a kabari, ashe tun tale tale ake rashin gaskiya a duniya ban sani ba, tirrrr" Hawaye kawai Jiddah ke yi a jikin Hajiya Dada, Hajiya Fatima ta fi kowa farin ciki a parlon nan, she was so happy Jiddah is closely related to her Husband, tun da ta ga Jiddah dama ta san da wani abu dake boye a kasa, she just like her for no reason, xurfin cikin mai gidanta bai sa ya ta6a bata labarin d'an uwansa da ya 6ata shekaru masu yawa da suka wuce ba, sauran yaran Hajiya Dada sun yi farin ciki sosai su ma da ganin daughter din d'an uwansu da ya bace shekaru hamsin kenan don su kansu ba wai saninsa suka yi ba sai a labarin mahaifiyarsu da take yawan yi masu duk sanda ta tuna da shi, Hajiya Dada ta goge idonta tace "Ina mahaifiyarta?" Hajja tace "Ahau, ance tun tana jaririya uwar ta rasu, a hannun matar uba ta taso tana ta gallaza mata tana bata tallan awara da doya da dankali tana bi layi layi da shi a kai tana siyarwa, shine fa jikana matukin jirgin sama ya ganta cikin mugun yanayi yaji tausayinta ya rabota da wnn anguwa ana kiransa da hayi, in dai kunsan kaduna xa ku san hayi, kuma duk wanda ya ji hayi ya san sauran, to a can dai jikina Aliyu ya aurota ya kawota cikinmu, babu abinda muka ragata da shi yau shekaranta biyu kenan tare da mu, kanwar uwarsa ce uwarta da ubanta matar ta rike ta da amana ko er ta sai haka, don isa da gadara kawai take xubawa a kanta tayi ta nuna ta fi kowa sonta" Duk aka dinga kallon Hajja a parlon, Hajiya Dada ta girgixa kai tace "Allah ubangiji yayi maku abinda ku ka mana Hajiya, Ina matar uban nata?" Hajja tace "Wa?? Tana can duniya ta juya mata baya aka ce, idan xa ku ji shawarata ku fita harkarta kawai, don wllh ina da yakinin har da bala'inta ya kashe isuhun naki, duk ita ce ta fitinesa, to me xa ayi da ita kuma?" Hajiya Dada tana hawaye tace "A dai a kawo min ita ko a kai ni inda take Hajiya, duk wani abu da ya shafi Yusif ba abinda xanyi banxa da shi bane" Hajja tace "Atoh, amma dai Jiddah kam yau shekaranta biyu rabonta da matar uban gaskiya" Hajiya Dada tace "Allah ya saka maku da alkhairi Hajiya, Allah ya saka, Allah ya saka, yau na daya daga ranakun farin cikina a rayuwa, Allah ya rubuta baxan bar duniya ba tare da na ga jinin yusif ba, har in koma ga mahaliccina ni da yarana baxa mu mance da wannan halaccin naku ba, Allah ya saka maku da alkhairi Hajiya" Hajja ta dinga wani murmushi tace "Ameen Ameen" Hajiya Zuwaira fourth born din Hajiya Dada ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh dangin mahaifiyarta fa?" Hajja ta gwalo ido tace "Ke kin ta6a ganin wanda ba a san asalinsa ba a dau yarinya me asali a basa? To wllh abinda ya faru kenan, ita kanta uwar Jiddan a yanda shi isuhun yake ita ma a haka take, wato dai ba a san asalinta ba, mu ai aiki biyu ne a gabanmu, yanxu munyi daya saura daya, duk inda dangin uwarta suke su ma sai mun nemo su, ko kuma mu bar ku da wahalan ku mu, ai munyi kokari haka" Alhaji Sulaiman yace "Haka ne Mama, wnn kam aikin mu ne in sha Allah duk inda yan uwan mahaifiyarta suke xa mu yi bakin kokarinmu na ganin mun nemo su, da izinin Allah kuwa" Hajja tace "Ina sha Allahu, shine kadai gatan da xa ku yi mata don duk wanda xaku mata ba birgeta xakuyi ba tunda ta samu a wajenmu da wajen jikana Aliyu" cikin sanyi Hajiya Dada tace "Toh shi jikan nawa baxai xo in sa mashi albarka wannan namijin kokari da yayi haka ba" Hajja tace "Huhuhu.... Namijin kokari kuwa, kaff Najeriya babu matukin jirgi bahaushe sai shi, hatta turawa ji suke da shi wllh don ya iya sarfa jirgi, a lkcn da ya auro Jiddah fa wllh ko da kudi aka hadaka da ita baxaka amsheta ba, talaka ma wllh da kyar xai amince ya aureta, wahala tayi wahala, ba arabi ba boko sai talla, fatar nan nata yayi wani dukun dukun malam, kai!!! wllh Aliyu yayi kokarin da ba kowa xai yi ba, amma sbda xuciyarsa irin tawa ce wllh haka ana masa dariya ana xolayarsa ya rufe ido ya aurota ya kawo mana gida, ranan da ya kawota kuwa duk sai da muka girgixa muka fita hayyacinmu, biyar baxaka siyi Jiddah ba wllh wllh, ko da yake dai duk ina Masar aka yi hakan" Hajiya Fatima dai sai murmushi take tana kallon Hajja, Hajiya Dada kuwa ta makalkale Jiddah kamar xa a rabata da ita.





*Wannan littafi dai ya ki karewa bayan nagaji da shi shima ya gaji dani☹️ ko da yake nasan me xanyi* 😁


_4 years later_..... 🫣



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp








Parking Aunty Rahama tayi a kofar gidan Abba, Hajja dake bayan motar tana washe baki tace "Allah ya maki albarka, in sha Allahu nan da kwana biyu xan dawo anguwan naku gaba daya kin ji?" Aunty Rahama na murmushi tace "Toh Allah ya kawo ki lafiya kaka" Jiddah dake gaban mota tace "Mun gode Aunty" Aunty Rahama na mata murmushi tace "In kun shiga ki gaida su mama kin ji" Hajja tace "Au ni da nake xaton xaki shigo ku gaisa" Aunty Rahama tace "Aiki xan tafi kaka, na makara wllh" Hajja tace "Aa kin makara gaskiya gashi har tara saura, to ke mijin naki ba a kasan yake bane?" Tayi murmushi tace "Allah ya mashi rasuwa kaka" Hajja ta saki wani salati tayi tagumi cike da damuwa tace "Allah sarki, Allah ubangiji ya gafarta masa, to baki da 'ya ya da shi ne?" Tace "Ina da, su biyu ne, suna gun yayansa a Abuja, sai hutu ake kawo min su" da sauri Hajja tace "Aa ki amshe yaranki, ce masu kika yi baxa ki iya kula da su ba ko salon kar yaran su ji kanki su san ciwonki" Ita dai murmushi kawai take, Hajja tace "Wllh amshe abin ki, ni ban yarda da rikon d'a ba..." Daga haka ta bude motar ta sauka, Jiddah ma ta sauka tana kara yi ma Aunty Rahama sallama suka shiga gidan da Hajja, tun daga parlor Hajja ke kwala ma Ummi kira, Ummi na fitowa tace "Toh dai Jiddah ba yar matsiyata bace, kuma kakarta na nan da ranta sai kin ga abun arzikin da aka mana a wannan gari na gombe, mutanen kirki mutanen arxiki suka cika garin, sun karrama mu sun daraja mu sun mutunta ba, wllh basu so mu taho ba amma wannan yayan baban nata Alhaji Sani naji ana ce masa ko wa? Wannan dai da ya mana jagora xuwa garin shi ya axalxala mu taho, in don ta nine da bamu dawo ba wllh, jiya da daddare muka dawo to yau naga wnn yarinya Jiddah sai wani nukurci take taki kulani nace to ko kewan mijinta take shine dai nace su maido mu gida da safe, amma wllh dangin ubanta en arxiki ne babu talaka ko kwaya daya a cikinsu, ke kin ga gidan ma kuwa, wllh yayi biyar din wannan, kuma kinsan gidan waye, gidan uwarsu ne, su suka gina mata gwanin ban sha'awa, ai ita kam ta more rayuwa wllh...." Ummi tace "Toh Alhmdlh, nayi murna sosai, Allah ya bayyana dangin mahaifiyarta haka" Hajja tace "Allah gidan yayi ukun wannan kuma tsohuwar kadai ke rayuwa a ciki, duka duka fa bai fi ta girmeni da shekara uku ko hudu ba, amma sai kin ga abinda yaranta suka kera mata, tana xaxxaune ta mike kafa sai dai ayi mata komai" Ummi ta amsa gaisuwar Jiddah da ta duka kasa ta gaisheta, Ummi tace "Ya hanya, fatan kun dawo lfya, ya kuma ku ka bar mutanen can din" Hajja ta amshe tace "Alhmdlh, babu abinda basu mana ba, yanxun ma fitowa muka yi ba shiri ita kuma warce ta kawo mu tana ta sauri xata aiki, banda haka in gaya maki ai tsarabanmu da yanxu haka ba a gama shigowa da su ba, to sunce anjima da yamma xa a taho mana da shi, ke dai ki bari kawai Hauwa, karramawa da mutunci na inda yake, ni kam bani da abinda xance ma mutanen nan" Daga haka ta wuce dakinta, Ummi da ta bi ta da kallo tace "A kawo maki kumallo Hajja" Hajja tace "Meye kuma kumallo? Aa mu mun yi lafiyayyen kari, kawai a bani makullin d'an kuturun dakina" Ummi ta tafi dauko mata makullinta ta kai mata, ta bude ta shige ciki tana kyabe baki, Ummi ta dawo parlor ta xauna tana kallon Jiddah tana murmushi tace "Kin je kin ga kaka da kawunnanki ko?" Murmushi Jiddah tayi ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh Alhmdlh, Alhmdlh, i am so happy for you daughter" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta kawai, Tashi Ummi tayi ta tafi parlon Abba, Jiddah ta dinga kallon hanyar dakin Abuturrab amma ta kasa tashi, ta fi minti biyar sai ta kalli dakin sai ta dauke kai, can dai ta mike a hankali ta nufi dakin kamar munafuka muryan Ummi taji tace "Ai bai nan ya koma aiki Jiddah" kunya ta ji kamar ta nutse, ta kasa juyowa ta kalli Ummi, jin shiru sai kuma ta juyo a hankali, gani tayi Ummi bata ma wajen, da sauri ta wuce dakin Hajja. Washegari da safe Jiddah na dakin Hajja, Hajja na cewa "Kin ga ai ni bana kai kaina inda Allah bai kaini ba kuma bana takura ma yarana ince sai sun min abu dole, da wata ce yanxu duk sai ta kwarzabi yaranta tace sai fa an mata gini irin na wannan kakar taki, amma ni kam Allah ya kiyaye inyi haka sai kace wata er banxa, ni ko burgeni gidan bai yi ba balle inji sha'awa ince a min irinsa" Jiddah dai kallonta kawai take amma bata ma san me take cewa ba, kewan Abuturrab kawai take, ji take kamar ta fi wata daya rabon da ta gansa, she's a kind of sad, gaba daya ta ji gidan ya isheta, gashi bata san sanda xai dawo ba, ga surutun Hajja dake sa mata ciwon kai, tayi mata xancen gidan Dada ya fi sau ashirin daga jiya xuwa yau, har Umma da ta xo jiya ta bata labari, Hajja ta ta6e baki tace "Ba ruwana da sa ma wani ido wllh, nagode Allah da inda ya ajiyeni, shege ne kawai xai dinga hangen abun wasu" Bude kofar dakin aka yi Ummi ta shigo tayi ma Hajja sannu, tana kallon, Jiddah tace "Ur husband said he will be back in the evening of today, so get ready after Zuhur, i will instruct the driver to drop u home" Tace "Toh Ummi" Juyawa Ummi tayi ta fita, Hajja ta ta6e baki tace "To ko matansa ma basa hanasa ya min kantamemen gini ba don bakin ciki, ai kai dai kawai ka haifar ma mace yaro kawai, bayan haka baka da sauran martaba a wajensa" Tun da Ummi ta fita Jiddah ke counting agogo sai taga baya sauri, wai karfe goma da rabi, har bacci tayi ta tashi wai karfe sha daya, kawai daga karshe ta mike ta fita daga dakin Hajja ta tafi part din Ummi... Ummi ta ajiye littafin hannunta tana kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Kunya taji ya rufeta, Ummi tace "Ko har kin shirya?" Tayi karfin halin cewa "Ehh Ummi ina son xanje inyi girki ne" Ummi tace "Eh gaskiya kam, bari in kira driver din, shiga ki dauko jakarki to" Kanta a kasa ta shiga dakin Ummi ta dau jakarta ta fito dama da Hijab dinta a jikinta, bayan Ummi ta kira driver ta mike ta tafi daki ta dauko mata makullin gidan nasu, tana mika mata tace "ki je ki ma Hajja sallama kice mata xaki gidan Umma ne" Jiddah tace "Toh" Ummi tace "Idan kin mata sallaman ki samu driver din yana waje" Jiddah tace "Ummi ina son in siya wasu abu a kasuwa ne..." Ummi tace "Kina da kudi wajen ki ne?" Girgixa mata kai tayi, Ummi tace "Toh bari in baki Atm card, idan ya dawo sai ya maido min da card din nawa" Atm card din ta dauko ta mika ma Jiddah ta gaya mata pin din tana kara nanata mata kar ta manta, Jiddah ta risina ta amsa tayi mata godiya ta fita, kallonta Hajja ta dinga yi sai kuma tace "Me ake yi a gidan Umman?" Jiddah tace "Kawai xan je ne" Hajja tace "Toh sai mijin naki ya dawo xamu koma can gidan kin dai ji abinda nace ma dangin ubanki kar su daukeni makaryaciya idan basu gan ni ba" Jiddah tace "Ehh sai ya dawo" Hajja tace "Toh ki gaida Ramlan" Jiddah ta juya ta fita, sai da driver ya fara ajiyeta kasuwa ta siya ingredients din fried rice da zobo drink, tunda suna da nama a deep freezer bata siyi komai ba banda liver, daga nan driver ya ajiyeta gida tayi masa godiya ta shiga ciki bayan ta gaida mai gadi. Tana shiga cikin gidan ta kai kayan girkin kitchen ta tafi sama ta canxa kaya xuwa kanana sannan ta fara gyaran gidan, ta tsaftace ko ina tayi mopping da goge goge ta kunna turare a burner, sai da tayi azahar sannan ta shiga kitchen.... Kafin la'asar ta gama hada lafiyayyen fried rice dinta with zobo drink, ta soya kajin tayi pepper chicken da shi, sai farfesun offals da tayi kadan, duk ta jera abincin a dinning, ta koma ta tsaftace kitchen din kamar bata yi komai a ciki ba ya dawo fes fes, sama ta wuce dakinta ta shiga wanka, da alwalanta ta fito sai da tayi salla snn ta fiddo da kayan da xata sa, ta dau kusan minti talatin tana shirya, ta saka wasu ubansun English wears masu daukan hankali, ko ina na jikinta wani sanyayyan kamshi ne ke tashi, tayi packing gashinta da ribbon leaving it that way, she look just like a princess, tayi kyau sosai, bude gate taji anyi ta karasa window tana kallon waje yaga Abuturrab ne ya shigo da motarsa... Sauka tayi downstairs ta tafi bakin kofa ta tsaya, she is just so happy, ta labe a gefe daya har ya bude kofar, wani kara tayi da nufin basa tsoro, ya jawota jikinsa yana kallonta daga sama har kasa yana murmushi, 6ata fuska tayi yayi kasa da murya yace "Jirgi bai bani tsoro ba sai matata?" Dariya tayi ta boye fuskarta jikinsa a hankali tace "Welcome my Man" Ya lumshe ido ya bude yana shafa bayanta yana kare ma dressing dinta kallo yace "U look sexy in this wife..." Sai kuma ya kankameta yace "Wllh i have missed u so much wife, Hajja bata kyauta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login