Showing 300001 words to 303000 words out of 346625 words

Chapter 101 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

karasa ya duka kusa da ita yana shafa hancinta ta bude ido a hankali, turo baki tayi ganinsa xata juya masa baya ya dagota yace "Baccin ya isa haka, yamma yayi..." Kamar xata masa kuka tace "My legs are aching" ya cire duvet din yana massaging kafar ta hade rai ta rike hannunsa gabanta na faduwa tace "Bana so" ya kalleta da lumsassun idonsa yayi kasa da murya yace "Baki son me?" Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba cause it started just exactly like this daxu, ya saketa da sauri, a rikice yace "Toh yi hakuri plss..." Ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, bai ta6a ta ba ya marairaice yace "Na fa ce kiyi hakuri wife, don Allah kiyi hakuri" ta dago kanta taba goge idonta a hankali, ya langwabar da kai yace "To taso ki gaisa da su Ahmad, they are around" ta bude ido sosai tace "Da gaske?" a hankali yace "Yea wife..." Mikewa yayi ya dagota tsaye, kamar xata sakar masa kuka tace "Ni wllh bana jin dadi" Ya xaunar da ita gefen gado da damuwa yace "Toh ko mu tafi asibiti yanxu?" Ita dai tayi shiru ya rungumeta tayi lamo jikinsa yana patting bayanta, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Toh baxan kuma ba, till u are healed...." Ta lumshe idonta tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa a kirjinta, murya can kasa yace "I love u with every breath of mine Wife" Ta kara shigewa jikinsa amma taki cewa komai kuma bata bude idonta ba, shi haka kadai ma ya ishesa ko bata mayar masa i love u din ba, narkar masa da xuciya da tunani gaba daya Jiddah take, she is the best thing that have ever happened to him, he felt complete with her, kamar me rada yace "Mu tafi asibitin a dubaki?" Ta make masa kafada, yace "Toh kin ce baxa ki iya tashi ba, ko in kira Ramlan ta shigo ku gaisa a nan kawai su tafi?" Da sauri ta bude ido tace "Aa xan je" Ya dago kanta ya shiga yi mata single lip kiss... Vibration din wayarsa ne ya dawo da shi ya mike xaune da sauri sannan ya dau wayar ya duba yaga Ahmad ne, buda ido yayi sosai sai kuma ya kalleta ganin yanda ta kulle idonta ya ja hancinta ya mike ya fita daga dakin, Yana sauka downstairs Ahmad yace "Captain da sai kace mana mu tafi kawai da dai shanya mu da kayi a parlor haka" Abuturrab ya kasa kallonsu yana shafa kansa yace "Ohk... I was suppose, ohhh sorry..." Sai kuma ya juya da sauri ya koma sama, dakin Aneesah ya shiga yana kallonta yace "Ki sauko ku gaisa da su Ramlah" ya juya ya fita ya koma downstairs yana kallonsu yace "Jiddah bacci take, she is having headache since morning, so Aneesah will be coming down now" Yana fadin haka ya nemi waje ya xauna, Ahmad dae kallonsa kawai yake yana murmushi ganin duk a birkice yake, masu gyara sababbin kayan dakin Jiddah dai na ta faman gyara a sama, Aneesah taji wani abu ya tokareta a makogwaro bayan ta fito, kallo daya tayi ma dakin Jiddah ta sauka kasa da sauri, babu yabo babu fallasa ta gaida Ahmad sannan ta amsa gaisuwan da Ramlah tayi mata, Shi dai Abuturrab fa gaba daya hankalinsa yayi sama, soul dinsa kawai ne a parlon amma spirit dinsa na can sama, can dai ya kalli Aneesah yace "Baki basu ko ruwa ba" ya mike ya dau abincin da ya siyo ya ajiye masu ya dau daya xai kai ma Jiddah sama, A stairs ya ganta tana saukowa a hankali, hakan ya sa ya ajiye ledan, har ta shigo parlon taki yarda ta hada ido da su Ahmad ta xauna kan kujera ta gaishesu cikin sanyin muryarta tana murmushi, Ahmad dake kallonta yace "Duk kewan Umma ne yasa kika rame haka Jiddoh" Ita dai murmushi kawai take ta d'an kalli Ramlah tace "Yaushe ku ka xo?" Ramlah dake ta kallonta ganin yanda ta kara haske tayi kyau amma kuma ta rame kamar yanda Ahmad ya fada, ta sakar mata murmushi tace "Yau da safe muka xo Aunty Jiddah, ya gida?" A hankali Jiddah tace "Alhmdlh, ya jiki?" Ramlah tace "Mun gode Allah" Tun da Aneesah ta shiga kitchen kmr xata dauko ruwa ta ki fitowa, Ahmad ya lura how uncomfortable Jiddah is a parlon kamar dai bata jin dadi, shi kuma ogan da ya xo wajensa sai kallonta yake kamar xae cinyeta, it's just as if he is obsessed with her... Ahmad yayi wani murmushi yana mamaki iri iri, sai kuma yace "Dama nace bari mu xo mu duba amarya Jiddah, yanxu kuma xa mu je can gida wajen Ummi, sae kuma wani lkcn in sha Allah" Abuturrab ya kallesa da sauri yace "So early, naga baku ci abincin ba fa...." Ahmad yace "Aa sae yanxu nayi reason, ba a wannan lkcn ya kamata mu kawo ziyara ba, in sha Allah xa mu dawo lkcn da ya kamata, but before then yaushe xaka barta ta koma makaranta Captain? cause satinsu biyu kenan da resumption" Abuturrab ya shafa kansa yace "Makaranta kuma?? Wani makaranta?" Ba Ahmad ba har Jiddah kallonsa take da mamaki, Ahmad yace "Ohh baka san ma wani makaranta ba ko, to Umma xata maka bayani da kyau" daga haka ya mike yace "Mu xa mu koma" Abuturrab yace "Shkkn sai mun yi waya" tare suka nufi kofa suka fita yana son gaya ma Ahmad abubuwa da yawa, bayan sun fita Ahmad bai basa daman magana ba yayi patting shoulder dinsa yace "Kar dai kayi ma er mutane ciki da wuri, kaga she is still very young...." Abuturrab ya d'an 6ata fuska yace "Ciki kuma? Aneesah bata dau ciki ba sai ita?" Dariya Ahmad yayi sosai ya ma kasa ce masa komai, wato Aneesah da suke yi for long bata dau ciki ba sai wata Jiddah tunda an gaya masa it's by that, kwafa Ahmad yayi yace "Xaka sha mamaki ka ci gaba da relying a kan haka... Sae kaga cikawar aikin ka" Jiddah na kallon Ramlah da ta mike da kyar, cike da damuwa tace "Baki ci komai ba kuma xa ki tafi, ko in kawo lemo sai ki tafi da shi?" Ramlah tace "Wllh mun ci abinci gidan Umma kar ki damu, Maimoon tace yaya ya siya maki waya da mota, and i saw the car da muka shigo yanxu, a very hearty congratulations dear, Allah ya sanya alkhairi" Da murmushi ta kare maganar, Jiddah dai ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Nagode" Ramlah ta bi parlon da kallo to make sure Aneesah bata nan ta mika mata ledan hannunta murya can kasa tace "Duk na rubuta maki yanda xa ki yi amfani da ko wanne, idan ma baki gane ba ki amshi lambata wajen yaya ki kirani" Jiddah ta amsa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Toh nagode, yanxu haka xaku tafi ko ruwa fa baku sha ba" Ramlah tace "Sai kace wata bakuwa, kar ki damu wllh... Sannan maganar makarantarki ki lallaba yaya don naga kamar in don ta shi ne baxai bari ki ci gaba ba, do all u can ya barki ki xana waec dinki kin ji?" Jiddah tace "Toh nagode" Ramlah bata bi ta kan Aneesah da ta walakanta su ba ta nufi kofa, ta juya ta kalli Jiddah dake biye da ita, ganin kamar tafiyar na mata wahala ta dafa ta tace "Ki koma Jiddah, we will talk on phone in sha Allah..." Daga haka ta fita parlon Jiddah ta daga mata hannu ta bi ta da kallo, dai dai nan Aneesah ta fito kitchen tayi wucewarta sama kamar xata yi tsuntsu Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido.... Bayan magrib Abuturrab na dawowa mosque ya shiga dakin Aneesah, earpiece ne jone kunnenta tana daga xaune kan duvet da ta kwana jiya, dakin nata dai babu kyan gani kamar anyi yaki a ciki, suna hada ido da shi tayi pausing wakar da take ji amma bata cire earpiece din ba, bai ga alamar tayi sallah ba ma shi ma kuma bai damu yace tayi ba, ya rungume hannunsa yace "Naga u didn't make any food ko baki amshi girkin bane har yanxu?" Tace "Make food for who?" Yace "For the entire house" tace "Ohk let me make this clear captain, ko wacce ta dinga girka abinda xata ci iya cikinta ko ranar girkinta ne ko ba ranan girkinta ba, idan ita ce da girki sae tayi har mijinta, yau da na amshi girki kuma ban yi maka ba ma sbda bani da lafiya!!" Ya dinga kallonta thinking if at all Aneesah xata iya canxawa daga yanda ya santa, duk da fa ba cikin fada take masa maganar ba, yace "Ke kika ajiyeni gidan nan ko ni na ajiyeki da xaki tsara min yanda xa ayi Aneesah?" Ta cire earpiece din kunnenta tace "Baxan kulaka muyi tashin hankali ba Captain, amma dai naga gidaje da yawa haka suke yi, ni idan na amince na ci abinda kishiya ta girka kana tunanin ita kishiyar xata yarda ta ci nawa? So u just have to reason it captain, shi yasa kawai na kawo wannan shawaran amma ba hukunci na yanke maka ba" Yace "Ki shirya in the next five minutes mu tafi asibitin" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta jawo wayarta da ta ajiye ta danna ma Chef salma kira, murya can kasa tace "Ke ya ake ciki ne wai shiru shiru har yanxu?" Chef Salmah tace "i am almost done my dear, ya xa ayi tahowan da shi kenan?" Aneesah tace "Probably yanxu xa mu fita hospital da shi...." Salmah tace "Tooo har da amaryar xa ku dugunzuma xuwa hospital din?" A takaice Aneesah tace "Akan wani dalili? Shi ma baxai fara wannan haukan ba tunda ai ba girkinta bane" Dariya Salmah tayi tace "Goben dai xai koma aikin ko?" Aneesah tace "Eh" Salmah tace "Yana tafiya xan shigo in Allah ya yarda, akwai magananganu da yawa ke dai" Aneesah na kyabe baki tace "Wai ki ji shigowa yayi yanxu wai ina abinci, ni kuwa nace kowa yayi nasa" Salmah tace "Kika gaya masa haka??" Aneesah tace "Eh mana" Salmah tace "Amma wani lkcn idan kin yi wani abun kamar warce bata ta6a shiga aji ba wllh Aneesah, ta ya xaki gaya masa haka bayan ga chatting da mu ka yi dake daxu?" Aneesah ta xaro ido tace "OMG na mance wllh..." Tsaki Chef Salmah tayi tace "Sai ki nemi yanda xaki gyara tunda kika bata, haba a gama magana dake kawai ki shigo da wani salon da xai 6ata, ni dai gaya min inda xa a bar maki abubuwan idan kun fita" Aneesah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kawai idan an kawo a xagaya a kai min ta kofar baya kawai a ajiye i will stock dem all in the freezer idan mun dawo daga hospital din cikin dare" Chef salmah tace "Ohk to, sai dai na shigo goben" Aneesah tace "Toh ki shigo da wuri don Allah gobe xa a kawo min furnitures, i have to borrow ontop of wanda kika ara min fa wllh..." Chef salmah tace "Sai dai na shigo din, kar ki wani damu" Daga haka suka yi sallama, Aneesah ta mike a hankali bayan ta ajiye wayar, wani kayan ta sauya ta cika turare ta dau karamin veil dinta da handbag ta fito ta kulle rubabben dakin nata da makulli tana ma kofar dakin Jiddah wani kallo, tun bayan da aka gama jera mata furnitures din ta koma dakin, sauka downstairs tayi taga Abuturrab xaune alamar ita yake jira, bayan ta shigo parlon ya mike ya wuce sama ta bi sa da kallo, dakin Jiddah ya bude ya ganta xaune saman darduma, ya xauna gefen gado yana kallonta yace "Me xaki ci Baby?" Wani iri ta ji sunan, ta dai daga manyan idonta ta kallesa, yyi mata murmushi yace "Yes tell me duk abinda kike so" a hankali tace "Anything" Ya d'an shafa kansa yace "Ohkk xan je in siyo yanxu in dawo" a hankali tace "Allah ya tsare" Ya sakar mata murmushi yace "Ameen" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta kwantar da kanta jikin gadonta a hankali, Aneesah na ganin saukowarsa parlor ta koma sama, ya bi ta da wani kallo yace "Kin san kina bata min lkci kuwa?" Tace "One minute" tana haurawa sama dakin Jiddah ta bude ta shiga dakin tana tsaye daga bakin kofa tana kalle kalle, Jiddah tayi mata kallon mamaki, Aneesah na murmushi tace "Pls ki d'an ara min body spray dinki i couldn't get access to mine sbda yanayin dakin..." Jiddah ta nuna mata gaban mirror dinta, ta tafi ta dau kala uku ta feshe jikinta da shi sannan ta juya ta kalleta tace "Thank you dear" Daga haka ta fita Jiddah ta bi ta da kallo, Bayan few seconds ta mike ta nufi jikin window tana kallon waje, sai ga Abuturrab ya nufi parking space din Aneesah na biye da shi a baya, yana shiga driver seat ta bude gaba ta shiga, kallonsu take ko kiftawa babu har ya ja motar suka fita compound din, sauke idonta tayi ta nufi kofa ta sa makulli ta bar makullin a jiki ta tafi ta kwanta gefen gado ta rufe har kanta da duvet. Sai da Abuturrab suka 6ata kusan 2 and a half hour a hospital din sbda series of test da aka yi ma Aneesah, ya so su wuce gobe ko ita ta koma ta amshi result din ta ki yarda wai ita gwara a tsaya ya fito a bata magunguna ko xata iya bacci yau, gaba daya hankalinsa na kan Jiddah sai kallon agogo yake, har karfe tara ya gota... wani kallo ya jefa ma Aneesah da ko ajikinta sai chatting take a reception din, yace "Yanxu meye amfanin haka Aneesah kina ganin karfe nawa yanxu kuwa?" Ta kallesa calmly tace "Kana da appointment da wani ne ko wata? Idan ma matarka ta can gida kake tunani naga dai ba girkinta bane ai, so ko kwana muka yi a asibitin nan girki na ne, lkci na ne... Sbda a ba a jikin ka ciwon yake ba shi yasa xaka axalxala haka kace mu tafi??" Dauke kansa yayi, ta hararesa ta ci gaba da chatting dinta, har ranta taji dadin wannan dadewar da suka yi a asibitin, sai kusan karfe tara da minti arba'in suka ga likita da test results din, magunguna kawai aka rubuta mata, bayan likitan ya sanar masu malaria din ma babu yawa a jikinta, kila tana stressing kanta ne kawai, shi dai Abuturrab fuskarsa a daure yake, ya mike ya amshi takardan da likitan ke basa na magungunan, Aneesah ta mike ta bi bayansa ranta fess, sai da Abuturrab ya siya mata duk drugs din a pharmacy din hospital din sannan suka fita, wani eatry ya tsaya yayi masu take away sannan ya dau hanyar gida, ba su suka shiga gidan ba sai kusan karfe goma da minti goma, Yana sauka motar bai tsaya ta fito ba ya kulle side dinsa yayi wucewarsa ciki yana rike da ledan abincin, ta bi sa da wani kallo ta kulle motar tana murmushi ta bi bayansa, dakin Jiddah ya nufa direct, ya murda ya ji a kulle knocking yayi nan ma no respond, juyawa yayi ya tafi part dinsa, Aneesah ta tsaya bakin kofar Jiddah tana kwankwasa tace "Jiddah, are u asleep, mun dawo ki bude ki amshi abincinki" Tana tsaye tana ta kiran Jiddah tana cewa sun dawo ga abincinta har ya dawo rike da spare key yana ganinta ya hade rai, ya sa makullin jikin kofar amma yaki buduwa sbda makulli na jiki ta ciki, Aneesah tace "Then probably she isn't hungry tunda ta kulle kofa don wanda ke jin yunwa xai jira har sanda aka kawo masa abinci" Tana fadin haka ta wuce dakinta, Abuturrab ya koma bangarensa, kasa cin abincin yayi shi ma, shayin ma da yake sha da daddare bai sha ba, yana kwance saman gadonsa karfe sha biyu saura bayan ya kashe wutan dakin Aneesah ta shigo sanye da kayan baccinta, rufe idonsa yayi as if sleeping, tsaff sai da jera duk abubuwan da Chef salmah ta bada a kawo mata a deep freezer dinta, tun daga soups kala uku, da stew me yawa, sannan ga danyen samosa da su spring rolls duk ta ajiye su a ciki, har da lafiyayyen jollof rice, da fried rice... kulle kofar dakin tayi bayan ta shiga ta tafi ta kwanta daga gefensa, duk da kamshinta da ya cikasa da abinda ya soma ji lkci daya, haka yayi ignoring yyi feigning bacci. Da ya farka cikin dare sai yaji hankalinsa ya tashi sbda wnn turaren Aneesahn amma ko kusa da ita xuciyarsa bai yarje masa yaje ba, amma wani lkcn cikin bacci sai ya ga kamar Jiddah ce a side din nasa sai yyi saurin kawar da thought din, dab da asuba yaji ta matso kusa da shi a hankali sbda dakin yyi sanyi tunda Ac a kunne yake, ya lumshe idonsa ya kai hannu ya ta6ata, Aneesah bata ta6a xaton bayan duk abinda Abuturrab yayi a wnn lkcn baxai kusanceta ba, infact mara lafiya ne kadai xai iya hakuri a wnn lkcn, haka kawai yaji xuciyarsa ya kasa yin hakan abun ya fita kansa lkci daya, ganin ya juya mata baya ta rikesa murya can kasa tace "Meye haka Captain?" Juyowa yayi, yayi kissing forehead dinta yace "I am only after the romance, nothing more" Daga haka ya mike ya shige bandaki ta bi sa da kallon mamaki. Yana dawowa masallaci da asuba ya murda kofar dakin Jiddah dake a kulle still, ya kwankwasa kofar ya tsaya for almost 3 mins bata bude ba, yayi kasa da murya yace "Meye haka pls Jiddah? Why are u doing this?" Bayan few seconds ya kara kwankwasawa bata bude ba, juyawa yayi ya koma part dinsa, shiryawa kawai yayi don gaba daya yaji ransa ya baci,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login