Showing 102001 words to 105000 words out of 346625 words

Chapter 35 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

ka taimakeni koh?" Ya d'an kalleta da sauri sannan yace "Haba?" Tace "Ehh, ko kuma in biya ma Umma" Murmushin gefen baki yayi yace "Ashe na taimake ki?" Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali, Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the silence yace "Bayan awaran da dankali babu wani sana'ar da xa ki yi?" Ya d'an kalleta da yaji bata amsa masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa, xagawa yyi ya bude side dinta ya bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke, yace "Sakko" sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan xata wuce dakinta yace "Ki tabbatar kinyi sallah" Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma'ah Jiddah na idar da sallan asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace "Baki da hankali har yanxu bacci kike?" Tace "Aa nayi wanka na gyara dakin" Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace "Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?" Buda baki tayi tana kallonsa tace "Ni yaushe nace baka da kudi?" Ya rungume hannunsa yace "Jiya a mota" Tace "Aa ni fa kudin jirgi nace baka da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??" Yace "Ehh abincin da kike ci ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh me yasa baka son kayi sana'a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci..." Kallonta yake ko kiftawa baya yi, tace "Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae" Ya shafa fine beard dinsa yace "Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana'an komai" Ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon tace "Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan kuma sai ka tafi kano, to ko sana'a kake xuwa yi a kanon?" Ya girgixa kai da sauri yace "Can ma kawai xama nake a gida, ai ba a bani sana'an da xan yi ba" Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace "Amma lkcn da kake xuwa hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?" Yace "Abbana ke bani" Tace "Toh, shkkn" Yace "Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan" Tace "Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka shago" Yace "Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?" Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me isarta tace "Dama mata na xuwa kasuwa?" Ya rungume hannunsa yana kallon large eyeballs dinta yace "Tunda xa su iya xaman gefen titi su siyar da awara da dankali me xai hana??"


*Toh Chamo dai tace banyi addu'ar Allah yayi min katangan rodi with some set of readers ba, duk da dai ra'ayinsu suke 6a6atu a kai nd they are entitled to der opinion, but oh God do not allow me to be seeing der comments so that i can write happily till end without mind spoilage Ameeeeenn* 🫣 to those of u reading my book for free know that u owe me dari biyar kacal ehe... 😚



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240


[6/11, 8:07 PM] +234 803 540 6041: Karfe hudu saura Abuturrab na xaune parlor wayarsa ya fara ring, kallon wayar ya dinga yi ganin Ahmad ne ke kiransa ya ki dagawa har ya katse, bayan few minutes ya ji wayar na ring kuma, dauka yayi xai yi silencing phone din ya ga Aneesah ce ke kiransa, sosai gabansa ya fadi, ya gyara xamansa da sauri yana kallon wayar har ya katse, ya lumshe ido hade da jinginar da kansa da kujera, mikewa yayi daga karshe walking slowly ya wuce sama, bude kofar dakin da Jiddah take yayi, da sauri ta dago kanta daga kan gwiwanta ta jawo ledan abincin, kallon idonta da yayi jajir sbda kuka ya tsaya yi, ta fara bude abincin ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, she looks sad and scared, karasawa yyi cikin dakin ya xauna kan stool din dake gaban mirror looking at her directly, kasa kunce ledan da abincin ke ciki tayi, cikin cool voice yace "Kukan me kike?" Ta girgixa masa kai kawai wasu hawayen na taruwa idonta ba tare da ta yarda ta kallesa ba still, yace "Tambayarki nake" Nan ma ta girgixa masa kai, shiru yayi yana kallonta, ta bude ledan abinci ta ciro ta fara ci a hankali, ya mike yace "Xan tafi masallaci, kafin in dawo ki tabbatar kin gama cin abincin" Ta gyada masa kai, ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita dakin... Ko kafin ya dawo ta rufe sauran abincin da ta rage, ba cikin dadin rai ta ci abincin ba, ko rabi bata iya ci ta kai ba, lemon ma bata bude ba tunda ba iya sha tayi ba, ruwa kawai ta sha, tunani ta shiga yi ko ta kai sauran kitchen kar ya dawo kuma yayi mata ihu, a sanyaye ta mike ta dau ledan abincin ta fita, kitchen ta shiga ta fiddo takeaway din abincin ta ajiye gefe daya, sannan ta ciro ruwa da lemon ta ajiye tana kallon ledan hannunta wanda bata san inda xata wurgar ba, window din kitchen din ta dinga kallo sannan ta karasa a hankali ta bude ta jefar da ledan ta kulle windown, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, babban ne kitchen din sosai, ga kuma store a ciki, cabinet din yayi kyau ba kadan ba sai dai babu komai a kitchen din sai electric heater da gas cooker, wanda bata ma san meye shi ba, sai fridge da deep freezer, a hankali ta juya xata fita ta gansa tsaye bakin kofar shigowa kitchen din ya rungume hannunsa yana kallonta, komawa baya tayi a tsorace tana kallonsa, ya nuna mata kofa wanda xai yi leading dinka to the back of the house, calmly yace "Bude kofar nan ki fita ledan da kika wurgar ki kwaso su" Da sauri ta nufi kofar tana murda makullin amma ta kasa budewa, karasawa yyi hakan yasa ta koma gefe da sauri, gaba daya a tsorace take, ya bude kofar ta fice, ledojin ta kwaso ta dawo ta tsaya bakin kofa tana kallonsa rike da ledan, ya karasa ya sa ma kofar makulli yace "Daga yau kada ki sake jefar min da komai wajen nan, don ba bola bane, ko kinga yayi maki kama da bola?" Ita dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, ya nuna mata wani waste bin a cikin kitchen din yace "Nan xaki dinga ajiye bola from henceforth" A hankali ta karasa shigowa ta saka ledojin a waste bin din, ya juya ya fita yace "Ki sameni sama" Bin bayansa tayi... ganin ya shiga dakin da take ta bi sa xuwa cikin dakin, gefen kofa ta tsaya bayan ta shigo, yana kallon tulin ledojin kayan da ta jera a kasa yace "Ga press can da xaki xuba kayanki" Ta kalli abinda yake nuna mata amma bata ce komai ba, yace "Yanxu xaki fara sa kayan ina gani...." Yana fadin haka ya ja stool ya xauna yana kallonta, ta karasa gun kayan ta bude, rasa ta yanda xata fara jera kayan tayi she look so confuse and Afraid at the same time, ta marairaice tana kallonsa amma bata ce komai ba, hakan yasa ya d'an yi tsaki bai ce mata komai ba ya mike, tun daga kananun kaya, undies, nighties, ya fara arranging dinsu a press din tana tsaye gefe tayi jigum tana kallonsa, har ya gama, ya bude akwatin da suka taho da shi jiya, atamfofin ciki dinkakku wanda baxa su wuce kala biyar ba ya ciro, linkin guga aka yi masu hakan yasa ya ajiye su cikin press din, da hijab biyu da suka rage suma gogaggu, sauran kananun abubuwan ciki duk ya samar masu maxauni cikin press din, gaban mirror yaje duk turarrukan ya jera su da mayukan shafawa da kayan kwalliya, lkci lkci yake kallonta ta madubin gabansa, Jiddah dai ta dinga kallon turarrukan da take ta tunanin su wa da su wa xasu dinga amfani da su haka da yawa, sun yi yawa sosai ba kadan ba, bayan ya tabbatar komai ya samu maxauni ya hade uban ledojin waje daya sannan yana kallonta ya nuna mata turarrukan yace "Kinga turarrukan nan?" Ta gyada masa kai, yace "They are not there for decoration?" D'an rufe idonsa yayi after he realized what he just spoke, sai kuma ya bude idanuwansa ya d'an hade rai yace "Kin gane abinda nace?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk, cewa nayi ba don jere na siya maki su ba, watanni kadan na baki duk su kare, idan kuwa basu kare ba xan sa sai kin shanye su, na siya maki ne don ki dinga amfani da su a kai a kai, safe, rana, yamma, dare, bbu takamaiman lkcn saka turare, sannan ba kadan kadan aka ce ki dinga fesawa ba, idan kinga dama xaki iya feshe gaba dayansu a lkcn daya, infact ba ma sai kin ga dama ba, haka nake son ki dinga yi, gaba daya xaki dinga fesawa a lkci daya, wata daya na baki in ga duk sun kare..." kai kawai take gyada masa, ya nuna mata body cream din yace "Wannan xaki dinga shafawa duk kika yi wanka, sannan wanka da safe, rana, dare.... kullum haka xaki dinga yi, ga sabulun nan xan kai maki bandaki, idan kina so ma xaki iya wanka sau goma a rana akwai enough ruwa a gidan" Nan ma ta gyada masa kai, ya hade rai yace "Ba ki gyada min kai kamar lizard ba malama, sau nawa nace xaki dinga wanka daga yanxu?" A hankali tace "Sau uku, idan ina so ma inyi sau goma" Yace "Idan ma baki yi ba ina da camera a gidan ai xan gani...." Xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Wanke baki kuma duk kika ci abu ki tafi bayi ki matsa MacLean ki wanke bakin ki, sannan ga na kuskura baki ma, bayan kin wanke bakin shi ma sai ki kuskure baki da shi, duk dare kada ki kuskura ki kwanta baki wanke bakin ki ba, da safe kafin kiyi alwala sai kin fara wanke baki, idan xaki yi wanka ki sake wankewa da safe... haka da rana sannan da yamma, ina son cikin sati biyu maclean dinki ya dinga karewa" Ta gyada masa kai, ya nuna mata mayukan gashi yace "Kullum sai ki shafa wannan a gashin ki, ki gyara..." Cikin sanyin murya tace "Toh" Nail cutter ya dauka gaban mirror din yace "Kinsan meye wannan?" Shiru tayi tana kallo, ya isa gabanta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta fara komawa baya a hankali, tsayawa yayi yana kallonta, lkci daya ya daure fuska yace "Meye haka?" Taki kallonsa gabanta sai faduwa yake, yace "Baxa ki dago kanki ba" Da kyar ta dago kanta amma ta kasa kallon cikin idonsa, ya daura nail cutter din a kan finger dinsa wanda babu farce yace "Shi ake yankewa da, duk ranan juma'ah ki tabbatar kin yanke faratanki, kar ki kuskura ki yarda in ga farce a hannunki, bana son ganin haka..." A hankali ta gyada masa kai, yace "In ga hannunki" a hankali tayi masa stretching dogayen fingers dinta wanda ita ma bbu farce, lkci daya kuma ta sauke kasa, ya dau shaving stick dake cikin leda yana kallonta yace "Kinsan wannan?" Sau daya ta kalli abinda yake nuna mata, ta Smsunkuyar da kanta, yace "Duk Jumma'ah xaki dinga amfani dashi shi ma" ita dai bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Sabulu ya dauka da Listerine mouthwash ya nufi bathroom, da ido ta bi sa, xai shiga ya juyo ganin bata taho ba yace "In dawo in dauko ki ne??" Da sauri ta bi sa, wajen da xata ajiye towel dinta ya nuna mata, ganin undies dinta da ta wanke a bandakin yace "Xa a sa maki igiya a baya, daga yau kada ki sake shanya a nan ki kai rana, nan ba wajen shanya bane, am i clear?" Ta sunkuyar da kai a hankali tace "Toh" da ido ya bi bandakin ganin it's clean ya juya ya fita ta bi bayansa, ya jingina da bango ya rungume hannunsa yace "Kinsan abinda yasa nake nuna maki duk abubuwan nan?" Ta girgixa masa kai tana kallonsa, yace "Saboda ba lallai wani abun ya sake hadamu a gidan nan ba, ba lallai ki sake samun privilege din tsayawa waje daya tare da ni ina maki bayani ba, ke kadai xaki dinga rayuwarki gidan nan babu wani da xai xo balle ya nuna maki wani abu shi sa nake bata lkci na yanxu, kina da ikon shiga ko ina a gidan nan amma banda bangarena.... sannan idan ina gari ba ke ba fitowa daga dakinki, kwana biyu xuwa uku kawai nake yi a kaduna shi ma sai karshen mako, don haka a wannan lkcn iyakar ki dakin ki, sai kuma probably kitchen, sannan baxan lamunci ki bar min gida da kazanta ba, kullum ki tabbatar kin yi shara kin yi mopping kin goge ko ina, nasan kin ga yanda ake yi a gidan Umma, tunda kin fi sati a can" Ji tayi hawaye ya kawo idonta, ta daga kai tana kallonsa, ya hade rai yace "Kin ji abinda nace?" Gyada masa kai tayi tana kokarin ganin hawayen bai karasa xubowa ba, Ya rungume hannunsa yace "Gobe xan koma wajen aiki, kafin in tafi xan siyo kayan abinci da komai da xa ki bukata a kitchen, don haka duk abinda na gaya maki yanxu baki da wani da xai sake gaya maki a gidan nan, it's better ki tabbatar kin gane komai...." Kallonsa kawai take tana jin wani kuka xai taho mata, ya ki yrda ya hada ido da ita, ya daga kafada kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta sauke idonta a hankali wani hawaye me xafi ya shiga sakko mata. Abuturrab na dawowa daga masallaci da magrib ya shigo da abinci, sama ya haura ya kwankwasa kofar sannan ya bude, tana xaune saman darduma, ya ajiye mata abincin bakin kofar, ya d'an tsaya wanting to ask what she is even reciting in her prayers, sai kuma kawai ya fasa, ya ta6e baki yayi wucewarsa, karfe tara da rabi ta gama saka kayan da ya nuna mata yace ire irensu xata dinga sa wa da daddare, wando ne dogo da riga, sosai kayan ya mata kyau tana tsaye gaban madubi ta saka daya daga hulunan da ya siyo mata, har makogwaro ta dinga jin turarrukan da ta fesa abin ka da bata saba ba, ta nufi saman gado ta takure waje daya ta kwanta ta lumshe ido... Abuturrab ya fito daga bangarensa rike da lallausan duvet, kana ganin duvet din kasan me tsada ne sosai, kamshin turarruka ne ya gauraye ko ina na upstairs din, ya isa kofar dakin, ya fi second biyar a tsaye kafin ya bude, ko motsi bata yi ba alamar ta fara bacci, ya karasa ciki ya bude duvet din ya rufeta da shi, da sauri ta bude ido, yana kallonta yace "Daga yanxu idan xa ki kwanta ki dinga kashe wuta" Ta gyada masa kai, gun switch din ya nufa ya kashe wutan dakin sannan ya fita ya kulle kofar dakin, Jiddah ta lumshe ido gabanta na faduwa don bata saba kwana ita kadai ba. Washegari Abuturrab ya tabbatar duk wani abinda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login