Showing 225001 words to 228000 words out of 346625 words

Chapter 76 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

xo" Abba na kallonta ya dau wayarsa yace "Toh Allah ya sa lafiya, in taso ne?" Tace "Ehh" tana fadin haka ta tashi ta fita, Abba ya mike ya bi bayanta, can kofar gida suka fita tana kallonsa tace "Yanxu Alhaji an xaunar da ita yarinyar an tambayeta ko tana son auren nan da ake shirin kulla mata? Domin bata da kowa ba yana nufin bata da gata Alhaji, this is wrong wllh" Abba yace "Domin bata da kowa mu ma ba yana nufin xa mu cutar da ita bane, did you know this is a great privilege to her also? Ki duba fa wanda ake son hadata aure da? Wa kike tunanin Hajja xata yi ma hakan banda ita din??" Umma tayi wani murmushi tace "Wato privilege? But she never begged for that privilege Alhaji, idan kuma xa ayi adalci kamata yyi a ji ta bakinta don a fita hakkinta, an ta6a yi ma mutum dole a aure? Shkkn sai aka ce ita bata da choice da dream dinta?" Abba ya duba wayarsa jin shigowar message yana dubawa yaga message din Abuturrab, and the content goes as thus "Kada ya kasance ana neman Aure ne a kan Aure Abba, that is highly prohibited in islam.... We plan but Allah plans best in sha Allah" Abba ya karanta text din ya fi sau uku, can ya mika ma Umma dake kallonsa, Umma ta amsa tana dubawa ita ma dai sau ukun ta karanta tana sake duba sender din, a ranta tace Aliyu?? A fili kuwa tana kallon Abba tace "Shashasha, to me yake nufi da text din? Wa ake nema ma aure a kan aure?" Abba yace "I am still trying to understand that too" Umma tace "Ka kirasa" Ba shiri Abba ya hau kiransa amma ya ji layin a kashe, ya kira sau uku duk a kashe, Umma tace "Wai wa yake nufi ne?? Wa ake nema ma aure kan aure?" Abba yace "Tare mu ka karanta text din nan yanxu Hajiya Ramlah" Umma tace "Toh ina jin shaye shaye ya fara a can din ko" Abba dai bai ce komai ba, Umma tace "Ni dai na gama magana, idan xa ayi mata adalci ayi mata, a tunaninku gata xa ayi mata tunda xa a aura mata d'an sarki, to amma kwanciyar hankalin xaman gidan auren fa, tunda naji ance uwar tasa ma ba so take ba, kuyi ma Allah a duba lamarin nan idan kuma shakkar yi ma Hajja magana ake ni sai inyi mata wllh" daga haka tayi ma Abba sai anjima ko gidan bata sake shiga ba ta bude motarta ta shiga, driving take amma tunanin solution da xata samar ma Jiddah take don in dai kuwa aka yi auren nan kilan bata doron kasa ne, samm baxata ta amince da auren ba, baxata ta6a bari a shiga hakkin yarinya ba. Abba na komawa cikin compound ya sa a kira masa Ummi, tana fitowa ya mika mata wayarsa yace "Ko xaki iya fahimtar wani abu a message din nan kiyi min bayani??" Ummi sai karanta message din take da surprise barin da ta ga cewar Aliyu ne sender din, can ta kalli mai gidan nata tace "What's the meaning of this?" Yace "Shine nake son ki min bayani" tace "Jiddar matar aure ce da xai ce kar a nemi aure kan aure?" Abba yace "Shine nake son fahimta Hauwa" Ummi tace "Ikon Allah, to ka kirasa" Abba na kokarin sake kiransa yace "A kashe wayar" sai gashi ance wayar a kashe, Ummi tace "Ji d'an rainin wayo, aurar da ita yayi ne ba a sani ba, ko ko?" Abba dai bai ce komai ba yayi shigewar sa ciki, Ummi ta bi sa da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunanin xata yi, anya kuwa Abuturrab na da kai? Menene manufar wnn text din wai kar a nemi aure kan aure, to ko aure yake nemar ma Jiddar basu sani ba ne. Abba na komawa gun brothers dinsa su ma ya basu wayar su duba message din, bayan sun duba da daddaya da daddaya, suka dinga kallon Abba, Alhaji Salmanu yace "Neman aure kan aure kuma? To ko dai bai saketa ba ne dama Alhaji Usman?" Abba yayi dariya yace "Ya fara hauka kenan, ai har yanxu takardan na nan bai je ko ina ba" Abba na fadin haka ya mike ya wuce daki sai gashi ya fito da takardan ya mika ma Alhaji Salmanu ya amsa ya karanta sannan ya ba duk sauran ma suka duba, Alhaji Salmanu yace "Ikon Allah, to me yake nufi da hakan? Is he even in his right senses?" Abba ya daga kafada yace "I thought as much" naxari duk suka yi shiru suna yi, Alhaji Umar yace "Try his line ko xai yi connecting" Abba ya sake kira yaji a kashe, Alhaji Lawal yace "Toh ko dai komawa yayi aka sake daura masa aure da yarinyar?" Kallonsa Abba yayi da sauri almost with shock, sai kuma yayi wani dariya yace "Aa he must be joking ashe, har ya isa ya sake yin hakan? Da kuwa nayi disowning dinsa wllh... Allah kuwa da ya ga the other side of me, wato ga yan iska ya ajiye, wllh in har hakan ne ya kasance Aliyu xai yi mamakina ainun" Alhaji Umar yace "Ikon Allah, that just dawn on me bayan Lawal ya fadi haka, in dai kuwa ba shi ya koma ya aureta ba to wani ya kai ya aureta, don babu yanda xai turo wannan message din idan ba dayan biyun abinda na fada ya kasance ba, but that's bad... Who does that, ya maida mutane kananun mutane kenan yake nufi ko me?" Abba dai da alama ransa idan yayi dubu ya baci, daukar wayarsa yayi ya tura ma Abuturrab text kamar haka, "call me immediately after switching on ur phone, i said immediately!!!" Alhaji Lawal yace "Lallai kuwa tunda har ya turo message din nan Komawa yaron nan yayi aka daura masa aure da yarinyar ba tare da sanin kowa ba, tunda ya san waliyanta sannan tun farko shi dama babu wanda yayi masa waliyyanci a cikinmu, don haka abu ne me sauki garesa" Abba dai baya cewa komai a parlon...
Har bayan sati da text din nan wayar Abuturrab a kashe yake, Jiddah na xaune daki tare da Maimoon da daddare tana son mata magana amma ta kasa, don bata ma san ta ina xata fara maganar ba, tun 3 days ago maganar ke cin ta amma ta kasa yi mata shi, can dai ta dake a hankali tace "Maimoon ya jikin Ya Aliyu?" Maimoon ta kalleta tace "Wllh I don't know, I can't reach him for a week now" Jiddah tace "Both Whatsapp?" Maimoon tace "Baya hawa...." Jiddah bata kuma cewa komai, Maimoon dai sai kallonta take, mikewa tayi ta koma side din da take kwanciya tayi kwanciyarta.... Ranan Friday bayan an sauko sallan Juma'ah, Jiddah na xaune xaune bakin tap din compound din gidan tana wanke hijabs dinta biyu don Safiyya na wanki a washing machine aka bude gate din gidan, daga kai tayi a tunaninta Ahmad ne don in dai ya shigo kd ya kan fara xuwa ya gaida Umma kafin ya tafi gidansa, tun da ya shigo take kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, saukarsa kasar kenan kuma babu inda ya fara nufowa sai gidan Umma......


My strength ends here wllh... Thank you!!


*Wa enda nake bi dari biyar su ji tsoron Allah su xo su biya bashi su sauke nauyi ko ince hakki!! alfarman wannan ranaku da muke ciki, domin fatan yin ibada amsasshe... Allah ya amshi ibadunmu ya sa muyi sallah lafiya Ameen*


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697





Jiddah ce ta fara dauke idonta ta ci gaba da wankin da take a hankali, har ya wuceta sannan ta bi sa da kallo ta durkusa tana ci gaba da daurayan hijabs dinta, bayan minti goma ta gama ta shanya su sannan ta dauraye hannunta ta wuce cikin gidan, Xaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, su Maimoon na daki Umma ma na bedroom dinta, Huraira kuma na kitchen tana girkin lunch, ta karasa cikin parlon tana kallonsa a hankali tace "Sannu da xuwa..." Kallonta shi ma yake yace "Kema sannu" Xata tafi dakin Umma taji yace "I will be back later" Ta juya tana kallonsa, mikewa yayi ya nufi kofa ita dai tana tsaye har ya fita parlon. A hankali ta nufi dakin Umma ta yi sallama sannan ta bude, Umma na xaune tana waya, Jiddah ta xauna saman carpet ta jira har ta gama ta ajiye wayar, Umma na kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Tace "Aa dama xan tambayeki sanda xa ayi awaran da kika ce ne" Umma tace "Au kinga ma na mance ni, duk sanda kika shirya ba matsala ki xo ki amshi kudin ingredients din, ke da Huraira ko Maimoon ku tafi kasuwa" Jiddah tace "Toh Umma" Daga haka ta mike ta fita daga dakin. Abuturrab na isa gidansa ya sauka daga d'an sahun da ya kawo sa, sai a sannan ya tuna ba shi da currency din kasar a tare da shi, ya nufi gun Mai gadinsa da ya taso yana welcoming dinsa da fara'a, yace "Ka basa dari biyar idan kana da shi" Mai gadin ya taho gun Mai adaidaitan da sauri xai basa kudin Abuturrab ya shiga cikin gidan, the compound looks so neat saboda yayi employing masu shara da gyaran flowers da ba su ruwa, yana isa entrance din shiga parlon ya murda kofar gently ya shiga ciki, kida ne ke tashi an kure sa har kusan karshe a parlon, ya dinga bin parlon that looks very untidy and unkept da kallo, ga plates sun fi kala biyar a kan carpet da duk ya baci da shinkafa da kwallin lemo, kayan kallon da suka yi uban k'ura ya dinga kallo, ya kalli dining area can ma duk plates da cups ne da breads ko kulle ledan ba ayi ba, calmly yake tafiya ya nufi stairs, shi ma duk yana jin yana taka k'ura kasan tiles din, bangarensa ya tafi ya bude kofa, sun fi su bakwai xaune parlonsa nan din ma dai plates ne da kwalaye na ciye ciyen da aka yi, suna ta labari ga kida na tashi a parlon ma amma bai kai na parlor ba, Duk suka juya jin an bude kofa, Aneesah dake xaune kan carpet sanye da zani da ves a jikinta ta mike da mugun mamaki tana kallonsa tace "My Captain saukan yaushe babu notice? Mun fa yi waya jiya baka ce min kana tasowa ba" Bai sake kallonta ba balle ta sa ran amsa ya bude kofar bedroom dinsa, Safara'u dake parlon ita ma da daurin kirjin ta mike da sauri tana cewa "In ji dai bai gan ni ba??" Bata jira an bata amsa ba ta fice da sauri daga parlon, Kawayen Aneesah duk biyar din su ma suka mike suka bi bayanta suka bar Aneesah tana xaxxare ido tana bin parlon da yayi kaca kaca da kallo, gashi takasa bin sa cikin bedroom din, Abuturrab ya fi minti biyu tsaye yana bin bedroom din nasa da kallo, kaya ne ta ko ina a xube tun daga kan gado har kasan tiles da carpet, bayan kaya har da takalma, ga farin bedsheet din saman gadon har ya fara fita hayyacinsa duk ya yamutse, sababbin jakunkuna na kayan sa wa har uku ya gani jere a dakin su ma duk a wangale, tun da yake bai ta6a sanin bedroom na iya xama haka ba sai ranan, wannan ya wuce untidy ko unkept, har wani tsami tsami mara dadi yaji bedroom din ke yi, ga kofar bandaki a hangame, ya lumshe ido ya juya ya bude kofar
ya fita, har sannan Aneesah na tsaye sai wuwwurga idanuwa take, bai kalli direction dinta ba ya fice, wani dakin daban ya tafi ya bude ya ga Safara'u xaune saman gado wanda shi ma din duk a yamutse yake, har lkcn daurin kirji tayi, ganin sun hada ido ya gaisheta, bai jira amsa dogon gaisuwan da take jere masa ba bayan ta jawo zanin gado ta yafa, yace "Alhmdlh mun gode Allah" Daga haka ya fice ya kulle mata kofa, wani dakin ya bude ya ga kawayen Aneesah sun yi dai dai a dakin ya kullo kofar ba tare da ya amsa gaisuwansu ba, bai sake bude wani dakin ba ya sauka downstairs ya fice daga gidan gaba daya, Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kofar gida gashi babu cash a jikinsa babu Atm card, luggages dinsa kuma bai dauko daga airport ba, wayarsa ya ciro daga karshe ya shiga kiran layin Maimoon, tana dagawa bayan sun gaisa yace "Give the phone to ur frnd" Maimoon ta mika ma Jiddah dake gefenta waya, Jiddah ta amsa tana duba me kiran kafin ta kai kunne, Maimoon ta fita daga dakin, Jiddah tace "Ina ji" Yace "Did u tell them i am back?" Ta girgixa kai tace "Aa" Yace "Ohk, kina da cash wajen ki?" Ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Aa sai a account, wanda Ya Ahmad ke sa min saboda makaranta" Calmly yace "Ohk ki bar wayar a wajenki..." Bai jira tace komai ba ya katse wayar ya karasa bakin titi, ya samu adaidaita ya koma gidan Umma, bai bari ya shiga can cikin layin ba ya sake kiran Number Maimoon, Jiddah ta daga, yace "Ki kawo min Atm card dinki waje yanxu" A hankali tace "Toh" ya katse wayar, ta mike ta dau jakarta ta cire atm card din ta mayar ta ajiye sannan ta dau gogaggen Hijab dinta ta saka ta bude kofa a hankali ta leka parlor bata ga kowa a parlon ba hakan ya sa ta fito da sauri ta nufi kofar fita, har ta isa gate tana waigen entrance din gidan, tana fitowa kofar gida ta dinga kalle kallen inda xata gansa, daga nesan ya hangota ya sauka daga kan adaidaitan, hakan ya sa ta gansa, ta karasa inda yake tana tafiya a hankali, idonsa na kanta har ta iso, ya sauke idonsa ya amshi Atm card din yace "Pin?" Ta gaya masa, yace "Thank you" daga haka ya shiga adaidaitan yace su tafi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. Abuturrab na cire kudin ya tafi yyi lodge a hotel, yana shiga dakin da aka bass ya kashe wayarsa, bayan ya huta yayi ordering abinci, Ana la'asar kuma ya fita xuwa airport don daukan luggages dinsa ya dawo hotel din a taxi, ya shiga da kayan ciki, bai sake fitowa hotel din ba sai da aka kira magrib ya fito yin sallah, bayan sun idar ya siya fruits ya koma cikin hotel din.... Washegari Asabar karfe tara ya kunna wayarsa ya shiga kiran Ramlah, tana dagawa da fara'arta tace "Yaya ka dawo ne?" Yace "Ahmad na gari?" Tace "Aa bai shigo ba satin nan, yace sai next week" yace "Ohk xan xo in amshi makullin motarsa yanxu" tace "Toh yaya sae ka xo" katse wayar yayi da yake ya shirya ya dau cash din da ya ciro jiya ya sa a aljihunsa sannan ya fita ya kulle dakin, a adaidaita ya isa gidan Ramlah, bayan ya sallamesa ya shiga ciki yana amsa gaisuwan mai gadi, ya wuce parking space, yana tsaye a nan ya shiga kiran Ramlah, bayan ta daga yace "Ki fito min da makullin parking space" tace "Yaya baxa ka shigo ba?" Yace "Ehh" tace "To bari in fito" ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motar, tana murmushi ta nufi parking space din ta risina ta basa tace "Ya hanya yaya?" Yace "Alhmdlh, ba sae kin ce masa na dawo ba" tace "Toh Yaya" bude motar yyi ya shiga yyi warming dinsa ita dai tana tsaye tana kallon sa, har daga karshe ta daga masa hannu ya fita da motar ita kuma ta koma cikin gida... Abuturrab ne xaune kansa a kasa yana sauraron uncle dinsa, Alhaji Lawal dake ta kallonsa da kyau yace "To ko dai kana shan wani abu ne wanda mu bamu sani ba Aliyu?" Shi dai bai ce komai ba, Alhaji Lawal yace "Dago ka kalleni ina maka magana" Ba musu Abuturrab ya dago kansa yana kallon Uncle din nasa, Alhaji Lawal yace "Tell me what exactly is wrong with u? Do we deserve being taking for granted Aliyu?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba ku yi hakuri, kuskure ne..." Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "You called this mistake also Aliyu?? Baka tsoron Allah ne da xaka kara kiran wannan ma da mistake??" Sake baki Alhaji Lawal yayi yana kallonsa, Abuturrab bai iya yace komai ba, Alhaji Lawal na jinjina kai yace "Lallai baka da hankali baka da manners, ka kuma mugun raina mutane ka daukemu for granted, ashe dama kai ka haifa kanka bamu sani ba?" Abuturrab yyi kasa da murya with remorse yace "Don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login