Showing 342001 words to 345000 words out of 346625 words
Chapter 115 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
min" amsar jakan hannunsa tayi tana murmushi tace "I missed u more dear... Abinci ko wanka?" Ya girgixa kai yace "Sallah" Tace "Toh mu je" Sai da yayi sallah sannan yayi wanka bayan ta hada masa ruwan wankan a bedroom dinsa, kafin ya fito ta ciro masa kayan da xai sa, sannan ta sauka downstairs ta dauko girkin da tayi xuwa parlonsa, xata shiga bedroom bayan ta gama hayowa da abincin suka kusa cin karo, sai taga ko kayan da ta ciro masa ma bai sa ba sai short, daukanta yayi kamar baby xuwa bed din dakin, ta marairaice masa tace "Dear ga fa abinci can..." Bai bata daman ta karasa ba, ya dinga ce mata yayi missing dinta so much, kamar yanda ya tara mata gajiya ita ma dai hakan tayi masa, bai ta6a tunanin da akwai sanda jiddah xata sake haka da shi ba balle har ta maida masa martani.... Sai bayan ya dawo magrib ta xuba masa abincin da ta girka masa, yana kallonta ta gefen ido yace "Ke dai fadi gaskiya Baby wannan abincin daga gidan Ummi kika taho da shi ko?" Murmushi tayi tace "Ae wannan ma da na ta6a xuba ma Colleagues dinka da dadewa ka kusa cinyewa baka sani ba... Shi ma ai daga gidan Ummi...." jawota yayi jikinsa ya matseta ya buda idonsa yace "Ni xa ki ma sharri?" Dariya tayi tace "Kai ka fara min sharri ai" ya lumshe ido yana murmushi yana shafa dogon gashinta yace "U are really a good cook wife, i know i am blessed... tun daga wannan ranan da kika xuba ma Colleagues dina abinci na dandana na san haka, i was stunned after tasting ur food that day, how possible i thought to my self many times" Tana murmushi tace "Saboda i am too local then ko?" Ya dago kanta yace "Daga sanda na raba ki da hayi kika bar locality dinki a can, u left that locality behind... Ban ta6a tunanin xaki fahimci abubuwa ki koyi abubuwa lkci daya ba jiddah, u were a fast learner... A iya xamanmu na farko I can't say ko na ta6a maki wani correction kan abubuwan da na koya maki" Ita dai murmushi kawai take, yayi kasa da murya yace "Tun daga sannan kika fara burgeni, when i notice u were always clean" Ta d'an saci kallonsa tace "Ashe ina burgeka" He couldn't help it but laugh, sai kuma ya rike kansa yace "Sosai Jiddah, in dai na barki a gida na tafi aiki bani da sukuni up in the sky sai na dawo gidan nan, i hate seeing u sad or worried hakan na karyar min da xuciya..." Ta kwantar da kanta kan shoulder dinsa tace "Kawai dai so na ne baka yi a lkcn ko??" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, kallonta taga yana yi babu ko kiftawa, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Na kan yi sha'awanki a lkcn" Ta d'an buda ido tana kallonsa tace "Wani iri" Ya lumshe ido yana shafa laps dinta yace "Irin wannan but i always try hard to fight it away, i always put in the back of my mind that i am just ur guardian" ita dai Murmushi kawai take, ganin ya ki daina abinda ya ke mata a kafa ta turo baki tana kallonsa, tuni taga idanuwansa suka canxa, ta marairaice tace "Ni wllh na gaji ko abincin fa ban ci ba..." Wannan fried rice din dai sai wajen karfe sha daya na dare aka ci sa, Abuturrab ne ya fara tafiya sama bayan ya wanke baki ya kwanta cause he is so very exhausted, ta gama wanke duk abubuwan da suka 6ata, ta sa turaren wuta ta jira yayi a parlon sannan ta kashe komai ta wuce sama, bedroom dinta ta tafi ta sake wanka ta wanke baki sannan ta saka kayan baccinta ta kashe wutan dakin ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa, can wajen karfe biyu Abuturrab ya koma dakinta ya kwanta because he can't resist sleeping without her close to him... Haka rayuwarsu ya ci gaba da gudana cike da so da kaunan kamar su maida junansu ciki, in dai yana gari bata da sauran sukuni har ma ta sa6a da kwarzabanta da yake, ya kuma yi programming dinta a yanda yake, ya maidata irinsa, shi yasa bata wani wahala ko gajiya da shi, kusan inda Abuturrab ya tafi wajen aiki ta kan shiga gidansu Hajiya Fatima har ma ta yini, Hajiya Dada kuwa duk bayan 2 days ko ita bata kirata ba ita xata kirata don Abuturrab ya siya mata exactly irin wayar da ya siya mata wanda Aneesah ta hade da kayan daki ta dagargazar, hka sauran Uncles dinta da aunt duk suna gaisawa a family group da aka sakata a ciki, she felt belong now, ko ba komai yanxu tana da wa enda xata nuna tace ai wa ennan dangina ne na jini, kowa a familyn ji yake da ita, sau dayawa idan Alhaji Ishaq ya shigo kaduna komai ya kawo ma su khaleesat sai ya raba dai dai da Jiddah ya bada a kai mata, hakan na yi ma Jiddah dadi sosai, jinsa take kamar mahaifinta na gaskiya, Hansai kuwa ta kusa sati uku yanxu a gombe wajen Hajiya Dada.... Yau duk da tasan Abuturrab na hanya sai duk ta kasa tashi tayi abinda ya kamata a gidan gaba daya wani kasala take ji tun da ya tafi ya bar ta, da ta yunkura xata yi aiki sai taji ta kasa sai dai ta koma ta kwanta, gashi gaba daya appetite dinta na cin abinci babu, ko a waya kuma bata sanar masa yanda take ji ba, ganin dai ya kusa shigowa ta mike da kyar tayi karfin halin shiga bandaki ta hada ruwan wanka tayi wanka sannan ta fito ta saka turare sama sama ta shirya, kwanciya ta koma tayi don taga alamar fa baxata iya ta6uka komai a gidan ba, tana jin shigowar motarsa bayan la'asar, ta daure ta kara mikewa ta sauko downstairs, dai dai nan ya shigo parlon karasawa tayi ta shige jikinsa kamar yanda ta saba in dai ya dawo, rike breathing dinta tayi sbda wani hautsine mata ciki da kamshin turarensa yayi, ta sa hannu ta rufe bakinta da hancinta, da mamaki yake kallonta yace "Baby me ya faru" Ta fara masa alamar amai na taho mata, da sauri ya ja ta xuwa bathroom dake parlorn, ganin yanda take aman yace "Oh my God baby dama baki da lafiya ne?" Ta kasa basa amsa sai sauke numfashi take, fitowa yayi da ita daga bandakin, ko minti biyar basu kara a gidan ba ya tafi da ita hospital, tun da suka shigo Aneesah dake xaune reception ta dinga rurrufe fuskarta tana kallonsu kasa kasa, shi kam ko lura da ita bai yi ba haka jiddah dake fama da kanta, bayan an duba Jiddah Abuturrab ya kasa boye farin cikinsa bayan likitan ya sanar masa tana dauke da ciki na sati uku, he felt like kissing and caressing her in public, he was so very happy, kasa daurewa yayi daga karshe ya rungumeta gam a office din likitan ya dinga sa mata albarka, sai bayan kusan 30 mins suka fito haraban hospital din yana rike da hannunta da few drugs da aka bata sbda amai da kasalan da take, gently yake tafiya da ita don bai son anything that will stress her, don ma cikin mutane ne da daukar abarsa xai yi baxata taka kasa ba, tun shigowarsu asibitin da minti goma aka sallami Aneesah amma ta kasa tafiya ta xauna karkashin bishiya a haraban asibitin tana jiran taga fitowarsu, tana ganin sun nufi mota ta mike a hankali ta nufesu, da farko Abuturrab bai ma ganeta ba sai da ya sake kallonta da kyau, ta dan yi murmushi tace "Good evening captain" Sosai gaban Jiddah ya fadi ta juya tana kallonta, yana bude ma Jiddah back seat yace "Evening Aneesah how are you doing, longest time" Tace "Alhmdlh" Jiddah ta shiga motar Aneesah na kallonta tace "Kwana da yawa Hajiya Jiddah" Jiddah tace "Alhmdlh" Rufe motar Abuturrab tayi dai sai kallonsu take ta cikin glass, ya bude driver seat yace "Toh ya aka yi Aneesah?" Tace "No dama gaisuwa ne" Yace "Toh nagode, baki da lafiya ne kika xo ganin likita?" Tace "Ehh" Hannu ya sa a aljihu ya ciro kudi masu yawa yace "Ohk take this little token" Ta dinga kallon kudin amma ta ki amsa, sai ta daga kai ta kallesa hawaye cike idonta tace "I just want to ask u for forgiveness..." Yace "Nahh I've done that long ago Aneesah, na yafe maki wholeheartedly, me yake damun ki kika xo gun likita?" Tace "Xaxxabi nake" Yace "Toh Allah ya sauwake... Allah ya kara lafiya, i need to leave now" Kai kawai ta gyada masa ya bude front seat ya shiga ya tada motar suka bar asibitin ta madubi yake kallon Jiddah ya ga yanda ta wani hade rai, yayi kasa da murya yace "Baby" ko kallonsa bata yi ba ta kauda kanta.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Jiddah ce xaune dakin bak'i tana yanka fruit din kankana a tray, xaune daga gefe daya kan darduma Hansai ce, Hansai tace "Ina ta son xan maki wata magana Jiddah" Jiddah ta daga kai ta kalleta ta dau tray din watermelon din ta ajiye a gabanta tace "Ina ji Baabarmu" Hansai tayi kasa da murya tace "Shekarun baya da dadewa akwai wata aminiyar mahaifiyarki ana ce mata Sadiya, baabarki tace min tun bata yi aure ba take tare da Sadiya hasalima Uwar sadiya ta san kakarki sosai ina jin kamar sun ma yi kawance, to a da dai Sadiya ta auri wani me rufin asiri a unguwan sanusi, don lkcn da Mahaifiyarki ma ta rasu wllh xuwan Sadiya uku tana son xata daukeki ta rike ki amma duk na hana, a xuwan karshe ma ba ta dadin rai ta bar gidana ba, nace kada ta sake dawo min gida, to wannan dalili ne yasa har yau bata sake waiwayo inda muke ba, to a lkcn har gidanta na sani a can unguwan sanusi don mun je sau uku da Baabarki a lkcn da take da rai, yanxu dai ban san ko tana nan har yanxu ba, ni nasan ko kadan ne Sadiya baxata rasa sanin wani abu a kan mahaifiyarki ko kakarki ba, xai iya yiwuwa ita Baabar sadiya sun ta6a wani hira da kakarki ta fada mata wani abun game da asalinku, shine nace kiyi ma mijin ki magana ko xa mu je gidan Sadiya idan yaga da halin yin hakan" Jiddah dake ta sauraronta tace "Toh Baabarmu xan masa magana in sha Allah" Hansai tace "Toh maa sha Allah...." Xaunawa Jiddah tayi don dama a durkushe take a dakin, Hansai tace "Aa tashi ki tafi gun mijinki ai dare yayi kuma haka" Jiddah tace "Xan jira idan kin gama in kai tray din kitchen" Hansai tace "Xan kai da kaina, ki tashi ki tafi sai da safe" Jiddah tayi mata sai da safe sannan ta mike ta fita... Xaune ta tarda Abuturrab yana operating laptop Little Jiddah na jikinsa tayi bacci, Ta cire Hijab din jikinta ta linke don dama tayi shirin bacci, ta xauna gefensa ta jinginar da kanta da shoulder dinsa tace "Dee" Jawota yyi jikinsa yace "Baby kina stressing kanki da yawa fa, u need housemaid seriously, kullum cikin gyara gidan nn kike ba dare ba rana" Tayi murmushi tace "Sai kace wani aikin duniya?" Kashe laptop din yayi ya kwantar da little Jiddah, ya jawota jikinsa yana kissing lips dinta, bata yi sanya wajen biye masa ba.... bayan an idar da sallan Asuba ya dawo masallaci ta basa d'an labarin da Hansai ta bata, ya d'an yi shiru sai kuma yace "Alright in the evening sai mu tafi tunda tace ta san gidan" Jiddah tace "Allah ya kai mu" A hanxarce Jiddah ta gama wanke few plates da aka 6ata a kitchen ta goge ko ina sannan ta fito tana kallon agogo, Abuturrab na xaune parlorn yana kallon wrestling ta nufesa ta xauna kusa da shi tace "Dee baka kira ayi fill din gas din ba till now" Ya jawota jikinsa yana kallon agogo yace "Sai mun dawo Baby, hope u are done now?" Tace "Eh na gama, ince ta sauko??" Yayi kissing din lips dinta yana murxa hannunta yace "Yeahh Baby" Mikewa tayi ta wuce sama, bude dakin da Hansai take tayi ta shiga ciki, Hansai na xaune kan carpet da Little Jiddah tana daure mata dogon gashinta da colorful ribbons, babu abinda wannan yarinyar ta mance bata dauka ba na ubanta, ko kadan bata kama da Jiddah ta ko ina sai ta beauty point da haskenta da ta dauko... Kyakkyawa ce yarinyar ta karshe, kamar er india, Tana ganin Jiddah ta 6ata fuska xata yi kuka, Hansai tace "Lah ji min yarinya wai ta 6ata fuska daga ganinki, lafiya fa nayi mata wanka na shiryata babu ko tari" Dariya Jiddah tayi tace "Baabarmu wai ki sakko mun gama" Hansai tace "Toh gani nan fitowa, dauketa ku tafi sai ki karasa daure mata gashin tunda ta fara haka baxata yarda ba kuma" Jiddah ta karasa ta dau daughtern nata ta fita daga dakin, dakinta ta fara shiga ta dauko Veil dinta da handbag sannan ta sauka kasa, Little Jiddah na ganin Abuturrab ta fara mika masa hannu tana masa dariya, she looks so happy seeing him, mikewa yayi ya amsheta yayi kissing Cheek dinta affectionately yace "I love u cute Mamina" rungumesa yarinyar da bata wuce shekara daya da wata bakwai ba tayi, Abuturrab ya mika ma Jiddah dake kokarin yafa veil dinta car key yana kallonta, ta xumburo baki tace "Aa ni baxan iya ba, kullum sai ka dinga min wayo kana bari na da tuki" murmushi yayi yace "Toh amshi er ki sai inyi driving din" Little Jiddah ta makalkalesa xata yi kuka, Jiddah ta rike ha6a tace "Dama idan xai koma aiki sai dai ya tafi da ke, baxai bar min ke ba..." Dariya Abuturrab yayi yace "Salon kiyi kuka idan na tafi da ita" Yana fadin haka ya jawota yayi mata side hug yace "Na lura kishi kike yi da Ummi na fa" Jiddah tace "Toh ba gashi baka da time dina yanxu ba sai dai nata" A tare suka fita parlon yana cewa "Ni ko nake da time dinki, during d day dama time din Mami ne, ke kuma throughout the night time dinki ne kinga equation balanced" Jiddah tayi murmushi kawai ta amshi car key din a hannunsa, Hansai ce ta fito daga parlor ganin makulli jikin kofa ta kulle sannan ta cire makullin ta nufi motar ita ma, duk da ba da sanda take tafiya ba amma har lkcn bata tafiya dai dai... Abuturrab na kallon Hansai ta madubi yace "Wani anguwan ma kika ce?" Hansai tace "Unguwan Sanusi" Suna isa gidan luckily har lkcn Sadiya bata tashi ba don gidan mijin nata ne, wanda shi ma ya rasu ya bar mata 'ya ya, duk da Sadiya bata ganesu ba, haka ta shimfida masu tabarma a tsakar gida tana bin su da kallo tace "Sannunku da xuwa" Hansai na murmushi tace "Hansai ce fa Sadiya naga kamar baki gane ni ba" Sadiya tayi shiru tana kallon Hansai, sai kuma ta mike da sauri tace "Hansan Amina?" Hansai na murmushin karfin hali tace "Ni ce Sadiya, kinga ga Jiddah nan" Sadiya ta saki wani salati tace "Jiddah er wajen Marigayiya Amina?" Sai kuma ta fashe da kuka ta dago Jiddah ta rungumeta tace "Allah sarki rayuwa, sannunku da xuwa Jiddah, ashe da rabon xamu sake ganawa Hansai, sannunku da xuwa, Allah sarki rayuwa" Hansai dai sai kirkiro murmushi take, Sadiya tace "Toh ina bibalo?" A hankali Hansai tace "Allah yayi mata rasuwa" Sadiya ta saki salati ta nemi waje ta xauna tace "Yaushe ni Halima?" Hansai tace "Yau kusan shekara uku kenan da rasuwanta" Sadiya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta mata Hansai, Allah ya ji kanta, wayyo rayuwa" Hansai dai ta sunkuyar da kanta, Sadiya tayi tagumi tana jimamin mutuwan Bibalo, Hansai ta dago tace "Dama mun xo gunki ne Sadiya tare da fatan Allah dai ya sa kinsan wani abu game da kakar Jiddah da mahaifiyarta" Sadiya tayi shiru, sai kuma tace "Toh, amma dai duk abinda ni na sani baxai kai wanda mahaifiyata ta sani ba, idan kun ga babu damuwa to mu tashi mu tafi gidan Mamanmu yanxu, tana nan anguwan ita ma" Hansai tace "Wannan ba damuwa bane" Fita suka yi gidan gaba daya suka shiga motar Abuturrab, Abuturrab ya gaida Sadiya dake gaishesa a back seat sannan ya nufi hanyar da tace masa ya bi, bai yi niyyar shiga gidan ba amma haka Sadiya ta matsa ya shiga ayi komai a gabansa kawai, babu yanda ya iya haka ya sauka ya kulle motar yana rungume da little Jiddah, duk da ba wani tsufa mahaifiyar Sadiya tayi ba amma yanayi na rashi da halin rayuwa ya sa duk ta wani yakune kamar warce ta shekara tamanin a duniya, bayan sun gaisa Sadiya ta gaya ma mahaifiyar tata abinda ke tafe da su, Mahaifiyarta ta dinga kallon Jiddah tace "Yanxu kuna nufin jikar Maijiddah ce wannan Sadiya?" Sadiya tace "Ita ce Inna" Inna ta girgixa kai tace "Allah me iko, ikon Allah ya fi gaban haka, Allah sarki rayuwa, Allah ya gafarta ma maijidda, Allah ya Rahama mata, Allah ya raya xuri'ar da ta bari" Duk suka amsa da Ameen, kamar yanda Hansai ta sanar ma Sadiya abinda ke tafe da su a can gidanta haka ta sanar ma Mahaifiyarta abinda ya kawo su, Inna tayi shiru sai kuma a hankali tace "Toh, ita dai Maijiddah