Showing 45001 words to 48000 words out of 346625 words
Chapter 16 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
dai Abuturrab murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Aunty ta mike ta nufi kofa bayan ta dau tray din da ta kawo ma Abba shayi ta fita, Abba na kallon Abuturrab yace "Hope babu damuwa Aliyu?" A hankali Abuturrab yace "Akwai Abba" Da mamaki Abba ke kallonsa, kafin yace "Talk to me, meye damuwar" Abuturrab ya kallesa lkci daya jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya yace "Abba i did something...." Sai kuma yayi shiru, Abba ya ajiye cup din hannunsa yana kallonsa da kyau yace "Feel free son, tell me what happened" Abuturrab ya sunkuyar da kansa nan ya sanar ma Abbansa komai tun daga farko, bai boye masa komai ba, Abba couldn't stop looking at him da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, Abuturrab ya xauna kan kneels dinsa a hankali feeling so remorseful yace "Kayi hakuri Abba, i neva thought things will turn out that way da ban yi komai gaban kaina ba, ban san haka lamarin xai kasance ba, i am sorry father, I don't know if this means failing you, kayi hakuri Abba..." Abba ya dafa shoulder dinsa ya sauke ajiyar xuciya amma kuma ya rasa ma abinda xai ce masa, da alama ya girgixa sosai da batun shi ma, Abuturrab yace "Xan iya kai ka gun mai anguwan ma so u can believe me 100%, ban ta6a xaton haka abubuwan xa su tafi ba da ban yi ba" Abba ya kara sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ka Aliyu, but this is astounding..." Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya dinga pondering kan lamarin, sai yake ganin abun kamar a mafarki, his son getting married babu shi, babu yan uwansa, infact unprepared marriage, hakan bai ta6a faruwa a xuri'arsu ba kaf" Abuturrab ya katse ma Abba tunaninsa ta hanyar cewa "Amma xan saketa Abba" Da sauri Abba ya kallesa yace "Why? Ba saboda ka taimaketa ka aikata hakan ba, xaka saketa saboda me kuma?" Da mamaki Abuturrab ke kallon Abbansa, can yace "Abba amma ai ni baxan iya xama da ita as a wife ba, i just can't Abba, she is not my class" Abba ya dinga kallonsa, Can ya girgixa kai yace "Dole hakan xaka xauna da ita kuwa, before making the decision of marrying her ai ya kamata ka fara naxarin ko xaka iya xama da ita din as wife or not, ka saki yarinya for what reason, i thought it's ur decision? Ko ka dau aure abun wasa ne, ka xata film ku ka yi acting a wajen ranan, ko kuma wasan yara ku ka yi?" Abuturrab ya marairaice hankalinsa a mugun tashe yace "Abba wllh kawai don in taimaketa a wannan moment din ne yasa na amince da auren ba wani abu ba, naga xa ayi ruining rayuwarta ne yasa na amince Abba, amma kuma nayi niyyar sakinta ai bayan daura auren" Abba na masa wani kallo on a serious note yace "Erase that harebrained idea right away, babu wani sakinta da xaka yi, tunda har aka daura auren shaidu duk sun shaida ka bada sadaki, babu wani abinda ya rage illa kayi accepting fact din ka tare da matarka, kada in sake jin ka yi xancen saki, ba drama ko film din Hausa kuka yi acting ba a wajen" Da mugun mamaki Abuturrab ke kallon Abban nasa baki bude, sanin arguing further won't favor him yasa yayi shiru, but deep down him yasan in har yana son ci gaba da rayuwarsa yanda yake yi a da to sai ya datse igiyar yarinyar nan a kansa, idan bai saketa ba he will never have peace of mind, he might even turn a Sadist, sakinta kuma da xai yi babu wanda xai bari ya sani, they will stay in the same roof but not as husband and wife, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Sai ka karasa gyara gidanka na nan garin ku tare, i will call all my brothers and inform them what happened, since u chose this for ur self" Abuturrab ya ji kamar yayi kuka sanin in har cousins da frnds dinsa suka ga cewar wannan yarinyar ce matarsa ai tasa ta kare kuma, he don't even want to imagine how they will make jest of him and even laugh at him, yayi narai narai da ido ya marairaice yace "Abba don girman Allah ba sai ka gaya ma kowa wannan abun ba pls I'm begging you Dad" Dariya ya kusa ba ma Abban nasa ganin yanda ya marairaice, wanda he couldn't help it but laugh, duk da kasancewarsa musulmin kwarai sannan dattijon kwarai ne kadai ya sa ya saduda yayi give up da wannan auren na d'an sa, amma banda haka shi da kansa xai iya sa Abuturrab ya saketa don har cikin ransa bai ji dadin wannan lamarin ba, Lkci daya idanuwan Abuturrab suka kada sosai ya kife kansa da kujera, Abbansa yaji tausayinsa ba kadan ba yana murmushi yyi patting shoulder dinsa cikin kwantar da murya yace "Abu me kyau kayi my son, and i am proud of you, Allah kadai ya san ladanka, kar ka damu it shall be well, Allah yayi maka albarka, and kada ka sake tunanin sakinta a ranka shine xai yi helping matters, ka xauna da ita tunda ka aureta, you won't regret it in sha Allah coz you've got a good heart, nasan wataran xaka yi alfahari da ita...." Da sauri Abuturrab ya dago ya kalli Abbansa da jajayen idonsa, ji yayi xaxxabi na neman kara rufesa, amma tunawa da yayi xai saketa ba tare da sanin kowa ba sai ya ji hankalinsa ya d'an kwanta, Abba yace "Xuwa yaushe xata tare din yanxu?" Abuturrab ya kalli Abbansa a sanyaye, Abba yace "Let me talk to ur mothers about it first, i hope they won't be disturb much..." Wayarsa ya dauka ya shiga kiran matan nasa, Abuturrab gabansa ya dinga faduwa don bai san yanda Umminsa da Aunty su kuma xa su dau lamarin nan ba, ba a dau lkci ba duk suka shigo, Abuturrab ya kalli Abbansa a hankali yace "Can i excuse my self sir..." Abba yace "Sure dear" Mikewa yayi ya nufi kofa walking slowly, Ummi ta bi sa da kallo, tun a shekaranjiya ta san abu na damunsa yana cin sa har cikin ransa, though tasan da kyar ya gaya mata koma meye da ya shafesa sai dai kishiyarta amma wannan karan ta lura ita din ma bai gaya ma ba, hakan yasa abun ya dameta sosai tun daga jiya bata da nutsuwa, don duk da baya gaya mata sabgarsa in dai xai gaya ma Auntyn da sauki, ko ba komai ita ma tana basa shawaran..... Aunty da ta bi sa da kallo tace "Alhaji ko ya gaya maka damuwarsa, tun safe nake fama da shi yace min ba komai, kuma nasan ba gaskiya bane, and this is so unlike him" Abba ya d'an sauke ajiyar xuciya yace "Kiran da nayi maku kenan yanxu" Duk suka maida hankali kan Abba don jin damuwar Abuturrab din.
*Tohm Khaleesat Haiydar dai bata Allah ya isa kuma baxata fara ba a kan littafin Jiddatul Khair, sannan nasan ni baxan iya hana fitar book din nan ba, kawai dai idan xaka yi ma kanka adalci if u should come across this book, keep it in mind that ba free book bane, littafin kudi ne, if u are willing to read just make ur payment ka sha karatunka ba wani shakku a ranka, and bana tunanin u will regret paying and reading this book in sha Allah....*✍🏻
_And i really appreciate my lovely fans patronage..... na samu sabbin fans da yawa da suka yi patronizing Jeedahh kuma naji dadin haka... Ina godiya da maku fatan alkhairi_ 🥰
The book is 500 via 3276052019
Fcmb
Hauwa Bello Jiddah... And u show ur evidence of payment via
07087865788....
Thank you.😇Mikewa Aunty tayi bayan Abba ya kai aya cikin tashin hankali tace "Ban gane ba Alhaji?? Are you for real? Shi Abuturrab din ne yaje ya daura ma kansa aure without our knowledge????" Abba yayi murmushin karfin hali yace "Dama mutum ya ta6a daura ma kansa aure, we just have to accept it Hafsah, it doesn't make sense though, to amma ya muka iya da lamarin ubangiji, Allah ya riga da ya tsara hakan" Ummi kallonsu kawai take ko kiftawa babu, wanda da alama duk ta fi su shiga shock din, Aunty ta dage hannu biyu sama tana girgixa kai da karfi tace "No wayyy, mu ba gantalallu bane gaskiya, yanda aka daura auren haka xai saketa wllh wllh, me xai yi da yar hayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yar hayi fa kace Alhaji?? To na rantse da Allah baxai yiwu ba" Wani kallo Abba ya dinga yi mata har tayi shiru tana huci kafin yace "Ja xa ki yi da lamarin ubangiji??" Aunty ta dalla masa wani harara ta nufi kofa rai bace tana cewa "Allah ya kiyaye, wllh sae ya saki wannan yarinya dai, banda fitinarsa ma ina shi ina shiga tsabgan talakawa mutan anguwan nan balle har wannan mummunan kaddararran ya fada masa, wllh saki kamar yayi sa...." sai kuma ta fashe da kuka ta fice ta rufe kofan, Abba ya kalli Ummi bayan kusan minti biyu da fitan Aunty jin taki cewa komai yace "Kinyi shiru Hauwa" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh me xance, jin abun nake kamar a mafarki ai, an ta6a aure haka dama Yallabai?" Abba yace "Gashi nan dai d'an ki yayi, kinsan babu abinda taimako baya sa mutum yyi, to kinga inda nasa taimakon yayi leading dinsa to" Ummi ta girgixa kai tace "Toh yanxu meye abun yi Yallabai? Wannan ai ba abun ayi shiru bane ayi ta kiran taimako, wani irin aure ne wannan kamar a wasan kwaikwayo" Abba yace "Meye kuwa abun yi banda ya tare da ita yarinyar, ai an riga da an daura aure, kuma lamarin aure ba lamarin wasa bane" Da mamaki Ummi ke kallonsa tace "Kana nufin haka xai yi rayuwa da ita? Ya tare da ita fa kace" Abba yace "Kwarai, tunda har an daura auren, ai yanxu matarsa ce ita din, ko ke wani shawara xaki bada a nan?" Ta girgixa kai tace "Haba Alhaji, a ina aka ta6a irin wannan auren, ni dai tunda nake ban ta6a jin irinsa ba ma, me xa muce ma 'yan uwa da abokan arxiki, me xa ace ma Hajja, ya kake ga xata dau lamarin nan? shi Abuturrab din shaye shaye ya fara da xai kai kansa ga irin wannan taimakon? Ba gwara ma ace yau kawota yayi gidan nan ba yace mana ga ta, ai babu wanda xai hanata xama gidan nan idan anyi bincike an gano gaskiyar lamarin, kuma baxa mu ki riketa ba, idan ma wani ya ki ni baxan ki ba ka sani" Abba yace "A takaice kema dai kin goyi bayan ya saki yarinyar kenan" Ummi tace "Toh idan bai saketa ba me xai yi, ai sakin kadai ne best solution a nan, ko a garin ga6a ga6a ba a irin wannan auren Yallabai" Abba yace "Toh duk kun yi kokari, amma ku sani auren nan bbu fashi tunda ba wani ya dau sadakin ya kai masa ba, da kansa ya aikata duk abinda ya aikata gaban kansa ba tare da ya duba cewa yana da iyaye da magabata ba, to don me xa ace sai yayi saki, tunda har ya amince aka daura masa aure da ita wllh dole ya amince ya xauna da ita, ba dai taimakonta yake son yi ba, gata nan sai ya taimaketa har karshen rayuwarta, nan gaba sai kiga ba shi ba har ke sai kiyi alfahari da ita a matsayin matar d'an ki, sannan a rayuwar nan there is reason for everything, Allah ya riga ya tsara hakan to mu a su wa da xa mu ce tsarin bai yi ba??" Mikewa Ummi tayi bata sake sauraronsa ba ta fice daga parlon, ya daga kafada yace "Yanda bai maku dadi ba nima lamarin bai min dadi ba ko kadan, but who am i to ask why tunda haka Allah ya tsara???" Aunty ce tsaye kan Abuturrab inda take shiga ba nan take fita ba duk ta hada xufa kai kace tayi wani tafkeken asara ne a rayuwarta, ko Salem ne yayi abinda Abuturrab yayi iyakan abinda xata yi masa kenan take ma Abuturrab, Abuturrab dai na xaune gefen gado ya rike kansa da yyi masa nauyi duk yana sauraronta ga wani bugawa da xuciyarsa yake, he just hate himself completely for this foolish mistake he made, me yasa bai yi duk wannan tunanin ba kafin ya aikata wannan shirmen, me yasa bai yi reasoning abinda xai biyo baya ba yayi abinda yayi?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kyar ya dago kai yana kallon Stepmum din tasa da idanuwansa da suka kada cikin sanyin murya yace "Wllh xan saketa Aunty, ba da dadewa ba kuma xan yi hakan, ni ko ba ace in saketa ba ma dama ba sa'ar aurena bace dole xan saketa" Aunty na huci tace "Toh uban me kake jira har yanxu? Mu xaka kwaso ma abun kunya a dinga nuna gidanmu a gari, wllh baxai yiwu ba ko almajiri baxa ayi masa irin wannan auren da kaje kayi ma kanka ba, aikin banxa kawai, ko yar cikin gari wllh wllh kafi karfinta balle yar kauyen hayi, to sai ta shigo gidan mu gani ai...." Tana fadin haka sai ta saki kuka ta fice daga dakin. Abuturrab ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, what has he done with his life, he wish he could wake up and see that all this is nothing but a dream, mikewa yayi a hankali ya karasa kofar dakinsa ya sa makulli don ma kar ta sake dawowa sannan ya dawo ya xauna ya dafe kansa hade da lumshe ido yana kiran Allah a ransa. Bayan azahar Abuturrab ya dau makullin motarsa ya fito daki, tun safe bai fito ba sai yanxu da yaje masallaci yayi sallah ya dawo, yana shigowa parlor ganin kallon da siblings dinsa ke masa yasan sun samu labarin kenan su ma, bai kuma kallonsu ba har ya fice daga gidan, ya hau motarsa ya bar gidan, gidansu Ahmad ya nufa, ko kallon matar mai gadi dake gaishesa bai yi ba ya nufi entrance din gidan, a yanxu dai komai haushi yake basa, underneath his breathe yayi sallama ya shiga parlon, Huraira ce da Siyama parlon, su ma bai sake kallon inda suke ba balle ya amsa gaisuwarsu, dai dai nan Ahmad ya fito daga wani daki dake nan parlon, ganin Abuturrab yace "I was planning on calling you now, welcome... Duk kayi scarce yau" Abuturrab bai ce komai ba ya nufi dakin Ahmad, Ahmad ya bi bayansa yana murmushi a ransa yana cewa the latest ango in town, xaune ya tadda shi gefen gado, Ahmad ya tsaya bakin kofa yana kallonsa yace "Ya ake ciki yanxu, hope it went well??" Abuturrab yace "Kamar yanda na fada, no much problem from Dad, but aunty took the matter tooo personal, Aunty tayi misunderstanding komai" Ahmad ya masa wani kallo yace "And so what? How about Ummi? Though she is here, daxu ta xo" Abuturrab ya xaro ido yace "Kana nufin Ummi na gidan nan?" Ahmad yace "Yea tana dakin Umma" Abuturrab ya lumshe ido ya bude, gaba daya abun duniya ya ishesa yanxu fisabilillah baxai farka yaga duk wannan abun mafarki bane, Ahmad yace "Amma Ummi tayi maka magana ne?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bata ce min komai ba har yanxu" Ahmad yace "Ka kwantar da hankalinka komai ya xo da sauki tunda Abba ya fahimce ka" Abuturrab yace "Ya fahimce ni?? Ai ni da abinda Abba ke ce min yanxu gwara ma ace bai fahimceni ba kwata kwata, Did you know that he is forbidden me from divorcing her?? Ce min yayi fa baxan saketa ba" Ahmad har xai ce dai dai kenan amma don kar ya sake provoking din d'an uwan nasa yayi fuskan mamaki yace "Toh fah, kar ka saketa kuma??" Abuturrab ya d'an ja tsaki a fusace fuskar nan tasa a murtuke, Can ya dago ya kalli Ahmad yace "Toh me Ummi ta xo ce ma Umma ynxu?" Ahmad yace "Don't know.... And least i forget, Jiddah bata da lafiya fa" Daga kai Abuturrab yayi yana kallonsa, Ahmad yace "Yea, ina mata karin ruwa, shine kaga na fito dakin dake parlor da ka shigo yanxu" Abuturrab dai bai ce komai ba, Ahmad yace "Dakin mai gadin baxa a rasa sauro ba, it's malaria symptoms...." Abuturrab na kallonsa yace "Kayi mata test ne? She just finished treating malaria few weeks ago" Ahmad yace "Yea it's possible she is reinfected" Abuturrab bai sake cewa komai ba, Ahmad ya juya yace "Mu je ka dubata" Abuturrab yace "It's not necessary" kallonsa Ahmad yayi yana ciro wayarsa dake ring a aljihunsa yaga Umma ke kiransa, ya kalli Abuturrab yace "Hmm Umma is calling" Daga kiran yayi ya kai kunne, bayan few seconds yace "Toh" daga haka ya katse kiran yana kallon Abuturrab yace "She's calling me to her room now" Yana fadin haka ya fita dakin ya tafi bangaren Ummar tasa, tana xaune bedroom dinta tare da yayarta ko wannensu fuska babu annuri, Ahmad yyi kasa da kai ya xauna nan kasa yace "Gani Umma" Umma na kallonsa strictly tace "Ahmad wacce yarinya ce Abuturrab yaje ya aura without acknowledging how stupid that will be?? Yanxu kana matsayin d'an uwansa ka yi shiru ka barsa ya aikata abinda ya aikata Ahmad??" Ahmad yayi kasa da kai a hankali yace "Wllh i knew nothing about that Umma, i swear to God ban san komai ba..." Umma ta daka masa tsawa tace "You are lying, ya xaka ce baka san komai a kai ba, akwai wani abu da Aliyu ke boye maka?" ya kalleta da sauri yace "Billah abinda ya sanar da ni jiya ne kadai nasani game da lamarin nan, a jiya nima nasan abinda ya aikata Umma"