Showing 210001 words to 213000 words out of 346625 words
Chapter 71 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
kanta ita Ummar, yo fitina mana... daga masarautan bauchi fa wayar ta fito ba ma kasuwa ba, to tayi ta kanta don babu wanda xai duba cewa kanwar Hauwa ce ita, hukuntata xa ayi yanda ya kamata" Babu dai wanda ya tanka Hajja, Tana bude goran ruwan hannunta tace "Yanxu ki tashi ki cire uniform mu je ki rakani gidan Aliyu, shi kuma ina ta jin jita jitan xai fita waje da wani babba a jirgi amma kun ga ni ai ya ki gaya min, ko da yake dai baxan biyesa ba, titin ma da ya yasar dani a hayi shekaranjiya ban gaya ma kowa ba, bakina alekum na dawo gida na shige daki na, tinda mu 'yan Masar dai da hakuri aka san mu..." Jiddah da duk hankalinta ya tashi ta dinga kallon Hajja ta ma rasa abinda xata ce, yanxu abu biyu ne ya dameta a rai, na farko Hajja tace wai an rushe gidansu, to me yasa xa a rushe gidansu su da ba a kan titi suke ba, ina babaarsu da Bibalo suka koma kenan yanxu?? Tunanin hakan yayi mugun daga mata hankali, na biyu kuma rakiyar da Hajja tace xata mata gidan Abuturrab, Ramlah ta mike ta tafi bandaki Hajja ta bi ta da kallo tana yamutse baki, tana dawowa daga bandakin ta kalli Jiddah da sauri tace "Tashi muje kada magariba tayi mana kin ji" Ramlah tace "Amma Hajja ai Ya Ahmad bai san xata fita ba, kuma babu kowa gidan sai ni kadai..." salati Hajja ta rafka tana kankance ido tace "Waye kuma Yaya Ahmad? Ina ruwana da shi? Me na hada da shi?? Kanin uban jiddan ne shi ko ko? Ku dai kun cika daukan magana wllh, shi yanxu ya isa hanata ta bi ni" Ramlah tace "Toh ai wajensa take dai yanxu" Hajja tace "Ja can ki ji da tsamin yawunki, ina ruwana da ke da Ahmad din, gashi nan ai ya hadaki da wahala kullum yana hanyar Abuja..." Jiddah ta kalli Hajja tace "Hajja ni fa ina da karatu gobe muna da jarabawa" Hajja ta dinga kallonta, can tace "Ni xaki walakanta ina yabonki sallah xaki kasa alwala?? Gidan jikana fa nace ki rakani ba gidan wani 6are ba, gidan nan kuma na samu labarin kin kusa wata uku a cikinsa, to meye don nace ki rakani xaki gatsa min wannan magana haka ba dadi" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta a ranta tana tunanin no amount of words can allow her go to Aliyu's house this evening, mikewa Hajja tayi ta dau jakarta ta nufi kofa, Jiddah taki yarda ta dago, Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce har Hajja ta fita parlon, Ramlah tayi kasa da murya tace "Ko dai xaki rakata don asirinmu ya rufu Jiddah??" Jiddah ta girgixa kai calmly tace "Ni baxan je gidan wannan matar tasa ba wllh, dama dai bata nan ne, kuma ba gwara ta sa a kira mata shi ya xo ba, amma sai inyi ta wani xuwa gidan mahaukaciyar a saboda me?? Baxan je ba" Ramlah sai kallon Jiddah take ganin yanda take maganar kamar she have grudges with Aneesah, murmushi Ramlah tayi tace "Ki dai yi hakuri, idan ya so kar ma ki shiga cikin gidan sai ki jira ta a waje" Jiddah tace "Na fa ce baxan je ba" Tashi tayi ta wuce daki Ramlah ta bi ta da kallo, sai kuma ta mike ta isa window tana lekan waje taga ko Hajja ta fita compound din, Tsaye ta ganta mai gadi na mata danne danne a waya alamar xai mata kira, Ramlah ta juya da sauri ta koma....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Bayan few minutes Ramlah ta sake komawa ta leka compound sai bata ga Hajja ba, wani ajiyar xuciya ta sauke ta wuce dakin da Jiddah take, tana cire Uniform ta sameta, Ramlah ta jingina da kofa tace "Toh Aneesah ta maki wani abu ne da baxa ki je gidan nata ba Jiddah?" Jiddah taki kallonta tace "Bata min komai ba, kawai dai baxan je bane..." Ramlah tace "Amma ai nace idan ma kin rakatan xa ki iya kin shiga kiyi tsayuwarki a waje har ta fito" Jiddah tace "Kofar gidan ma baxan iya tsayawa ba" Murmushi kawai Ramlah tayi ta juya ta fita daga dakin. Ranan Friday da daddare Aneesah na xaune parlor downstairs bayan Magrib tana kallon wani indian Series tana shan fruit salad, ta ji footstep ana saukowa downstairs din, daga kai tayi ta gansa yana sakkowa, lkci daya kamshinsa ya baxa ko wani lungu da sako na parlon, kafin tace komai yace "You still haven't pray Aneesah" Tace "I know, ina xaka je da daddaren nan haka Captain?" Ya shafa beard dinsa yace "Wajen Budurwa ta" tayi wani dariyar da bata shirya ba tace "Hmm, kar Allah ya nuna min wannan bakar ranan, ni fa kasan wani abu captain?" Yana sakkowa yace "Sai kin fada" tace "Wllh duk ranan da yau aka ce da gaske kayi wata budurwa Allah xan iya kashe koma wacece har lahira, sai dai nima a daureni...." Yana kallonta bayan ya sakko parlon yace "Toh duk ranan da aka ce nayi wani auren fa?" Ta kallesa kamar baxata ce komai ba don gaba daya mood dinta ya canxa, sai kuma tace "Wai ka auri wata matar a duniya bayan ni?" Yace "Ehh" Wani murmushin ta kuma yi tace "Gwara a bar xancen kawai Captain..." Sai kuma ta hade rai tace "Kasan Allah? Wllh wllh xan iya kasheta in kashe kaina sannan kai ma in kashe ka duk mu hadu a lahira" Da mamaki ya dinga kallonta ganin how serious she is, cikin bacin rai tace "Wllh duk ka bata min mood wnn xancen da kayi captain, mu fa kaf xuri'armu fa ba a mana kishiya wllh, Aunty Salaha ma da aka yi ma satin amaryar uku ta bar gidan babu wanda ya koreta" Shi dai Abuturrab kallonta kawai yake ganin da gaske ran nata ya baci sosai, D'an murmushi yyi yace "Sai na dawo..." Ta mike babu yabo babu fallasa tace "Wai ina xaka da daddaren nan ne?" Yace "Ban ma Umma sallama ba, daxu gida kawai naje" kauda kai tayi ta ta6e baki, sai kuma ta kallesa tace "Toh bari in saka hijab mu je tunda ban ta6a xuwa gidan nata ba dama" Yace "No, ni kadai xanje, duk ranan da kika shirya sai kije ki gaisheta" Da mamaki take kallonsa tace "Ban gane No ba, yanxun idan naje laifi ne?" Yace "Eh saboda sai da xanje mata sallama sannan kika san xaki gaisheta" Bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da wani irin kallo xancensa na sake yawo a kanta wai duk ranan da aka ce yayi wata matar fa?? Tabb shi me ma ya kai sa fadin wannan mugun xance, ai daga ita ya rufe aure har karshen rayuwarsa, ita ce first and last dinsa, shi din nata ne ita kadai, tsaki tayi ta koma ta xauna ta ci gaba da kallonta amma ba cikin dadin rai ba... Abuturrab na parking ya dau wayarsa yayi dialing number ya kai kunne, wayar na fara ring aka daga, ya amsa gaisuwarta yace "Ki turo ta ta amsar maku sako!" Ramlah tace "Wa xan turo yaya?" Yace "Warce ke gidanki" Kallon agogo tayi don anyi isha, sai kuma ta mike ta fita xuwa dakin Jiddah, Jiddah ta gama sa kayan baccinta kenan tana shafa turare kafin ta dau takardanta ta fara karatu saboda exams da take da shi gobe Ramlah ta shigo, tsaye Ramlah tayi bakin kofar tana kallonta, Jiddah ta ajiye turaren hannunta tace "You need something?" Ramlah tace "Wai sako xaki amso a kofar gida" Jiddah ta dinga kallonta tace "Sako kuma? Sakon me? Kuma wajen wa?" Ramlah tace "Ya Aliyu" sosai gaban Jiddah ya fadi jin sunan da Ramlah ta ambato, Jiddah ta girgixa kai tace "Sakon me da daddaren nan, maimakon kice ya shigo da shi ki amsa don Allah, ji fa karfe nawa" Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce, Jiddah ta tafi ta dau takardanta ta xauna gefen gado, irin ita baxata je din nan ba, wayar Ramlah dake hannunta ne ya fara ring, ta daga ta sa handsfree tana kallon Jiddah, daga daya bangaren yace "Kuna bata min lokaci" Ramlah ta d'an fara kame kame, sai kuma tace "Yaya ko dai in fito in amsa ni? ita naga ta kwanta ne" Calmly yace "Taso ta" Tace "Wai dama exams..." Katse ta yyi yace "Ki taso ta nace" a hankali tace "Toh Yaya" ya katse wayar, Ramlah ta kalli Jiddah da ta 6ata fuska kamar xata yi kuka jin duk abinda yace, cikin rawar murya tace "Bayan ya Ahmad bai sani ba xan je kofar gida amsan sako, to gwara ki kirasa ni dai" Ramlah ta xaro ido tace "Ince masa me, salon ya kira yayan?? ke dai kawai ki sa hijab dinki ki daure kije kiga sakon meye" Jiddah ta girgixa kai da kyar tace "Ni baxan iya fita ba wllh, dubi fa agogo" Ramlah tace "Toh me kike so in ce masa bayan kinji yanda muka yi da shi Jiddah" Jiddah ta kwanta kan gadon ta lullube tace "Da gaske fa ni baxan je ba kawai ki kashe wayarki gaba daya, tun da rana me yasa bai kawo sakon ba" Ramlah dai ta rasa abun cewa tana ta tsaye, sai ga kiransa ya sake shigowa, ta xaro ido tace "Na shiga uku Jiddah ki rufa min asiri ki tashi kije, ni dama ba ni ya kira ba, bakin gate ne fa kawai xaki tsaya ya baki sakon da yace ki juyo ki shigo, wllh ban san kuma me xance masa ba idan na daga kiran nan" Ganin ya kusa katsewa ta daga tana rawar baki tace "Yaya na kuma ga tana wanka ne..." Yace "Ramlah" ta xaro ido tace "Na'am yaya" Yace "Mika mata wayar" karasawa tayi ta ajiye wayar kusa da Jiddah tace "Ga ta" Jiddah tayi narai narai da ido tana sauraronsa, yace "Fito ki amshi abinda nace yanxu, minti biyu na baki..." daga haka ya katse wayar, Jiddah ta mike xaune har hawaye ya kawo idonta, Ramlah na lallabata tace "Ki daure ki je pls Jiddah ai nan da kofar gida ne, kawai yana mika maki sai ki shigo kin ji" Mikewa Jiddah tayi daga kan gadon ta bude wajen kayanta ta dau hijab har kasa ta saka sannan ta fita, tun da ta isa gate gabanta ke faduwa, tana fita taga motarsa ta karasa tana tafiya slowly ta tsaya kusa da motar ta tsaya, sauke glass yayi yace "Shigo ki amsa" kamar xata yi kuka tace "Don Allah ka bani a nan, wllh ya Ahmad...." Yana kallonta directly in the eyes yace "Shiga nace" Sosai hankalinta ya tashi ta rasa yanda xata yi, da kansa taga ya bude motar ta matsa gefe ganin kallon da yake mata sai kawai ta shiga xuciyarta na bugawa, amma bata kulle motar ba, yace "Kulle min mota" Ta xaro ido tace "Don girman Allah ka bani sakon in koma wllh karatu nake gobe ina da exams, kaga dare yayi" da kansa ya kulle motar ya tada motar, hawaye ya shiga sauka idonta tace "Na shiga uku don Allah ka bude min in fita" barin layin yayi ba tare da ya saurareta ba, ta fashe da kuka sosai tana kallonsa cikin tashin hankali.... Bai ko kalleta ba ya ci gaba da driving dinsa, jingina tayi da kujeran motar tana kuka a hankali, bayan tafiyar kusan minti ashirin taga sun shiga wani katon shopping mall wanda wajen kamar da rana saboda fitilu da ya haska ko ina, ya nemi waje yyi parking ita dai bin wajen take da kallo gabanta na faduwa, sauka yyi daga motar ya xaga ta inda take ya bude motar, kasa kallonsa tayi shi kuma bai ce mata komai ba, bayan few seconds ta goge idonta ta sauka daga motar ya kulle, tafiya ya fara, da farko ta d'an yi jim ta bi sa da kallo, amma tsoron kada ya bace mata ta bi bayansa da sauri, tare suka shiga ciki tana bin wajen da kallo, inda ya ta6a kawota ya mata siyayya Washegarin ranan ta na farko a gidansa ne, cart ya tafi ya dauka tana biye da shi, ya mika mata handle din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta amshi cart din, ya dau wani ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana turawa a hankali, wajen turarruka ya nufa, yace "Pick" tace "Ni ina da turare da yawa" Bai kuma sauraronta ba ya dinga debar mata turaren, ta dinga bin sa da kallo tana mamaki, bayan ya gama ya tafi gun mayukan shafawa da sabulu da shower gel, su ma ya dibar mata, ita dai bin sa kawai take da cart din hannunta, duk wasu kananun abu na bukatar yau da kullum sai da ya dibar mata, har ta fara gajiya da binsa, don sun siya kaya da yawa, wajen sanitary pads taga ya nufa, ganin uban pads din da ya debo bata san lkcn da tace "Ai basu kare ba na gida" Yana juyowa ta sunkuyar da kanta, yace "Meye basu kare ba" Kasa cewa komai tayi, ya xuba pads din a cart ya bar wajen, ta bi bayansa tana tafiya a hankali, sai da yaga cart din ya cika sannan suka tafi wajen kayan ciye ciye, nan ma bai jira yace ta dau komai ba, ya dinga debar mata duk wani abu da shi yake ci yana xubawa a cart din da take turawa, har kayan shayi duk sai da ya daukar mata, Jiddah dai sai kallon wani chocolate dake side dinta take ta yi don Ahmad na kawo masu irinsa daga Abuja, chocolate din kuma ba dai dadi ba, ta d'an kallesa taga yayi backing dinta yana duba wani tsadadden biscuit, kwasan chocolate din tayi kusan biyar ta juyo da sauri xata xuba su a cart din dai dai nan shi ma ya juyo rike da biscuits din da yake kallo suka kusa cin karo, juya masa baya tayi da sauri taji kamar ta nutse ta rufe ido, xata maida chocolates din taji ya fixgota, tayi narai narai da ido tana kallonsa da manyan idonta, ya amsa ya xuba su a cart din yana kallonta shi ma, ita ta fara sauke idonta, sauran siyayyan duk tana gefe har ya gama, suka tafi wajen biyan kudi, a booth duk aka xuba ledojin kayan siyayyan, eatry din mall din ya shiga ya siyi ice cream da pizza with shawarma sannan ya fito, ita dai tana tsaye bakin motarsa tana jiransa, bayan ya shiga ita ma shiga motar, cikin minti ashirin da biyar suka iso kofar gidan Ramlah. Jinginar da kansa yayi da kujeran motar ita dai jira kawai take taji ya bude lock din motar ta sauka, amma sai taga yaki budewa, bayan five minutes, taji muryarsa calmly yace "Xan mu fita
Dubai gobe in sha Allah, from there xa mu tafi Uk..." Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya kalleta.... ta sunkuyar da kanta tace "Allah ya kiyaye" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Xan yi few months a can" Bata ce komai ba, yace "Kina da bukatar wani abu ne??" Ta girgixa masa kai tace "Wani abu kamar me bayan su Umma na yi min komai ni" Ya dinga kallonta yace "Wannan ne amsan tambayar da na maki?" Kin cewa komai tayi, yace "Bude baki kiyi min magana" Tace "Bana bukatar komai" shiru duk suka yi, ita dai wata magana ce ke cinta amma ta rasa ta ina xata fara masa, ji tayi yace "Do u have anything to say to me?" Ta kallesa da sauri, sai kuma tace "Ehh.." yace "Ina jin ki" cikin sanyin murya tace "Ranan Hajja tace wai kunje hayi an rusa gidanmu, ba kowa yanxu" Ya dinga kallonta yace "Sai aka yi yaya?" Ta fashe da kuka tace "Baabarmu da Bibalo fa?" Yace "Kina son xuwa wajensu ne yanxu??" Hawaye na sauka ido ta ta kallesa tace "Ehh ina so don Allah" Yace "Me xaki yi masu idan kinje" Cikin rawan murya tace "Ina son in gansu mana, saboda nayi kewarsu... Ban taso na gan ni da kowa ba sai su, and it's been long... Nayi kewarsu sosai" Tada motar yayi bai kuma ce mata komai ba yayi reverse suka bar layin. The journey was so silent, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso titin hayin rigasa, tunda suka shigo hayi Jiddah ta dinga bin anguwar tasu da kallo, ta rasa wani irin farin ciki xata yi a moment din, farin cikin nata bai bayyana a fili ba sai da ta gansu kan layin gidan Babaarta, ta kallesa da farin ciki amma ta rasa abinda xata ce masa, she looks so happy... shiga layin yyi da motarsa xuciyarta na bugawa tace "Don Allah ko xaka tsaya in fara shiga gidan Iyah in gaisheta???" Ya kalleta sannan