Showing 60001 words to 63000 words out of 346625 words

Chapter 21 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

shi ma ni xan xabar maki?" Kasa kallonsa tayi wai duk kunya, ta sunkuyar da kanta inda take tsaye, yace "Heyy kina bata min lkci" A hankali ta karasa ta fara daukan panties din tana ajiyewa a cart din, ya hade rai yace "Idan kika dauki wanda suka fi karfin ki kina da wanda xaki ba ma ne?" Kasa kallonsa tayi kamar xata yi kuka, yace "Madam kina bata min lkci fa, baxa ki dinga dubawa ba...." kamar xata yi kuka tace "Ni baxan iya ba" that sounds so funny, amma ya dake yace "Baxa ki iya me ba?" Juya masa baya tayi, bai san lkcn da ya d'an yi murmushi ba, karasawa yayi ya gun undies din, daga sama har kasa ya kalleta doing survey with his eyes, ita dai ta ki juyowa, da kansa ya xabar mata undies din ko wanne dozen dozen, ya tura cart din ya bar ta wajen a tsaye, satan kallonsa tayi, sai kuma ta fara bin sa a hankali, gun nighties ya tsaya nan ma ya xabi sha biyu.... Kananun wears ma ya xabar mata isassu, ganin she is already tall, flat shoes iri iri masu kyau ya xabar mata shi ma dai kusan sha biyu, da handbags, a mall din nan atamfofi ne kawai Abuturrab bai siya mata ba, komai da mace xata bukata sai da ya siya ma Jiddah enough a lkcn, sai dai idan cart din ya cika ya ajiyesa sa can gun da xa abiya kudi ya dau wani shopping cart din, Creams da sabula da turarrukan da Aneesah ta turo masa ne karshen abinda ya duba a mall din, kala uku ya dau mata cream din da sabulu da shower gel, turarruka kuwa kala biyar kawai ya kara mata har da miski a ciki, a mall din Abuturrab yayi azahar, Jiddah dai iya gajiya ta gaji, bayan ya biya duk kudin kayan an kai masa mota ya nufi bangaren cin abinci dake cikin mall din, Jiddah dai na biye da shi, xaunawa yayi ya nuna mata table din dake opposite din wanda ya xauna yace "Can xa ki xauna" Karasawa tayi ta xauna wajen tana kallonsa, fried rice yayi ordering da kaza sai Chivita da bottle water, bayan an kawo masa abincin a gabansa ya juya ya kalleta, da sauri ta sunkuyar da kanta, yace "Me xa ki ci" Ta girgixa masa kai tace "Aa na koshi" Wani shegen kallo ya jefa mata yace "Me xa ki ci nace?" Kasa cewa komai tayi, ya kalli waitress din ya umarceta da ta kawo mata exactly abinda ta kawo masa amma takeaway xata yi, waitress din na wucewa ya soma cin abincinsa, lkci lkci Jiddah ke satan kallonsa, cikin rashin sa'a suka hada ido, da sauri ta kauda kanta, shi dai ya ci gaba da cin abincinsa, Waitress din ta kawo abincin ya amsa ya ajiye kan table dinsa, sai da ya gama cin abincin sannan ya mike ya saka sauran drink din da bottle water a ledan abincin dake kan table din, cash ya ba waitress din har xai fara tafiya ganin jiddah bata taso ba yace "In xo in daga ki ne malama" Mikewa tayi xata wuce ya nuna mata ledan yace "ohk bar masu abincin xa ki yi" bata ce komai ba ta dauki ledan ta bi bayansa, suna isa gida da kansa ya dinga kwasan kayan yana kai wa parlor har ya gama, tana tsaye kamar wawuya bakin kofa sai dai ta basa hanya, har ya gama shigar da kayan yayi xamansa a parlor yyi powering Tv, jin bai ce ta shigo ba taki shigowa parlon, bayan kusan minti sha biyar ya mike ya isa bakin kofar yace "Ke wai baki da hankali ne dama ban sani ba? Meyasa kike behaving kamar yar kauye?? Yanxu me kike yi a nan a tsaye" Kamar xata yi kuka tace "Ai baka ce in shigo ba" Ya mata wani shegen kallo yace "Get out my frnd, sai nace ki shigo, idan kina son xaman lafiyar ki a gidan nan ki daina behaving kamar wawuya" Har hawaye ya kawo idonta ta bi ta gefensa ta shiga parlon, bata san dama kayan da ta bar sa da shi yake ta kwasa tana kallonsa ba ya basa haushi, tsaye tayi parlon tana tunanin ta wuce sama ko ta tsaya, ganin kallon da yake mata ta juya da sauri ta nufi sama, yace "Dawo nan" Dawowa tayi yace "Kwashi duk kayan nan ki wuce da su sama dakin ki" Daukan ledojin ta dinga yi daya bayan daya tana kai wa dakin nata har ta gama, ta dau na karshen xata wuce ya dawo da ita ya nuna mata ledan abincin durkusawa tayi ta dauka sannan ta wuce sama yace "Idan kin je saura ki ajiye abincin ki jirani in xo ince ki ci" Bata ce komai ba a sanyaye ta wuce sama ta shiga dakin ta kulle.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do ur self justice by subscribing before reading, Thank you!!
Karfe hudu saura Abuturrab na xaune parlor wayarsa ya fara ring, kallon wayar ya dinga yi ganin Ahmad ne ke kiransa ya ki dagawa har ya katse, bayan few minutes ya ji wayar na ring kuma, dauka yayi xai yi silencing phone din ya ga Aneesah ce ke kiransa, sosai gabansa ya fadi, ya gyara xamansa da sauri yana kallon wayar har ya katse, ya lumshe ido hade da jinginar da kansa da kujera, mikewa yayi daga karshe walking slowly ya wuce sama, bude kofar dakin da Jiddah take yayi, da sauri ta dago kanta daga kan gwiwanta ta jawo ledan abincin, kallon idonta da yayi jajir sbda kuka ya tsaya yi, ta fara bude abincin ba tare da ta yarda ta sake kallonsa ba, she looks sad and scared, karasawa yyi cikin dakin ya xauna kan stool din dake gaban mirror looking at her directly, kasa kunce ledan da abincin ke ciki tayi, cikin cool voice yace "Kukan me kike?" Ta girgixa masa kai kawai wasu hawayen na taruwa idonta ba tare da ta yarda ta kallesa ba still, yace "Tambayarki nake" Nan ma ta girgixa masa kai, shiru yayi yana kallonta, ta bude ledan abinci ta ciro ta fara ci a hankali, ya mike yace "Xan tafi masallaci, kafin in dawo ki tabbatar kin gama cin abincin" Ta gyada masa kai, ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita dakin... Ko kafin ya dawo ta rufe sauran abincin da ta rage, ba cikin dadin rai ta ci abincin ba, ko rabi bata iya ci ta kai ba, lemon ma bata bude ba tunda ba iya sha tayi ba, ruwa kawai ta sha, tunani ta shiga yi ko ta kai sauran kitchen kar ya dawo kuma yayi mata ihu, a sanyaye ta mike ta dau ledan abincin ta fita, kitchen ta shiga ta fiddo takeaway din abincin ta ajiye gefe daya, sannan ta ciro ruwa da lemon ta ajiye tana kallon ledan hannunta wanda bata san inda xata wurgar ba, window din kitchen din ta dinga kallo sannan ta karasa a hankali ta bude ta jefar da ledan ta kulle windown, bin kitchen din ta dinga yi da kallo, babban ne kitchen din sosai, ga kuma store a ciki, cabinet din yayi kyau ba kadan ba sai dai babu komai a kitchen din sai electric heater da gas cooker, wanda bata ma san meye shi ba, sai fridge da deep freezer, a hankali ta juya xata fita ta gansa tsaye bakin kofar shigowa kitchen din ya rungume hannunsa yana kallonta, komawa baya tayi a tsorace tana kallonsa, ya nuna mata kofa wanda xai yi leading dinka to the back of the house, calmly yace "Bude kofar nan ki fita ledan da kika wurgar ki kwaso su" Da sauri ta nufi kofar tana murda makullin amma ta kasa budewa, karasawa yyi hakan yasa ta koma gefe da sauri, gaba daya a tsorace take, ya bude kofar ta fice, ledojin ta kwaso ta dawo ta tsaya bakin kofa tana kallonsa rike da ledan, ya karasa ya sa ma kofar makulli yace "Daga yau kada ki sake jefar min da komai wajen nan, don ba bola bane, ko kinga yayi maki kama da bola?" Ita dai bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, ya nuna mata wani waste bin a cikin kitchen din yace "Nan xaki dinga ajiye bola from henceforth" A hankali ta karasa shigowa ta saka ledojin a waste bin din, ya juya ya fita yace "Ki sameni sama" Bin bayansa tayi... ganin ya shiga dakin da take ta bi sa xuwa cikin dakin, gefen kofa ta tsaya bayan ta shigo, yana kallon tulin ledojin kayan da ta jera a kasa yace "Ga press can da xaki xuba kayanki" Ta kalli abinda yake nuna mata amma bata ce komai ba, yace "Yanxu xaki fara sa kayan ina gani...." Yana fadin haka ya ja stool ya xauna yana kallonta, ta karasa gun kayan ta bude, rasa ta yanda xata fara jera kayan tayi she look so confuse and Afraid at the same time, ta marairaice tana kallonsa amma bata ce komai ba, hakan yasa ya d'an yi tsaki bai ce mata komai ba ya mike, tun daga kananun kaya, undies, nighties, ya fara arranging dinsu a press din tana tsaye gefe tayi jigum tana kallonsa, har ya gama, ya bude akwatin da suka taho da shi jiya, atamfofin ciki dinkakku wanda baxa su wuce kala biyar ba ya ciro, linkin guga aka yi masu hakan yasa ya ajiye su cikin press din, da hijab biyu da suka rage suma gogaggu, sauran kananun abubuwan ciki duk ya samar masu maxauni cikin press din, gaban mirror yaje duk turarrukan ya jera su da mayukan shafawa da kayan kwalliya, lkci lkci yake kallonta ta madubin gabansa, Jiddah dai ta dinga kallon turarrukan da take ta tunanin su wa da su wa xasu dinga amfani da su haka da yawa, sun yi yawa sosai ba kadan ba, bayan ya tabbatar komai ya samu maxauni ya hade uban ledojin waje daya sannan yana kallonta ya nuna mata turarrukan yace "Kinga turarrukan nan?" Ta gyada masa kai, yace "They are not there for decoration?" D'an rufe idonsa yayi after he realized what he just spoke, sai kuma ya bude idanuwansa ya d'an hade rai yace "Kin gane abinda nace?" Ta girgixa masa kai yace "Ohk, cewa nayi ba don jere na siya maki su ba, watanni kadan na baki duk su kare, idan kuwa basu kare ba xan sa sai kin shanye su, na siya maki ne don ki dinga amfani da su a kai a kai, safe, rana, yamma, dare, bbu takamaiman lkcn saka turare, sannan ba kadan kadan aka ce ki dinga fesawa ba, idan kinga dama xaki iya feshe gaba dayansu a lkcn daya, infact ba ma sai kin ga dama ba, haka nake son ki dinga yi, gaba daya xaki dinga fesawa a lkci daya, wata daya na baki in ga duk sun kare..." kai kawai take gyada masa, ya nuna mata body cream din yace "Wannan xaki dinga shafawa duk kika yi wanka, sannan wanka da safe, rana, dare.... kullum haka xaki dinga yi, ga sabulun nan xan kai maki bandaki, idan kina so ma xaki iya wanka sau goma a rana akwai enough ruwa a gidan" Nan ma ta gyada masa kai, ya hade rai yace "Ba ki gyada min kai kamar lizard ba malama, sau nawa nace xaki dinga wanka daga yanxu?" A hankali tace "Sau uku, idan ina so ma inyi sau goma" Yace "Idan ma baki yi ba ina da camera a gidan ai xan gani...." Xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Wanke baki kuma duk kika ci abu ki tafi bayi ki matsa MacLean ki wanke bakin ki, sannan ga na kuskura baki ma, bayan kin wanke bakin shi ma sai ki kuskure baki da shi, duk dare kada ki kuskura ki kwanta baki wanke bakin ki ba, da safe kafin kiyi alwala sai kin fara wanke baki, idan xaki yi wanka ki sake wankewa da safe... haka da rana sannan da yamma, ina son cikin sati biyu maclean dinki ya dinga karewa" Ta gyada masa kai, ya nuna mata mayukan gashi yace "Kullum sai ki shafa wannan a gashin ki, ki gyara..." Cikin sanyin murya tace "Toh" Nail cutter ya dauka gaban mirror din yace "Kinsan meye wannan?" Shiru tayi tana kallo, ya isa gabanta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta fara komawa baya a hankali, tsayawa yayi yana kallonta, lkci daya ya daure fuska yace "Meye haka?" Taki kallonsa gabanta sai faduwa yake, yace "Baxa ki dago kanki ba" Da kyar ta dago kanta amma ta kasa kallon cikin idonsa, ya daura nail cutter din a kan finger dinsa wanda babu farce yace "Shi ake yankewa da, duk ranan juma'ah ki tabbatar kin yanke faratanki, kar ki kuskura ki yarda in ga farce a hannunki, bana son ganin haka..." A hankali ta gyada masa kai, yace "In ga hannunki" a hankali tayi masa stretching dogayen fingers dinta wanda ita ma bbu farce, lkci daya kuma ta sauke kasa, ya dau shaving stick dake cikin leda yana kallonta yace "Kinsan wannan?" Sau daya ta kalli abinda yake nuna mata, ta Smsunkuyar da kanta, yace "Duk Jumma'ah xaki dinga amfani dashi shi ma" ita dai bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Sabulu ya dauka da Listerine mouthwash ya nufi bathroom, da ido ta bi sa, xai shiga ya juyo ganin bata taho ba yace "In dawo in dauko ki ne??" Da sauri ta bi sa, wajen da xata ajiye towel dinta ya nuna mata, ganin undies dinta da ta wanke a bandakin yace "Xa a sa maki igiya a baya, daga yau kada ki sake shanya a nan ki kai rana, nan ba wajen shanya bane, am i clear?" Ta sunkuyar da kai a hankali tace "Toh" da ido ya bi bandakin ganin it's clean ya juya ya fita ta bi bayansa, ya jingina da bango ya rungume hannunsa yace "Kinsan abinda yasa nake nuna maki duk abubuwan nan?" Ta girgixa masa kai tana kallonsa, yace "Saboda ba lallai wani abun ya sake hadamu a gidan nan ba, ba lallai ki sake samun privilege din tsayawa waje daya tare da ni ina maki bayani ba, ke kadai xaki dinga rayuwarki gidan nan babu wani da xai xo balle ya nuna maki wani abu shi sa nake bata lkci na yanxu, kina da ikon shiga ko ina a gidan nan amma banda bangarena.... sannan idan ina gari ba ke ba fitowa daga dakinki, kwana biyu xuwa uku kawai nake yi a kaduna shi ma sai karshen mako, don haka a wannan lkcn iyakar ki dakin ki, sai kuma probably kitchen, sannan baxan lamunci ki bar min gida da kazanta ba, kullum ki tabbatar kin yi shara kin yi mopping kin goge ko ina, nasan kin ga yanda ake yi a gidan Umma, tunda kin fi sati a can" Ji tayi hawaye ya kawo idonta, ta daga kai tana kallonsa, ya hade rai yace "Kin ji abinda nace?" Gyada masa kai tayi tana kokarin ganin hawayen bai karasa xubowa ba, Ya rungume hannunsa yace "Gobe xan koma wajen aiki, kafin in tafi xan siyo kayan abinci da komai da xa ki bukata a kitchen, don haka duk abinda na gaya maki yanxu baki da wani da xai sake gaya maki a gidan nan, it's better ki tabbatar kin gane komai...." Kallonsa kawai take tana jin wani kuka xai taho mata, ya ki yrda ya hada ido da ita, ya daga kafada kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta sauke idonta a hankali wani hawaye me xafi ya shiga sakko mata. Abuturrab na dawowa daga masallaci da magrib ya shigo da abinci, sama ya haura ya kwankwasa kofar sannan ya bude, tana xaune saman darduma, ya ajiye mata abincin bakin kofar, ya d'an tsaya wanting to ask what she is even reciting in her prayers, sai kuma kawai ya fasa, ya ta6e baki yayi wucewarsa, karfe tara da rabi ta gama saka kayan da ya nuna mata yace ire irensu xata dinga sa wa da daddare, wando ne dogo da riga, sosai kayan ya mata kyau tana tsaye gaban madubi ta saka daya daga hulunan da ya siyo mata, har makogwaro ta dinga jin turarrukan da ta fesa abin ka da bata saba ba, ta nufi saman gado ta takure waje daya ta kwanta ta lumshe ido... Abuturrab ya fito daga bangarensa rike da lallausan duvet, kana ganin duvet din kasan me tsada ne sosai, kamshin turarruka ne ya gauraye ko ina na upstairs din, ya isa kofar dakin, ya fi second biyar a tsaye kafin ya bude, ko motsi bata yi ba alamar ta fara bacci, ya karasa ciki ya bude duvet din ya rufeta da shi, da sauri ta bude ido, yana kallonta yace "Daga yanxu idan xa ki kwanta ki dinga kashe wuta" Ta gyada masa kai, gun switch din ya nufa ya kashe wutan dakin sannan ya fita ya kulle kofar dakin, Jiddah ta lumshe ido gabanta na faduwa don bata saba kwana ita kadai ba. Washegari Abuturrab ya tabbatar duk wani abinda Jiddah xata bukata a kitchen ya siya, tare da Ramlah suka tafi siyayyen, duk ita ke fada masa abinda xa su siya na foodstuffs, har da filling din gas sun yi, kitchen din ya dawo well stocked up with foodstuffs, few pots, and some kitchen utensils, Jiddah dai na xaune parlon tun bayan dawowarsa da Ramlah, shi ma ya aika Ramlan taje ta kirata ne, yana tsaye kitchen din Ramlah ta jera komai, yana kallonta yace "Ahmad ya koma Abuja ne?" Ta gyada masa kai, ko ranan ma Ahmad ya kirasa amma yaki dagawa kamar dai shi ya aura masa jiddah, Ramlah na gamawa Abuturrab ya bata 2k transport ta fito daga kitchen din tana kallon Jiddah dake ta xaune, da murmushi fuskarta tace "Aunty amarya xan koma" ko lura


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login