Showing 114001 words to 117000 words out of 346625 words
Chapter 39 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ma kansa aure da yarinyar nan?" Ummi tace "Me yasa kika ce haka yaya" Ummi tayi wani murmushi tace "Ai ni na haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa nawa rabonsa da gidan nan yanxu?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Nima ae ya daina xuwa min yaya..." Ummi tace "Toh yayi kyau... Xai gane bashi da wayo" Umma tace "Amma duk da haka akwai ayar tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya, ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu" Ummi tace "Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban aminta da xaman nan ba" Umma tace "Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi" Ummi tace "Ni kuma haka kawai naji ina son rabuwan nasu Ramlah" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn't look happy always...." Ummi tace "Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu? dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina" Umma tace "Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba..." Ummi ta girgixa kai tace "Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong, kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban bargo a gidan nan" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce" Bayan kusan minti talatin Umma ta gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace "Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai ta" Ummi tace "Aa wannan kuma ban sani ba" Umma tace "Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben" daga haka tayi ma yayarta sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi, yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata tsohuwa ce ta mika mata purse tace "Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki" Jiddah ta amsa tace "Toh" lkci daya Jiddah ta gane warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace "Ummi wai ajiya aka ce a kawo maki" Ummi ta amshi purse din tace "In ji waye?" Jiddah tace "Ai ban santa ba" Ummi tace "Dama baki je saloon din ba ke" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace "Toh gobe sai a kai ki ke" a hankali Jiddah tace "Toh" daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace "Dama Aliyu na ciki?" Ummi ta kirkiri murmushi tace "Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba" Tuni Jiddah ta fita daga parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace "Keee" tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace "Yaushe kika xo gidan nan" Ta sunkuyar da kanta tace "Umma ce tace mu taho..." ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro makulli a aljihunsa yace "Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani" Tana kallon makullin tace "Bude kofar xan yi?" Ya hade rai yace "Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?" Juyawa tayi ta bar wajen don ta gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki, sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace "Baki cin abinci ne?" Ta girgixa kai tace "Aiki nake yi shi yasa ban ci ba" Yace "Wani aiki?" Tace "Nayi wanke wanke da safe na share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata...." Katseta yayi yace "Duk wa yake sa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Aunty" Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar yace "Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka" Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming din bak'in da suka shigo da mugun fara'arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace "Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?" Aneesah na murmushi tace "Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan" Kofa Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace "Aliyu get them something meaningful to eat, kasan sha'anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba" Toh kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na abinci yace "Ku kai ma Aunty" Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace "Baki ce ma Ummi baki ci abinci bane duk yau?" Ta girgixa kai tace "Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako" Yace "Toh wa ya kawo ki gidan nan?" Tace "Nace maka Umma tace in taho tare da su seeyama" ajiye ledan hannunsa yyi ya mike ya koma can karshen katifar ya xauna ya fiddo wayarsa dake vibrate a tunaninsa Ahmad ne don yana restaurant ma ya kirasa, amma sai ya ga akasin haka don Aneesah ce ke kiransa, silencing wayar yyi, Jiddah ta bude abincin da ya ajiye mata ta fara ci. Mikewa yayi ya fita dakin ya kulle, kiran Aunty ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne bai ce komai ba yana tafiya, cike da fada tace "Amma walakancin ka da yawa yake, kasan bakin nan takanas daga Abuja suka xo, ba sai ka tafi ka samesu a masaukinsu ka xauna a nutse ka gaida su ba, amma ka wani gaishesu a tsattsaye ka fita kamar mara gaskiya, ko baka san mahaifiyar Aneesar bace?" A hnkli yace "Yanxu nake tahowa" Tace "Toh suna can uwar dak'ana" Yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya nufi bangaren Aunty a ransa yana tunanin har ta huce kenan, or did she have anything in mind to punish him with, bude kofar parlon yayi, ya gaida frnds dinta dake xaune parlon, sannan ya nufi bedroom dinta, sai bayan da aka amsa sallamarsa sannan ya shiga, Mahaifiyar Aneesah na xaune tare da kanwarta sai Aneesah a dakin ga abinci iri iri a gabansu bayan wanda ya siyo masu, xaunawa yayi kasan carpet ya gaishesu da ladabi kansa a kasa, kanwar mahaifiyar Aneesar ce kawai ta amsa masa a dakile, uwarta kuwa sai cin abincinta take, Aneesah dai na xaune kan kujera sai kallonsa take ko kiftawa babu, kananun kaya ne jikinsa da suka yi matukar amsarsa, ga kamshin turarensa da ya cika ko ina na dakin, Kanwar mahaifiyar Aneesah Hajiya Maryam tace "Allah ya sanya alkhairi a bikin" Ya amsa da "Ameen" Ya d'an saci kallon mum din Aneesah dake fama da kaza, Mikewa Aneesah tayi ta fita daga dakin, Bayan few seconds ya mike yayi masu sai anjima ya fita shi ma, Hajiya Maryam ta tabe baki tace "Kaga mutum kamar shi yayi kansa, sannan ga nera, shi yasa Aneesah duk take daga ma mutane hankali, to in sha Allah komai ya kusa karshe ynxu ai" tsaye Abuturrab yaga Aneesah corridor tana jiransa, ya shafa kansa yace "U didn't tell me tare da su Mumy xa ku xo" Tace "Ehh ai baka tsaya ka gama saurarata ba daxu kace ana kiranka ka katse wayar" Yace "Ohk, kinci abincin?" Tace "Bayan leda biyu ka siyo me xan ci a ciki?" yace "Ehh ai banga Hajiya ba i only saw u and mum" Ta tabe baki tana gyara siririn gyalenta, ya rungume hannunsa yace "Toh yanxu ya xa ayi?" Tace "Xuwa xa mu yi ka siya min abincin" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh ki jirani wajen motar xan dauko makulli a dakina" Tace "Ohkk" daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallo sannan ya sauka xuwa dakinsa, makulli ya sa ya bude kofar xai shiga yaji muryar Aunty tana kiransa alamar tana biye da shi a baya, da farko niyyar kulle dakin yyi da makullin amma sanin xata yi suspecting abu sai ya fasa ya shiga dakin kawai bayan ya amsa kiran nata, Jiddah na tsaye bakin window ya nuna mata alamar ta shige bandaki, ai da gudu ta shige ciki ita ma jin muryarta, ta kulle har da sa makulli hakan ya kusa basa dariya, dai dai nan Aunty ta shigo dakin, ya xauna gefen gado yana shafa kansa yace "Ya gajiyan aiki Aunty?" Maimakon ta amsa sai ta sa makulli dakin ta shigo, shi dai kallonta kawai yake, ta kalli ledan abincin tace "Wannan fa?" Yace "Ni na siyo na ci" Kujera ta ja ta xauna tace "Abuturrab!!" Ya daga manyan idanuwansa ya kalleta, sake kiransa tayi murya can kasa yace "Na'am...." Tace "Dama Abuturrab ra'ayinka ne xuwa hayi kayi aure ban sani ba? Dama haka ka mayar dani gantalalliya ban sani ba" Ya girgixa kai yace "Wllh ba ra'ayina bane Aunty" tace "To son yarinyar ka fara all of a sudden? Da ka toxarta ni gaban ubanka?" Ya girgixa kai yace "Ko daya wllh Aunty" tace "Toh kawai xubar min da mutunci da walakanta ni gaban iyayenka ka so yi??" ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ba haka bane Aunty, kiyi hakuri" tace "Inyi hakuri?? Dama shirga ni kayi baka saketa ba Aliyu??" Da kyar yace "I'm finding it hard to confide in u anymore aunty..." Tace "Why??" Yace "U did what i never expected, kema kin san na kowa me sauki ne kan na Abba, how will u expect him to take it cewar na saketa da gaske? Wllh he can even disown me, kin fa san waye Abba, kin fi kowa saninsa, amma kika yi exposing dina wajensa" Da karfi tace "Karya kake, wllh baka saketa ba ni xaka mayarda sha sha sha yanxu? Are u stupid?" Yayi kasa da murya yace "Xa kiyi kaffara Aunty, nace maki ba aure tsakaninmu da yarinyar nan amma kuma bai kai har ki je ki gaya ma Abba ba, i trust u shi yasa na sanar maki" Shiru tayi tana kallonsa tana huci tace "Toh dadin xama kake ji da ita ne da kaki rabuwa da ita har yanxu???" Yace "Ko daya, idan na rabu da ita bata da wajen xuwa Aunty, Aunty da xa ki kwantar da hankalinki ki xuba min ido xaki ga me xai faru in sha Allah, i have plans wallahi, ba haka nan kawai na ajiyeta gidana ba, the house isn't meant for her..." tace "Which nonsense plan Aliyu, dubi fa yanda yarinya tayi wani kyau ta kara uban haske fatarta lui lui kamar a latsa jini ya fito, a haka ne xan amince da kai baxan sa shakku a raina ba? Dubi fa yanda tayi fresh alamar bata da wani damuwa ta samu gida kawai, sbda ita ko weekend ka daina dawowa gidan nan sai dai ka sauka can kayi yanda kaga dama da ita, don wllh ban yarda baka harkanka da ita ba" Kallon Aunty ya dinga yi ba ko kiftawa, sannan yace "Inyi harka da ita fa fa kika ce Aunty" Tace "Toh eh mana, kana xaune da budurwa irin wannan a gida baxa kayi yanda kaga dama ba?" ya girgixa kai yace "Ba yanda kike tunani bane aunty, amma dai yanxu ya kike son ayi?" Aunty tace "Kawai ka dawo da ita gidan nan gaba daya da xama, she will be very useful wllh" Kallonta kawai yake yi, tace "Ko baka ji abinda nace ba?" Yayi murmushi yace "Na ji" tace "Wato baxa ka yi ba kenan??? Wato wllh ban ma yrda cewar babu abinda ke shiga tsakaninka da yarinyar nan ba da ya sa kaki rabuwa da ita har ynxu duk da ba auren" Ya girgixa kai yace "No plss, Wllh babu wani abu Aunty ai kinsan ba haka nake ba" Tace "Toh ka maidota gidan nan nace idan na isa da kai, tunda already tana nan kawai kayanta xaka debo gaba daya ka maido su nan" Ya shafa kansa yace "Toh Aunty amma sai mun yi magana da Ummi ko...." Wani kallo ta jefa masa tace "Sai kun yi magana da Ummi? Ni ban isa da kai ba kenan da xaka yi involving Ummi??" Yace "Kin isa" tace "Toh ba sai ka sanar mata komai ba, kawai taga ta dawo nan din, idan tace don me, sai kace ita kadai ce a gida kuma aiki ya maka yawa" Yace "Ohkk" mikewa tayi tace "Xan koma wajen bak'ina, bayan bikin xa muyi magana a tsanake" Daga haka ta bude kofa ta fita ya bi ta da kallo, mikewa yayi ya karasa ya kulle kofar dakin sannnan ya dawo ya bubbuga kofar bandaki, bude kofar Jiddah tayi ta fito tana kumbure kumbure tace "Don Allah kar ka dawo dani gidan nan kayi hakuri" sai kuma ta sakar masa da kuka, dariya abun ya basa, ya dake yace "Gidan namu kike kuka kar in dawo da ke??" Tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Dole ma ki xauna nan din ki samu saiti sosai" Durkushewa tayi gabansa ta hade hannayenta tana kara rushewa da kuka tace "Aa don girman Allah kayi hakuri" Xaunawa yayi gefen gado yace "Kin fi son xama tare da ni kenan, duk da kince ni ba muharraminki bane?" Ta gyada masa kai a hankali tana share idonta, ya kauda kai yana