Showing 324001 words to 327000 words out of 346625 words

Chapter 109 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

kallonta a gefensa, bayan yayi parking kofar gidan Iyah Hajiya Fatima ta bude motar ta sauka, ya jawo Jiddah don motarsa tinted ce ta bude ido a firgice, da damuwa yace "Wani bacci ne wannan kike yi haka throughout Baby?" Ta langwabe masa a hankali tace "Kilan aikin da nayi ne ya sa na gaji sosai" Yace "Toh baxa ki sake wani aiki ba, beside the house is too big for you to clean all alone, xa mu samu house help ko da biyu ne, i don't want my wife to be stressing her self" Girgixa masa kai tayi da sauri tace "Aa ni bana son wasu house help, xan iya yi da kai na...." Xaro ido tayi tana bin anguwan da kallo tace "Lahh har mun kawo ashe" sai kuma ta kalli bayan motar tana xaro ido don gaba daya ta mance tare da Hajiya Fatima suke, sai taga bata motar, bude side dinta tayi ta xame hannunta daga nasa a hankali, ta sauka... shi ma ya sauka ya kulle motar suka shiga cikin gidan don tuni Hajiya Fatima ta shiga.




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp







Jiddah ta tafi kusa da Iya tana murmushi ta gaisheta, Iyah ta amsa tana washe baki tace "Sannunku da xuwa Jiddah..." Abuturrab ya xauna saman tabarman dake shimfide yace "Ina yini Baaba" Da fara'a tace "Lafiya lau Alhmdlh... Sannunku da xuwa" Hajiya Fatima tace "Ina saurarenki Mama" Iyah tace "Shine nace ko xa ku je wajen Jibirilun a gwada sa'a tunda Zulan tace babu tantama yasan inda take, mu dai nan yayi ta rantsewa bai san ina Hansai ta nufa ba... Zulai kam na can tana fama da kanta duk babu kafafuwan wai yanke su xa ayi, ita kanta Hansan ta gudu da dubu ashirin dinta tace min.. " Hajiya Fatima tace "Toh Allah ya kiyaye, mun gode kwarai mama Allah ya saka da alkhairi, yanxu wa xai kai mu can gidan wan nata?" Iyah ta kalli Jiddah tace "Ba kin san gidan Jibirilu ba?" Jiddah tace "Na sani" Hajiya Fatima tace "Au to shkkn, ashe ma ta san gidan" Abuturrab na kallon Iyah yace "Kiyi hakuri Baaba har yanxu ban kai ki can inda muke ba kamar yanda nayi alkawari, in sha Allah xan sa lkci in xo in dauke ki, ina sane, yanayin aikina ne ya sa bana samun lkci" Iyah tace "Allah ubangiji ya dafa maka, babu komai wllh, ai ka gama mana komai tunda ka rike Jiddah da amana, Allah ya saka maka da alkhairi ya dafa maka a lamuranka" Yace "Ameen nagode" Dubu goma ya ajiye mata, ta dinga godiya kamar xata ari baki, ta rakosu har bakin mota tana daga masu hannu har suka bar layin, tana murmushi tace "Allah sarki Isuhu, kyawun halinka kadai ma ya ishi a rike maka er ka da amana har abada kuwa" Parking Abuturrab yayi kofar d'an kuturun gidan Kawu Jibiril, Hajiya Fatima da Jiddah na tsaye daga gefe Abuturrab yayi sallama bakin kofar Zauren, Wata yarinya ce da baxata wuce Jiddah ba ta leko tana tambayar waye, kallon Jiddah ta dinga yi irin kallon sani, Hajiya Fatima tace "Babanki fa?" Tace "Baya nan, Hajiya Fatima tace "Yaushe xai dawo?" Tace "Ya tafi kauye duba gonarsa" Hajiya Fatima tace "Mamarki fa?" Tace "Tana ciki" Hajiya Fatima tace "Kice ana sallama da ita" Juyawa tayi ta koma ciki, sai ga ta sun dawo da uwarta, Lantana na gyara daurin kirjinta a d'an tsorace tace "Lafiya wa ku ke nema?" Hajiya Fatima na murmushi tace "Maganar ba ta tsayuwa bace, kar ki wani damu alkhairi ne ya kawo mu" Lantana ta hangame baki tana kallon Jiddah tace "Wacece wannan kamar Jiddar Hansai?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajiya Fatima tace "Ita ce" wani salati lantana ta rafka tace "Ku shigo ku shigo, tsakar gidan ne dai babu shara, Bismillan ku" Da sauri ta koma ciki ta fito da wani bak'in tabarma ta shimfida masu, tana yi tana kallon Jiddah har sannan ta kasa rufe bakinta, Jiddah ce ta fara xama tace "Ina yini Maman Jummai" Lantana ta kasa amsawa sbda mamaki tace "Yanxu Jiddah kece kika dawo haka kamar wata er sarki?? Allah mai iko" Hajiya Fatima ta xauna kusa da Jiddah tana bin tsakar gidan da kallo, Abuturrab kuma ya ki xama saman tabarman, Hajiya Fatima na kallon Lantana tace "Mun wuni lafiya?" Da sauri Lantana ta xube kasa ta fara jero masu gaisuwa, Hajiya Fatima tace "Alhmdlh, fatan mun sameku lafiya" Lantana tace "Lafiya lau wllh, Wai yanxu Jiddah ce haka Jama'a" sai kuma ta rike kai tace "A gaskiya wanda bai ji tsoron Allah ba yayi asara a rayuwar nan" Jiddah dai kanta na kasa, Hajiya Fatima tace "Yau dai shine nace bari mu shirya ta xo ta gaida Baabarta, sai kuma da muka je anguwan muka samu labarin ai ta tashi gidan" Lantana ta rike ha6a tace "Cabdi, wannan ai tsohon xance ne, tun yaushe en lapun suka xo suka siyar da gidan suka cire kudinsu suka bata sauran canjinta, ai ko dai Hansai bata Hayi yanxu, bashin da ke kanta na jama'a ya fi dubu dari biyu.... Nemanta ake ido rufe" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah, to yanxu ina ta koma?" Lantana ta dinga bin su da kallo daddaya da daddaya, Hajiya Fatima tace "Kar ki ji komai wllh, mu alkhairi ne ya kawo mu ba sharri ba, mun xo sada xumunci ne kawai, idan da wani taimakon da xa mu yi kuma sai mu yi..." Lantana tayi kasa da murya tace "Sai dai in kai ku a boye mu dawo a boye don ban ma son mai gidana ya sani, abun sirri ne, sannan Hansai dai bara take a Kana rad, er ta kuma fama take da cutan xamani, shegun da ta haifa ma Allah yayi masu rasuwa, kun san yan biyu ne, to ance dai cutar ce ta kashesu satinsu 3 a duniya, ni ko yaran ban gani ba don ba a hayi ta haihu ba, Iliya ne dai yayi mata cikin ya goga mata kanjamau" Hajiya Fatima ta bude jakarta da sauri ta fiddo en dari biyar biyar tace "Mun kuwa gode wllh, ki kai mu ko da taimakon da xa mu iya mata..." Ajiye mata kudin tayi a gabanta, Lantana ta mike da sauri tana kallon kudin tace "Bari in saka riga, Allah ya so mai gidan nawa baya nan, ina nuna maku inda ta koma xan juyo ni kuma" Da sauri ta shiga ciki sai ga ta ta fito sanye da riga ta yafa mayafi tace "Ku taso mu yi maxa kafin magariba yayi" shi dai Abuturrab sai kallon Jiddah da ta jingina da bango idonta a lumshe yake, Hajiya Fatima ta mike without noticing baccin da jiddah take, Xagawa yayi ya d'an ta6a shoulder dinta ta bude ido da sauri sai kuma ta mike tsaye ganin su Hajiya Fatima sun nufi xaure da Lantana, yayi kasa da murya yace "Baby are you okay?" Ta langwabe tace "Bacci nake ji" Kama hannunta yayi ta xame a hankali suka fita daga gidan... Can cikin Kabala lantana ta kai su, Abuturrab ba abinda ya damesa sai irin portholes da ya dinga shiga da motarsa a anguwan, parking yyi dai dai inda lantana ta nuna masa yana kallon gidan, wanda gidansu na hayi ya fi sa mutunci da daraja sau 100, Hajiya Fatima ta sauka motar Lantana ma ta sauka tace "Toh kun ga inda take yanxu, Allah ma ya sa ta dawo daga baran, amma ku shiga Bibalo na nan na sani tunda bbu inda take iya fita ciwo yaci karfinta" Abuturrab ya jawo Jiddah dake xaune gefensa yace "Baby are u sure Tse tse fly bai cije ki ba kuwa" Buda ido tayi da sauri sai kuma ta turo baki tace "Me ka ce?" Yace "Aa cewa nayi mun kawo..." Bin anguwan ta dinga yi da kallo kafin ta bude motar ta sauka, shi ma ya sauka, Lantana tace "Toh kunga ai gwara in yi wucewana ko?" Abuturrab ya ciro dubu uku ya mika mata yace "Mun gode" Har kasa ta risina ta amsa tana masa godiya.... Hajiya Fatima ta shiga d'an karamin tsakar gidan wanda ke dauke da kananun dakuna hudu, ga wani makeken kwata a tsakiya sai doyi yake, kallon wata mata dake daka a d'an mitsitsin tsakar gidan tayi tace "Ina yinin mu?" Matar tace "Wa ake nema?" Hajiya Fatima tace "Hansatu" Matar tace "Aiho bata dawo 6ara ba kuwa, amma kilan tana hanya yanxu" Jiddah dai na tsaye gefe duk jikinta yayi sanyi, yanxu wannan gidan su Baabarta suka dawo?? Hajiya Fatima tace "Ina dakin ta?" Matar ta nuna mata wani daki da babu ko labule tace "Ga ya can, er ta na ciki ma ai" Hajiya Fatima ta nufi kofa Jiddah na biye da ita, tun da Abuturrab ya shigo yayi arba da wannan gutter din ya fice daga compound din da sauri, Hajiya Fatima ta ciro wayarta tana haska dakin sbda duhu ta ga Bibalo da ta dawo uwa skeleton a can kan wani yamutsen karamin katifa irin ta yan boarding a kwance, babu komai cikin dan karamin dakin da duk cement din kasa ya dagargaje sai wasu bakaken Ghana must go biyu, da kwandon kwanuka da risho, Jiddah ta kasa karasawa cikin dakin xuciyarta na bugawa tana kallon Bibalo with shock, Hajiya Fatima dake kallonta ita ma ganin idonta biyu tace "Sannu" Kai kawai Bibalo ta gyada, Jiddah ta kasa cewa komai hawaye ya hau sintiri idonta ta xube nan kasa ta hade kanta da gwiwa abubuwa masu yawa na dawo mata a kai, Hajiya Fatima tace "Mamarki fa?" Murya can kasa wanda idan ba ka saurara ba ma baxa ka ji ba Bibalo tace "Bata dawo bara ba" Hajiya Fatima ta dinga furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarta, Sallama Hansai tayi a tsakar gida Hajiya Fatima ta juya da sauri tana kallonta, ita kuwa tsaye tayi tana mamakin wanda ya kawo masu wnn fitila me uban haske da ya haska daki haka ga kuma takalma ta gani bakin kofa, Hajiya Fatima tace "Sannu da xuwa" kasa karasowa tayi kana ganinta kasan a tsorace take, Hajiya Fatima tace "Ki karaso mana... baki ne daga cikin gari, babu abinda ya kawo mu sai alkhairi" Hansai ta shigo dakin da kyar tana dogara sandarta tace "Wa ku ke nema" Tuni Jiddah ta dago kanta tana jin muryan Hansai na mata echo a kunne, and she remembered nothing but those days, those days she was her slave, those days that she was under her prison, memories marasu dadin tunawa ne suka yi ta dawo mata... hawaye masu xafi suka dinga xuba idonta, Hajiya Fatima ta haska ma Hansai Jiddah, Hansai ta saki roban baranta da sandan hannunta cikin rawan murya tace "Jiddah??" Mikewa Jiddah tayi da kyar tana kallonta hawaye na saukowa idonta, Bibalo ta fara kokarin xaunawa ita ma bayan hasken fitila ya gwada mata fuskar Jiddah amma ta kasa kawai sai ta hakura tana ta kallon Jiddah babu kiftawa, juyawa Hansai tayi, tayi backing Jiddah bata sake cewa komai ba, Jiddah ta dinga share hawayen da ya ki tsaya mata cikin sanyin murya tace "Ina yini Baabarmu" Kamar jiran jin hakan Hansai take ta fashe da kuka tace "Ni babu wanda ya ta6a xaunar da ni ya nusar da ni a kan kamun da Allah ke ma duk wanda ya ci amanar maraya ko ya xalunci maraya, babu wanda ya ta6a nusar da ni, da na samu me nusar dani da ba haka ba.... Yau ga yanda rayuwata da na 'ya ta tilo da nake bala'in so a duniya ya dawo, kaico..." Kuka take tana girgixa kai tace "Lallai Allah baya yafe hakkin wani..." Hajiya Fatima dai tayi shiru, Jiddah ta durkusa kasa tana kuka sosai tace "Ni baki ta6a min komai ba baabarmu, idan ma kin min ni na yafe maki tun tuni saboda ke mahaifiyata ce" Hansai ta juyo ta xauna kasan dakin hawaye na xuba idonta tace "Kin ga yanda rayuwa ta juya mana baya ko Jiddah, ba komai bane illa hakkin ki, idan ma ni ban cancanci yafiyar ki ba, ki yafe ma er uwarki Bibalo ubanku daya..." Jiddah ta hade kanta da gwiwa ta ma kasa ce mata komai sbda kuka, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Hansatu ai da Jiddah bata yafe maku ba da baxa ku ganta a nan ba, rike kun da bata yi a xuciya ba yasa ta taho har inda ku ke yau...." Hansae na share hawayenta tace "Ai kuwa na gode, na gode, Allah ya ji kan mahaifanta..." Bari in shimfida maku abu ku xauna, da sauri ta tashi ta dauko wani bugun cement ta shimfida masu, Hajiya Fatima ta xauna, Hansae ta koma can gefe ta rakube, Hajiya Fatima ta kalli Jiddah tace "Je ki ki kira Aliyu" Tashi tayi da kyar ta fita xuwa kofar gida. Fitowa Abuturrab yyi daga mota yana kallon Jiddah ganin hawaye idonta, ta sunkuyar da kanta ta nufesa ta rufe fuskarta jikinsa wasu hawayen na xuba idonta, bin wajen yayi da kallo ganin da mutane ya bude back seat ya sa ta shiga shima ya shiga ya kulle motar ya rungumeta a rikice yace "Why are u crying?" Kuka kawai take ta kasa ce masa komai tana kallonsa, duk tunaninsa Hansai ce tayi mata wani abu don ya ga shigarta gidan, ganin xai fita motar ta rikosa ta boye fuskarta jikinsa tana shessheka tace "I don't know what would have become of me da ace baka shigo rayuwata da wuri ba, I don't know what my fate will have been..." Kasa ci gaba tayi ta rungumesa sosai tana kuka, da damuwa yace "I am begging you Jiddah, forget the pass and face the future, forget ur pass... iyayenki mutanen kirki ne shi yasa Allah bai bar ki kin tagayyara ba..." Gyada masa kai kawai take hawaye na sauka idonta, ya dago kanta yayi kissing lips dinta yayi kasa da murya yace "Say Alhamdulillah for everything wife" Cikin sanyin murya tace "Alhamdulillah" yace "Ba xa ki sake shiga gidan ba kuma, u wait for us har mu fito" Tace "Noo plss, ban yi magana da kanwata ba" bai saurareta ba ya sauka motar ya kulle ya wuce cikin gidan don baxai iya jure ganinta tana kuka ba, Ba tare da ya kalli Hansai ba ya gaisheta yana tsaye a dakin, ita ma din dai ta kasa kallonsa sai sunne kai take, Hajiya Fatima na kallon Hansai tace "Ina jin ki Hansatu" A hankali Hansai tace "Toh wllh iya abinda na sani kenan Hajiya, amma da xa a gano inda kakar Jiddan tayi aiki nasan su mutan gidan baxa su rasa sanin wani abu a kan kakar ba don a can ma aka ba Marigayi isuhu auren Marigayiya Aisha wato mahaifiyar Jiddah, yanxu haka ma ina da hotan kakar tata da mahaifiyarta, ita Aishan ta bani hoton da kanta ana sauran watanni ta rasu wai in ajiye ma Jiddah, amma ban ta6a nuna ma Jiddah hoton mahaifiyarta ba" Tana magana ne tana goge sabon hawayen dake xuba idonta, Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ko xaki bamu hoton..." Mikewa Hansai tayi ta bude Ghana must go dinta ta tono har can kasa ta ciro wasu hotuna, Hajiya Fatima na ta haska mata da wayarta har daga karshe tace "Toh ga hoton nan" Amsa Hajiya Fatima tayi tana ta kallon hoton Mahaifiyar Jiddah wanda da ace kyan mahaifiyar ta tayi da ba haka ba, babu ta inda take kama da mahaifiyarta da kakarta wanda hakan ke nuna cewa da Abbanta tayi kama, can ta girgixa kai tace "Allah sarki, amma ke baki da masaniyar inda tace maki kakar Jiddan tayi aikin? Wato ita Marigayiya" Hansai tace "Wllh ban sani ba, wanda xai san gidan dama Isuhu ne, Kuma rai yayi halinsa" Hajiya Fatima tace "Toh shkkn mun gode, xa mu tafi da hoton a ga abinda hali xai yi" A hankali Hansai tace "Toh shkkn Hajiya" Hajiya Fatima tace "Ita wannan yarinyar taki kin kaita asibiti kuwa?" Hansai tace "Ina muka ga kudin asibiti Hajiya?" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajiya Fatima tace "Babu damuwa in sha Allah, gobe ko ni kadai xan dawo nan sai in baku abinda xan baku a kai ta asibiti, Allah ya tashi kafadunta" Hansai na matsar hawaye tace "Ameen Hajiya" Abuturrab ya juya ya fice daga dakin don shi ko kadan bai ji tausayin Hansai ba idan ya tuna irin gallazawan da ta dinga yi ma Jiddah sai yaji ransa na baci, Hajiya Fatima ta mike tayi masu sallama ta bi bayansa. Bude back seat yayi ya ga Jiddah na bacci, kallonta ya dinga yi with surprise, Hajiya fatima da ta karaso wajen tace "Kyaleta kar ka tasheta" Bai ce komai ba ya shiga driver seat tace "Baxa ka tsaya kayi magrib ba son?" Yace "Aa bari mu tafi Mama, xanyi a gida" Dai dai kofar gidan Hajiya Fatima Abuturrab yayi parking, ya juya yana kallonta yace "Mun gode sosai Mama Allah ya saka da alkhairi, we appreciate ur effort" Tace "U are welcome son, ga hoton ka ajiye wajenka, sai kuma mu ga abinda Allah xai yi" Ya amsa yace "In sha Allah" daga haka ta sauka ta shiga cikin gidanta shi kuma ya juya xuwa kofar gidansa, mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki yayi parking ya sauka ya bude back seat yana kallon Jiddah yace "Jiddah" Dagota yayi ta bude ido da sauri, sauko da ita yayi daga motar ya kulle suka wuce ciki, Da kyar Jiddah ta iya jira aka yi Isha sannan ta kwanta ko wanka bata yi ba. Horn Abuturrab yyi kofar gidan Umma misalin karfe sha biyun rana, ana bude gate din gidan ya shiga yyi parking, har sannan bai nuna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login