Showing 270001 words to 273000 words out of 346625 words
Chapter 91 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
him to go back to Aneesah kamar yanda ya fada mata, Ganin he is becoming uncontrollable ya saketa babu shiri don baxai so ta ci gaba da tsoronsa da take cewa ba, da kyar ya rada mata good night a kunne sannan yayi kwanciyarsa, ita dai har lkcn bata bude idonta ba, yana jin sanda ta fara bacci jin saukan breathing dinta a hankali, amma shi ya kasa baccin sai juye juye yake, daga karshe ma ya sauka kan gadon ya fita dakin ko xai samu relieve.... Da asuba bayan ya dawo masallaci ya shiga dakin ya ganta xaune kan darduma duk da bai tasheta ba, abinda bai ta6a ganin Aneesah tayi ba duk xamansu, kasa kallonsa Jiddah tayi, ya xauna gefen gado a hankali yace "Good morning...." tana wasa da fingers dinta a hankali ita ma tace "Ina kwana" yayi kasa da murya yace "How was ur night?" Kin ce masa komai tayi, ya shafa kansa yace "Ki shirya xa mu tafi kano anjima" Yana fadin haka ya mike ya fita dakin. Karfe sha daya saura suka nufi airport a Uber, kamo hannunta yayi jin tayi shiru, yayi kasa da murya yace "Tell me what you are thinking now... Yesternight?" Ai bata san lkcn da ta daga kai ta kallesa da sauri ba, ya kashe mata ido yace "You like it?" Dauke kai tayi ta turo baki, shi dai murmushi kawai yake yana kallonta yana murxa hannunta har suka isa airport. Kafin 12 suka sauka airport din kano, ita dai Jiddah kallon Abuturrab kawai take yana gaisawa da ma'aikatan airport din, duk inda ya bi xaka ji an kirasa da Captain, inda yake parking din motarsa a airport din suka tafi, bayan ya ajiye kayansu a bayan motar ya bude mata front seat ya wara manyan idanuwansa yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba ta karaso ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga motar, bayan yayi warming dinsa suka fita airport din, muryarta ya ji tace "Me yasa ake kiranka Captain?" Ya d'an kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Kema ki fara kirana da hakan mana" ta ta6e baki tace "Baxan kira ba" Yace "Saboda me?" Tace "Haka nan" Yace "Toh kinga ai Aneesah ma haka take kirana" ta kallesa da kyau tace "Dalilin da yasa baxan kiraka haka ba kenan ai, na fi ka sanin haka take kiranka" Sosai ta basa dariya jin how serious she was, yace "Ohh really" confidently tace "Ehh, kuma ka daina min magananta bana so, komai sai ka wani kira min ita as if i have anything to do with her, meye hadina da ita?? To ni bana so, ka daina min haka" a hankali yace "Toh ya hakuri, na daina" Hade rai tayi ta dauke kai tana kallon wajen glass, haka nan kawai yaji reaction din da tayi displaying ya masa dadi, murmushi kawai yake yana tukinsa, can ya kamo hannunta a hankali yace "Na fa ce kiyi hakuri na daina tunda baki so, why are u sulking? Why the pout now" Hade kai tayi da gwiwa xata fara kuka tace "Komai sai ka wani ce min Aneesah ni meye ruwana da ita to?" Cikin sanyin murya "Toh ai nace kiyi hakuri baxan sake ba koh?" Ta dago kanta tana matsar kwallan da ya kawo idonta, yayi kasa da voice dinsa yace "i am sorry dear" Ita dai bata ce komai ba, suna fara nisa a tafiyar ta jinginar da kanta da kujera ta lumshe ido, yana ganin alamar bacci xata yi, yayi parking ya d'an kwantar mata kujeran motar sannan ya ci gaba da tafiya. Suna shigowa garin kaduna Abuturrab ya dau wayarsa yayi dialing number Aneesah, har ya katse bata dauka ba, ya sake kira nan ma sai da ya kusa katsewa sannan ta daga tayi shiru, ajiye wayar yayi bayan ya sa a handsfree yace "Baki ga miss calls dina bane jiya da daddare da yau da safe?" Jiddah ta d'an sace kallonsa sai kuma ta dauke kanta, A takaice Aneesah tace "Ehh" yace "Ohk good, ya gida?" Tace "Yana nan yanda ka bar sa" Yace "Bak'in ki sun tafi?" Tace "Su tafi ina? Dama ashe a kanka suke xaune ban sani ba, dama sun tare maka wani abu kenan? kuma ai naga bak'in nawa guda biyu ne a ciki, kuma su kadai nake da ikon ce ma su tafi, Daya bakuwar kuwa kai ke da hurumin ce mata ta tafi ba ni ba ai" Shiru yayi na few seconds sai kuma yace "Kina son xaman lafiya da ni kuwa Aneesah?" Tace "Inaaa sai xaman tashin hankali, xaman lafiya kam ai sai da uwar gida kamar yanda ka taso kaga ake yi a house, to meye abun mamaki don ka bi footstep din? ai ba abun mamaki bane wannan" Yace "What???" Tace "Ya uwargida? Fatan ana cin amarci yanda ya kamata..." katse wayarsa yayi, Jiddah ta kallesa tace "Kaga ka ja mata kunne ta cire bakinta da idonta a kaina babu abinda na hadata da ita, ba ruwana da ita..." Abuturrab da xuciyarsa ke tafarfasa jin maganan da Aneesah tayi masa ya nufi gidansu kawai, a compound yayi parking ya kalli Jiddah da ta wani hade rai tun bayan tambayarta da Aneesah tayi, bude motar yayi ya sauka, ta bude ita ma ta sauka, xagayowa yayi yana kallonta, a hankali yace "Toh xan ja mata kunne Ummi" banxa tayi masa, yayi murmushi suka shiga gidan a tare, parlon Ummi suka shiga bayan ya gaida Umminsa ya fita ya bar su ya shiga dakin Hajja, Nafisah na xaune dakin sai dariya take kasa kasa, Hajja kuma na xaune saman darduma ta maka wani uban glass a idonta ta sa wani lafiyayyen leshi ta yafa mayafi, ga dankunnenta da sarka kai kace anguwa xata amma wayar Nafisah ne a hannunta suna gaisawa da wasu makotansu na Masar bakinta har kunne, duk ta cika dakin da muryarta tana jagwalgwala larabci da Hausa, Tun Nafisa na dariya kan kujera har ta sauko kasa, ko bin ta kan Abuturrab dake tsaye yana kallonta Hajja bata yi ba, da sauri ta mika ma Nafisah wayar tace "Ke taho ki duba sun daina motsi ko notwork din ne ya dauke" Abuturrab ya amshe wayar ya kashe data sannan yace "Daga can network dinsu ya dauke sai xuwa dare xaku iya sake magana da su" rai bace Hajja tace "Toh Allah ya tsine wnn notwork din, don rashin tsoron Allah baxai bari ayi xumuncin da Allah yace ayi ba?? Ni naga bala'i amma lefin wanda suka dauke shi notwork din ne, to ya wuce arnaye da basu san meye xumunci ba..." Abuturrab dai bai tanka ta ba ya mika ma Nafisah wayarta, Hajja tace "Kawai ina xaune fa Nafisah ta shigo wai ai gashi takwararta daga can Masar ta kira tace ta kawo min waya xamu gaisa da mokatanmu da aka yi xaman mutunci na can Masar din, baka ga yanda suke ji da ni suke sona ba wllh, ashe duk sun yi kewata ni ina nan ban sani ba, kasan fa duk safiya ina fitowa in xaga titin anguwan su Nafisah ba irin rubabbun titunan Najeriya ba da idan baka yi hankali ba idan ka afka wani ramin da kyar xa a fiddoka idan ma ba shi ne ajalinka ba, makociyar tata ma tare suke da uwarta shine muke kawance da uwar amma uwar duk ta kwararrabe, kasan tsufansu fa bashi da kyau, wllh yamushewa kawai suke kamar fanken da ya huce, to Nafisah na gaya min na yi maza maza na bude akwati na ciro tsadadden leshi na da mayafi wanda na sa da bikinka da yar iskar can, na ciro dankunne da sarkata na saka, sannan nayi maxa na ciro gilashina na saka shi ma, na shimfida darduma na xauna, to ai dai gwara haka ko?" Abuturrab yace "Gaskiya" Hajja tace "Atoh, kawai sai su ganni su xata wahala nake sha a Najeriyan duk da dai wahalan nake sha don babu komai xama gidan Usman sai wahala, kawai saboda Hauwa nake xaune in ga ta yanda xai dawo da wancan bokanniyar da na ya saka...." Xaunawa Abuturrab yayi yana kallon Nafisah yace "Ba an gama wayar ba?" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, Hajja tayi kasa da murya tace "Ina Jiddar??" Yace "Tana parlon Ummi, na xo mu yi magana da ke ne" Hajja ta gyara xama ta cire gilashinta ta ajiye tace "Ina sauraronka, ai gwara da ka korata don bakinta baya haila" Yace "Dama tun ana gobe xa a kai Jiddah can gidana Aunty da yan uwan Aneesah guda biyu ke gidan, kuma har yanxu sun ki tafiya ban san xaman me suke ba" Hajja tace "Wacece kuma Aunty?" Kallonta kawai yake, ganin da gaske bata gane wace Auntyn ba yace "Auntyn nan gidan" Hajja ta gwalo ido tace "Hafsah???" Yace "Ehh" Salati Hajja ta rafka ta rike kai tace "Huhuhu dama Hafsah na kaduna ban sani ba, sannan kadunan ma gidanka? Me ya kai ta gidanka ni 'ya su?" Abuturrab yace "Nima ban sani ba" Buda baki Hajja tayi tace "Yaushe ta tare gidan naka bani da labari?" Yace "Fin sati daya kenan" Mikewa Hajja tayi tana gyara yafin gyalenta tace "Mu tafi gidan, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin inda matar uba ta tare gidan d'an kishiyarta ba bayan miji ya saketa, ai shkkn kuma ta kashe maka gida don Allah kadai yasan karatun da ta dinga xuba ma Aneesah na makirci da kuma gun bokaye nawa ta kai ta, Amma Allah ya tsine ma Hafsah albarka, Allah yayi daya daya da ita, mu tafi gidan yanxu duk xa su ci kuturin ubansu, ni da nake er banxa kuma, ae ba canxawa nayi ba" daga haka ta fice daga dakin, murmushi Abuturrab yayi ya mike ya bi bayanta, parlon Ummi ya fara shiga ya tarda ita tana yi ma Jiddah dake xaune kasa ta sunkuyar da kanta Nasiha, Ummi na ganinsa tace "Toh tashi ki je ki gaida Hajjan" Abuturrab yace "Xa mu je can gidan tare da ita yanxu" Ummi tace "Hajjan?" Yace "Ehh" tace "Toh Allah ya tsare, baxa ku tafi da abinci ba?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh ki bata ta taho da shi, xan je mota Hajja na waje" Ummi tace "Toh shkkn" Juyawa Abuturrab yyi ya fita, Bayan Ummi ta xuba ma Jiddah abincin a warmer biyu ta ba Nafisah ta kai mota Jiddah na biye da ita a baya suka fita kofar gida, a bayan motar Jiddah ta xauna bayan ta gaida Hajja, sannan ta ajiye warmer din abincin gefenta, Hajja na kallon Abuturrab tace "Ya naga ta xabge haka daga tarewa Aliyu? A cikinsu ka bar ta ka tafi tukin jirgin naka ne?" Yana kallonta ta madubi yace "Daga kano muke yanxu haka" Hajja tace "Atoh dole ta rame, maxa kai ni gidan, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin wannan tabargaxan ba sai yanxu da xanje in gane ma idona, matar ubanka ta tare gidanka bayan an saketa matar da ba shiri take da uwarka ba ta rasa yanda xata yi da ita ne kawai? Mu je kawai in fatattaki yan iska, Allah da a Masar ne har kai da ka bar su na sati dayan a gidanka sai an hukunta ka don cewa xa ayi kai ne babban d'an iskan, ai duk wanda bai xauna a Masar ya ga yanda suke rayuwa ba yayi asara a duniya, Allah yayi ma kasar Masar da mutanen cikinta albarka sun koya min abubuwan rayuwa iri iri wllh, ba gashi ba daxu sbda xaman mutuncin da muka yi da su kirana suka yi ta wayar salulan Nafisah muka gaisa muna ta xabga larabci da su" Babu wanda ya tanka Hajja a motar har suka isa gidan Abuturrab, parking yayi a parking space sannan ya sauka motar, Jiddah ma ta sauka ta dau warmers din biyu, tuni Hajja ta bude daya side din motar ta sauka tayi cikin gidan, Abuturrab ya kalli Jiddah ya xaga ya amshi warmer daya a hannunta yayi kasa da murya yace "Kin gaji ko?" Bata ce komai ba ya dau makullin dakinta a mota ya mika mata yana kallonta yace "Mu je" Ta fara tafiya yana biye da ita, tuni Hajja ta shige parlon gidan ta ci sa'ar ganin Aunty, Safara'u, da Falmata xaune a parlon, Aneesah kuma na kitchen tana dafa masu indomie don dawowarsu daga wani waje kenan, Duk suka juya suna kallon Hajja, Hajja ta rafka wani uban salati tace "Wacece wannan nake gani kamar Hafsah tsohuwar matar Usman??" Tun da Aunty ta kalleta sau daya ta dauke kai tana ci gaba da danna wayarta tana taunar chewing gum, Hajja ta karasa tsakar parlon tana kallon su Safara'u tace "Su kuma masu k'iran samudawan nan fa??" Hajja ta rike kai tace "Huhuhu gidan Aliyu ya xama dandalin zawarawa, an shiga uku an lalace, to wllh baxai sa6u ba ko wacce ta tashi ta tafi gidan ubanta, idan ya kama ku tafi har da Nanisar ce to ku tafi don ai sbda ita ku ka xo dama...." Aneesah ta fito daga kitchen da sauri jin hayaniya, Safara'u na kallon Aneesah cike da izgilanci tace "Ke... wacece wannan kuma ta shigo mana haka ba control?" A fusace Hajja tayi mata dakuwa tace "Uwaki ce ta shigo.... shegiya kawai 'ya yan banxa gayyar tsiya, har ni xaki kalli tsabagen idona kice baki san ni ba, to uwar uban Aliyun ce, kuma tun muna imu imu ba a jiyo kanmu a titin anguwan nan ba ko wacce ta tashi ta dau jakanta ta kama gabanta, gidan jikana ba dandalin karuwai bane, mu ba arnaye bane..." Falmata ta mike tana mata wani kallo tace "Ai kuwa mu ba karuwai bane wllh... Mun fi karfin a kira mu da haka..." Tuni Hajja tayi hanyar stairs bayan ta jefa mayafinta saman kujera xata je watso duk jakunkunan da ta gani a sama, Dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, Safara'u ta mike ta nufesa tana huci ya ki tsayawa har yaje ya ajiye abincin hannunsa saman dining table, ita kuwa bata fasa bin sa ba tana cewa "Ashe dama kai ka gayyato mana tsohuwar can ta xo ta mana tijara tayi mana rashin mutunci?" Abuturrab ya juya yana kallonta yace "Ehh, 'yar ku nake aure ba ku ba ai, so i see no reason xa ku tare a gidana for more than a week now..." Mikewa Aunty tayi ita ma ta nufesa xuciyarta na bararraka tana nuna sa da yatsa tace "Don ubanka ai baka burge ba da har kai ka kasa magana sai da ka gayyato mental kakarka... Kuma baka burgeni ba da baka gayyato axxalumar uwarka ta xo mun goga a nan da ita ba, ita ya kamata ta xo ta nuna iko ba tsohuwar can ba, daga nan sae mu cashe da ita" Abuturrab na kallonta da kyau yace "I do respect u for being my father's wife then.... Kar ki sake involving mahaifiyata a lamarin ki, take my mothers name off ur mouth Aunty Hafsah, do not push me...." Bude baki Aunty tayi tana kallonsa da mugun mamaki, Ita dai Jiddah tunda ta lallaba ta shigo gidan ta haura sama abunta ba tare da ma anyi noticing dinta ba, mari Aunty ta kai masa tana huci, cikin tsawa tace "Ni kake warning Aliyu?? Ni yau kake warning a kan uwarka?" Kallonta kawai yake trying so hard to control his rising temper, ta cakumosa tace "I am asking u, ni kake yi ma warning? To da kai da matsiyaciyar uwar taka kun ci kaxa kaxan ku" Falmata dake tsaye wajen tace "Atoh ae ba ke kika haifesa ba what did u expect..." Ko rufe baki bata yi ba Abuturrab ya sauke mata tagwayen mari masu lafiya, lkci daya ya nufi Aneesah dake tsaye har sannan bakin kofar kitchen, sae da idanuwansa suka bata tsoro amma ta dake tana kallonsa, strictly yace "Minti ashirin idan suka kara min a gidan nan to a bakin aurenki, minti ashirin din na cika dama ki tattara ki bi su, don ko kayanki baxa su kwana min a gida ba" Daga haka ya nufi stairs kamar xai tashi sama, Aunty ta bi sa da kallo baki a hangame, Falmata kuwa ji tayi gaba daya jinta ya dauke sai dumm kawai take ji, daga sama aka dinga jefo jakunkuna da handbag downstairs, Aneesah ta nufi Safara'u da sauri cikin tashin hankali tace "Don girman Allah Aunty ku rufa min asiri ku tafi kar ku kashe min aurena, i will sort everything out my self, don Allah ku rufa min asiri ku tafi" tana gama fadin haka ta tafi da sauri tana dauko jakunkunan da Hajja ke watsowa tana ajiye masu a tsakar parlon, tsaf sai da Hajja ta watso komai kasa sannan ta sauko tana huci tace "Ko wace karuwa ta dau jakarta ta bar min gidan jikana, idan kuwa ba haka ba wllh yanxun nan sai in sa shi ya saki Nanisar in ga ta tsiya, daga nan kunga ba ku ba, har ita baxata kwana gidan ba...." Aneesah da duk ta rikice ta nufi Hajja da sauri tace "Xa su tafi Hajja, duk yanxu xasu tafi idan Allah ya yarda" Safara'u da tunda take ba a ta6a mata cin mutunci irin na ranan ba a tunaninta ta nufi jakarta ta dauka ko gyale bata tsaya yafawa ba ta nufi kofa tana rike da shi a hannu, Falmata ma ta tafi ta dau jakanta ta bi bayan Safara'u, Hajja tace "Banda ma arne wa xai yi wannan abinda ku ka yi?? Ke an sake ki kin ki tafiya benue kin tattaro kin dawo gidan d'an kishiyar da kika yi ta cuta na shekara ashirin da shidda, tirrrr anji kunya wllh Hafsah" Hafsah na kallon Hajja tayi Murmushi rainin hankali tace "Ai ni da Usman mutu ka raba, ko ke da kika haifesa baki isa ki raba mu ba wllh, ke dai ce kike tunanin ai ya sakeni, amma babu abinda ya canxa game da matsayina a wajensa lkci kawai ake jira" Daga haka ta nufi kofa bayan ta