Showing 126001 words to 129000 words out of 346625 words
Chapter 43 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
tayi mata sae jiran takardan take ya xo garesu, ai ko ana miko mata bayan ta karanta tayi wani murmushi ta mika ma Umma, Umma ma ta mika ma Ummi bayan ta karanta, Hajja tace "Amma na tsorata da lamarin Aliyu, Kunga da yana sonta da gaske ai kuka xai sakar mana a nan yace shi baxai saketa ba, amma almurin kamar jira yake gashi ya cike takarda da rubutu, aa gaskiya ba sonta yake ba, ku duba fa babu wani gardaman a xo a gani ya rubuta takardan, Lahh wanne mutum a masar, to amma ai shkkn sae a bani ita mu tafi Bauchi don kwana biyar xanyi a can kafin in koma Masar, idan ma kunga xaku iya biya mata jirgi kawai sai mu tafi tare, ai d'a na kowa ne bawa sai mai shi..." Umma ta kalleta da sauri tace "Hajja karatu xa a sata ai" Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Shi kuma masar din duk jahilae ne ba a karatu.... Banda neman magana ina ruwanki Ramlah, ni fa da d'a na nake kika tsomo baki, ko Ahmad ne ya tsintota a hayi?" Ta gefen ido Ummi ke kallon Hajja, Abba yace "Dama haka ake tafiya Masar din Hajja, ina laifin ma kice idan kin tafi a turo ta?" Hajja tace "Kai ba ruwana ni ku rabu dani, xa a Wani min caaa, dangin uwa ko na uba, meye hadina da ita banda Aliyu da ya aurota a gantale ya saketa kuma a gantale, kuma ma wasa nake, haka kawai inje in daura masu nauyi nima da ya ake bani yar gurasar da ake ban balle na tafi da wata?" Mikewa tayi tace "Banda Najeriya ina ake aure a gantale ayi saki a gantale, Hauwa taho ki bani sakon da na baki" Tana kai wa nan ta fita, Ummi ta mike ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da harara, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Alhaji xan tafi da Jiddah ta koma gidana ta fara karatu" Caraf Aunty ta amshe tace "Me xai hana tayi a nan din, ga dai sa'aninta su Aisha" Abba yace "Da nan din da can ai duk daya ne, Allah dai ya bata ilimi mai amfani" Ko kadan Aunty bata ji dadin haka da Abba yace ba, Umma tace "Toh nagode Alhaji, Allah ya tayani riko" Duk suka amsa mata da "Ameen" amma banda Aunty da ranta ya baci, can dai tace "Amma ai xata dinga xuwa nan din ko" Umma tace "Aa me xai hana kuwa" Umma na fadin haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je Jiddah" Jiddah ta mike a hankali ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da kallon tsana, shi kam Abba tausayinta kawai yake ji, banda rashin gata ya xa ayi hakan ya faru gareta ma. Bangaren Ummi Umma ta kai ta, Ummi na xaune parlonta da Hajja dake mata magana kasa kasa, amma ganin Umma sai tayi shiru, Umma tace "Toh yaya mun tafi sai da safe" Ummi tace "Baxa ku yi isha ba?" Umma tace "Eh to bari inyi" Daga haka ta karasa bedroom din yayarta, Jiddaj dai na rakube jikin kujera, Ummi ta kalleta tace "Kije kiyi sallan ke ma" Mikewa Jiddah tayi ta fita, Hajja ta tabe baki tace "Toh ai gwara ma da aka kashe wannan auren don ai Aliyu d'an usuli ne, ita kuma bamu san yaya ba" Ummi tace "Ai babu wanda bashi da usuli Hajja" Hajja tace "Aa Hafsat dai bata da shi, an rasa gane ko kwatakwali ce har yau, duk da tace uwarta yar Benue ce" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja tace "Shi yasa gashi duk ta amshe gida tayi bake bake, komai sai inji Usman yace Hafsa, to wacece kuma Hafsa, dama Hadiza ta bani labarin irin xaman da ku ke yarda ce kawai ban yi ba, gashi duk ta rufe maki baki ta amshe gida, wa ya sani ko ma har da ya yanki? Tunda na xo naga take takenta komai sai ace sai ita, to a kan me?" Ummi tace "Aa Hajja kowa ai da matsayinsa a gidan" Hajja tace "Toh kunga lalacewa ko? Wani matsayi matar da ta kwace maki miji ta karfi, me yasa kike abu sakwa sakwa kamar warce aka ce ma je ki kya gani Hauwa, komai fa na bikin nan naga sai dai ace Hafsat to wacece kuma Hafsat, gashi ana maganan tabargaxan da yaro yayi mata tayi bake bake a kan xancen kamar d'an ta, to ni tunda na xo ma ba sau daya Salem ya shigo gaisheni ba, duk sun tsotsa a nono wllh, dubi fa Aisha kamar yar karuwai Allah na tuba, to ba dai komai tunda duk jikokina ne, amma idan xaki tashi tsaye ki amshi gidanki ki tashi" Fitowar Umma yasa Hajja tayi shiru, Umma tace "Toh sai da safe Hajja, yaya sai mun yi waya" Hajja tace "Toh Allah ya ba yara xaman lafiya ya kauda fitina amma ki dai je asibiti kiga kibar ta mecece kika narka haka kinji" Umma bata tankata ba har ta fita, Hajja tace "Toh sai da safe" Sai da Jiddah ta sake shigowa tayi ma Ummi da Hajja sai da safe sannan suka bar gidan tare da Umma, har driver ya maida su gida Jiddah bata cewa komai, duk tayi sanyi sosai, ta rasa ko farin ciki take ko bakin ciki, Wajen karfe tara Umma ta xaunar da ita a dakinsu Maimoon tace "Kina ji na Jiddah?" Jiddah ta daga kai ta kalleta, Umma tace "Kin dai ga yanda abubuwa suka kasance, ni nasan Abuturrab bai da niyyar cutar dake a ransa, kuma har abada ina son ki daukesa da girma da mutunci don ya maki abinda ba kowa xai iya maki ba a rayuwa, duk abinda xaki xama a rayuwa nan gaba Allah ne ya tabbatar da hakan amma Abuturrab ne sanadi, ina son kuma ki maida hankalinki kiyi karatunki, kin san wacece ke kinsan daga inda kika fito" Hawaye ne ya shiga xarya idon Jiddah tana kallon Umma, Umma tace "Ni kuma ina fatan Allah ya bani ikon yi maki duk abinda ya kamata a rayuwarki Jiddah" Cikin rawar murya tace "Toh Umma baxan sake ganinsa ba kenan?" Da mamaki Umma tace "Don me baxa ki gansa ba, in dai Allah ya kawosa gidan nan ai xaki gansa, sannan xaki dinga yawan xuwa gida Ummi, idan baku hadu a nan ba xaku hadu a can, balle ma nace tsakaninki da shi kawai girmamawa ki daukesa kawai a matsayin babban wan ki, nasan shi ma a matsayin kanwarsa xai daukeki" Jiddah ta share hawayen idonta a hankali tace "Toh Umma nagode" Umma ta sakar mata murmushi, har ranta taji tana son Jiddah tana kuma son inganta rayuwarta, Umma tace "Gobe da safe sai mu je can gidan a kwaso duk wani abu naki" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Umma ta mike tace "Toh sai da safe" Daga haka ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo wasu hawayen na kawowa idonta, Umma na fita Maimoon ta shigo dakin. Washegari misalin karfe Goma Umma ta kira Abuturrab, miss calls tayi masa kusan uku kafin ya daga, bata amsa gaisuwan da yake mata ba tace "Kana gidanka ne?" Yace "Ina nan" Umma tace "Ohk i am coming now" Bai ce komai ba ta katse wayar, tare driver ya kai su gidan Abuturrab da Jiddah da Maimoon da safiyya, mai gadi ya bude masu gate driver ya shiga da motar cikin compound, Umma ta sauka motar sannan su Jiddah, Hijab ne har kasa jikinta, suka bi bayan Umma xuwa entrance din parlon, a bude suka tarda parlon, yana kwance saman doguwar kujera da jallabiya, suna hada ido Jiddah tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na bugawa da karfi, sanye yake da jallabiya ya mike xaune a hankali yace "Ina kwana Umma?" Tace "Lafiya lau, ya gajiyan jiya?" Yace "Alhmdlh" Maimoon ta gaishesa ya amsa, Jiddah ma tace "Ina kwana?" Sai dai taki yarda ta kallesa, bai amsa ba ita dai ta xauna kasa kusa da kujeran da Umma ta xauna, Umma tace "Jiddah xata debi kayanta na nan ne" Ba tare da ya kalli Umma ba yace "Ohk" Umma ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je" Mikewa Jiddah tayi ta nufi stairs Umma na biye da ita Maimoon ma ta bi bayansu, da ido Abuturrab ya bi su har suka haura sama, Kaf sai da Umma ta kwashe duk abubuwan Jiddah dake dakin, Maimoon ce ke kai wa booth din mota, Ita dai Jiddah na tsaye jikin kofa sai kallonta take, ta rasa dalilin da yasa taji tana son tayi kuka, Umma ta mika mata babban ledan da ta hada duk abubuwan gaban madubi a ciki tace "Ki kai wannan" Jiddah ta karasa ta amsa ta nufi kofa ta fita, a stairs suka hadu da Maimoon, Maimoon tace "Kawo in kai toh" Jiddah ta kirkiri murmushi tace "Xan kai" Maimoon ta shiga dakin ita kuma fita, satan kallon parlon ta dinga yi taga baya nan, ta fita balcony, sosai gabanta ya fadi da ta gansa a xaune kan kujera yana danna wayarsa. Xata sauka stairs din balcony din taji yace "Toh ni dake wa yyi lose?" Ta juya tana kallonsa don bata gane me yace ba, yayi wani murmushi ya mike, speaking calmly yace "Kema kinsan wllh idan ba kaddara ba babu abinda xai hadani dake a rayuwa balle har in aureki bisa kuskure, aurenki da ni babban kuskure ne wanda nayi sbda in taimaki rayuwarki.. banda haka ai ni nafi karfin ki, komai da ya faru ya faru ne sbda haka Allah ubangiji ya tsara, duk da fin ki komai da nayi haka na hakura na xauna same roof dake sbda biyayya da kuma xuciyar musulinci, amma wai har ke xaki je ki sanar ma iyayena na sakeki? Toh yanxu da na maki sakin me hujja akwai wani abu da xai ragu a rayuwata ko kuma wani asara xan yi?" Ita dai kallonsa kawai take ko kiftawa babu, yayi wani murmushin kuma yace "Toh na maki duk abinda na maki saboda Allah ba don ki nuna kin san ni wataran ba, kai ni ko a hanya kika gan ni kar ki ta6a nuna kin ma san ni don kunya hakan xai bani, kiyi wucewarki inyi wucewata, na kuma fi kowa farin ciki da murnan xuwa karshen wannan al'amarin, i am now free like every other...." Jiddah dai kallonsa kawai take bbu ko kiftawa, ganin ya koma ya xauna cikin sanyin murya tace "Toh nagode" Daga haka ta juya ta kai ledan mota... Tare suka fito gidan da Umma bayan duk an kai komai mota, Har sannan yana xaune balcony, Umma tace "Toh sai anjima, yaushe xaka koma aikin" Yace "Anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya tsare" Daga haka ta nufi mota, Maimoon tace "Sai anjima yaya" Yace "Ohk" Sai da Jiddah ta sauka balcony ta d'an kallesa tace "Sai anjima...."
*Rumor Creators how market? A masar dai ba a haka idan xaku gyara ku gyara, ku kuma masu karanta na bati da kuka fi kowa xakalkalewa a xo a biya bashi dai ko xa a samu nutsuwa, my fans dat wished me speed recovery ina godiya Allah ya saka da alkhairi sbda ku nace let me manage and give this little update na karfin hali, nagode sosai, snn abinda ke ci mun tuwo a kwarya shine yanda masu karantawa a free suka fi kowa bada hakuri, wllh duk sun cika min inbox, don Allah bakwa jin kunya ne, baka biya abu ba ka dage sai an ci gaba, tsaf ina da saved number din duk wanda yayi subscription din littafin nan ku ji in gaya maku* 🙄
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*
*Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*
*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*
*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing😍*
_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_
*Akwai hadin:*
*Mai da tsohuwa yarinya*
*Uwargida ta koma amarya*
*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*
*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*
_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_
_Call/WhatsApp:08061570778_
_IG@mik_yaaj_saady_
[6/11, 9:05 PM] +234 803 540 6041: Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta, da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba, tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata ga ya dau jakar laptop dinsa ba. Bayan fitarsa da minti kusan talatin ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fita, a reception din hotel din ta gansa xaune da shayi a kan table din gabansa idonsa a kan screen din wayarsa, sosai gabanta ya fadi tayi still a inda take, dago kai yyi suka hada ido, tana ganin haka ta nufi kofar fita da sauri, da ido ya fara bin ta da mamaki, lkci daya kuma ya mike ya bi bayanta, fita tayi compound din hotel din, ya fara kalle kalle sbda baya son attention, luckily babu mutane haraban hotel din, hakan ya kara masa kwarin gwiwan bin ta ya fixgota ta fashe masa da kuka tace "Ni ka kyaleni in yi wucewata, wllh baxan xauna a nan ba wajen Baabarmu xan koma" Bai saurareta ba ya ciro makullin motarsa a aljihu ya ja ta xuwa parking space da motarsa yake ya bude back seat, turata ciki yyi ya kulle motar, sannan ya jingina jikin motar ya rungume hannunsa yana imagining... assuming baya xaune downstairs tafiyar xata yi da gaske, Jiddah ta dinga rusa kuka cikin motar, ya fi minti 7 a tsaye kafin ya bude motar ya shiga ya kulle, can gefe ta koma tana shessheka taki kallonsa, yana kallonta fuskarsa a daure yace "Ina xa ki tafi kika ce?" Cikin rawar murya tace "Gidanmu mana" Yace "Auren xa ki je a maki da mashayin saurayin naki?" Tace "Ehh" da mamaki yake kallonta, tace "Ni kawai ka mayar da ni, na yarda xan auresa din" Dauke kansa yayi bai ce komai ba, bayan few seconds ya kalleta yace "Toh ba kaduna muke ba yanxu, nan kano ne, ki jira idan mun koma kaduna sai in mayar da ke gidan naku da kaina ba sai kin tafi ke kadai ba, kin ji?" idonta ta fara gogewa tace "Yaushe xa mu koma kadunan?" Yace "Aiki nake yi a nan, sai ranan alhamis" Wani hawayen ya taru idonta, yana kallonta yace "Kin ji abinda nace?" Hawayen ya xubo mata tace "Har sai alhamis kuma?" Yace "Jibi ne alhamis din ai" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayenta, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, a hankali tace "Toh" Bai kuma cewa komai ba, ya juya ya bude motar ya sauka yana dubanta yace "Sauko" Ba musu ta sauko daga motar tana wani kumbure kumbure, yana kallonta yace "Wani man kike shafawa?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Wanda ka siya min mana" Bai ce komai ba, bayan few seconds yace "Toh kar ki kara shafawa" ta kallesa yace "Mu tafi ciki" Ba musu ta fara tafiya ya bi bayanta, ba komai ya sa ya tambayeta ba sai ganin yanda ta kara haske, which he don't like, ko kadan baya son idan mace ta doso waje ayi noticing dinta, haske kuma na daya daga abinda yake sa ayi noticing mace a waje, ita kam Allah ya hore mata wannan, juyawa tayi ta kallesa suka hada ido ta ci gaba da tafiya yana biye da ita, har suka shiga reception din sannan taji yace "Tafi ki shirya ina jiranki, minti