Showing 6001 words to 9000 words out of 346625 words

Chapter 3 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

kasa, duk in samesu kan igiya da lema" Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace "Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai, na nawa kake son awaran?" Yace "Dubu daya" da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk 'yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace "Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?" Aunty tace "Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?" Ummi tace "Gashi ai naji a bakin ki yau" Aunty na kallon Abuturrab tace "Kai ka ji fa Aliyu.... Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu...." Abuturrab ya d'an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign.... Sai kuma ya dago kai a bayyana yace "To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty" Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace "That's the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take...." Aunty tace "Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?" Ummi tace "Toh Allah ya baku sa'a, idan walakanta d'an Adam abun yi ne, ku ci gaba" Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace "Ina xa ka Captain?" Yace "Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york...." Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da 'yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it's very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace "Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?" Tayi fari da ido tana kallonsa tace "Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba" Yace "Ohk, ita warce take soyawan tana ina??" Ta wani yatsine fuska tace "Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje" yace "Ohkk, sai anjima" Tana murmushi tace "Toh sunana Bibalo kai fa?" Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace "Wani gida ne ake awara a layin nan?" Yaron yace "Gidansu Bibalo ne" Ya sauko motar ya kulle sannan yace "Toh kai ni gidan" Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace "Shiga ka kira min me awaran" Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace "A xaton ki an mareki jiya sbda ni?" Kauda kai tayi, ya hade rai yace "Ki juyo ki kalleni ina maki magana" Ba tare da ta juyo ba tace "Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba" kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace "Nace maka babu awara yau" Yace "Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?" Ta wani xare ido tace "Ni nace maka banyi wanka ba??" Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace "Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu" Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.💖💖 *Jiddatul~ Khair*💖💖



_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻




3.....

Karfe taran dare Jiddah ta fito tsakar gida ta xauna kan tabarman dake bakin kofar dakinsu, muryar Hansai ne ya kaurade d'an tsakar gidan tana ma mai gidanta isuhu masifan ita ta gaji da ciyar da shi, shi dai yana xaune baya cewa komai hakan yasa tayi ta daga murya wanda da kyar ba a jin ta a kofar gida, a hankali Jiddah ta mike ta sa takalminta ta fita gidan, wani karamin gida can karshen layinsu ta tafi, tana waige waige ta shiga zauren gidan sannan ta karasa ciki, Wata yar dattijuwa ce tsakar gidan xaune tana ma yara uku dake kwance kan tabarma fifita, Datijuwar tace "An gama tuyar kenan..." Jiddah ta kwance ha6ar xaninta ta ciro dubu biyu tace "Aa yau ai bamu yi ba Baabarmu taje gidan gaisuwa, Iyah ki ajiye min wannan Usman ne ya bani daxu mun hadu bakin titi naje auno waken suya, ki dau dari biyar, sai ki ajiye min dari biyar sai ki sa dubu dayan a asusun da nayi ma Abbana" Iyah tace "Kai Allah dai yyi ma yaron nan albarka, kwana biyu ma bai shigo ya gaisheni ba, ni da a shirye yake ai da ya fito kawai ko Allah xai yanke maki wnn shegen wahalan, kai ko da akwati daya yayi maki indai xai rabaki da Hansai yafi maki wllh, ba yace min a can cikin gari yake da iyayensa ba, nan kuma wajen kanwar babarsa yake xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai ta mike ta nufi kofa tace "Sai da safe Iyah kar baabarmu ta nemeni" Tana fadin haka ta fita da sauri kafin a lura bbu ita a can gida, Iyah ta girgixa kai tace "Allah sarki, tsakaninsa da Allah yake sonta wllh, tsorona daya makirar bakar matar can kada ta shiga ta fita ta raba su, tunda ga bibalo babu mashinshini har yanxu sai yawon unguwa unguwa take a hayi, kuma duk sa'annin juna ne, to dai bbu ruwana tunda babu dangin iya balle na baba"

Ahmad ya gama sa cover shoe dinsa yana kallon Abuturrab dake kwance kan 3 seater hannunsa rike da remote yace "Ya naga kamar duk ka damu in tafi ne Captain?" Abuturrab ya kike xaune yace "Ohh toh ka yi xamanka mana ina ruwana, dama don kace kana night duty ne yasa nake ta reminding dinka, naga it's almost 6, an kusa kiran magrib" Ahmad ya ta6e baki ya mike yace "Yaushe xa ku wuce kanon ne?" Abuturrab yace "Am off for someday kawai i just decided to be in Abuja for a while, may be on friday xan bi train in sha Allah" Ahmad yace "Ohh that's great nima friday nake son xuwa kadunan, rabona da kaduna ai an kwana biyu" Daga haka ya nufi kofa ya fita, yana fita gidan ko minti goma ba ayi ba Aneesah ta shigo, Abuturrab na kallonta yace "Sorry i kept u waiting kinsan Ahmad...." Ta karaso parlon tace "Yeah i understand..." Xaunawa tayi ta ajiye jakarta, ya dawo kusa da ita yace "Kwana uku xan yi a Abuja...." Ta wara ido tace "Har uku?" yace "Yea, ko baxa ki tayani xama ba?" Ta juya ido tace "Aa kaga Dad dinmu yana gari, sai dai in dinga xuwa Ina tafiya..." Ya jingina da kujera yace "No need inyi kwana uku kenan, gobe inyi tafiyata kaduna dama sbda ke na sauka Abuja" Ta marairaice masa tace "Haba dear, to kar ka damu i will try and be with u" Mikewa tayi tace "Me xan girka maka nasan har yanxu baka ci abinci ba" Yace "Just a cup of tea now, mun sha fruits tare da Ahmad" bude kofar aka yi duk suka juya lkci daya, Ahmad ne ya shigo parlon, kallo daya yyi masu ya nufi gun da ya mance wayarsa ya dauka, yana kallon Abuturrab yace "Shi yasa ka damu in tafi kenan" Aneesah dai daure fuska tayi, kamar baxata ce komai ba sai da ya nufi kofa tace "Ina yini?" Banxa yyi mata ya fita ya kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa, a hankali tace "But am afraid Captain..." Yace "You are afraid of what?" Komawa tayi ta xauna da damuwa tace "I think this is the 5th time da Ahmad ke ganina a gidanka, ina tsoron kada ya sa iyayenku su ki amincewa da aurenmu" Abuturrab yace "Ni xan xauna da ke ko wani, don kina xuwa gidana does that mean anything?" Ta girgixa kai bata dai ce komai ba, ya mike ya isa kusa da ita ya kamo hannunta yace "Cheer up dear, beside Ahmad will never do that, i know who he is" kallonsa tayi da manyan idanuwanta ya sakar mata lallausan murmushi ya kai hannu dogon hancinta yace "Basu san samun me tsafta irin ki yanxu sai mutum ya dage ba?" Murmushi kawai tayi yyi pecking cheeks dinta yace "Babu wanda xai raba mu in sha Allah" hanyar kitchen ta nufa ya bi ta da kallo. Suna fitowa train station suka nufi motar dake tsaye yana jiransu, Ahmad ya bude back seat yana kallon saurayin dake xaune driver seat yace "Sorry for keeping u waiting salem, mun hadu da wani abokinmu ne muka tsaya gaisawa" Salem na murmushi yace "Ina yini ya Ahmad" Ahmad yace "Lafiya lau, ya su Aunty" Salem yace "Lafiya kalau" Abuturrab ya xaga ya shiga front seat bayan ya gama wayar da yake yana kallon stepbrother din nasa yace "How are you" Salem yace "Fine, how was the journey?" Abuturrab yace "Cool" Driving din motar salem yyi suka fara tafiya, tunda suka hau saman titin hayi idon Abuturrab ke gefen hanya, Ta madubi ya kalli Ahmad dake danna wayarsa, da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yau baxa ka siyi awara ba kenan" Sai a sannan Ahmad ya dago kai ya kalli inda suke, ganin sun kusa wajen da yake siyan awaran yace "I had no intention but let me get it for Umma and my siblings" Abuturrab ya ta6e baki bai ce komai ba, Ahmad na kallon Salem yace "Kana wuce layin nan ka tsaya a layin gaba" Salem yyi parking dai dai inda Ahmad yace, Ido hudu Jiddah tayi da Abuturrab da sauri ta sunkuyar da kanta tana gyara hijab din jikinta, Ahmad ya bude motar ya sauka yana kallonta smiling broadly ya rungume hannunsa yace "Sannu me awara" Bata yarda ta kallesa ba tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya kasuwa?" Tace "Na nawa xa a sa maka?" Yace "Ki sa na dari biyar ko?" Satan kallon Abuturrab tayi suka sake hada ido ya dauke nasa idon yana kallon gefen hanya, ta gama sa awaran ta mike ta mika ma Ahmad, ya amsa yana kallonta, sae kuma ya juya ya kalli Abuturrab yace "Bani 1k wajenka I'm not with cash" Abuturrab bai ce komai ba, ita dai tana tsaye, can ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika ma Ahmad, Ahmad ya amso ya mika mata ta amsa ta koma ta durkusa xata dauko canji yace "Aa ki bari idan na xo sake siya, shkkn ba sai na sake bada kudi ba koh?" shiru tayi, lkci daya ta mike tace "Toh ai akwai canjinka dari biyar a wajena da ka siya ranan nan, ka tuna?" tana fadin haka ta mika masa dubu dayan, yace "Aa ni na manta..." Daga haka ya shiga mota yace ma Salem su tafi, da ido ta bi motar sannan ta koma ta xauna gun kaskon awaranta. Hansai ta rike ha6a tace "Yau naga ikon Allah, baxa ki fito ana jiranki ba Jiddah???" Sai kuma tana murmushi ta kalli Iliya dake xaune kan tabarma tace "Da yake bata yi la'asar ba kilan sllh ta fara, bari in shiga ciki dai" daga haka ta mike daga kan kujeran tsugunno da take ta shiga dakin, can taga Jiddah xaune kusa da ghana must go din kayansu tana kuka a hankali, Bude baki Hansai tayi tana kallonta, can ta karasa a mugun fusace ta fincikota ta bugata da bango murya can kasa tace "Don ubanki kina ji na kika kyaleni bawan Allah ya xo tun daxu yana jiranki? Saukansa fa kenan daga legas yace kuma anjima da daddare xa su bi tirelan kaya su koma" Cikin rawan murya hawaye na sauka idonta tace "Wllh Baabarmu bana sonsa, shaye shaye fa yake...." Bata rufe baki ba Hansai ta buge mata bakin da karfi ta rankwasheta ta hankadata bakin kofa tace "Fita kar in sumar da ke, yar bakin ciki kawai muguwa" Goge hawayenta tayi ta fita da sauri tana hadiye kukan dake son subce mata, Can nesa da tabarman ta xauna ta hade rai taki cewa komai, Iliya na murmushi da jajayen idonsa yace "Hauwa kuluwa kwandon kilishi..." Sosai ta kara hade rai, yace "To d'an kalleni mana farin cikin xuciyataa" wani harara ta xabga masa, yayi wani murmushin da lebensa da ya dafe saboda shaye shaye ga idanuwansa kamar garwashi, yace "Mun sauke wani kayan ne yau, amma mun yi lodi xa mu koma xuwa nan da bayan magariba" Ita dai ko kallonsa bata sake yi ba, ya ciro rafan 'yan ashirin ashirin guda biyu sababbi ya ajiye kusa da ita yace "Hansai tace Babanki ya bukaci in turo magabatana, to in sha Allahu ranan laraba xamu yo lodi daga lagos, ina dawowa kuma xan turo tsohona da yayansa, a nan take ma xa a bada sadaki a saka mana rana, don ni a shirye nake" Wasu hawaye suka kawo idon jiddah, ya mike yace "Kice ma Hansai na tafi sai Allah yayi mana dawowa" daga haka ya fita ta bi sa da kallo da dafaffen farin shaddan jikinsa, yana fita Hansai dake la6e tana sauraron duk abinda yace ta fito, dauke kudin tayi tace "Allah yayi masa albarka, ai iliya ba dai xuciya ba, ga masara can ya kawo mana rabin buhu, da wake xai yi kwano biyar wllh, Allah yayi masa albarka" tana gama fadin haka ta dau gyale ta fita gidan..... Jiddah ta hade kai tana kuka sosai, mikewa tayi ita ma ta fita gidan, ta shiga gidan iyah, Iyah ta dinga salati tana kallonta ganin yanda take kuka, duk lallashin duniyan nan tayi mata amma taki sauraronta balle tayi shiru, Iyah tace "Atoh bari in je in ci gaba da tankade gari na kawai" daga haka ta mike ta koma gun da take tankadenta ta xauna ta ci gaba, Da kyar Jiddah ta dago kanta bayan wani lkci tana share sauran hawayen idonta cikin rawar murya ta shiga gaya ma Iyah abinda ya faru, Iyah ta ajiye matankadin hannunta tace "To ubanki ya xama sususu shashasha kenan, banda haka meye mutum xai maida kansa kamar gunki, ko min wani irin asiri tayi masa ai bai ci ya xama kamar gunki haka ba, mutum kawai bai da amfani Allah na tuba, Hansai dai wllh baxata gama da duniya lafiya ba, me yasa bata ba ma Bibalo iliyasun ba, waye bai san iliya ba a garin nan, kawai don axxaluma ce ita ta dage sai ta hadaki da d'an gwangwan d'an shaye shaye? Ranan babu inda labari bai kai ba kan cewar Iliya ya mari mahaifinsa, ba ga uwarsa can a kana radd ba tana 6ara, kanninsa mata kuwa duk karuwanci suke kowa yasani ba wani boyayyen abu bane, ohh na shiga uku


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login