Showing 222001 words to 225000 words out of 346625 words
Chapter 75 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
ta nufa ta tafi parlor ta xauna kan kujera sannan ta fara kyalkyale dariya har da kyakyatawa, Safiyya tace "Meye haka??" Dariya kawai Maimoon take, Safiyya tayi tsaki ta mike ta wuce daki, Sae da Maimoon tayi dariyar me isarta sannan ta tashi ta koma dakin, Jiddah dai ta rufe har kanta ko da Maimoon ta koma dakin. Da safe Jiddah taki amincewa su hada ido da Maimoon, Maimoon dai sai harkan gabanta take, karfe goma Umma da Safiyya suka fita xuwa kasuwa, Bayan fitarsu Maimoon ta shigo daki ta dinga jan Jiddah da hira don sun gama aikinsu tun safe, tun Jiddah na kin tanka mata har dai ta sake, labarin wata kawarta da tayi aure mijin ke gallaza mata Maimoon ke yi mata, Jiddah tace "uHum! To ko dai ita ma akwai abinda take masa ne kawai fada maku ne baxa tayi ba" Maimoon ta takarkare tace "Aa wllh, babu wani abu da take masa, d'an iska ne kawai ta aura, ke kinga soyayya kamar xa su cinye kansu kafin ayi auren?? Wllh soyayya kamar indiyawa har suna intimidating dinmu, to yau dai ga shi sun koma enemies din juna, abun da mamaki" Jiddah tace "Ke dai kawai kiyi shiru tunda ba a gidan nasu kike ba balle kiyi siding dinta, ba dole sai ta fada maku gaskiya ba" Maimoon tace "Ji wani magana da kike, to ke duk xamanki gidan yaya Aliyu kullum ne yake kula da kin ci abinci ko baki ci ba? Ba wahala ya dinga baki ba duk kika rame kika kanjale har kika gwammace bai dauko ki daga gidanku ba" Kallonta kawai Jiddah ke yi, sai kuma ta dauke kai tace "Aa ni bai ta6a bani wahala ko ya bar ni da yunwa ba, in ji waye yace maku haka..." Maimoon tace "Aa fa xancen gaskiya muke yi a nan Jiddah kar ki wani rufa masa asiri, kuma kinsan a yanda take bamu labarin mijin nan nata wllh kamar halinsu daya da Yaya Aliyu, ai ke kin xauna gidansa kinsan wanene shi" Jiddah dake kallonta tace "Wani irin hali ne irin nasa?" Maimoon ta gyara xama tace "Kin ga Zainab bata da wani freedom tun da ta shiga gidan nan, sannan kullum a hantare take wajensa, gashi babu wani kulawa, ga masifa ga fada, ga yunwa, ga shi yayi ta depriving dinta of so many things, to mention but a few..." Katse ta Jiddah tayi tace "Aa ni dai ban tuna sanda ya hantareni ba, sannan ni yana kula da ni... freedom kuma dama xaka auri mace ne ka saketa tayi ta yawo a gari? Sannan ni dai ban ta6a xama da yunwa a gidansa ba, and he never deprived me of anything all through my stay in his house, in dai Aliyun da na sani kike magana a kai to ba halinsu daya da mijin kawarki ba" Maimoon ta rike ha6a tace "Ohh har kin manta duk abinda kika yi facing lokacin kina gidansa kenan Jiddah?" Jiddah tace "Ban yi facing komai ba, ni dai nasan ko baya nan nace ga abinda xan ci yana kawo min, ba fa wai sae yana within kaduna ba, A'a ko daga kano ne yana kawo min, sannan xan iya kirga sau nawa nayi girki a gidan sa, kullum sai yayi min take away din abinci ko xan ci ko baxan ci ba" Maimoon tace "Tabb da gaske haka yake da caring? Ni wllh irin mijin da nake so kenan" Sau daya Jiddah ta kalleta ta dauke kai, Maimoon tayi tagumi tace "Toh ai kuwa in haka ne koma meye bai cancanci ki watsar da shi ko me xai faru ba, Toh Allah dai ya kyauta, na manta ma ban kirasa naji ya jikinsa ba" Daga haka ta jawo wayarta ta shiga kiransa, har ya katse bai dauka ba ta ajiye wayar tayi tagumi tace "To ko dai jikin nasa ne" Jiddah bata ce komai ba, sai gashi ya kira, da sauri Maimoon ta daga cike da damuwa tace "Hello Yaya A, ya jikin naka?" Kusan minti uku suna magana, Jiddah dai na wajen bata ko kara kallonta ba, can Maimoon tace "Yaya A, ga Jiddah xata yi maka ya jiki" daga haka ta kamo hannunta ta saka wayar, Jiddah dai kallon wayar kawai take, Maimoon ta mike ta dau cup din da ta sha shayi ta fita, Jiddah ta kai wayar kunne, jin yyi shiru tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Tana wasa da edge din xanin gado tace "Ya jikin?" Yace "Wa yace maki bani da lafiya" Shiru tayi, yace "Ina jin ki" Ta d'an turo baki tace "Maimoon" yace "Amma baki min ya jikin tun jiya ba ai" Bata ce komai ba, yace "Da sauki" tace "Allah ya kara lafiya" yace "Ameen... Me Awara" dago kai tayi da sauri ta d'an wara ido, sai kuma ta rufe fuskarta da pillow din dake kusa da ita tana murmushi, yyi kasa da murya yace "Ko ba ita bace?" Ta turo baki tace "Ni ai ba awara nake yi ba yanxu" Yace "Ohkk... Ko xaki fara ne?" Ta d'an yi murmushi taki ce masa komai, yace "Har yanxu ae kina da burin fara awara a bakin titin gida na...." Murmushi take yi sosai, a hankali tace "Toh ai ba a unguwar nake ba yanxu..." Yace "Toh idan kika dawo anguwan fa?' ta xaro ido tace "Me xai maida ni?" Yace "Ni xan maida ki duk sanda kika shirya" Tayi wani murmushin bata ce komai ba, yace "Ko baki son komawa?" Tace "Wai in koma inyi mene??" Yace "Ki koma kiyi ibada" Ta xaro ido tace "Wani irin ibada?" Yace "Irin warce baki samu daman yi ba" Tayi shiru kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace "Ni ban gane ba" Yace "Irin warce Allah yace ayi" Tace "Ban san shi ba" Yace "Xaki san shi kwanan nan" Bata kuma cewa komai ba shi ma yayi shiru, a hankali tace "Allah ya kara lafiya" yace "Ameen, sai dai ban ta6a cin awaranki ba tun da can ma" Tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Yeahh" tace "Sai ayi maka" Yace "Irin na Baabarku?" Shiru tayi, ya shafa kansa yace "Sai anjima" daga haka ya katse wayar ta kalli screen din sannan ta ajiye a hankali... Abba ne xaune parlor da Hajja sae Aunty, Hajja na gyara daurin dankwalinta tace "Ae kaga saboda xuciyata me kyau ce bana riko duk da rashin kunyar da yarinyar nan ta min hakan bai hanani tsayawa har sae da na tika uwar Bashir da kasa ba, don da cewa tayi inaaa d'an ta baxae ta6a auran mara asali ba, to duk duniya banda shege waye bai da asali, da yake kabiru na jin maganata yana min biyayya don har ma ya fi ka, ba shiri ya taka mata birki ya dau maganata da muhimmancin gaske, to ba gashi komai na tafiya dai dai ba" Abba dai sae kallonta yake, Aunty dake ta boiling from inside sai kallon Hajja take amma ba daman cewa komai, kasa hakura tayi daga karshe ta dake tace "Toh shi Bashir din me yace Hajja?" Hajja tace "Aa baya ma kasar, yo shi Ina ruwansa, galallawa ne fa yaron nan da kuke gani, duk yanda nayi yace dai dai ne yasan baxan masa xa6in da xai cucesa ba, toh ni abinda yasa na makale ma yarinyar saboda tsaftarta ne baxan biye rashin kunyan da tayi min ba, duk da nasan wannan narkekiyar matar Ramlah ce xata koya mata ta min haka, amma da baxa ta min haka ba... Yanxu dai Kabiru yace kai sai ka xama madaurin aurenta wato waliyyinta, so nake kafin Bashir ya dawo an daura sai dai kawai a wanketa a kai masa dakinsa, uban ma ya amince da hakan...." Abba yace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Hajja tace "Cewa xaka yi Allah ya baki ladan wannan jihadi Hajja, ka ga ai da ni tsohuwar banxa ce baxan so in hada Jiddah da jinina ba don wllh gidan da Aliyu ya kai ni a hayin rigasa yace nasu ne, duk da a rushe gidan yake amma kana ganin gidan kasan na fakirai ne, su talaucin ma ba karamin kamu yyi masu ba, da kyar ake samun masu talauci irinsu, mu dai ba saboda Allah kawai muke abun mu ba dama, Allah dai kawai ya bamu lada" Mikewa Aunty tayi ta nufi kofa ta fice Hajja ta bi ta da wani kallo tace "Ae kaga da yake ta kaina nake, ni ko da wasa ban ta6a kawo d'an ta Salem a rai ba balle wataran ta zageni ko shi ya xageni, amma yanxu haka da xaka shiga xuciyarta xaka san hadin nan bai mata ba, na rasa abinda jiddah tayi mata da wannan tsana haka" Abba yace "Xan d'an fita Hajja, sae na dawo anjima" Tace "Toh Allah ya tsare, cikin satin nan Kabiru yace xa a kawo komai kilan har sadaki, wato shi ma xaman yaron a haka ya ishesa ashe, magana ce kawai baya yi, gashi sae yyi ta fita kasar waje an rasa uban me yake xuwa yi a can" Daga haka ta mike tace "To ba ruwana, ita warcan narkekiyar sae ka tafi har can gidanta ka yi mata bayanin komai don kar ta xo ta min rashin albarka ta cuce ku, ba karamin aikinta bane, don duk tayi bake bake kan lamarin yarinyar" shi dae bai ce mata komai ba har ta fita, girgixa kai kawai yake yana mamakin Hajja, ya dau wayarsa ya shiga kiran Ummi, tana shigowa ya tsara mata duk yanda suka yi da Hajja, Ummi ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Haka dama auren yake da sauki Yallabai, ina laifin ma ta kare secondary din tunda ta dauko hanya? Ita fa Hajja idan ta shirya abu a ranta babu me canxa ta, sannan tana ta nuna Bashir din ma yace ba ruwansa, tayi duk yanda tayi.. to an ta6a aure haka babu fahimtar juna tsakanin mata da mijin? Ko magana fa basu ta6a yi ba a waya" Abba yace "Ba dai tace shi Kabir ya amince ba ya bata goyon baya? To Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, ita ma yarinyar Allah ya sa hakan babban alkhairi ne a gareta" Ummi dai tayi shiru, can tace "Ba fa a tambayi yarinyar nan ko tayi na'am da hakan ba, it's more or less like auren dole xa ayi mata, gwara a fara jin ta bakinta Yallabai, kar a ga kamar don ba mu muka haifeta ba shi yasa ake juyata yanda ake so, hakan ba dai dai bane wllh" Abba yace "Wannan kuma ai aikin ke da Hajiya Ramlah ne, xuwa anjima sai kije can gidan kiyi mata bayani sannan a ji ta bakin ita yarinyar, don a yanda Hajja ta axalxali batun nan sai ta iya cewa cikin sati biyu ma take son ayi bikin" Ummi tace "Toh Allah ya kyauta, amma ya dace ka kira shi mai martaban kaji ta bakinsa, kilan ma shirinta ne ita kadai wa ya sani?" Abba yace "Ehh ina jiran nan da d'an anjima ne xan kirasa in sha Allah" Ummi tace "Toh Allah yayi mana me kyau" Abba ya amsa da "Ameen" mikewa tayi ta fita daga parlon. Umma ce xaune bedroom dinta tare da Ummi, ta jira har Ummi ta kai aya sannan tace "Kinga yanda baxan so ayi ma Maimoon ko Safiyya ko Siyama auren dole ba, to haka ita ma Jiddah baxan yarda da hakan ba Yaya, a ajiye batun ai ko bani na haifeta ba, wllh yanda xanyi ma 'ya yan cikina ita ma haka xan mata, ku yaya Hajja sai tayi ta wasu abubuwa kamar dai notiran kanta sun kwance amma ku dinga biye mata a rasa me gaya mata gaskiya? Meye amfanin hakan fisabilillah? Ni fa na xata tunda nace aa an bar xancen ne ashe abinda ya kai ta bauchi kenan ma? To ni dai sai dai a fadi duk abinda xa a fada amma Jiddah is too young for that marriage, sannan har take ikirarin uwar Bashir din bata so amma tayi ruwa da tsaki a kan lamarin har sai da ta sa kowa ya amince, wani xaman aure take son yarinyar taje tayi a wannan babban gidan Ummi, shikenan saboda bata da iyaye ita marainiya ce sai aka ce bata da gata? Aa wllh tana da gata don yanda na dau su Maimoon haka na dauketa, Hajja taje can ta samar ba Bashir wata matar amma ba Jiddah da ko secondary din ma bata kare ba" Ummi tace "Toh ina ga xai fi ki tashi kije ki samu Hajja kiyi mata duk bayanin nan, ke wani lkcn kina magana kamar baki san Hajja ba, kin gan ni nan duk fa abinda xai dameni ko ya bata min rai bana so yanxu, ta kaina kawai nake babu ruwana, In dai Bashir din da bakinsa yayi admitting yana son Jiddah kuma xai xauna da ita i see nothing wrong with that, domin kuwa shi din ba wani xama yake a kasar ba, bini bini ya fita, to ba sai ya tafi da matarsa ba, ina Jiddah xata ga uwarsa idan ba dawowa kasar suka yi ba, kinga wllh yanda kike hakikancewa a batun nan tsaf Hajja xata ce Hassada kike tunda ba er ki bace, don haka ina baki shawara ki bi komai saisa saisa babu ruwanki..." Umma tace "Aa kiyi hakuri yaya a gaskiya da ruwana, Hajja kuma ba tun yau na saba da tijararta ba, kuma ni kema kin san raga mata nake kawai sabida ke, banda haka ni baxan yi tolerating haka ba, kuma a gaskiya idan haka abubuwa xa su ci gaba da faruwa gwara ki tafi da Jiddah can gidan don ma kada taga kamar ban tsaya mata ba tunda ni ba uwarta bace.. ki tafi da ita kawai ku yi yanda ku ka ga ya dace da ita, dama ai Hajjar ta sha fada min ba don Aliyu ba a ina xa a santa, don haka ki tafi da ita ku yi mata bayani a can amma ba a nan ba" Ummi dai kallonta kawai take, Umma ta mike tace "Haka kawai ga gaskiya a dinga takesa kiri kiri, ita Hajjar Allah ce da dole sai an bi abinda tace mata gigin tsufa duk ya rikitata kuma ayi ta bin ta a haka, ba ga jikokinta sa'annin jiddar ba, tayi masu auren mana idan haka ne, kiyi hakuri fa kar kice rashin kunya nake maki Yaya, aa gaskiyata nake fadi, kawai don Jiddah bata da gata a duniya sai a tauyeta?? To dauketa ku tafi kuyi yanda ya dace da ita, babu ruwana" Mikewa Ummi tayi ta fita daga dakin tayi wucewarta... Bayan tafiyar Ummi da kusan awa daya su Maimoon suka dawo Islamiyya, bayan sun gaida Umma dake xaune parlor xa su wuce dakinsu Umma tace "Da wani number kike waya da Aliyu Maimuna?" Maimoon ta dawo, Jiddah ta d'an saci kallon Umma sannan ta wuce ciki, Maimoon tace "Da numbersa ne yana shiga" Umma tace "Toh" daga haka ta mike ta wuce dakinta ta hau kiran Abuturrab wayar bai yi connecting ba hakan yasa ta ajiye ta fito... Sai can da daddare Umma ta sake kiransa sai ya shiga, yana dagawa bayan sun gaisa tace "Kana ji na Aliyu?" Yace "Ina ji Umma" Tace "Ka dai ji abinda iyayenka ke shirin aikatawa ai ko?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Na me fa?" Tace "Ohh duk baka sani ba, to Hajja ta dage ita dole sai tayi ma Jiddah aure da Bashir, na kiraka ne kuma saboda naga kamar tana jin maganarka, i want u to put a stop to that, ko secondary bana fatan Jiddah ta gama ace xa a aurar da ita, don haka talk sense into Hajja" Abuturrab dai yyi shiru, ta hade rai tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Ina ji Umma, xan kirata in sha Allah, nobody told me about it, tace to wa xai gaya maka dama tunda cutar yarinyar ake son yi" a hankali Abuturrab yace "Shkkn, i will call her in sha Allah" Tace "Do so immediately" Daga haka ta katse wayar ta ajiye lamarin na kara kona mata rai, wai aure kamar xa a aurar da wata mara makabuli, to su yi ta gani. Hajja ta gama sauraron Abuturrab tsaff sannan tace "Toh ko ubanka Usman wanda shine lallai dole ne bai isa yace xai dakatar da ni kan abinda nayi niyya ba, kai kuma a wa Allah na tuba? Kai da ka walakanta yarinya ka cuceta ka mayar da ita baxawarar karfi da yaji sannan ka saketa? Kai fa ba wani abu ke damunka ba banda kishi, kuma sai dai ka hadiyesa don tayi maka nisa wllh, idan ma sa ka aka yi ka kirana ka koma ka fada ma wanda ya sa ka ai ba Hajjar da bace yanxu, bana nufin er yarinyar nan da sharri banda alkhairi, yanda ta taso cikin bakar talauci da rashin ga ta so nake ita ma ta ci arxiki ta bar sa a inda ta gansa, so nake ita ma ta shiga babban gida a dama da ita, to na meye kowa sai bakin ciki abinda ni Allah bai daura min ba kenan, to kowa dai ya ci kansa ya kurkure da bakin ruwa, kai kuma ina baka shawaran ka kauda idonka a kan duk wani abu da ya shafi yarinyar kayi mana me wuyar tunda ka kawota cikinmu" Tana kai wa nan ta katse wayar, Abuturrab murmushi kawai yake yi... Kawai bayan sati daya sai ga shi Aunty ta kira Umma wai an kawo kudin Jiddah daga masarautan bauchi... Ummi ta fi minti talatin rike da wayarta bayan aunty ta katse, Allah kadai yasan yanda take ji a xuciyarta a lkcn.... Sai yamma ta shirya ta tafi gidan don bata son xuwa ta tadda mutane, ai ko duk yan kawo kudin sun watse, parlon Abba ta shiga direct, yana xaune shi da duk brothers dinsa, Umma ta xauna bayan sun gaisa gaba daya tace "Alhaji Usman dama wajenka na