Showing 75001 words to 78000 words out of 346625 words
Chapter 26 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete
xo?" Tace "Yanxu muka shigo" yace "Maa sha Allah sannunku da xuwa" Tafiya take yana gefenta shi ma yana tafiyan, can yace "Amma baki da damuwa ko Jiddah, kar ki boye min komai ki gaya min" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "Ina son dawowa nan wajen Umma" Shiru yayi bai ce komai ba, don yasan taurin kan Abuturrab ya wuce ya amince Jiddah ta dawo nan gidan, a hankali yace "Kar ki damu Jiddah, nasan xama ke kadai ne baki so ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kar ki damu nasan me xanyi" Da damuwa tace "Amma kar kayi masa magana ihu xai yi min" Murmushi Ahmad yyi yace "No baxan yi masa ba" Abuturrab suka gani bakin kofa tsaye alamar lkcn ya iso wajen ganin jiddah bata shigo ba, Jiddah sai da taji gabanta ya fadi ganinsa, shi kuwa sai ya hade rai, suna isa balcony din Ahmad yace "Sai ga amarya yau ta xo gidanmu, kun xo gaida Umma kenan" Abuturrab da yayi masa wani kallo underneath his breath yace "Half-wit" daga haka ya juya ya koma parlon. Rungume Umma jiddah tayi, sosai tayi farin cikin ganinta kamar yanda Umma ma taji dadin ganinta, Shi dai Abuturrab na yi yana kallon agogo don bai ma son la'asar yayi masu a gidan, Kitchen Jiddah ta tafi bisa umarnin Umma na cewa taje ta taya su Siyama da mai aiki girki, Umma na kallon Abuturrab tace "Why is she this lean? Bata da lafiya ne?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh tayi xaxxabi kwana biyu, amma ta samu lafiya yanxu" Ahmad dai sai wani kallo yake masa, Da damuwa Umma tace "Toh Allah ya sauwake, ita kadai din ce a gidan kenan yanxu?" Da sauri yace "Aa Umma ai nace akwai me aiki, kuma ma yawanci one day on, one day off nake yi" Umma tace "Toh shkkn Allah ya taimaka, karatun fa?" Yace "Xata fara in sha Allah" Umma tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Abinda Abuturrab bai so bane ya faru don sai da la'asar din yayi yana gidan, dakin Ahmad ya tafi yin alwala, Ahmad dake ta jiran ya shiga alwala ya jawo makullansa na gida bayan ya shiga bandaki, cikin few seconds yayi abinda xai yi ya ajiye sauran sannan ya fita dakin....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Albishirin ku jama’a ko kusan akwai wani company da ya shahara wajen siyar da kayan alatu da abubuwan more rayuwa??
Wato Unique & Luxury Stores yana da bangararori daban-daban kamar haka,
@unique_home_store_ng wanda ya shahara wajen siyar da kayan ado da qawata gida, kayan kitchen, furniture, carpet na gani na fada da sauran su.
Sannan akwai @elegant_projects_ng
Bangaren tsara gida kamar home styling na amare da uwar gida, interior designing da finishing....
Company bai tsaya a sashe 2 kawai ba yana da bangaren ado da kwaliya wato
@uniquefashion_ng. Duk bai tsaya anan ba ya kara zuwa maku da @unique_souq_ng inda zaku samu kayan kwadayi, makulashe da kayan da zasu kara inganta maku lafiyar jiki.
Karku bari ayi babu ku domin gane ma idon ku, ku garzaya shafukan su a Instagram kamar haka....
@unique_home_store_ng
@uniquefashion_ng
@unique_souq_ng
@elegant_projects_ng
Sannan zaku iya samun su ta WhatsApp a +2349071721586
Jiddah ce xaune bedroom din Umma dake mata tambayoyi, ita dai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Kar kiji komai ki fada min gaskiya Jiddah" Tayi murmushin karfin hali ta dago kanta tana kallon Umma tace "Da gaske ba komai Umma" Umma tace "Kin tabbatar?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Yace ya kawo maki mai aikin haka ne?" Ta kalli Umma sannan cikin sanyin murya tace "Eh" Shiru Umma tayi tana kallonta don sai take ganin kamar ba gaskiya take fadi ba, tausayin Jiddah take a xuciyarta, ta kwantar da murya tace "Ni baxan ce masa mun yi maganan komai da ke ba Jiddah, ki bani amsan tambayoyina kafin su dawo masallaci yanxu" Jiddah ta kuma wani murmushi tace "Umma na baki amsan ai" Umma tace "Toh kina jin dadin xaman gidan?" Kallonta Jiddah ta dinga yi ta kasa cewa komai, Umma tace "Ina saurarenki..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin, Ahmad ya shigo tare da Abuturrab, sosai gabansa ya fadi, ya kalli Umma sannan ya kalli Jiddah, Umma dai ta daure fuska tana danna wayarta, Ahmad dai na tsaye bakin kofa bai karaso ba, ya dinga fatan Jiddah ta sanar ma Umma bata boye mata komai ba, Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Umma dare na yi xa mu wuce gida" Umma tace "Ohk" wasu sabbin hawayen ya dinga sauka idon Jiddah, gaba daya Abuturrab ya kasa nutsuwa, kana ganinsa ka ga mara gaskiya, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ku je sai da safe" Ta kalli Abuturrab tana goge idonta, ya jefa mata wani kallo a fakaice, a hankali ta mike hawaye yaki tsaya mata tace "Sai da safe Umma" Umma bata iya ta amsa ba Jiddah ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umma yyi kasa da murya yace "Sai da safe Sai Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kai mu" Ya kalli Ahmad that is still standing wanda har ransa yake jin hawayen da jiddah take, Abuturrab ya ki ce masa komai ya fita dakin, Maimuna da siyama ne suka dau ma Jiddah abubuwan da Umma ta hada mata tun daxu xuwa motar Abuturrab, Jiddah dai na xaune gaban motar kamar ana dada tunxurata da kukan da take, Abuturrab ya tada motar ya bar gidan, sai a sannan ya sauke ajiyar xuciya, he even love it da Umma taki ce masa komai, har suka isa gida bai ko kalli Jiddah ba, yana parking ya sauka ya tafi ya kulle gate din gidan ya dawo, tsaye ya ganta jikin motar fuskar nan nata kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ya hade rai yace "Ni xan dauko maki kayan naki dake cikin motar" ta juya ta bude bayan motar tana goge guntun hawayenta ta dau ledan hijabs din da Umma tayi mata da warmer din tuwo da miyar kuka da Umma ta sa a xuba mata, da harara ya bi ta yace "Xaki ga ko xaki sake leka kofar gate din gidan nan balle har in kai ki gidan Umma ki samu daman hawayen iskanci" Kamar jiran jin hakan take ta fashe da kuka sosai tana kallonsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, wllh kewarta nake bana son in rabu da ita shi sa nake kuka, don Allah kayi hakuri" ko tanka ta bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan ta bi bayansa da sauri tana kuka, ko tsayawa bai yi a parlor ba ya wuce bangarensa, ta shiga dakinta ta ci kukanta me isarta bayan ta sannan ta kwanta. Karfe sha daya da kusan rabi yayi knocking kofar dakin ya shiga, ganin tayi bacci ya bude warmer din abincin da ta ajiye kasan dakin, yaga bata ta6a ba duk da yasan ta ci abinci a can gidan, ko kayan jikinta bata cire ba, wannan dalilin ne yasa ya tasheta, mikewa xaune tayi da sleepy eyes dinta tana murxawa, yace "Me ya hanaki wanka kafin ki kwanta?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Dama bakya wankan daren da nace maki kenan?" Da sauri ta bude ido sosai tace "Wllh ina yi bansan sanda nayi bacci ba" Yace "Toh tashi kije kiyi wankan" Kallon agogo tayi da sauri, ya hade rai yace "Tashi nace" A sanyaye ta mike xata shiga bandakin yace "Da kayan xaki yi wanka?" bata ce komai ba, amma ta ki cire kayan a gabansa, ya daure fuska yace "Ba magana nake maki ba" Ta d'an kallesa tayi narai narai da ido tace "Tawul din yana bandaki ne" tana fadin haka ta shige bandakin, gefen gadon ya xauna yana naxarin maganganun da Umma tayi masa a waya bayan sun dawo gida, he is finding it hard to forget her words and move own, yasan no matter what Ahmad baxai ta6a gaya mata xaman da yake da Jiddah a gidan nan ba, yasan baxai ta6a ce mata ma bbu aurensu da Jiddah kamar yanda ya sanar masa ba, but her words carried weight this night, he have a very good intention toward jiddah, ba shi da nufin ya cuceta ko ya walakantata ko ya saka rayuwarta a garari, his intentions are nothing but pure, dafe kansa yyi, lkci daya ya dago jin wayar dake hannunsa yayi vibrate ya duba ya ga Aneesah ce ke kiransa, bai sake kallon wayar ba coz sun yi magana not too long, bayan kusan minti sha biyar jiddah ta fito daga bandakin sanye da kayan da ta cire, kasa kallonsa tayi ta ja gefe ta tsaya, wani kallo ya dinga mata kafin yace "Meye hakan kika yi?" Ta ki yarda su hada ido tace "Ni baxan iya fitowa babu kaya ba bayan kana xaune dakin" Daga sama har kasa ya dinga kallonta yana mamakin abinda ta fada, can dai yace "Ke kina da wani abinda xaki boye min a jikin ki dama, kwaila da ke?" Ta d'an turo baki ta juya masa baya, Tsaki yyi ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo, murya can kasa tace "Eh amma ai ni ba muharramarka bace da xan cire kaya...." Ganin ya juyo tayi tsit, ganin impression din fuskarsa gabanta ya fara faduwa, yace "Kika ce me?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ban ce komai ba" Dawowa dakin yyi, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah kayi hakuri ni bance komai ba" Yace "Kika ce ni ba muharraminki bane?" Ta girgixa masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Aa bance haka ba" Sai da ya iso gabanta ya tsaya, sbda tsoro taji ta ma kasa tsayawa, calmly yace "A ina kika san wanda muharraminki ne da wanda ba muharraminki ba?" Jin taki cewa komai ya mata wani tsawa da yasa ta duka hawaye ya kawo idonta, yace "Idan baki bani amsata ba na fara ball dake sai kin ganki downstairs yanxu" Cikin rawan murya tace "Ai da ina xuwa islamiyya" Ya gyada kai yace "A islamiyyan kuma basu sanar maki hukuncin wanda yace xai kashe kansa ba?" Kasa cewa komai tayi, ya wani hade rai yace "Mike ki cire kayanki" Ta sake marairaice masa amma ganin kallon da yake mata ta mike da kyar, ta gefen ido ta kalli bandakinta, lkci daya kamar kiftawan ido ta shige ta sa makulli hannunta na rawa, ya dinga kallon kofar, can yyi murmushi yana shafa kansa, lkci daya kuma ya hade rai ya fice daga dakin, bai karasa bangarensa ba wayarsa yyi vibrate ganin me kiransa sai da gabanaa ya fadi, har ya katse bai dauka ba, sai da aka sake kira sannan ya daga, murya can kasa yyi sallama yace "Ina yini Aunty" ba tare da ta amsa ba tace "Aliyu kana ina??" ya d'an bude ido yace "Aunty ai ina kano, ban dawo ba..." Bude kofarsa yyi ya shiga ya kulle hade da lumshe ido jin abinda take cewa. Washegari da safe wanda Abuturrab ya sa ya samar masa mai gadi ya iso gidan da mai gadin, Abuturrab na kallon matashin mai gadin yace "Yaranku nawa da matar taka?" Mai gadin yace "Daya ne kawai Alhaji, sabon aure ne" Abuturrab yace "Ba damuwa, yau nake son xaka fara aikin sai ka koma ka taho da iyalan naka" Mai gadin ya risina da ladabi yace "Toh nagode Alhaji, xan je kauyen namu yanxu sai in taho da su in sha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Abuturrab yace "Ameen, amma kada ka wuce karfe biyar na yamma don xan koma gun aiki a yau" Mai gadin yace "In sha Allah Alhaji" dubu biyar Abuturrab ya basa kudin motar xuwa taho da iyalan nasa, shi ma wanda ya kawo sa ya basa dubu biyar, bayan sun tafi ya koma cikin parlor.... jiddah na kitchen tana dumaman tuwon da umma ta bata jiya, yatsine fuska yyi yana kallon kitchen din don ko by mistake baya son warin miyar kuka, barin ma yanxu da take dumamawa, hakan ya sa ya dau makullin motarsa ya bar gidan xuwa inda xai je yyi breakfast, jiddah na jin fitan motarsa ta jigina jikin bango tunda taji yana waya ko minti sha biyar ba ayi ba yace yau xai koma gun aiki ta ji duk mood dinta ya canxa, gaba daya bata son xama ita kadai a gidan, a sanyaye ta kashe gas din ta xuba tuwon amma ta kasa ci, Duk da xamansa a gidan da rashin xamansa kusan daya don ba wai wani magana me tsayi yake mata ba, kuma ba waje daya ma suke xama ba amma idan yana gidan bata jin kadaici da kewa na damunta, duk sonta da tuwon saboda yanayin da ta shiga sai ta kasa ci da yawa, haka nan ta mike ta kai kitchen ta wanke plate din, sama ta wuce ta wanke bakinta, komai da take yi a gidan tayi, turaren wuta ne kawai bata sa ba, ta dau turaren ta sauka parlor ta sa sannan ta xauna tana kallon yanda yake fita a hankali, kana ganinta kasan jikinta a sanyaye yake, bude kofar parlon aka yi Abuturrab ya shigo ta daga kai ta kallesa sannan ta sauke idonta, sai da ya karaso cikin parlon tace "Sannu da dawowa" Bai amsa ba yyi wucewarsa sama ta gefen ido ta bi sa da kallo har ta daina ganinsa, a sanyaye ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta ta kwanta tana kallon fuskarta ta madubin press din dakin. Da yammacin ranan tana tsaye jikin window aka bude kofar dakin, tunda ta kallesa sau daya ta dauke idonta, yana bakin kofar a tsaye yace "Shuka kika yi wajen nan da kike tsayawa ko da yaushe?" Tana wasa da fingers dinta ta girgixa masa kai, juyawa yyi ta bi sa da kallo ganin jakar hannunsa, da sauri ta bi sa tace "Tafiya xaka yi?" Ya juyo yace "Kina bukatar wani abu ne?" Lkci daya jikinta yyi wani sanyi, shi dai kallonta yake yana lura da ita duk a lkci daya, sauke idonta tayi saboda hawayen da ya kawo idonta, yace "Nace kina bukatar wani abu ne" ta girgixa masa kai hawayen dake makale idonta ya gangaro ta juya da sauri ta koma ciki, da ido ya bi ta, kafin ya bi bayanta xuwa dakin, durkushe ya ganta ta daura kanta saman gado, da mamaki yake kallonta, can yace "Ke kina da lafiya kuwa" kin dagowa tayi tana shessheka, ajiye jakar yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita ya tsaya yace "Tambayar ki nake, kina da lafiya kuwa?" Still taki dagowa, ya daka mata tsawa yace "Baki ji na ne" mikewa tayi hawaye na kai koma a idonta, ya dinga kallonta kafin yace "Me aka maki?" Ta girgixa masa kai, ya mata wani kallo yace "Me aka maki nace?" Cikin rawar murya tace "Ba komai" rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kina bukatar wani abu ne" Wasu sabbin hawayen na xubo mata cikin rawar murya tace "Tafiya zaka yi ka barni ni kadai babu kowa, alhalin tsoron gidan nake ji" kallonta kawai yake ya ma rasa me xai ce mata, can dai yace "Shine yasa kike kuka?" Ta gyada masa kai tana kallonsa with tears in her eyes, yace "Ohk, ynxu in tafi da ke kenan?" Tayi shiru still crying tana kallonsa, yace "Bude baki ki bani amsa, in tafi da ke kenan yanxu?" A hankali ta gyada masa kai, daga sama har kasa yake kallonta, tausayinta yake ji har kasan ransa amma bai nuna hakan ba, to ina ma xai kai wannan yanxu wani yayi xaton matarsa ce?? Ta ina xai fara tafiya da ita? Ita dai kanta na kasa, bayan few seconds yace "Ina wayar da na baki" juyawa tayi a sanyaye ta nufi gaban madubi ya bi ta da kallo, har ta dauko wayar ta dawo, ta mika masa, amsa yyi ya shiga call log, yace "Matso" ba musu ta matso kusa da shi tana kallonsa, ya hade rai yace "Wayan xaki kalla ba ni ba" Kallon wayar tayi, ta madubin press din dakin ya kallesu, duk tsayinta iyakarta kirjinsa, jin bai ce komai ba sai kallon wayar take ta daga kai a hankali ta d'an kallesa, ganin inda yake kallo ta kalli madubin ita ma, a hankali ta d'an koma baya ganin dab take da shi ta sunkuyar da kanta, dauke idonsa yyi daga madubin, as if bai son maganan yace "Ga number na nan, duk idan kina son wani abu ko kina da wani magana sai ki danna nan sannan ki sake dannawa ki kirani" Kai kawai ta gyada masa ya jefar da wayar kan gado ya nufi kofa ta bi sa da kallo sabon hawaye na taruwa idonta har ya fita, yau din ma ta waje ya kulle kofar parlon duk da kasancewar mai gadi da matarsa da yaronsu dake gidan yanxu. Kuka sosai Jiddah tayi bayan tafiyarsa, taji komai bai mata dadi a duniyar ynxu, kullum ita kadai kamar mayya a gida babu kowa, tun tana tsoro sosai har tsoron ya ragu, tana sallan isha ko abinci bata ci ba ta kwanta ta takure cikin duvet, nan da nan bacci ya dauketa.... Abuturrab na xaune saman gadon hotel wajen karfe goma da rabi, ya gama abinda yake a laptop ya ajiye yana duba agogon wayarsa, call log dinsa ya shiga har yyi dialing number sai kuma ya katse, mikewa yyi ya kashe wutan dakin ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya, jawo wayar yyi ya d'an yi dube dubensa, sai kawai ya shiga call log din yyi dialing number, he just can't because he have a problem with conscience, abu kadan ke sawa conscience dinsa yyi judging dinsa... Karan wayar ya farkar da Jiddah, bacci ne sosai idonta haka dai ta dau wayar dake saman gadon tayi picking sannan ta kai kunne ta rufe ido bata ce komai ba, jin shirun yyi yaww Abuturrab yace "Ni xan gaisheki" ta bude ido cikin muryar bacci tace "Aa"