Showing 144001 words to 147000 words out of 346625 words

Chapter 49 - Jiddatul Khair Book 1 Hausa Novel Complete

dabanci xai xo yayi mana a nan ni Dijeee, anya kana son gamawa da duniya lafiya kuwa d'an nan, ashe haka kake Aliyu" Cikin dakewa Umma tace "Aliyu!!" sai a sannan ya juyo ya kalleta tace "Xan baka takarda kayi list din duk abinda ka kashe ma Jiddah tun daga lkcn da ka fara saninta har xuwa lkcn da ka rabu da ita, idan ma kudin sun fi karfina xan kai ma Abbanka ya bada su, sannan after that wallahil azeem ka sake kallon inda Jiddah take, i mean ka sake kallan min ita wllh sai ka sha mamakina a duniyar nan, xan maka tijara Aliyu, babu kai babu Jiddaha har abada, idan kuma kai ka cika d'an halaq ka dauketa ka mayar da ita hayin kaga, sannan maxa ka kama hanya ka koma gidanku kada ka sake xuwa min gida, idan kuwa kayi gigin xuwa sai nayi maka walakancin da baka ta6a xato ba" Hajja tayi mitsi mitsi da ido tace "Algungumi kawai, ana ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe shi abinda xai kawosa nan gidan daban, to wllh har abada kai da wannan baiwar Allahn don ta ma fiye min kai sau dubu yanxu tunda bata ta6a xagina ba balle manyanta, kai kuwa idan aka ce xa a kirga adadin xagin da ka min ai sai da a tafi kotu don xuciya xai iya dibana inki yafe maka, to meye kuma xaka sa yar mutane a gaba bayan an raba ku, ko dai har yanxu sonta kake bamu da labari? Banda tsautsayi ma da ya fada mata me xata yi da d'an banxa irin ka?" Umma da taji xuciyarta na tafarfasa tace "Wato shi yasa dama babu musu ka yarda ka biyomu don ka ci mata xarafi da mutunci, to wllh kayi na farko kayi na karshe, Jiddah da kake gani tafi karfin walakancinka yanxu tunda ba kai ke ciyar da ita ba, wanda kayi a baya ma duk nace kayi list a biyaka" Hajja tace "Ko ni sai in dage gidana daya in siyar a biyaka wllh" Sai a snn ya kalli Hajja yace "Saboda nace maki don ke nayi da xaki biyani" Da karfi Hajja tace "Huuuuu ka dai ji kunya duk ka xubda ladanka, gantalalle kawai" Ta gefen ido ya kalli Jiddah dake share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai Ahmad ya ma rasa abun cewa sai kallon Abuturrab yake da mamaki, kofa Abuturrab ya nufa ba tare da ya kallesu ba kamar xai tashi sama, Hajja ta dafe kirji tace "Mu ka xaga ka fita Aliyu?? Mu??" Ko kallonta bai yi ba har ya fice gaba daya, da karfi Hajja tace "Wawa kawai me xuciyar Hafsah, da kyar idan matar nan bata faki idon Hauwa kana jariri ta dura maka nononta ba, don babu halinta da ka xubar al-qur'an" Umma na kallon Jiddah tace "Daga yau ko gidan uban wa kika hadu da shi kika sake kallon inda yake balle ki gaishesa ko wata magana ta hadaki da shi sai na sa6a maki, babu ke babu shi har abada, a duk inda xa ku hadu kuwa...." Hajja tace "Dama kina ganinsa ki gudu kiyi ta kanki, ko kuma ki fasa ihu kawai idan wani taimakon ne a kai maki da gaggawa, ni ai nafi kowa sanin halinsa tunda a hannuna aka haifesa, sau nawa idan an bata masa rai yake take kaza ya kasheta har lahira a lkcn ma yana d'an mitsitsi.... Yanxu ai sai dai ya take d'an mutum" Jiddah dai kanta na kasa, Hajja tace "Kuma tun ban tafi Masar ba ya xama d'an daba fa, fada ne kawai banyi ba kar uban ya kullaceni nayi tafiyata bakina alekum, wa ya sani irin mugun abun da ake koya masu idan sun daga jirgi sama, shi sa har yau ban yarda na hau jirgin da yake ja ba wllh ko don yanda ya tsaneni ma ba sai ya sake jirgin da gangan duk mu hantsulo kasa ba" tana fadin haka ta nemi waje ta xauna tana fifita saboda xufan da ta hada don bala'i, Umma na kallon Jiddah tace "Dauka abincinki ki wuce daki" Jiddah ta karasa a hankali ta dau abincin ta wuce daki, Hajja tace "Ni wllh don baxa ku yarda bane amma da kun bani yarinyar nan kawai in tafi da ita" Umma tace "Sai dai taje maki hutu" daga haka ta bar parlon. Jiddah ta maida hankali sosai a karatunta babu wasa, wanda hakan yasa Umma ke kara jin sonta a rai domin kwazonta ya wuce misali, both Islamic da western din duk she's flowing well, kusan duk bayan kwana biyu Yousuf ke xuwa gidan da daddare, kuma duk idan ya xo ba wai wani hira suke da Jiddah ba iyaka ya sake guiding dinta a karatun nata shi ma, yawanci kuma turanci yake nace mata ta koya, kuma babu laifi she is really catching up, duk weekend Ahmad ke shigowa kaduna sbda duba Ramlah dake laulayi, shi ma kuma yana assisting din Jiddah a bangarori da dama na karatunta. Umma na parlor ranan wata asabar Jiddah ta fito rike da wayarta dake ring ta karaso ta mika mata, Umma ta amsa tana duba me kiran nata, Ganin Ummi ke kira ta daga, bayan sun gaisa Ummi tace "Toh sun gama hada lefensu wai sai ki xo ki gani gobe xa a tafi da shi" Umma tace "Kai ba lallai ba yaya, Allah ya sanya alkhairi kawai" Ummi tace "Aa da dai ki daure ki xo din Ramlah xai fi" Umma ta d'an yi shiru kafin tace "Allah da kawai kin bari su tafi da shi goben Yaya, ai ba sai na gani ba" Ummi tace "Toh ni kuma nace ki xo ki gani" Umma ta d'an yi shiru sai kuma tace "Toh shkkn, bari ruwan ya tsagaita xan sa driver ya kawo ni ko da yamma ne" Ummi tace "Allah ya kai mu" ajiye wayar tayi ta ci gaba da kallon da take a Tv. Da yamma kamar yanda Umma tace ta shirya wajen karfe biyar ta fito parlor tana kallonsu Maimoon da basu je Islamiyya ba sbda ruwan da aka yi, tace "Xa ku je can gidan ne ganin lefe?" Maimoon ta mike da sauri tace "Eh Umma dama ina tsoron gaya maki ne" Umma tace "Toh sai ku shirya ni ina ruwana kuma da xan hana ku" Maimoon da Safiyya suka mike gaba daya, ganin Jiddah bata motsa ba Umma tace "Ke baxa ki ba Jiddah?" jiddah ta girgixa kai tace "Aa xanyi assignment dina Umma" Umma tace "Ai ba dadewa xa muyi ba, tunda babu kowa gidan kawai ki shirya mu je yanxu xa mu dawo, idan muka tafi ma babu ke Hajja sai ta fassara mu tace ba a haka a Masar" Jiddah bata iya tace ma Umma komai ba, amma ba don ranta ya so ba ta mike ta wuce daki, Hijab ta saka suka fito parlon tare da su Maimoon......


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you






*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166

Slowly Jiddah ke tafiya kamar bata son yi a compound dinsu Abuturrab, su Maimoon duk sun yi gaba tare da Umma, ita ce karshen shiga parlon, tsaye tayi bayan kujera ganin Abuturrab dake sakkowa cikin parlon waya kare a kunnensa, tayi bakin kokarin ganin bata kallesa ba, bayan ya shigo parlon ta xaga ta bayan kujera tayi wucewarta part din Ummi ya bi ta da kallo, Bayan Jiddah ta gaisa da Ummi, Ummi tace "Ki tafi dakin Hajja suna can" Mikewa tayi tace "Toh" sannan ta fita xuwa dakin Hajja, Umma na xaune su Maimoon na ta bude akwatunan da aka jera a dakin, Hajja tace "Yanda kika san wata yar gwal xa a auro, haka aka hada lefen har da na Allah ya isa..." Akwatuna biyar ne set biyu each da kit, Umma ta dinga kallon uban kayan da aka hada na lefen bayan su Maimoon na ta budewa, Hajja tace "Aa kar ki ji komai Ramlah ai nace duk xan dibar ma kanninsa abinda ya sauwaka a ciki, mu ba 6arayi bane da xa mu kai masu wannan ubansun kayan, ni kaina xan cire atamfa me tsada daya da jaka, takalmin ma baxai min ba sbda me tsini ne kar in je in karye shi sa baxan dauka ba, amma duk wa ennan yan matan xan cire masu duk abinda Allah yayi wllh" Umma tace "Aa Hajja ki bar masu kayansu kawai, Allah ya sanya alkhairi, ya bama yan baya haka" Hajja tace "Kaji wata magana irin ta 'yan kasar nan, wllh wllh babu shegen da xai yi haka a Masar, sannan me yasa baki bari Ahmad ya hada ma Ramlah irin wannan lefen ba? Ba shi ma yana da dukiyar ba na samu labari?? to shine ni xaki ce jikana ya dauka ya kai ma su gaba daya sbda sata yake yi a sararin samaniya? Aa wllh duk xan bi in rage ni ba gantalalla bace" Umma bata kuma ce mata komai ba, ita dai Jiddah na xaune ta rakube jikin kujera tana bin akwatunan da kayan ciki da kallo. Abuturrab ne tsaye parlon step mum dinsa da duk ta firgice masa, yayi kasa da murya yace "Toh ke ba dai kinsan duk abubuwan da kika xuba a ciki ba Aunty, komai kika ga yayi missing kar ki damu xan bada kudi ki siya wani ki saka" Aunty tace "Ni dai cewa nayi ka tafi ka xauna a dakin, idan aka ganka babu wanda xai ta6a komai cikin kayan, kafi kowa sanin Hajjan nan fa" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aunty don girman Allah ki bari su yi ta daukan duk abinda suke so ni xan sake replacing, i just can't go to that room" Aunty ta wani hade rai tana kallonsa tace "Wato ban isa da kai ba Aliyu, ban isa in sa ka abu kayi ba??" Yace "Toh shkkn, bari in je" Daga haka ya juya ya fita parlon, sai da ta bisa ta tabbatar ya shiga dakin Hajja sannan ta koma parlonta, Ya d'an shafa kai bayan sun hada ido da Umma da ladabi yace "Ina yini" Banxa tayi masa, su Maimoon suka gaishe sa yace "Lafiya lau" Jiddah dai tunda ya shigo bata kalli inda yake ba idonta na kan akwatuna, Hajja dake ta fiddo kayan akwatunan tare da Safiyya ta mike tana kallonsa tace "Lafiya ka shigo kayi mana sandandan a kai Aliyu?" Yace "Takardan da na baki nake so in amsa yanxu" Hajja ta kalli Umma tace "Kinga jaraba ko, tun fa ban tafi Masar ba ya bani wasu shegun takardu da ban san isilinsu ba yanxu, shekaranjiya ya xo nace masa yayi hakuri ban san wani shirgin suka shigw ba amma har gidana xan sa aje a bude mu shiga mu bincika ko da rabon a gani, a haka muka rufe kess din da shi, to meye yanxu xai dawo ya tsaya min in basa takardu kamar wasu takardun jaraba, to gaskiya ban san isilinsu ba ka rabu da ni, ni bance ka dauko takarda ka bani ba" Daga haka ta ci gaba da abinda take, Umma ko kallon direction din Abuturrab bata yi ba banda daure fuska da tayi, Hajja ta dauki wani gyale me kyau ta jefa ma Maimoon tace "Gwada wannan" Umma ta girgixa kai tace "Hajja nace ki bari don Allah, wannan bai dace ba..." Hajja ta mike ta katseta tace "Kinga baiwar Allah tashi kiyi wucewarki in gama abinda nake, babu ruwanki da harkana, kin wani narka uban kiba kina bani oda kamar yar ki, nace ki tafi asibiti a dubaki kin ki, Da a Masar ne da tuni an kai asibiti wllh, to kuma ina ruwanki da abinda nake banda dai kawai kina kanwar uwar Aliyun uwa daya uba daya" Umma ta mike tace "Toh Allah ya sanya alkhairi na ga lefe sun yi kyau Maa sha Allah, Allah ya nuna na yan baya haka" Hajja tayi banxa da ita, Umma ta nufi kofa ta fita, Hajja tace "Banda kema cutar Aliyun xaki yi tunda ba ke kika haifesa ba kuma haushinsa kike ji kamar ki kashesa, wacece ita wannan yarinya da xa a kai ma lefe guda sha biyu komai na ciki kuma dozen dozen, ina kokarin ragewa kuma xaki kawo min raini, to wllh baxai sa6u ba, Dukiyar Aliyu ba banxa ba..." Rungume hannu Abuturrab yyi yana kallon Hajja, ta dau atamfa daya me tsada ta jefa ma Jiddah tace "Yayi maki kyau ko a canxa?" Jiddah ta bude ido sosai tana kallon Hajja, ta dau jaka ta jefa ma Maimoon ma, a takaice dai sai da ta ajiye ma Jiddah atamfa, mayafi, da jaka da takalmi da kayan kwalliya, su Maimoon ta basu kayan kwalliya da mayafai kawai duk don sbda haushin abinda Umma tayi mata, Jiddah dai gabanta sai faduwa yake tana kallon kayan gabanta, Hajja ta nemi waje ta xauna tana kallonsu Maimoon tace "Toh ku kulle masu kayansu, Allah ya sa albarka a abinda suka rage" Maimoon da Safiyya duk suka rufe akwatunan, Sai a sannan Abuturrab ya juya ya fita daga dakin, sai bayan da ya fita Hajja ta nemi ledoji duk ta sa ma kowa abinda ta basa a ciki, Jiddah dai duk jikinta yayi sanyi ta ma kasa ta6a ledan da Hajja ta ajiye mata a gabanta, Hajja tace "Ki tafi kice ma Zubaida take ko wa, kice mata baxata bani ruwan xafin bane in shiga makota in samo?" Jiddah ta kalleta don bata san ko da wa take ba, Hajja tace "Da ke nake, tunda barinsu kika yi da rufe akwatin kin xauna kamar sarauniya, banda dai Allah ya rufa maki asiri Usman ya rufa maki asiri ai da ke xa ayi ma kishiya yanxu, to kamar ya san da haka yasa aka sakeki" Mikewa Jiddah tayi ta nufi kofa ta fita, xaune ta tadda Abuturrab shi kadai a main parlor, duk da sun hada ido tayi wucewarta xuwa kitchen, bata tadda mai aikin a kitchen din ba, tayi ta tsayuwa daga karshe kuma ta fito, taki kallon inda Abuturrab yake ta wuce dakin Hajja, tana kallon Hajja tace "Hajja bata kitchen din" Hajja tace "Toh ta ci kanta, tafi da flask dina idan kin ga an daura ruwa ki juyo min ko bai yi xafi ba, tun daxu nake bin bakar matar ta ban ruwan xafi in sha shayi ta ki, Da a Masar ne wnn ruwan da aka tsuga yau ko wani gida kya ga butan tafasasshen shayi da kofuna kowa na ta sha" Jiddah bata ce komai ba ta dau flask din ta fita, har sannan Abuturrab na xaune parlon, tayi wucewarta kitchen, ta bude tukunyar da ta gani kan gas taga ruwa ne amma bai tafasa ba, ta dau cup kenan xata fara xuba ruwan cikin flask aka bude kofar kitchen din, sosai taji gabanta ya fadi wanda hakan yasa bata san lkcn da ta saki flask din hannunta ba, da sauri ya karasa ya amshi cup din ruwan xafin hannunta shi ma kar ta sake, iyakar rikicewa ta rikice a lkcn, cikin rawar murya tace "Ina yini" jin bai amsa ba ta durkusa ta dau flask din ta ga ya fashe, sae a sannan ta kallesa hankali tashe tayi narai narai da ido tace "Na shiga uku flask din ya fashe, me xan ce mata?" Yace "Ni kike tambaya?" Ta goge hawayen da ya kawo idonta, yace "Toh yanxu da kika hadani da Umma da Every of my family sae aka yi yaya?" Bata tsaya basa amsa ba tabi gefensa rike da flask din xata fita kitchen din ya jawota, kallon mamaki tayi masa yace "Ki bani amsata" Tace "Ni bani da amsan da xan baka" ya dinga kallonta, taki yarda ta kallesa, ya karbi flask din hannunta ya fita ta bi sa da ido, Hajja ta dinga kallon Abuturrab bayan ya shigo dakin, ya ajiye mata flask din gefenta yace "Ga flask dinki ya fashe sai ki fadi nawa kika siya a biyaki...." Da farko Hajja bude baki tayi tana kallonsa, sai kuma ta dauka da sauri ta jijjiga, lkci daya ta sake flask din ta mike sai kuma ta fashe da kuka tace "A Masar fa mijin Nafisa ya siya min flask din, waye yayi min wannan aika aikan??" Abuturrab yace "Ni ne, kuma shi yasa nace ki fadi nawa yake" Tace "Toh Allah ya isa wllh, don kaf


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login